Showing 129001 words to 132000 words out of 154131 words

Chapter 44 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

buɗe...

Tana turo baki ta ce,
"Kaji mutum... wai shi malami. Ka sani sarai idan mahaifiyata ta ji labarin abinda kake yi min, sai ta sa an kora ka daga kasar nan."

Uncle Jalal ya yi wani murmushin gefen baki, ba tare da ya kalle ta ba..

"Mahaifiyarki? Wacce take malamar jami'a a Mumbai? Wacce aka girmama a duniya saboda ilimi? Ke kike tunanin za ta goyi bayan jahilcin ki? Maayah, kin zama babban abin kunya ga asalinki. Kina SS3 amma ko sunan mahaifiyar taki ba za ki iya rubutawa ba... kin taɓa ganin inda aka taɓa irin wannan asarar?"

Maayah ta ji maganar ta soke ta a zuciya, ta kawar da kanta tana kallon titi..

"Nidai kawai ka kaini makarantar, idan mun je can zan san abin yi."

Suna isa kofar makarantar, Uncle Jalal bai tsaya a inda sauran manyan motoci suke tsayawa ba, ya kai ta har kofar ajin da aka rage ta aka mayar (SS1/Senior Secondary 1)...

"Sauka maza. Kuma ki sani, daga yau duk wanda ya nuna miki rashin kunya a makarantar nan, ni zan dauki mataki. Amma idan ke kika yi wa wani, ni zan fara horonki."

Maayah ta sauƙa tana gurnani, yayin da daliban makarantar suka saki baki suna kallon gimbiyar da suka saba gani da ayarin motoci, yau tana fitowa daga mota da Uncle Jalal kuma a aji ɗaya za ta cigaba da zama!..

Maayah ta shiga ajin SS1 tana taku kamar tana takon ƙaya. Duk ɗaliban ajin suka yi shiru, kowa ya zura mata ido...
Waɗanda ta saba yi wa wulakanci duk suna nan..dake duk makarantar yaran attajirai ne, kowa yana ji da kuɗin mahaifinsa..

Ta kalli yaran dake ajin duk ba sa'o'inta ta ji wani irin amai yana taso mata...

Ta zauna a wata kujera ta baya-baya, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta, amma ina! Tuni labari ya bazu cewa Gimbiyar Alhamra an dawo da ita baya...

Wata ɗaliba mai suna Zaitun, wadda Maayah ta taɓa sa aka ci mutuncinta tin kafin ta shigo SS1, ta tashi tsaye tana nuna Maayah da yatsa, ganin yanzu babu wannan isar kuma Uncle Jalal ya tsayar mata..

Zaitun ta ce, "Iyeee! Kowa ya ga abin da nake gani kuwa? Subhanah, gimbiyar da take ganin kanta a sama, yau gata a aji ɗaya da mu? Maayah, ashe duk wannan takamar takarda ma ba ki iya rufawa kanki asiri ba?"

Daukacin ajin suka ɓalle da dariya...
"Hahaha! Gimbiya mai repeat!"
"Yau dai kishin fada ya ƙare a bakin allo!"

Maayah ta ji ranta ya ɓaci, ta tashi tsaye tana huci..

"Ku yi mun shiru anan, banzaye kawai! Kun san ko ni wacece? Idan na sa aka kama ku duka a gidan yarin masarauta sai kun gwammace ba'a haife ku ba!"

Daidai lokacin, wani malamin lissafi mai tsanani ya shigo ajin. Ganin hayaniya ta yi yawa, ya buga teburi..

Malamin ya ce, "Me ke faruwa a nan? Ke kuma menene wannan dake ta ihu?"

Zaitun ta ce, "Yallabai, sabuwar ɗaliba ce, Maayah ce."

Malamin ya gyara madubin idonsa...
"Ah, Gimbiya Maayah. Uncle Jalal ya ba ni labarinki. To tunda yau ne farkon dawowarki ajin, maza zo nan gaban blackboard. Solve mana wannan simple equation ɗin.. 2x + 5 = 15. Nemo mana darajar x."

Maayah ta daskare. Ta kalli allon, ta kalli ɗaliban dake mata dariya a ɓoye, ta kasa ko takawa ta nufi allon. Ta saba ne kawai a riƙa ce mata "Ranka ya daɗe," amma yanzu lissafi ya zo mata da darasi.

Tana nan tsaye tana hawayen takaici, sai ga Uncle Jalal ya leƙo ta taga. Idanunsa suka sarƙe da nata. Cikin takaici yayi mata kallon da ya nuna mata "kin gani ko?" ya fi komai ciwo..

