Showing 30001 words to 33000 words out of 154131 words
Chapter 11 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
fatar aljani ya mayar da ita toka a cikin daƙiƙa kaɗan...
Duk da azabar zafin da yake ji a jikinsa, bai cire idonsa daga kan Ayat ba...
"Wannan shingen ba zai taɓa rabani da ke ba Ayat,"
ya raɗa a cikin zuciyarsa.
"Zan nemo hanyar da zan shigo, ko da kuwa hakan zai kai ni ga rasa dukkan ikona."
Ayat ta miƙi hanyar masarautar tana shirin tafiya ciki, kwatsam sai ta ji wani irin sanyi mai ratsa jiki ya ziyarce ta, sanyin da bai dace da yanayin zafin rana na lokacin ba. Wani irin yanayi ne na daban wanda ya sanya kowace gashi na jikinta tashi tamkar akwai wanda yake kallonta daga can sama da idon ɗan Adam ba zai iya gani ba...
Ta tsaya cak, ta kasa ci gaba da takun da take yi. A hankali ta ɗaga kanta tana kallon sararin samaniya, idanunta suna yawo a cikin gajimare. Ba ta ga komai ba amma zuciyarta tana gaya mata cewa akwai wani abu...
Ibrahim wanda yake shirin barin wurin zai je ƙiran sarki, ya ji takun Inuwa ya tsaya. Ya juyo ya gan ta a tsaye tamkar gunki, kanta a ɗage tana kallon sama cikin wani irin yanayi na shauƙi da fargaba...
Ya nufe ta, ya tsaya kusa da ita, ya bi layin kallon idonta amma bai ga komai ba sai hasken rana. Ya dafa kafaɗarta, wanda hakan ya sanya ta firgita ta dawo cikin hayyacinta...
"Inuwa, me kake kallo a sama?" Ibrahim ya tambaya cikin sautin mamaki...
"Ko akwai wani tsuntsu ne da kake neman gani, ko kuwa tunanin ɗazun ne ya dawo?"
Ayat ta sauƙe idanunta cikin sauri, tana ƙoƙarin saita numfashinta da ya fara hargitsewa. Ta kawar da kai tana shafa wuyanta..
"Ba... ba komai Master. Kawai dai na ji kamar iskar sama ta canza launi ne, kila gajiya ce."
Ibrahim bai gamsu da amsar ba, domin ya ga yadda idanunta suka firfito, amma sai ya share kawai ya ce, "To mu ƙarasa ciki na rakaka, kafin rana ta ƙara dukan ka ka fara ganin abubuwan da babu su."..
Ayat ta ce, "a'a zan ƙarasa da kaina, domin wurin kwanan namun ba nisa..."
Ta ci gaba da tafiya..
Bayan ta koma sashenta, ta cire kayan maza da suka matse asalin jikinta, ta shiga wanka don wanke duk wata gajiya da ƙurar birnin Alhamra. Bayan ta fito, ta sanya kayan gimbiyanci na alfarma waɗanda suka ƙara fito da asalin kyawunta da kwarjininta na mace...
Ta tsaya a gaban babban madubin dake ɗakinta, tana kallon kanta. Kwatsam sai tunanin wannan baƙon mutumin da suka haɗu a bakin kogi ya dawo mata a rai. Nan take annurin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka sauya launi, ta haɗe gira cikin wani irin azababben fushi...
Zuciyarta ta fara zafi tana bugawa da sauri. Wannan mutumin ya zame mata tamkar ƙayar dake maƙale a maƙoshi. Ta yi fatan ace yana gabanta a wannan lokacin, da lallai ta yi amfani da takobinta ta sare masa wuya don ta huta da wannan kallon rainin hankalin da ya yi mata...
"Waye kai da za ka keta min hurumi?"
Ta faɗa a fili tana kallon madubin, muryarta na rawa cikin fushi...
Babban abin da ya fi ƙona mata rai shi ne, ya karya mata babban alƙawarin da ta yi na tsawon shekaru. Ta haramta wa kowane ɗan Adam ganin asalin surar jikinta ko fuskarta a matsayin mace, amma shi a rana ɗaya ya ga abin da kowa ya daɗe yana nema ya rasa. Ta tuna lokacin da ta cire kayanta a bakin kogi, ashe yana can yana kallon sirrin jikinta...
