Showing 135001 words to 138000 words out of 154131 words

Chapter 46 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

Helmet dinsa, gashin kansa ya dan hargitse kadan wanda hakan ya kara masa wani irin kwarjini na daban...

Yana sanye da farar riga ta alfarma da aka yi wa ado da baƙin zare a wuya. Takunsa ɗaya bayan ɗaya ya ƙarasa cikin taron, inda aka ware wa malamai gurbi.
🔥
Ganin Uncle Jalal ya sa kirjin Maayah bugawa
Dub-dub-dub!. Wani irin kishi da haushin marin da ya mata a makaranta ya taso mata, amma kuma kwarjininsa yana tsorata ta..

Ta riƙa watsa masa wasu harara masu zafi, tana turo baki gefe ɗaya, tana so ta nuna masa cewa har yanzu ba ta yafe masa ba. Duk lokacin da Uncle Jalal ya kalli ɓarin da take, sai ta yi fari da ido ta juya kai tare da jan tsaki Tcheeeew a ranta, amma bakin na nuna alamun tsaki saboda tana turo shi ne....

Shima Uncle Jalal ya hango ta. Ya kalli inda take zaune, ya ga yadda take faman harara. Maimakon ya biye mata, sai ya yi wani dan murmushin gefen baki, murmushin da yake nuna kina nan dai a karkashi na...
Ya gyara zamansa ya mayar da hankalinsa kan tilawar da Ayat take yi, kamar bai ma san tana yi ba..
Wannan ya kara wa Maayah haushi. Ta ji kamar ta tashi ta je ta shashshaƙe shi...

Yayin da fada take ta ɗaukan karatun Alkur'ani, can bayan fada a cikin Cell, Gimbiya Zayana tana takure. Sautin muryar Ayat dake tilawa yana dako wa har cikin kunnenta ta jikin katangar kurkukun...

Tana kuka tana shakar warin wurin da sanyi. Babu mai tunawa da ita, kowa yana murnar saukar Ayat da Yumna.... Zayana ta kifa kanta a gwiwa, tana jin yadda duniya ta yi mata zafi...

Ana tsaka da raba albarkar karatun Alkur'ani, sai aka fara jin wani irin ruri daga sararin samaniya. Iska ta hargitse, rawuna da mayafan mutane suka fara tashi. Kowa ya ɗaga kai sama, sai aka hango Jirage guda goma masu kalar bakin karfe suna shawagi, kafin su fara sauƙa ɗaya bayan ɗaya a filin dake kusa da fadar...

Sarki ya miƙe tsaye, yana tunanin ko wani babban bako ne ya kawo ziyara ta ba-zata don taya shi murna. Amma yana ganin tambarin dake jikin jiragen, tambarin Sarkin Pavilion sai gabansa ya bada wani sauti...

Kofofin jiragen suka buɗe, hayaki mai sanyi ya fara fitowa. Daga ciki, Chief Onyx ya fito da wani irin takun isa da kwarjini..

Yana sanye da wata doguwar bakar riga har ƙasa, amma botirorin gaban rigar a bude suke, wanda hakan ya bayyana riga da wando na suit dake ciki...
Rabin fuskarsa a rufe take da wani karfen azurfa wato Silver Mask wanda ya kara masa kwarjini da firgitarwa...
A gefensa, katafaren Robot ɗinsa wato Gely, wanda take tafiya tana fitar da sautin karfe, sannan dimbin sojojinsa da Bodyguards na take masa baya...

Sarki yana tsaye daram, duk da kwarjininsa, amma ganin Chief Onyx ya sanya shi jin wani irin yanayi na dar-dar. Shi kansu baƙin da malamai, kowa ya shiga ruɗani, domin Chief Onyx babban makiyin masarautar ne, kuma zuwansa a yau ba tare da gayyata ba alama ce ta tashin hankali...Duk da matsayin ƴan uwa suke.

Master Ibrahim ya damke hannun takobinsa, ya matso kusa da Inuwa..

"Inuwa, ka kasance cikin shiri. Wannan mutumin bai zo da alheri ba. Onyx ba abokan wasa ba ne..."

Yayin da kowa ya tsorata da saukar Chief Onyx da Robot dinsa Gely, Uncle Jalal yana zaune daram, ko kwayar idonsa bata motsa ba. Ya kalli Onyx ne kawai a matsayin wani baƙo, ba tare da fargaba ba...

Maayah ta kalli Uncle Jalal ta ga ko zai nuna tsoro, amma ganin yadda ya hadiye natsuwa ya sanya ta kara jin kwarjininsa a ranta...