Ya kalli malamin sannan ya ce,
"Malam, idan ba ta sani ba, ka ba ta bulala biyar a hannu. Ta saba ana mata komai, yau kuma dole ta koya da kanta."

Maayah ta zaro ido, ta kalli hannunta mai laushi dake sanye da zinarai, tana tunanin yadda bulala za ta shige shi...

Daga nan Uncle Jalal ya bar wurin, ya koma office ɗinsa.

Malamin ya zo gaban Maayah cikin takun izgilanci daman ko wani malami tarko yake ɗana mata yadda zai rama wulaƙancin da tayi mu su..

Ɗaga bulala yayi ya zabga wa mata a tafin hannunta. Maayah ta ji wani irin zafi ya ziyarci ƙwaƙwalwarta. Tun kafin malamin ya sake ɗaga ta biyu, Maayah ta nuna cewa ita jinin sarauta ce mai zafi..
Ta ɗaga hannunta ɗayan, ta wanke Malamin da wani lafiyayyen mari wanda ya sa madubin idonsa ya goce!..

"Ka kuskura ka sake taɓa ni da wannan datti-dattin hannun naka, sai na sa an fasa maka kanka!"

Ajin ya kaure da hayaniya. Ɗaliban ajin, waɗanda duk ƴaƴan manyan attajirai ne, suka saki baki suna kallon jarumtar Maayah, wasu kuma suna jin tsoron abin da zai biyo baya. Maayah ta kwashe jakarta, ta fice daga ajin da gudu, ta nufi hanyar gate domin komawa gida..

Uncle Jalal yana ofishinsa yana duba takardu, sai ya ji hayaniya ta barke a harabar makarantar..

"Gimbiya ta mari Malam!" Labari ya isa kunnensa. Ya fito cikin matuƙar fushi, idanunsa sun yi jawur..

Ya hango Maayah tana sauri za ta fice daga gate ɗin makarantar..

"Maayah! Tsaya a nan!" Uncle Jalal ya daka mata wata uwar tsawa.
Maayah ta waigo, tana kuka tana huci. "Ba zan tsaya ba! Mugu, azzalumi! Gida zan koma, kuma sai na sa an raba ka da duniyar nan!"

Uncle Jalal ya taro ta da wani irin zafin nama, ya damƙe hannunta ya juyo da ita. Bai saurari komai ba, ya ɗauke ta da mari har sau biyu, fuskarta ta juya hagu da dama..

Maayah ta fizge hannunta, tana kuka tana gudu tare da zaginsa da duk kalaman da suka zo bakinta...

"Allah ya isa! Ba zan yafe ba! Mugu, matsiyacin bawa, azzalumi!"

Uncle Jalal ya rasa inda ransa ya yi, ya bi ta ya girbe mata sawu. ta yi sama, ta faɗo a ƙasa timm! Tana ƙoƙarin tashi, ta sake cewa..

"Mahaukaci! Ɗan akuya kawai!"
Nan take Uncle Jalal ya sake kai mata wani zafaffan marin da ya sa kanta ya ɗauki kukan ƙararrawa...

Mutane sun taru, malamai suna ba Uncle Jalal haƙuri, amma ya toshe kunnensa. Maayah ta ƙi daina zagi, shi kuma ya ƙi daina duka. Fuskar Maayah mai kyau da haske ta rikkiɗa ta yi jawur, shatar hannun Uncle Jalal guda biyar ta fito radau a kumatu biyun...

Yaa damƙe hannunta, ya riƙa jan ta kamar rago. Ya kaita ofishinsa, ya tura ta ciki ya jefar da ita a ƙasa.

"Zauna a nan! Idan na sake jin muryarki, wallahi sai na sa ki yi fitsari a wando! A nan za ki wuni har sai kin gane cewa ke ɗaliba ce, ba gimbiya ba!"

Maayah ta duƙunkune a ƙasa tana kuka mai cin zuciya, tana kallon hannayenta da suka yi dumu-dumu saboda ƙura, tana mamakin yadda rayuwarta ta canza a cikin sa'o'i kalilan..

✨✨
Bayan mintuna kalilan, kofar ofishin ta budu da wani irin karfi Baaaaam!....

Maayah ta zabura ta mike cikin matukar tsoro, idanunta jajur. Ganin Uncle Jalal ya shigo rike da jakarta a hannu daya, dayan hannun kuma yana rike da wata zabgeger dorina mai baki uku, ya sa ta ji cikinta ya bada wani sauti...

