Showing 21001 words to 24000 words out of 154131 words
Chapter 8 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
ba, kasancewarsa sarkin Jinn bai taɓa jin son yayi dariya ba sai yanzu amma haka ya make daga bisani ya yi ɓacewarsa...
Sai da ta gama barazanarta tana nunnuna takobinta kafin ta hau dokinta ta tafi....
Tana shigowa masarautar, ta ga komai lafiya, babu wani tashin hankali... Sai dai zuciyarta tana kan hasasho mutumin nan da dogon farin gashi... Ta kai dokinta wurin ajiyar dawakai, sannan ta nufi sashen jami'an tsaro...
"Mai farin gaji ko? To ko me yellow gashi ne bazan sake jin tsoronsa ba...
Tana tafiya tana waige-waige, sai ta ci karo da Mama Liyatu Uwar ɗakin Maayah... Mama Liyatu ta tsaya tana kallon Inuwa, domin tana sane da yadda Maayah take ruɗewa a kansa..
"Inuwa, daga ina kake haka jikinka duk ƙura?"
Mama Liyatu ta tambaya tana binsa da kallo.
Inuwa ya gyara muryarsa zuwa ta maza..
"Daga zagaye nake, ina duba tsaro ne." Ta wuce ta da sauri kafin a gano yanayin fuskarta.
Tana ƙoƙarin wucewa ta sashen fadar sarki, sai ta jiyo muryar Chingching tana ihu... Tana nufar wurin, ta tadda Chingching tana birgima a gaban sarki, yayin da Uma Altine ke durƙushe tana ba da haƙuri..
"Daddy! Sai ka kore Uma Altine! Wai ni ce mai datti! Kuma har ruwan zafi ta zuba min a jikina!"
Sarki yana zaune yana yana murmushin ciki domin bai bayyana a fuskarsa ba, yana lallashin autarsa...
"To yi haƙuri Auta, gobe zan sa a siyo miki lallausan soso daga ƙasar waje wanda ba zai cire miki fata ba."
Ayat ta tsaya daga nesa tana kallon wannan farincikin, wani rauni ya ziyarce ta. Ta ji tana son cire wannan rawanin ta ruga ta rungume ƙanwarta da mahaifinta, amma asirin dake kanta ya fi ƙarfin hakan...
Tana tsaye can nesa da babban falon Sarki, tana kallon yadda Chingching take ta rigima tamkar za ta tada fadar. Uma Altine tana durƙushe tana ba da haƙuri, yayin da Sarki yake ta faman rarrashin Autar tasa.
Kwatsam, sai idon Chingching ya sauƙa a kan Inuwa. Ta ɗaga hannu tana nuna shi, fuskarta ta washe da murmushin shagwaɓa...
Fadawan sarki ganin inda yatsan gimbiya ya nuna, suka nufi Inuwa da gudu.. Kafin Inuwa ya ankara, fadawa biyu sun cafko shi, suka yi sama da shi!
Ayat ta zazzaro ido, zuciyarta na bugawa don tsoron kada asirinta ya tonu ko kuma laifi ta yi. Ta damƙe wuyan fadawan sosai don kada ta faɗi, har aka shiga da ita gaban Sarki aka dire ta a ƙasa... Saboda yadda aka sake ta da ƙarfi, sai da ta zauna da mazaunanta a kan kafet ɗin falon.
Chingching ta kalli Inuwa, ta turo baki ta ce,
"Ni... wannan ne zai kai ni part ɗina!"
Sarki ya jinjina kai, ko da yake yana mamakin yadda autar tasa ta zaɓi wannan matashin sojan, sai ya ce,
"Ƙaramin jarumi, tashi ka raka ta part ɗinta."
Uma Altine ta yi maza ta miƙe don su tafi, amma Chingching ta karkaɗa kai, ta haɗe hannaye a ƙirji..
"Ni sai dai ya goye ni! Ba zan je da ƙafata ba."
Tafida dake zaune yana kallon ikon Allah ya ce
"To ai Auta da mota za a kai ki ko kuma doki."...
"Ni goyo nake so!" Tana bubbuga ƙafa cikin sakalci..
Sarki ya kalli Altine ya ce,
"Altine, goye ta ku tafi."
Nan ma Chingching ta fara buga ƙafa a ƙasa
"Ni! Na yi faɗa da Uma Altine, ba za ta goye ni ba! Ba wanda zai goye ni sai kyakkyawan jarumin nan!"..