Sarki ya ɗaure fuska, amma a cikinsa fargaba yake yi kada Chief Onyx ya tona asirin cewa Yumna ba jininsa bace, kanwarsa ce shi da Reems.. Sarki ya riƙe ta ne tun tana jaririya don boye asali, kuma ya nemi alfarmar Onyx kan kada kowa ya sani.
Yumna ta ji zuciyarta na wani irin bugu. Tana son ta mike ta ruga ta rungume dan uwanta Onyx, amma alkawarin da ta yi wa Sarki na boye dangantakar su ya sanya ta tsumaye a mazauninta, idanunta cike da hawayen farin ciki da raɗaɗi...

Ayat ta kalli Chief Onyx, wani irin ɗaci ya ziyarci makogwaronta. Ta tuna yadda ya tafi da Autar sarki, wato kanwarta uwa daya uba daya, ya mayar da ita baiwa a Pavilion. Ta so ta mike ta shaƙe shi, amma hasken Alkur'anin da ta gama karantawa ya sanya mata wata natsuwa, ta kasa motsawa sai dai kallon tsana...

Chief Onyx yana takowa cikin isa, ya zo wucewa ta inda Inuwa yake tsaye... Lokaci guda, Chief Onyx ya ji tsikar jikinsa ta tashi, wani irin ƙiran jini ya ziyarce shi. Ya tsaya cak, ya juyo a hankali ya ƙura wa Inuwa ido...

King Diamond wanda yake matsayin Inuwa shima bai ɗauke idonsa ba. Ya kalli Onyx har cikin kwayar idonsa, anan ya tabbar da akwai alaƙa a tsakaninsu...
A ransa yana wani irin farin ciki na ganin twins ɗinsa da aka raba su tun suna kanana..

Chief Onyx ya zare idonsa cikin zargi. Ya tuna lokacin da ya zo daukar Autar sarki, ya ga wannan Guard din Inuwa, kuma a lokacin ya san mace ce. Amma yanzu da yake kallonsa, kwarjinin da yake gani ya wuce na mace, kuma wannan jan ragamar tsikar jikin da yake ji ya tabbatar masa akwai wani boyayyen abu a tare da wannan bawan...
Ba tare da ya ce uffan ba, Onyx ya wuce ya je ya zauna a kujerar dake kusa da Sarki, ya shimfida ikonsa...

Duk da wannan tashin hankalin, aka cigaba da rabon abinci da abin sha na walima...

Maayah tana faman satar kallon Chief onyx Daman bata san shi ba, sai kawai labarinsa...ta haɗiye yawu a ranta take faɗin
"Wayyoo, wannan ne Chief onyx? Tsararren sarki, wannan ya wuce yadda nake tunani...haɗaɗɗe da shi..."

Amma da zaran idonta ya sarƙe da na Uncle Jalal sai ta fara yatsine fuska, tana nuna masa har yanzu dukan da ya mata yana nan a ranta. .

Uncle Jalal ya ɗauki kofin ruwa ya sha, ya kalli Maayah ya girgiza kai kadan, yana mata kallon babu wanda zai saurari jahila fa...

A daidai lokacin da Chief Onyx yake zaune yana kallon kanwarsa Yumna cikin alfahari, can Zayana tana ta faman dukan kofar cell ɗinta. Tin sautin jiragen da ta ji ya isa kunnenta, ta ɗauka mahaifiyarta ce ta zo... Domin tasan ba za ta ƙyale kowa ba...



Chief Onyx ya ba da umarnin a shigo da wasu manyan akwatuna na zinare. Abubuwan dake ciki sun fi karfin kwatancin dan adam, akwai sarƙoƙi na duwatsun Ruby masu haske, akwai turaren da akayi masa haɗi na gaske wanda kamshinsa kawai zai iya warkar da marar lafiya, da kuma agogo na musamman da ke nuna yanayin tsaron jikin mutum...

Bayan ya miƙa wa Sarki wani sirrin Memory Card wanda ganin haka yasa Sarki ƙara ruɗe wa, Chief Onyx ya nufi inda Yumna take...

Ya durkusa a gaban Yumna, ya ɗora hannunsa a saman kanta cikin wani salo na girmamawa da kauna. Ya fara tofa mata addu'o'i cikin sanyi, yadda mutane za su ɗauka girmama karatunta yake yi...

Yumna cikin muryar raɗa ta furta
"Nagode Yayanaa..."