Ta bude baki zata fasa kuka, ya daka mata wata tsawa..

"Ki rufe min baki! Idan na ji kukan nan, yanzu zan raba jikinki da fata!"

Ya shimfiɗa wata lallausar dadduma akan tiles din ofis din, ya nuna mata daddumar..
"Zauna a nan!" ya fada cikin muryar soja..

Maayah ta zauna jiki na ɓari, shima ya zauna a kusa da ita, ya ajiye waccan dorinar a gefensa domin ta riƙa kallonta tana jin tsoro. Ya buɗe jakarta, ya zaro littafin rubutu da biro, ya tura mata gabanta..

"Rubuta sunanki gaba daya... SHAHZADI MUHAMMAD NOURDEEN."

Maayah ta kama biron da hannunta dake karkata. Ta fara kokarin rubutun, amma haruffan sai rawa suke yi, wasu sun fi wasu girma, rubutun ya fito a karkace kamar ɗakin gizo-gizo...
Uncle Jalal ya kalli littafin, ya saki wani uban tsaki Tcheeeew!....

"Baki iya komai ba sai rashin kunya da zagi? Dubi rubutun ki kamar na kaza?"

Ya fizgi biron daga hannunta, sannan ya matso kusa da ita. Ya sata a gabansa, ta yadda bayanta yake gogar faffaden kirjin sa. Ya ɗora hannunsa akan nata, ya damke yatsunta tare da biron, kamar yadda ake koya wa yaro dan Nursery rubutu..

Maayah ta ji wani irin bakon yanayi. Kamshin turarensa mai karfin gaske ya ziyarci hancinta. Ta kasa daurewa, ta juyo da fuskarta tana kallon sa. A lokacin, fuskokinsu suka kasance kusa da juna, hancinsu ya hade wuri daya, suna shakar numfashin juna...

Bakin su ya kusa hadewa, idanun Maayah suka lumshe saboda wani irin shock da ta ji. Amma Uncle Jalal, duk da shima ya danyi tsuru na dakikani, sai ya tuno zaginsa da ta yi ɗazu. Ya haɗa rai, ya ce da ita cikin muryar dake nuna fushi..

"Look your front!.."

A sanyaye ta kalli littafin, zuciyarta na bugawa.. Uncle Jalal ya cigaba da rike hannunta, yana gwada mata yadda ake rarrabe haruffan sunan nata daya bayan daya. Ya nuna mata yadda za ta zauna daram akan layin littafin..

"Dole ki iya rubuta sunan ki yanzu. Jarrabawa ta kusa, kuma idan baki iya rubuta sunan ki ba, ba za a taba barinki kiyi exam din ba. Kuma muddin kika faɗi, to sai kin shekara goma a aji daya!"

Maayah ta fara nanata rubutun tana bi biyu, tana jin dumin hannunsa akan nata. Duk da zafin marin da ya mata dazu, sai ta ji wata irin natsuwa tana ratsa ta, tana mamakin yadda malamin dake dukan ta, yanzu kuma shine yake koya mata rubutu cikin wannan kusancin....

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 3️⃣5️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



Asuba ta gari, iska mai sanyi tana kaɗawa a wani boyayyen fili dake kewaye da daddadan bishiyoyi. Shiru kake ji, sai sautin tsuntsaye dake rera kukan sanyin asuba.... Inuwa yana tsaye, sanye da rawaninsa da saje da gemunsa na bogi wadanda suka ƙara masa kwarjini...

Master Ibrahim ya matso ta bayanta domin fara koyar da ita dabarun yaƙi da takobi. Ya tsaya daidai bayan Inuwa, ya sa hannunsa ya kama nata dake rike da takobin, domin ya nuna mata yadda ake jujjuya shi cikin kwarewa...

A take, wani irin Shock mai karfin gaske ya ratsa Ayat tun daga kwakwalwarta har zuwa tafin kafafunta. Taɓa jikin Master da ta ji ya sa tsikar jikinta tashi, musamman yadda gemun Master yake gogar wuyanta yayin da yake mata bayani cikin raɗa...

Shi ma Master Ibrahim, hancinsa ya shaki wani daddadan kamshi dake tashi daga wuyan Inuwa...ƙamshi ne mai rikita tunanin namiji, wanda bai kamata soja namiji ya kasance dashi ba. Hankalin Master ya fara barin jikinsa, yana jin wani yanayi dake neman rinjayar dabarunsa na soja..