Sarki bai ji daɗin hakan ba. A matsayinsa na mai kishin ƴaƴansa, ba ya son namiji ya riƙa taɓa su ko su riƙa mu'amala da maza amma ganin yadda Chingching ta nace kuma ba ya son ɓata mata rai, sai ya gyada wa Inuwa kai alamar ya ɗauke ta.
Ita kuwa Ayat, wani farinciki ne ya ziyarci zuciyarta. Ta daɗe ba ta riƙe ƙanwarta ba saboda shigar badda kamar da take yi. Ta duƙa a hankali, Chingching ta daka tsalle ta hau bayanta, ta ƙanƙame wuyanta....
Tana tura baki ta ce, "Dan nace maka kyakkyawa kar kayi tunanin ka fini kyau too..."
Murmushi kawai Inuwa yayi..
Ya miƙe da ita da ƙyar, domin duk da ƙarancin shekarun Chingching, tana da ɗan nauyi, sannan ya fara takawa zuwa wajen fada, Uma Altine da sauran bayi suna biye da su a baya...
Suna tafe a kan dogon kwaltar masarauta, iska mai sanyi tana kaɗawa. Chingching ta saki jiki sosai a bayan Inuwa, ta ɗora kanta a kafaɗarsa..
"Wai kai meye sunanka?"
Ta tambaya tana wasa da kwalliyar jikin rigar sojan...
Inuwa ya ɗan yi murmushi, ya rage sautin muryarsa don kada sauran bayin su ji yadda muryarsa take zama ta mace idan ya yi magana mai tsayi, ya ce..
"Sunana Inuwa, ya ke gimbiya."
Chingching ta yi dariya, "Inuwa? Suna kamar inuwar bishiya. Amma ka san me? Jikinka yana da taushi, ba ka da tauri irin na sauran sojoji. Kuma kana ƙamshi mai daɗi, ba irin na Uma Altine mai ƙamshin sabulun wanka ba."..
Inuwa ya ɗan zaro ido, ya ce.. "Haka ne gimbiya, ai sojoji ma suna wanka."
Chingching ta ƙara matse shi, ta ce,
"Inuwa, me ya sa kake da kyau haka? Idanunka manya ne kamar na Aunty Ayat. Ka san Aunty Ayat kuwa? Ita ma tana da kyau sosai, amma kullum tana kulle a ɗaki."
Wani ƙwallar farinciki ya cika idon Ayat, ta amsa..
"Na san ta gimbiya. Ita ma tana sonki sosai."
Chingching ta bushe da dariya,
"To idan na sake rigima, zan sa Daddy ya ce kai ne za ka riƙa yi min wanka, tunda kai ba ka cire fatar mutum da soso."
Inuwa ya kusa yin tuntuɓe saboda dariya, ya ce,
"A'a gimbiya, wanka kam sai dai Uma Altine."
Haka suka riƙa yin hira cikin nishaɗi har suka isa part ɗin gimbiya, kowa yana mamakin yadda wannan jarumin ya saba da Auta cikin lokaci ƙanƙani....
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 8️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Bayan Inuwa ya sauƙe Chingching a part ɗinta, ya fara takawa cikin sanyin jiki yana shirin komawa tasa muhallin. Zuciyarsa tana cike da farincikin hirar da suka yi da kanwarsa..
Kwatsam yana shirin shiga wata kusurwa sai ya ji an rufe masa fuska da wani baƙin mayafi mai kauri. Kafin ya yi yunkurin kwata, wasu jami’an tsaro guda biyu masu ƙarfi suka cafko shi, suka fara jansa da karfi. Ba su ba shi damar yin magana ba, suka jefa shi cikin wata mota dake fake a gefe, suka tada motar da gudu suka nufi part ɗin Gimbiya Maayah....
Motar ta tsaya a harabar katafaren sashen Maayah. Jami’an suka fito da Inuwa, yana ta faman kokawa yana son ya ɓalle ya gudu, amma riƙon da suka yi masa na maza ne. Saboda yadda suka ji ba shi da nauyi sosai, ɗaya daga cikinsu sai kawai ya yi masa ɗaukan kafaɗa, ya saɓo shi tamkar buhun shinkafa, suka nufi cikin falon gimbiyar.
Suna shiga suka dire shi a tsakiyar katafaren falon dake shimfide da kafet mai tsada...