Chief ya ce, "Kada ki damu, kyakkyawar kanwata. Ba zan taba barin ranar murnarki ta wuce ba tare da na shaidi nasararki ba."

Ya sakar mata wani murmushi wanda shi kaɗai ne yake da shi, sannan ya tashi..

Domin kada mutane su zargi wani abu, Chief Onyx ya nufi inda Ayat take zaune domin ya bata nata kyautar... Ya natsu zai dora hannunsa a kanta don yi mata addu'a kamar yadda ya yi wa Yumna, amma kafin hannunsa ya taɓa mayafin kanta, Ayat ta buge hannun da wani irin zafin nama...

"Kada ka kuskura ka matso kusa da ni! Ka janye wannan hannun naka mai cike da jinin mutane!...Ba na son ko iskar jikinka ta gogi tawa!"

Chief cikin muryar sanyi mai tsoratarwa ya ce,
"Gimbiya, ina ƙoƙarin nuna miki girmamawa ne saboda wannan rana ta Alkur'ani, amma naga kina son wuce gona da iri."

Ayat muryarta na rawa saboda kuka da bacin rai ta ce,
"Girmamawa? Daga gare ka? Tun yaushe azzalumi ya san girmamawa? Ka gaya min, da wane ido kake kallon mutane a nan? Kana tunanin na manta ne? Na manta yadda ka shigo fadar nan ka fizge ƙanwata, jini na, ka tafi da ita cann a matsayin baiwa?"

Taron ya yi tsit, kowa ya zura ido. Ayat ta ci gaba da magana cikin daka tsawa..

"Me ta yi maka? Me yarinya ƙarama kamar ta ta sani na gaba da mulki da za ka mayar da ita baiwa? Ka raba uba da ɗiyarsa, ka raba ni da kanwata ba tare da wani dalili ba! Ka sani sarai, duk ranar da na samu iko, sai na ga bayanka! Mugun banza, azzalumi!"

Ran Chief Onyx ya ɓaci fiye da yadda kowa yake tunani. Kalmar Azzalumi da aka nanata a gaban baƙi da malamai ta soke shi...

Ba tare da ya furta komai ba domin shi ba mai son hayaniya bane, cikin zafin nama ya zabga mata wasu lafiyayyun mari guda biyu a kunci biyu har sai da ta kife akan kujerarta...

Marin ya sauka a kuncin Ayat da duk ƙarfin hannunsa. Marin ya kasance mai ƙarfi yadda har sai da hular Rolling ɗin kanta ta fice, ta dafe kuncinta tana kallonsa cikin rashin yarda tana ƙasi zaune...

Sarki ya miƙe tsaye a gigice, amma kwarjinin Onyx da sojojinsa ya sanya shi daskarewa...domin a wannan ranar ba ya buƙatar tashin hankali domin ranar farin cikinsa ne, yana son duk baƙin da suka zo, su koma gida cikin ƙoshin lafiya...

Master Ibrahim ya zare takobinsa, yana jiran umarni, amma ya san taɓa Onyx yanzu tamkar taɓa wutar lantarki ne...
Sarki ne ya ɗaga musu hannu akan su ajiye makamansu...

King Diamond ya dunƙule hannunsa har jijiyoyinsa suka fito raɗau... Idanunsa suka fara rikiɗe wa zuwa launin blue...Yana jin kamar ya bayyana asalin sa ya fatattaka Chief Onyx a nan, duk da jikinsa na gaya masa akwai alaƙar jini a tsakaninsu....kuma alkawarin da ya yi wa kansa da kuma sirrin Ayat ya sa ya tsaya yana rawar jiki saboda bacin rai...

Ayat tana dafe da kuncinta, idanunta suka cika da hawayen radadi da wulakanci, tana kallon Chief Onyx wanda yake huci kamar zaki....

Uncle Jalal ya miƙe tsaye ganin haka, kwarjininsa ya cika wajen... Ya kalli Chief Onyx ba tare da tsoro ba..

"Haba bawan Allah, wannan ba halin girma ba ne. Ka daki mace a gidan mahaifinta a ranar farin cikinta?"

Chief Onyx ya juyo ya kalli Uncle Jalal cikin sauri, idanunsa suka rine...
"Kai kuma wanene da za ka sa baki a harkar Pavilion da Alhamra?"

Maayah tana hararar Uncle Jalal a cikin ranta take faɗin
"Ku ji! Ku ji!! Munafiki, jiya ka gama duka na makaranta amma yanzu kana magana akan dukan mace..."