Inuwa cikin muryar dake rawa ya furta
"Master... na koya, zan yi da kaina yanzu."

Ta samu ta zare jikinta daga gareshi, tana kokarin daidaita numfashinta da ya riga ya jagule.

A can gefen wani kududdufi na alfarma wato Power Pool...King Diamond yana zaune tare da Prince Zarith. Suna shan wani ruwa mai launin shuɗi mai suna Al-Kautharul-Jinn, wani irin ruwa ne da ba a samunsa a duniyar mutane, wanda yake ƙara ƙarfin jini da sanya natsuwa a kwakwalwa..

Lokaci guda, King Diamond ya ji tsikar jikinsa ta tashi. Ya shiga wani irin yanayi na shauƙi da bai san daga inda ya fito ba.

Nan take idanunsa suka juye, sai ga Ayat ta bayyana a gabansa cikin shigar gimbiyancinta na alfarma. Ta sa hannu ta yaye mayafin dake fuskarta, tana sakar masa wani irin kasaitaccen murmushi mai sace zuciya..

King Diamond ya daskare, ya kasa daina kallonta, shima ya fara sakar mata murmushi har fararen hakwaransa suka bayyana..

Prince Zarith ya cika da mamaki, domin tunda yake da King, bai taba ganin dariyarsa da ta kai ga bayyanar hakwara ba.

Prince Zarith yana taɓa kafar King cike da mamaki ya furta.
"Lafiya kuwa King? Me kake kallo haka kake murmushi kai kadai?"

King ya firgita, ya dawo hayyacinsa. Ya waiga, ya ga babu kowa, sai Prince Zarith dake kallonsa cikin rashin fahimta. Anan ya tabbatar da cewa Ayat ta riga ta mamaye ransa, har ta kai tana masa gizo a fili...

A ransa ya furta "Wane irin sihiri ne wannan yarinyar take yi min? Tana can tana training, amma ina jin ɗumin jikinta a nan."..

Prince Zarith ya matso kusa da King, ya shaƙi iskar dake kewaye da shi, idanunsa suka rine da launin mamaki..

"King... ina jin ƙamshin shauƙin soyayya a jikinka? Wannan ba yanayinmu na jinnu ba ne kaɗai. Shin wacece a ranka?"

Ya tsaya ya ƙura wa King ido, muryarsa ta rikkiɗa ta koma ta gargaɗi... "Fatan ba bil'adam ba ce... domin akwai babban matsala idan har ita ce. Ka san dokokinmu, kuma ka san abin da zai biyo baya."

King Diamond bai ce uffan ba, sai dai wata uwar harara da ya wurga wa Zarith, wadda ta sa iskar wajen ta yi sanyi lokaci guda. Shima ya sani, mallakar Ayat ba abu ne mai sauƙi ba. Akwai babban ƙalubale daga manyan shugabannin aljanu waɗanda ba za su taɓa amincewa da wannan sarƙaƙƙiyar soyayyar ba. Dole za a fafata, kuma dole jini ya zuba kafin burinsa ya cika...

A can duniyar mutane kuwa, Master Ibrahim ya canza salon horon. Ya kai Inuwa bakin wani katon tafki mai zurfin gaske domin gudanar da training ɗin numfashi a cikin ruwa.

Master Ibrahim ya tsaya a bakin ruwan, idanunsa sun yi ja saboda tsananin son ganin Inuwa ya zama jarumi.
"Wannan karon, za mu ga juriya da jarumtarka a cikin ruwa. Dole ka nitse, kuma ba za ka ɗago ba har sai mintocin da na ɗiba maka sun cika. Wannan shi ne zai nuna idan kai soja ne na gaske."

Ayat ta ji gabanta ya faɗi, wani irin sanyi ya ratsa ƙasusuwanta. Ba tsoron ruwan ne ya firgita ta ba, sai umarnin da Master ya biyar da shi...

"Inuwa, cire waɗannan kayan naka na soja! Ba za ka iya yin wannan training ɗin da nauyin kakin nan a jikinka ba. Cire su yanzu ka shiga ruwan!"

Inuwa ta daskare a inda take. Ta san muddin ta rage kayan jikinta, asirinta na mace zai iya bayyana. Master Ibrahim kuwa yana tsaye yana jiran ganin ya fara cire kayan, idanunsa kyam akan Inuwa...

Muryar na rawa ta ce, "Master... ina jin zan iya yi da kayan nan. Ba sa min nauyi."