Maayah tana zaune a kan wata Plate Sofa kamar katifa a ƙasi tana sanye da riga ta alfarma wadda ta bayyana kyan fatarta. A gabanta akwai wani katafaren tray cike da yankakken kayan fruits masu sanyi, tana ci a nutse tamkar ba ta san abin da ke gefen ta ba..
Ba tare da ta kalli inda suke ba, ta daga dogayen yatsunta ta yi musu nuni da su fita. Nan take jami’an da sauran ma’aikatan mata dake falon suka fice cikin hanzari, suka bar Inuwa tsaye a tsakiyar falon cikin ruɗani.
Daga nan ne aka cire wa Inuwa baƙin mayafi dake fuskarsa. Da farko ya rintse ido saboda hasken fitilun dake walwali a falon, yana buɗe su sai ya yi ido hudu da Maayah. Mamaki da fargaba suka mamaye shi.
Maayah ta ajiye ƙaramin wuƙar dake hannunta, ta ƙura wa Inuwa idanu. Wani irin kallo take yi masa, kallo mai cike da nuna isa da kuma wani ɓoyayyen saƙo dake nuna sha'awa da burgewa.... Idanun Maayah sun yi wani irin sheƙi, gata kyakkyawa ajin farko..
Inuwa ya ji jikinsa ya fara sanyi. A matsayinsa na mace, ta san ma'anar wannan kallon. Ta san cewa inda asalin namiji ne babu abin da zai hana sha'awarsa ta tashi a wannan lokacin saboda yadda Maayah ta baje kyan surarta a gabansa cikin kissa da kisisina...
"Inuwa..." Maayah ta kira sunansa cikin wata irin murya mai sanyi da take ratsa jijiya. "Ka ga yadda ka yi nasarar sa ni tunani tun daga ranar da idona ya fara ganinka? Meye sirrinka? Me kake boyewa a karkashin wannan rawanin naka?"
Inuwa ya sunkuyar da kai kasa, yana tunanin yadda zai fita daga wannan tarkon na Gimbiya Maayah ba tare da asirinsa ya tonu ba.
Maayah ta tashi daga kan katifar ta a hankali, tana taku ɗaya-ɗaya tamkar kyanwar da ta ga ɓera...
Rigar jikinta tana jan ƙasa, ƙamshin turarenta na Oud mai tsada ya mamaye hancin Inuwa. Ta zo daidai gabansa, ta tsaya tana kallon kwayar idonsa, kafin ta fara zagaye shi kamar yadda zaki yake zagaye abincinsa...
Ta sanya hannunta ɗaya ta fara shafa kafaɗarsa tana gangarawa zuwa hannunsa. Muryarta na fita ƙasa-ƙasa, tana raɗa masa a kunne..
"Inuwa... na yi bincike a kan duk sojojin masarautar nan, amma ban ga kamaninka ba. Ba ka da ƙasusuwa irin na maza sojoji. Ka yi fita daga daban, kuma hakan ne ya sa zuciyata ta kasa nutsuwa."
Ita kuwa duk wannan shashshafa da kalaman Maayah ba su motsa mata komai ba face takaici da haushin yadda ƴar uwarta take nuna rashin kamun kai. Ta ɗaure fuskarta cikin yanayi na gatsine, tana jujjuyar da manyan idanunta tana kallon silin ɗin ɗakin. A ranta tana cewa,
"Wannan mahaukaciyar me take nufi ne? Shin ba ta da sauran abin yi ne sai bibiyar sojoji?"
Maayah ta kai hannunta tana son ta shafi gefen fuskarsa, Inuwa ya kauce da sauri yana harararta..
Maayah ba ta fasa ba, ta sake zagayawa ta bayansa, ta tura kanta a tsakanin kafaɗunsa, ta rungumo shi ta baya tana ƙoƙarin jin bugun zuciyarsa...
"Me kake gudu Inuwa? Izza kake nuna min ko kuwa tsoron matsayina kake ji? Idan ka karɓi soyayyata, zan mayar da kai babban kwamandan da kowa zai rurrusuna masa a ƙasar nan," tana goga fuskarta a bayan rigarsa.
Inuwa ya ja wani uban tsaki a cikin ransa, wanda ya kusa fitowa fili. Ya fara jin ƙyamar yadda Maayah take ƙanƙame shi. Ya yi amfani da dabarar maza sojoji, ya juyo da ƙarfi ya raba jikinsa da nata, ya matsa baya taku biyu yana huci..