King Diamond zuciyarsa ta gama harzuƙa, wani irin hasken shuɗi ne ya bayyana a cikin kwayar idonsa... Ya ɗora hannunsa akan makamin dake ƙugunsa, yana jiran kawai ya ga Ayat ta zubar da hawaye na biyu don ya fito da dukkan asalin sa ya koya wa Onyx darasi, ko da hakan zai tona asirinsa...

Ayat dake ƙasi har yanzu tana riƙe da kunci, ta kalli yadda King Diamond yake domin tasan dole zai ce zai aiwatar da wani abu, ganin yanayinsa ya sauya hatta idonsa yasa tayi sauri girgiza masa kai akan ya dakata...
Haka ta fara masa magana ta zuci..

"Ka da kayi komai, ka bari, ka koma yadda kake, Master Ibrahim zai kalleka yanzu, ka koma..."

Dai-dai lokacin da master ya kalli Inuwa wanda yayi ready zaro ido, King bai bari ya ga yanayin da yake ciki ba...

Gely kuwa ta nufi Uncle Jalal da wani irin gudu na inji. Ganin Boss dinta ya fusata, ta yanke shawarar koya wa wannan mutumin darasi, ya daina shiga shirgin da bai shafe shi ba...

Uncle Jalal, wanda asali jarumi ne kafin ya zama malami, bai girgiza ba. Ya fizge takobi daga hannun wani jami'in tsaro dake kokarin buya a karkashin teburi. Gely ta matsa wasu maballai a hannunta, nan take wani takobi mai dauke da wutar lantarki ya fito daga jikinta...

Sai ƙarar Kwang! Kwang! Kwang ake ji...

Sautin takubansu ya riƙa tashi. Uncle Jalal yana kare kansa cikin kwarewa, yayin da Gely take amfani da karfin karfe...
Maayah tana can takure, zuciyarta na bugawa. Tana hawaye tana cewa, "Don Allah kar a kashe shi!" Duk da dukan da ya mata, ta gane cewa rayuwarta ba za ta taba zama ɗaya ba idan babu Uncle Jalal..

Ayat ta kasa jurewa. Marin da ya mata da kuma tunanin kanwarta da yake hannunsa ya sanya ta rasa nutsuwa...Ta miƙe tare da zaro wata matacciyar takobi, ta kewaya ta bayan Chief Onyx tana nufin soka masa a tsakiyar bayansa...

Shi kuwa Chief tin tinin ya ga yanayin jami'in tsaro wato Inuwa wanda King Diamond ne, tin daga lokacin da ƙwayar idonsa ta koma shuɗi, Chief onyx ya ri ga da ya gane cewa shi ɗin ba kowa bane face REEMS...
Ya gano komai yanzu, domin Chief na da saurin fahimta da hangen nesa, tinin ya gane cewa akwai alaƙa a tsakanin Reems da Ayat, kuma a baya yasan Ayat ce take matsayin guard, saboda a yau dole ta fito a matsayin gimbiya da kuma guard yasa Reems taimaka mata..gaba ɗaya ya tafi dogon tunani, idonsa na kan King Diamond...

Ganin Ayat tayi baya da takobi zata soka masa, gaba ɗaya mutane suka zaro ido a gigice, har sarki kam ya daskare a yadda yake..

"Ayat! Don Allah kada ki yi haka!" Yumna ta dakawa Ayat tsawa cikin tashin hankali...

Kafin Bodyguards ɗinsa su ankara domin suna ɗan nesa da su..

Amma Ayat ba ji ba gani.. Ta tura wukar da nufin kashe shi, amma Chief Onyx kamar mai idanu a baya, ya sa hannunsa ya cafke bakin takobin daidai lokacin da zai taba jikinsa...

Ayat ta yi firgigit, ta yi kokarin fizge takobin ta yadda za ta feɗe masa tafin hannu, amma sai ta ji takobin kamar an manne shi a cikin dutse. Chief Onyx ya rike wurin kaifin wukar sosai ba tare da hannunsa ya tsage ba ko da digon jini ɗaya...

Sojojin Pavilion sun nufota da gudu, amma Onyx ya ɗaga musu hannu su tsaya. Sarki ma ya dakatar da dakarunsa don kada a fantsama cikin yaƙin da ba za su iya ba...

Chief Onyx ya saki wani murmushin gefen bakin nan nasu domin a jininsu yake, sannan ya yi wani uban janyo, ya jawo Ayat tare da takobinta. Saboda karfin jan, Ayat ta tafi luuu ta faɗi a gabansa tana huci...