Wani irin tsanarsa ne ya ziyarci zuciyarta, tsanar da ba ta taɓa ji wa kowane ɗan Adam ba. Ta kura wa madubin ido tamkar tana ganin hotonsa a ciki, tana jan numfashi mai zafi..
"Ka kalle ni... ka kalli abin da na adana wa wanda zan aura kadai," ta cigaba da magana a fili tana nuna kanta a madubi, "amma ka sani, wannan kallon da ka yi min zai zama silar halakar ka. Ko kai waye, ba zan taɓa yafe maka ba. Wallahi sai na ga bayan ka!"
Tana tsaye tana huci, idanunta cike da tsanar mutumin da ya keta mata alfarma.
"Wallahi duk inda kake, sai na sare maka wuya! Ka kalle ni ka ga asirin da na adana, amma ka sani wannan shi ne ganinka na ƙarshe!"
Tana cikin wannan zafin muryar, sai ta ga wani abu ya fara canzawa a cikin madubin..
Ba zato ba tsammani, sai hoton kanta lokacin da take matsayin Inuwa ya bayyana a cikin madubin ya fara yin dishi-dishi. Ta zaro ido, ta daskare a inda take tana kallon yadda siffarta na yanzu ya ɓace, Inuwa ne ya bayyana a cikin madubin...
Ayat ta ja baya da sauri, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi....
"Wannan ni ne ai a matsayin Inuwa...."
Ba tare da ta ga leɓensa yana motsi ba, sai ta ji wata murya ta ratsa ɗakin, muryar tana tashi ne daga cikin madubin, tana amo tamkar ana hura busa..
"Kada ki ɓata kyawun fuskarki da fushi Ayat.... Idan har sarar wuyana shi ne zai sanyaya miki rai, to ki sani... wuyana yana nan yana jiran takobinki. Amma kafin hakan ta faru, ki sani cewa abin da na gani, ba zan taɓa mantawa da shi ba har abada."..
Ayat ta ɗauki wani butar fure dake kusa da ita ta kwala wa madubin da ƙarfinta..
"Kaaaaaaassss!"
Madubin ya fashe, ya farfaske ya zama guntu-guntu a ƙasa. tana sauke numfashi tana kallon fasassun gilasan. Jikinta yana rawa, gumi ya jige mata goshinta...
"Ta ya ya san suna na? Ta ya ya shigo cikin madubi na?" Ta raɗa tana kallon yadda kowane guntun gilashi yake nuna fuskarta guda guda..
Tsoro ya maye gurbin fushin da take ji. Ta gane cewa wannan mutumin da take nema ta kashe, tabbas ba mutum ba ne...
Cikin fushi ta furta, "Ƙarya ne ba aljan bane, mutum ne kamar kowa, kawai yana amfani da sihiri na tsafi ne kuma sai na wargaza tsafin nan..."
Ta sulale ta zauna a ƙasa, tana kallon fasassun gilasan, tana jin tamkar har yanzu idanunsa suna kallonta ta cikin tarkacen gilashin...
Can sai ga Saratu ta shigo da gudu jin ƙarar har ya sauƙa falo..
Haka take bin madubin da ya farfashe a ƙasi ga kuma Gimbiya a durƙushe cikin ɓacin rai..
Saratu ta ƙaraso tana faɗin
"Gimbiya meya faru ne? Ke da wa? Meyasa kika fasa madubin ki? Wa ya ɓata miki rai?..."
In short answer Ayat ta ba da
"Ba komai..."
Haka Saratu ta lallashe ta..
Sannan ta share mirror ta gyara ɗakin gaba ɗaya...
Bayan Saratu ta share fasassun gilasan ta fita, Ayat ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na kunci da fargaba. Shirun da ɗakin ya yi ya dawo mata da sauti da kuma kwarjinin muryar da ta ji daga cikin madubin....
Tana zaune a gefen gado, tana kallon inda madubin yake a dā, yanzu kuma babu komai sai bango. A ranta tana tambayar kanta..
“Waye wannan mutumin? Ta yaya har ya san sunana?”....
✨✨✨
A can bangaren Gimbiya Maayah, ɗakin ya cika da sautin nishi mai ban tausayi...
Maayah tana kwance rubda-ciki, fuskarta jiƙe da hawaye da gumi. Faɗuwar da ta yi a kan treadmill ba ƙaramin rauni ta ji ba..
ƙunƙuminta ya taɓu, ƙashin bayanta kuma yana mata wani irin raɗaɗi tamkar ana huda ta da mashi...