Master cikin tsawa ya ce, "Wannan umarni ne Inuwa! Soja baya musu da shugabansa. Cire kayan nan yanzu!"

Ayat ta fara ƙoƙarin taɓa maɓallan rigarta, hannunta yana karkata, tana kallon Master wanda ya ƙi ba ta sararin ko da ƙifta ido ne. A ranta tana kiran King Diamond, ko zai kawo mata ɗauki a wannan mawuyacin lokacin...

Ta ji zuciyarta tana bugawa kamar ganga. Ta kalli Master Ibrahim, wanda yake tsaye tamau kamar gunki, yana jiran ganin ta cire kakin soja..

A hankali ta sake furta
"Master... don Allah, ina neman alfarmar ka bar ni in shiga bayan wancan shingen, domin in rage kayana. Al'ada ta ce ba na son rage kaya a gaban kowa, ko da kuwa shugabana ne."

Master Ibrahim ya haɗe girare, yana kallon Inuwa da wani irin kallo na mamaki. "Inuwa, kai soja ne! Soja ba shi da kunya a gaban ɗan uwansa, musamman a wajen horo."

Inuwa ya ce, "Ina rokonka Master... wannan karon kawai."

Master ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ya nuna mata bayan shingen da hannu..

"To, ka je maza! Amma ka sani, duk daƙiƙar da ka ɓata tana raguwa ne daga lokacin numfashinka a cikin ruwa. Ka fito nan da daƙiƙa talatin!"

Ayat ta ruga bayan shingen da gudu. Da sauri ta rage kayan jikinta, amma ta bar wata siririyar riga ta ciki wato vest, ta ciki akwai bell da ya ɗaure mata ƙirji sosai don kada siffarta ta fito. Ta fito tana sauri, ba tare da ta bari Master ya kalle ta sosai ba, ta afka cikin ruwan tafkin..

Ruwan ya kasance mai sanyi sisai, amma hakan ya ba ta damar ɓoye kanta.

Tana nitsewa cikin ruwan, Master Ibrahim ya matso bakin tafkin, yana kallon agogonsa amma hankalinsa yana kan yadda Inuwa ya yi firgigit wajen boye jikinsa...

A ransa ya furta
_"Wane irin soja ne wannan mai kunyar mata? Akwai wani abu da wannan yaron yake ɓoyewa, kuma zan gano shi ko ba jima ko ba daɗe."_

A can gefen Power Pool, Prince Zarith ya lura cewa King Diamond ya tafi wani tunani na daban, idanunsa sun yi haske kamar taurari...

Ya ce, "King, muna magana ka yi shiru. Shin kana nufin za ka sadaukar da matsayinka na Sarkin Aljanu domin wannan bil'adama? Ka sani, idan manyan majalissar aljanu (The Elder Jinn Council) suka ji wannan labarin, yaƙi zai ɓarke tsakanin masarautunmu."

King Diamond ya miƙe tsaye, dogon farin gashinsa yana shawagi a iska...
"Zarith, ba zan sadaukar da komai ba, amma kuma ba zan bar ta ba. Idan dole sai an yi yaƙi don a tabbatar da soyayya, to ni ne zan jagoranci yaƙin. Babu wani aljani da ya isa ya gaya min wadda zan so!"

Ya kalli sararin samaniya, yana jin yadda Ayat take fama da numfashi a cikin ruwa. Ya tura mata wani irin sanyin ƙarfi ta hanyar iska domin ta jure sanyin ruwan da take ciki...


Inuwa ya ɗago daga cikin ruwan bayan minti biyar, numfashinsa yana fita sama-sama "ha...ha...ha"..

Ruwan yana wuyansa, idanunsa sun yi jawur saboda sanyi da juriya. Rawani yana nan daram a kansa, ya jike jagaf ba tare da ya faɗi ba domin an ɗamara shi sosai...

Cikin mamaki da fushi Master ya ce,
"Wai kai Inuwa, meye a cikin rawanin nan da ya fi karfin a cire shi? Ka taɓa ganin soja yana horon nitsawa a ruwa da rawani? Wannan wane irin iskanci ne?"

Inuwa ya ce, "Master... kayi hakuri. Al'ada ce ta gidanmu, ba ma taɓa barin kanmu a fili..."

Master Ibrahim ya matso har bakin tafkin, ya duƙa ya kalli kwayar idon Inuwa. Ya kasa gane dalilin da yasa wannan yaron yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login