Chief ya kalle ta kyau sannan ya furta..

"Matsalo ne kawai yake kawo farmaki ta baya... Ki kiyaye gaba yarinya. Ƙarfin zuciya ba shi ke ba da nasara ba, sai idan an haɗa da ƙwarewa..."

Ya ɗaga wa Gely hannu, nan take ta janye takobinta ta kyale Uncle Jalal, wanda shi ma ya sauƙe numfashi yana kallon wannan robot ɗin cikin mamaki, dake yana da kwarewa shima bai ba ta damar cutar da shi ba..

Chief bai sake cewa uffan ba, ya gyara bakar rigarsa, ya yi wa Sarki wani kallo na raini, sannan ya juya tare da bodyguards ɗinsa da Gely zuwa wurin jiragen su..

King Diamond ya bi su da kallo, idanunsa suna faɗin abubuwa da dama. Ya so ya bi ɗan uwansa amma ya san ba a wannan lokacin ba...


Sarki yayi wani fusata ya miƙe tare da yo wa kan Ayat wadda take durkushe a ƙasa, tana karkarwa saboda raɗaɗin marin Onyx da kuma ɗacin zuciya...Bai tsaya wata-wata ba, ya fizgota da karfi ya sake zabga mata wani lafiyayyen mari wanda ya sa kanta sarawa..

​Yana huci, idanunsa sun yi jawur ya ce,

"Wace irin mahaukaciyar yarinya ce ke? Wace irin dabba ce ke da ba ki da tunani? A gaban waɗannan dubunnen mutanen za ki nuna wa duniya cewa ba ki da tarbiyya? Har kina da ikon fito da takobi ki nufi Chief Onyx?"

​Ayat ta ɗago fuskarta dake cike da hawaye ta cikin niƙab, muryarta na rawa cike da tauri...

​ "Abul... me ya sa ka kyale shi? Me ya sa ya zo ya ɗauke min kanwata ya tafi da ita Pavilion? Jini na ne ita fa!"

​Sarki ya sake daka mata tsawa..
"And so what? Kin fi ni son Ching-Ching ne? Ko kuma cewa aka yi miki cutar da ita yake yi a can? Ko kina tunanin Pavilion ɗin wasan yara ne?"

​Ayat ta ce,
"Amma Abul... baiwa ya mayar da ita! Kanwata tana bauta a karkashin azzalumi!"

​Girgiza kai yayi yana zaro mata idanuwa..

"Baiwa? Wa ya gaya miki hakan? To ki shiga taitayinki! Onyx ba abokin wasanki ba ne. Shi wuta ne, kuma duk wanda ya taɓa shi sai ya ƙone ya zama toka. Shin idan aka barki dake da shi, kina tunanin za ki iya cin galaba a kansa ne? Kina tunanin takobi ɗaya zai kifar da Pavilion?"

​Ayat ta kalli takobin dake gefenta, wanda akwai jinin Onyx a jiki, ta yi wani murmushi na ɗacin zuciya.. ta ce,

​"Abul, ai ko yanzu na ci galaba a kansa. Dubi wannan takobin, jininsa ne a jiki. Ya riƙe takobi ta wurin kaifi, haƙiƙa salon jarumta ne, amma ko ba komai... na sa ya zub da jini a gaban mutanensa. Na taɓa fatarsa!"

​Sarki a ruɗe kuma cikin fushi ta ce,

"To ke marin da ya zazzabga miki fa? Shegiyar yarinya! Ai shi wannan ɗan ciwon tafin hannun ba komai ba ne a wurinsa. Mutumin da yake yaƙar dubunnan sojoji shi kaɗai kuma ya rayu lafiya, don ya ji wannan raunin sai me? Ko a matsayin cizon sauro bai ɗauki wannan ba! Amma ke... kin janyo wa kan ki, kuma ki kiyaye ni!"

​Sarki ya juya cikin zafin rai ya kalli Uncle Jalal, wanda har yanzu yake rike da takobin da ya yi faɗa da Gely da shi...

​"Kai kuma Malam! Daga yau, kada ka ƙara kuskuren shiga maganar da ba ta shafe ka ba. Ka kame bakinka ka yi shiru kamar yadda kowa ya yi. Idan har kana son rayuwarka, to ka sani cewa takobinka ba zai taɓa kare ka daga fushin Pavilion ko na Alhamra ba. Kai malami ne, to ka tsaya a matsayin malami!"

​Uncle Jalal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login