Mama Liyatu tana gefe guda tana lallashi, amma Maayah ihu take ta saki..
"Abul! Spinal cord ɗina ya samu matsala! Shikenan ba zan sake tashi ba! Wayyo Allah na... ku taimake ni! Ba zan iya motsa ƙafata ba!"
Sarki Nourdeen, wanda yanzu ne labarin hatsarin ya isa gare shi, ya shigo ɗakin da fadawansa suna biye da shi cikin matuƙar damuwa..
Ganin ƴarsa a wannan yanayin sai da zuciyarsa ta girgiza...
Sarki ya zauna a bakin gadon, ya dafa kanta cikin muryar rarrashi,
"Kiyi haƙuri Maayah... komai zai wuce."
A daidai wannan lokacin Doctor ya shigo da sauri, ɗauke da kayan aikinsa. Ya gaishe da Sarki cikin sauri sannan ya fara duba Maayah. Kowane taɓi da zai yi mata a baya sai Maayah ta tsandara uban ihu dake firgita kowa...
Doctor ya duba idanunta, ya duba yadda ƙafafunta suke motsawa sannan ya yi shiru yana nazari...
Sarki ya kalle shi cikin fargaba, "Doctor, ya ake ciki? Shin raunin yana da girma?"
Doctor ya gyara gilashinsa, ya kalli Sarki sannan ya kalli Maayah dake kuka...
"Mai martaba, ƙashin ƙunƙuminta ya ɗan goce ne, kuma tsokokin bayanta sun kumbura sosai. Za ta yi jinya ta tsawon lokaci, kuma dole ne ta daina yawan motsi ko fushi, domin kowane tashin hankali zai iya sa jikinta ya yi paralysis."
Jin haka Maayah ta ƙara fashewa da kuka. Girman kanta da izzarta duk sun bi ruwa, a yanzu kawai neman sauƙi take...
A daidai lokacin da Doctor yake ƙoƙarin yi wa Maayah allura, ihun kukanta ya ƙaru sosai
"Wayyo bayanaa! Wayyo Allah na!",
Ta can gefe guda kuma aka fara jin waƙe-waƙe da raye-raye...
Ba zato ba tsammani, sai ga Chingching ta shigo, tana sanye da doguwar riga mai sheƙi, tana riƙe da toy ɗinta a hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma tana riƙe da gorar ruwa. A bayanta wasu bayinta ne guda biyar suke mata rakiya, kowaccen su tana ɗauke da tiren fure da lemo, suna tafiya a jere yayin da Chingching take ta rera waƙarta da ƙarfi..
_🎶🎶 Gimbiyar mata, Firdausi autar mataa, Firdouss babu kamar kiii, Firdouss, Firdausi ƴan mata, Firdouss tauraruwar mataaa..🎶🎶_
Chingching ta ƙaraso tsakiyar ɗakin, ta tsaya tana kallon Maayah dake kwance tana murƙususu. Dai-dai lokacin ta gama waƙar...
Ta turo baki, ta zura wa Maayah idanu na wasu daƙiƙoƙi kafin ta ce cikin muryarta ta shagwaɓa...
"Haba Aunty Maayah! Tun jiya nake jin kina ta ihu kamar wadda aka sace maki takalmi... Me ya faru ne? Wai dama gudu kike yi? To ai na gaya miki ke ba doki ba ce, me ya sa kike son gudu irin na dawakai?"...
Maayah ta buɗe jajayen idanunta, tana kallon Chingching cikin tsananin takaici. Ta so ta daka mata tsawa, amma zafin ƙunƙuminta ya hana ta ko motsawa...
"Ching...ching... tafi nan! Ba na son ganinki!"
Maayah ta faɗa cikin raunannen murya..
Amma ina, Chingching sai ma ta ƙara kusanto gadon, ta kalli Doctor ta ce..
"Doctor, shin gaskiya ne Aunty Maayah ba za ta iya sake tashi ba? Naji ana faɗa a waje wai bayanta ya rabe gida biyu. Idan haka ne, to wa zai riƙa tura ta a keken guragu?.."
Ta juya ga mahaifinta, ta rungume shi tana magana...
"Daddy, ka ga Aunty Maayah ko? Ai ni na san me ya sa hakan ta faru. Kullum tana cikin fushi-fushi da masifa-masifa a zuciyarta, shi ne injin ya yi kaca-kaca da ita ya yar da ita ƙasa."
Kowa a ɗakin ya yi shiru..
