Showing 45001 words to 48000 words out of 154131 words

Chapter 16 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

17 Mar 2026

103

shawagi kusa da ita. Ba tare da ɓata lokaci ba, ta zura hannu ta ɗauko majaujawar dake jikinta, ta saka dutse mai kaifi ta saita shi da kyau...

Dutsen ya tafi da gudun gaske, ya doki fikafikin tsuntsun. Na'urar ta fara fitar da wuta tana sparks, ta faɗo ƙasa tana tangal-tangal. Ayat ta ruga da gudu ta ɗauko shi kafin kowa ya gani. Ta dubi cikin idon tsuntsun, wanda kyamara ce ta leken asiri, ta ji gabanta ya faɗi. Ta gane cewa daga wannan kyamarar wani can nesa yana kallonta...



A can ɗakin Chingching, tana zaune tana murnar samun kazar da aka soya mata da yaji, kwatsam sai wutar lantarki ta ɗauke gaba daya..

"Wayyo! Uma Altine! Wutar ma satarsa aka yi ne?"

Chingching ta fara kuka tana laluɓar kazar ta a cikin duhu..
Ta fito waje tana ƙiran "Daddy! Daddyy!!...", tana tsoron kada wani ya kwashe mata kazar... Ita a tunaninta ba babban al'amari ne ya faru ba, kawai dai an hana ta jin daɗin abincin dare ne. Wanda hakan ya sa wasu ma'aikatan suka ɗauka ko an kawo wa fadar hari ne..


Sarki Nourdeen yana cikin ɗakin taro na sirri lokacin da duk fuskokin kwamfutocinsa suka nuna alamar Access Denied..
Ya buga teburin gabansa cikin matsanancin firgici.

"Yau ne? Chief Onyx, ashe ba za ka jira kwanaki ukun su cika ba?"
Sarki ya raɗa cikin tsoro. Ya gane cewa daren nan ne fushin Pavilion ya fara sauƙa. Ya gane cewa duk wani shiri da yake yi na ɓoye 'ya'yansa, Chief Onyx ya riga ya san inda suke ta hanyar waɗannan drones ɗin...

✨✨

A can Pavilion, Chief Onyx yana kallon allon dake gabansa, inda kyamarar tsuntsun da aka harbo take nuna masa fuskar Inuwa kafin ya ɗauke gaba ɗaya. Ya saki wani murmushi mai sanyi...

"Wannan yaron... ko kuma ince wannan 'yar tawayen,"

Chief ya faɗa a fili...
"Kina da ƙoƙarin ɓoye asirinki, amma baku san cewa duk motsinku yana karkashin ikona ba."...

Wannan lokaci ne da lamura suka hargitse a masarautar Alhamra, inda fasahar Pavilion ta mamaye kowane lungu...

A daidai lokacin da Ayat take tsaye tana juya tsuntsun ƙarfen da ta harbo, sauran dakarun fada sun ruɗe. Waɗanda suke da bindigogi suna ta harbi zuwa sama, yayin da wasu suke saran tsuntsayen na'urar da takobi suna ihu. Cikin wannan hargitsin, Robot Z-01 ta bayyana a fadar tamkar iska, ba tare da kowa ya lura da shigowarta ba...

Ayat ta ga wata inuwa ta rufe ta, tana ɗagowa sai ta yi ido huɗu da wata kyakkyawar budurwa, fara sol tamkar 'yar kasar China, sanye da bakaken kaya matsattsu. Kafin ma Inuwa ta yi tunanin ko ita wacece ko kuma ta kai hannu ga takobinta, Robot ɗin ta yi wani irin zafafan taku.

Wani uban mari Robot din ta zabga wa Inuwa, marin da ya sa Inuwa ganin taurari, ta tafi luu ta durƙushe a ƙasa. Ƙarfin hannun Robot ɗin ya wuce na ɗan Adam. Ba tare da bata lokaci ba, Robot din ta fizgo hannun Inuwa da karfi, ta damko ta tamkar yadda ake damkar tsuntsu...

Cikin kwarewa da sauri, ta janyo Inuwa wacce har yanzu take cikin jiri, ta nufi wata boyayyar hanyar fita da ita...

Robot ɗin ta jefa Inuwa cikin wani ƙaramin jirgi mai saurin gaske wanda yake jiran su a bayan fada. Cikin 'yan daƙiƙu jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya, ya bar Alhamra cikin hayaki da rugujewar tsaro...

Ayat tana zaune a cikin jirgin, hannunta a ɗaure da wasu ankwan ƙarfe na lantarki, tana kallon Robot ɗin dake zaune a kusa da ita ba tare da ko kifta ido ba...