Cikin muryarsa ta maza wadda ya riga ya koyi kwaikwayonta, ya ce..
"Gimbiya Maayah! Na zo nan ne don hidimar tsaro, ba don wasan kwaikwayo na soyayya ba. Ni talaka ne, ke kuma gimbiya ce. Bai kamata ki ɓata mutuncinki a kaina ba. Kuma idan har kika sake sanya a kamo ni ta wannan hanyar, zan kai ƙararki gaban mai Martaba Sarki, duk abin da zai faru ya faru!"
Maayah ta daskare a wurin, ta zaro ido tana kallon Inuwa. Ba ta taɓa tunanin akwai wani namiji a duniya da zai ƙi wannan tayin nata ba. Maimakon ta ji tsoron barazanar sarki, sai kawai ta ji Inuwa ya ƙara mata kyau da kwarjini a idonta. Ta ciza laɓe, tana murmushin mugunta...
"To ka je ka faɗa wa Sarkin! Amma ka sani, duk inda ka shiga a masarautar nan, idona yana kanka. Ba za ka taɓa tsira daga tarkona ba har sai na mallaki abin da nake so a tare da kai."
Inuwa bai sake tankawa ba, ya juya cikin fushi ya nufi ƙofa, ya buɗe ta da ƙarfi ya fice, ya bar Maayah a tsaye tana kallon inuwarsa tana shafa wurin da ya taɓa, tana jin wani irin shauƙi daban.
Ya fara takawa cikin sauri yana ficewa daga sashenta, yana muzurai shi kaɗai ƙasa-ƙasa...
"Banza! Mahaukaciya! Jaka kawai!"
ya furta tare da jan wani dogon tsaki. "Wato ita a tunaninta kowa ma namiji ne ko? Ta rasa wanda za ta bi sai ni? Yarinya ba ta da sauran aiki sai lalata da ma'aikata? Allah ya kyauta!"
Haka ya riƙa surutai yana gunguni har ya ɓace a cikin duhun dake tsakanin gine-ginen masarautar, ya nufi tasa part don ya cire wannan kayan sojan da yake ji sun yi masa nauyi saboda haushi.
A can cikin falo kuwa, Mama Liyatu tana laɓe a bayan labule tun ɗazu tana kallon duk abin da yake faruwa. Bayan Inuwa ya fice ta fito a hankali tana takawa zuwa inda Maayah take a tsaye, tana kallon ƙofa tamkar gunki...
Mama Liyatu ta ga yadda Maayah ta zama wata iri, fuskarta na sheƙi, kuma tana shafa hannunta da Inuwa ya taɓa..
"Gimbiyata," Mama Liyatu ta kira sunanta cikin muryar tsoro. "Wannan yaron da kike bi... shin kin tabbata namiji ne na ƙwarai? Na ga kyan fuskarsa ya wuce na namiji, sannan yadda kika rungume shi ɗazu bai nuna wani yanayi na namiji ba. Meye sirrin dake tattare da shi?"
Maayah ta juyo ta kalli Mama Liyatu, wani murmushin mugunta na nan a kwance a fuskarta. Ta koma ta zauna a kan kujera, ta ɗauki koren apple ta gutsura..
"Mama Liyatu, shi ya sa nake son sa. Domin ya banbanta da kowa. Sannan ya nuna mjn ba ya buƙatar soyayyata. Wannan shi ne babban kalubalen da nake so. Amma ki sani, koda mace ne shi a siffar namiji, sai na mallaki zuciyarsa, balle kuma ina da yakinin cewa jarumi ne mai jinin sarauta a jikinsa."..
Mama Liyatu ta girgiza kai, "Amma Gimbiya, idan Sarki ya ji labarin nan fa? Kin san yadda yake kishinku."
Maayah ta yi wata 'yar dariya mai sauti. "Sarki yana can yana fafutukar yadda zai kare masarautarsa daga barazanar Pavilion, ba shi da lokacin binciken wanda nake so. Ke dai kawai ki sa ido a kansa, duk inda ya sanya ƙafa ki sanar da ni."
✨✨✨
A ɗayan ɓangaren kuwa, Ayat ta isa sashenta. Ta banka ƙofa ta shiga, ta cire rawanin kanta ta wurgar a kan gado. Ta kalli kanta a madubi, gashin kanta ya bazu a kafaɗarta, idanunta sun cika da ƙwallar takaici...