Chingching ta nuna wa bayinta alamar su ajiye abubuwan da suka kawo..
"Ga fure na kawo miki Aunty Maayah, don idan kika kalle su kya ji sanyi. Amma gaskiya ki daina gudun nan, ni gashi ina zaune ina kallon katun ɗina, amma babu abin da ya faru da ni."
Ta ƙara matsawa daidai kunnenta ta raɗa mata..
"Kiyi haƙuri kin ji? Amma idan ba za ki iya tashi ba, inaso duk takalmanki masu bala'in tsayin nan ki kwaso mun su...."
Daga nan ta juya, ta yi nuni ga bayinta, suka fita tana ta rangwaɗa sannan ta cigaba da waƙar ta, ta bar Maayah tana huci, ranta ya ɓaci fiye da yadda jikinta yake ciwo...
Sarki ya dafe kansa, ya san cewa halin Chingching sai dai addu'a...
"Maayah, kiyi haƙuri... yarinya ce," ya ce a hankali.
Amma Maayah a ranta tana faɗin...
"Wallahi idan na tashi, Chingching za ki san kin shigo ɗakina kin mun rashin kunya!".....
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣1️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Bayan ficewar Chingching ɗakin ya ɗan yi tsit, amma sanyin iskar ya sauya yayin da aka fara jin takun takalmin Gimbiya Zayana.. Ba surutu, ba hayaniya sai kawai ƙamshin turarenta mai tsada wanda ya riga ta shigowa ɗakin..
Zayana ta shigo ɗakin da takun alfarma, kanta a ɗage tamkar ba ta son taka ƙasa. A bayanta wasu bayinta ne guda uku sanye da kaya masu kyau, kowaccensu tana riƙe da tiren azurfa dake maƙil da zaɓaɓɓun fruits waɗanda aka yanka su cikin fasaha..
Zayana ta tsaya nesa kaɗan da gadon Maayah, ta nannaɗe hannuwanta a ƙirji tana kallon Maayah da wani irin kallo na isa da kuma tausayi mai haɗe da izgilancu. Ba ta zauna ba domin ita a ganinta zama a gefen gadon mara lafiya ƙasƙanci ne..
"Ashe abin har ya kai ga kwanciya, Maayah?"
Zayana ta furta cikin muryarta mai sanyi dake soka mutum tamkar kibiya...
Maayah ta ɗaga kanta da ƙyar, idanunta suka sarƙe da na Zayana. Duk da ciwon dake jikinta, ba ta bar izzarta ta fito ba. Ta haɗe rai ta ce,
"Kamar yadda kika gani Aunty Zayana. Amma kada ki damu, wannan kwanciyar ta ɗan lokaci ce. Ba zan ba ki farin cikin ganina a haka har abada ba."
Zayana ta yi murmushin mugunta, ta nuna wa bayinta alamar su ajiye tiren fruits ɗin.
"Na kawo miki waɗannan ne don su ƙara miki ƙarfi. Na ji ance faɗuwar taki ta yi muni, har ana zargin ƙashin bayanki ya samu matsala. Gaskiya ya kamata ki riƙa sani cewa jikinki ba na ƙarfe ba ne, akwai abubuwan da suka fi ƙarfinki."
Zayana ta ƙara takawa kusa da gadon, ta sunkuya kaɗan ta yadda Maayah kaɗai za ta ji abin da za ta faɗa..
"Kina ta gudun neman Inuwa, gashi Inuwa ya jefar da ke. Yanzu wa zai zama gwarzon fada tunda jarumar gidan tana kwance tana kuka?".
Maayah ta cije laɓe, ran ta ya ɓaci matuƙa...
"Fita ki ba ni wuri Aunty Zayana! Bana buƙatar fruits ɗinki, kuma bana buƙatar tausayinki na ƙarya."..
Zayana ta miƙe tsaye tana gyara riga, ta kalli mahaifinsu dake gefe ta gaishe shi cikin girmamawa sannan ta juyo ga Maayah..
"Kiyi sauri ki warke... Masarautar tana buƙatar hayaniyarki. Amma kafin nan, ki ji daɗin kallon rufin ɗakin nan."
Ba tare da ta sake cewa uffan ba, ta juya ta fice daga ɗakin, bayinta suna biye da ita. Ta bar Maayah tana jin wani irin ɗaci a ranta, domin kalaman Zayana sun fi allurar Doctor zafi...
Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya kalli Maayah ya ce,
"Ku daina haka, gimbiyoyi ne ku fa..."