Ayat tana zaune a cikin wannan ƙaramin jirgi mai gudu, tana jin yadda iskar sararin sama take ruri a wajen jirgin. Duk da zafin marin da ta sha da kuma jirin dake kanta, ƙwaƙwalwarta ta fara aiki da sauri.
Ta kalli Robot ɗin dake zaune kusa da ita, wadda idanunta suke kallon gaba ba tare da motsi ba..

Ayat ta lura cewa hannayenta suna ɗaure da waɗancan ankwan na lantarki masu fitar da wani ɗan haske... Ta fahimci cewa wannan yarinyar Robot ce ba ɗan Adam ba ce, yanayin numfashinta da yadda ba ta kifta ido sun tabbatar mata da hakan..

Don haka, dole ne ta yi amfani da dabarar da ta fi ta ƙarfin jiki..

Ayat ta tuna tsuntsun na'urar da ta harbo ɗazun, har yanzu akwai guntuwar wayar da ta ciro daga cikin tsuntsun... Da sanɗa, ta fara goga guntun wayar nan mai magnet a jikin ankwan dake hannunta...

Ta sani cewa idan ta samu ta haɗa wutar lantarki a tsakanin ankwan da wayar, za su iya buɗewa...

Wani ɗan tartsatsin wuta ya fito. Robot ɗin ta juyo da kanta da sauri, amma Ayat ta yi saurin dunƙule hannunta da wayar tana rarraba ido tamkar tana kuka ne saboda tsoro..

Ganin Robot ɗin ta ɗauke kanta, Ayat ta ƙara haɗa wayar kwatsam ankwan suka buɗe, ta cire ankwan...

Ba tare da ɓata lokaci ba, ta kai wa Robot ɗin duka da sauri, amma Robot ɗin ta tare ta tare da damƙe wuyanta..

"Ba za ki iya tserewa ba,"

Robot ɗin ta faɗa da muryarta mai sanyi..

Ayat ta yi murmushin yaƙi tare da faɗin..

"Ba tserewa zan yi ba, jirgin zan lalata!" Ta buga ƙafarta kan wani babban jan button dake kusa da mazaunin matuƙin jirgin.

Jirgin ya fara tangal-tangal, hayaƙi ya fara tashi daga injin ɗinsa. Robot ɗin ta saki wuyan Ayat don ƙoƙarin saita jirgin, hakan ya ba Ayat damar nufi ƙofar gaggawa Emergency exit...

Kafin Robot ta ankara, Ayat ta tura ƙofar, ta jefa kanta waje zuwa ƙasi daga sararin sama...

Ayat tana ta shawagi a cikin iska, tana faɗowa daga sama da gudu...

A wannan lokacin, ta rufe idanunta ta sadaukar da rayuwarta ga mutuwa. Ta gwammace ta tarwatse a ƙasa da ta shiga hannun Pavilion da hatta mahaifinta shakkarsa yake..

Kafin jikinta ya daki ƙasa, kwatsam sai wani haske mai ƙarfi da kwarjini ya bayyana. Wannan hasken ya riƙe ta tamkar wani bargo mai laushi, ya naɗe ta cikin sanyin da ya fi kowane irin ni'ima. Cikin ƙiftawar ido, hasken ya wuce da ita kamar walƙiya..

Inuwa ba ta sauƙa a ko'ina ba sai a tsakiyar gadonta na alfarma, asalin gadon Gimbiya Ayat. Ma'aikatanta da suke can falo ba su ma sani ba, domin a tunaninsu Gimbiya tana ciki tana barci..

Ta zaro ido tana waige-waige, numfashinta yana fita da sauri "Hah... hah...!"

Ta kalli rufin ɗakin, ta kalli jikinta, ta kasa yarda cewa yanzu take sararin sama amma yanzu tana cikin ɗakinta...

Zuciyarta ta fara wani irin bugun sauri, nan take hoton King Diamond ya bayyana a ranta. Ta ji a jikinta cewa shi ne ya cece ta. Duk da cewa King Diamond ba zai iya shigowa cikin fadar ba saboda shingen tsafin dake kare masarautar, amma ya samu nasarar dasa mata tunaninsa da siffarsa a cikin zuciyarta..

Wani irin yanayi mai sarƙaƙƙiya ya baibaye ta. Ta ji tana son yin dariya saboda farin cikin tsira, tana son yin kuka saboda tsoron da ta fuskanta. Ta dafe ƙirjinta inda take jin ɗumin wannan hasken har yanzu, ta raɗa a hankali..

"Nagode... da taimako."

A can wajen masarautar, a saman iska, King Diamond yana tsaye idanunsa suna haske kamar taurari. Ya ji kalmomin da ta faɗa a cikin zuciyarsa, ya gamsu da cewa ya fara samun gurbi a cikin zuciyar gimbiya mafi taurin kai a duniya..

A daidai wannan lokacin, a gefen masarautar Alhamra, King Diamond ya tsaya ya miƙa hannunsa guda zuwa sararin sama. Ya kalli tsuntsayen na'ura na Chief Onyx da suke ta faman addabar mutanen fada..