"Wace irin rayuwa nake ciki?" ta tambayi kanta...
"Ina tsaka-tsakiyar yaƙi da kaina.."
Ta shige banɗaki don yin wanka..
Bayan ta kammala wanka ta cire duk wata siffa ta Inuwa, ta saka lallausan leshi mai kyan gaske wanda ya dace da jikinta. Ta sauko ƙasa zuwa babban falonta tana takawa a hankali, fuskarta a rufe..
Tana isa falon, sai ta tadda ma’aikatanta, karkashin jagorancin Saratu, suna tsaye jere tamkar wadanda suke jiran sako daga sama. Fuskar kowacce dauke da tambaya da kuma damuwa.
Saratu tana kallonta, sannan ta yi gyaran murya ta ce.
"Gimbiya, me ya sa yanzu kika koyi wannan halin ne? Tun safe ba kya fitowa sai dare, anya lafiya kuwa? Abun ya yi yawa ai..."
Ayat ta ji wani irin haushi ya taso mata, domin ranta ya riga ya ɓaci da rigimar Maayah. Ta tsaya cak, ta kalli Saratu da idanuwanta wadanda suka nuna bacin rai a fili...
"Kuna so ne na fito na taya ku aiki?"
ta tambaya cikin kakkausan harshe.
Saratu maimakon ta yi shiru, sai ta kara matsowa,
"A'a, amma dai ki fito kowa ya ganki, a ga lafiyarki. Idan kina kulle kanki kullum, me kike so mutane su ce?"
Ayat ta ji tamkar ana huda mata zuciya da mashi. Ta girgiza kai cikin takaici ta ce..
"Hakan ya zamo wajibi ne? Ba na so ku riƙa shishshige wa rayuwata! Kowa ya yi aikin dake gabansa, ku yi rayuwarku na yi tawa. Ban hana ku yin farin ciki ba, ban rage ku da komai ba, to me ya sa kuke son takura ni?"
Saratu ta ɗaure fuska, "Ai dole mu shiga lamuranki Gimbiya, domin amanarki aka ba mu, kuma ya zama wajibi mu kula da ke yadda ya kamata."..
Kallonsu ta shiga yi, sai kuma ta tuna yadda ma'aikatan Maayah suke rawar jiki idan suka ganta, ba su isa su hada ido da ita ba balle su yi mata magana barkatai. Amma nata ma’aikatan, saboda sun san ta da saukin kai da tausayi, sun mayar da ita tamkar tsararsu...
Ta ji wani raɗaɗi a ranta, kowa a masarautar nan yana son ya tsara mata yadda za ta yi rayuwa..
Ta ɗaga musu hannu ɗaya alamar ta gaji da maganar su fita su ba ta wuri.
Duk suka fita suka bar ta a tsakiyar falon, tana jin tamkar ta fasa ihu don ta huta...
*Washegari*
A sashen Gimbiya Yumna, kowace safiya tana farawa ne da nishaɗi. Yumna tana zaune a gaban babban madubin ta na alfarma, yayin da bayinta suke ta faman gyara mata gashi da sanya mata lalle. Suna cikin wasa da dariya..
Ummi ɗaya daga cikin baiwa ta ce,
"Gimbiya, gaskiya yau fuskarki ta yi wani irin haske na daban. Anya ba mafarkin alheri kika yi ba kuwa?"
Yumna tana murmushi ta ce,
"Ke dai Ummi kullum maganarki kenan. Kawai hutu ne ya karɓe ni."
Zainab ta ce "Hutu dai ko kuwa tunanin Malam? Ai muna sane yau ne ranar karatunki...!"
Duk bayin suka sa dariya, Yumna kuwa ta ɗan ji kunya, ta duƙar da kanta tana murmushin dake bayyana fararen haƙoranta.
Suna tsaka da wannan wasan ne, sai wata amintacciyar baiwarta, Safina, ta shigo ɗakin da sauri. Ta zagaya bayan Yumna, ta rungume ta ta baya sannan ta raɗa mata a kunne cikin muryar raɗa..
"Yau kin manta ne? Dream Lover ya zo... Yana can lambu yana jiran ki."
Yumna ta zaro ido, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi. Wani irin farinciki ya rufe ta, ta kalli Safina ta ce
"Malam ya zo? Da gaske kike yi Safina?"
Safina ta ce