Amma Maayah ba ta ko saurare shi ba, ta juya kanta gefe tana kuka, kukan takaicin yadda kishiyoyinta na gidan sarauta suka zo suna ganin rauninta...
Bayan ficewar Zayana, ɗakin ya rage saura ɗacin kalaman da ta bari...
Maayah tana kuka ranta ya ɓaci, tana jin tamkar kowa ya tsane ta. Sai dai kwatsam sai ga Gimbiya Yumna ta shigo...
Yumna ba ta zo da takun alfarma ko takun nuna mulki ba. Ta shigo ne tare da bayinta guda hudu waɗanda kowa ya sani ba bayinta ba ne kawai a wurinta, ƙawayenta ne.. Suna hira cikin kulawa har suka shigo ɗakin..
Ganin Maayah a kwance cikin wannan halin, idanun Yumna suka cika da kwalla nan take. Ta bar sauran bayin nata a baya, ta ƙarasa da sauri har gaban gadon Maayah...
Ba tare da bata lokaci ba Yumna ta durkusa a kasa a gefen gadon, ta kama tafin hannun Maayah tana murza su a hankali, tana kallon fuskarta cikin matukar damuwa da tausayi..
"Aunty Maayah, dan Allah kiyi hakuri," ta fada cikin muryar kuka, "Wallahi tun da na ji labarin hatsarin nan, hankalina ya tashi. Allah Ya baki lafiya, Allah Ya kawo miki sauki..."
Maayah ta kalli Yumna. A karon farko ta ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta. Ta lura cewa Yumna ba ta zo domin yi mata gatsali ko nuna mata gazawarta ba.. ta zo ne da gaskiyar zuciya...
Kodayake Maayah mutum ce mai girman kai, amma ta kasa kwace hannunta daga cikin na Yumna..
"Yumna... na gode," ta faɗa a hankali, muryarta a sanyaye..
Yumna ta cigaba da murza hannun ta, tana kokarin sanya mata kwarin gwiwa...
"Kada kiyi kuka, Doctor ya ce za ki warke. Kuma zan riƙa zama dake ina taya ki hira har sai kin tashi. Duk abin da kike bukata, ki fada min zan sa a shirya miki."
Sarki wanda yake kallon dambarwar da ta faru tun daga kan Chingching, Zayana, har zuwa kan Yumna, ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya. Ya ji daɗi ganin yadda Yumna ta sanyaya ran ƴar uwarta...
Bayan Yumna ta gama rarrashi, ta sa bayinta suka ajiye duk wasu kayan bukatu da suka kawo sannan ta sake sumbatar hannun Maayah kafin ta miƙe...
✨✨✨
Washegari da safe, masarautar tana cikin wani yanayi na daban. Ayat tana cikin babban ɗakinta, yau ma ta riga ta kammala shigarta ta mazaje, tana duba takobinta da sauran kayan aikinta...
Saratu wadda ita ce amintacciyar ma'aikaciyar ta tana tsaye a wajen kofar dakin tana magana, domin Ayat ta kulle kofar yadda babu mai shigo wa...
"Gimbiya! Labari ya iso cewa halin Gimbiya Maayah ya tsananta. Faduwar jiya ta taɓa ƙashin bayanta sosai. Yanzu haka ana shirin fita da ita kasar Indonesiya domin neman lafiya a manyan asibitocinsu,"
Saratu ta fada cikin damuwa.
Ayat tana zaune, ta gyara rawuninta sannan ta amsa ta cikin kofa..
"Allah Ya ba ta lafiya.... Saratu ki haɗa kai da sauran ma'aikatana ku kai mata gaisuwa, na wakilce ku gaba ɗaya. Ku faɗa mata cewa idan sun dawo daga kasar wajen zan duba ta da kaina. Yanzu ina da ayyukan da zan kammala ne."
Saratu ta amsa da "To shikenan Gimbiya," sannan ta juya ta tafi domin cika umarnin...
Bayan jin tafiyar Saratu, Ayat ba ta bata lokaci ba. Ta nufi ɗakin sirrinta, ta danna madannin da ya buɗe mata elevator. Ta lula can karkashin kasa, ta bi dogon ramin nan dake cike da sirri har ta fito ta tsakiyar lambun masarauta inda iskar safe ta bugi fuskarta. Ta fara nata takun domin fita wajen masarautar...
A ɗaya ɓangaren kuma, ɓangaren