Ba tare da ya furta uffan ba, sai ya girgiza yatsunsa. Nan take, wasu bakaken harshen wuta na aljanu suka fara tashi daga ƙasa suna bin tsuntsayen nan ɗaya bayan ɗaya.

"Buum! Buum!! Buum!!!"

Tsuntsayen na'urar suka fara fashewa a sararin sama, suna narkewa tamkar tsohon dalma. Duk wani leken asiri da Chief Onyx yake yi ya daukewa gaba ɗaya allon kwamfutocin Pavilion.. haka yake nuna Static..

Robot Z-01 ta sauƙa a filin saukar jirage na Pavilion cikin sauri. Tana taku cikin natsuwa amma akwai alamun damuwa a tattare da tsarin na'urorinta....

Ta bayyana a cikin katafaren falon Chief Onyx, takun ƙafafunta kawai ke tashi. Ta tsaya nesa da shi kaɗan, fuskarta ba ta nuna alamar tsoro ba amma tsarin na'urorinta ya nuna cewa tana cikin yanayi na Internal Error saboda rashin nasarar da ta samu...

Chief Onyx yana tsaye a bakin wata ƙatuwar taga dake kallon daular birnin Pavilion, hannunsa ɗaya riƙe da kofin abin sha na alfarma..ba tare da ya juyo ba yake sauraronta..

Cikin muryarta mai sanyi, Robot ɗin ta fara magana,

"Chief... na kasa kammala aikin. Abin harin ta kuɓuce daga hannunmu a cikin sararin sama. Wani iko dake wuce tunanin na'ura ya ɗauke ta."

Chief Onyx ya yi shiru na ɗan lokaci, iskar dake busawa daga taga tana kaɗa dogon gashinsa. Ba tare da ya kalle ta ba, ya furta cikin murya mai zurfi dake cike da natsuwa da kuma nauyin gaske..

"Yau ne karon farko da kika taɓa kawo mun rahoton gazawarki..."

Jin waɗannan kalmomi daga bakin Chief Onyx ya sa Robot ta sunkuyar da kanta ƙasa da sauri. Duk da cewa ita na'ura ce, an ƙera ta da wani irin tsari na kishin aiki da biyayya ga jagoranta. Sunkuyar da kanta da ta yi ya nuna tsananin rashin jin daɗin yadda ta ba shi kunya a wannan babban aikin da ya sanya ta...

Falon ya sake yin shiru, sai ƙarar tartsatsin wuta dake tashi daga allon kwamfutar dake gefe, wanda ke nuna cewa duk tsuntsayen na'urar da aka tura Alhamra an tawarwatsa su.

Chief Onyx ya ci gaba da kallon waje, amma a ransa ya san cewa wannan yaƙin ya sauya salo. Tunda har akwai wani iko da zai iya ƙwace mutum daga hannun Z-01, to tabbas akwai wani Sarki na daban dake kare Alhamra wanda ba Sarki Nourdeen ba...

✨✨

Ayat tana nan zaune a kan gadonta, ta cire kayan maza ta ɓoye su a yanda take ajiye su.
Ta sanya kayan barci na alfarma na gimbiyoyi, ta zauna tana sauraron ƙarar fashewar tsuntsayen na'urar dake faruwa a waje...

Zuciyarta tana gaya mata cewa daren nan ya zama daren canji. Ta gane cewa akwai mai tsaronta a ko'ina, tana da wani babban masoyi kuma kare-dangi wanda ko shingen tsafi ba zai iya dakatar da tausayinsa gare ta ba. Ta gyara kwanciyarta, tana murmushin da ita kaɗai ta san ma'anarsa, yayin da tsoron Chief Onyx ya fara fita daga zuciyarta....

Gimbiya Zayana jin abinda ke faruwa ba ƙaramin tsorata tayi ba, domin tsawon shekaru abu makamantan haka bai taɓa faruwa ba...

✨✨

Bayan sati biyu da faruwar dambarwar tsuntsaye..

Masarautar Pavilion ta yi tsit. Chief Onyx bai sake turo wani hari ba, kuma bai sake maganar yarjejeniya ba. Amma wannan shirun ya fi kowace ƙarar bindiga tsoratarwa a wurin Sarki Nourdeen. Ya sani cewa Chief Onyx baya hakura, kawai dai yana jira ne ya ga sarki ya nakasa kafin ya karkare shi...

Sarki Nourdeen ya zauna a cikin tsararren falonsa na sirri, yana tunanin ko ya faɗawa Ruma halin da ake ciki ne. Amma nan take ya girgiza kai. Ruma mace ce mai son zubar da jini, ita a wurinta duk matsalar da aka samu kisa ne kawai mafita.

"Idan na gaya mata, to karshen Alhamra ya zo, domin zata tunzura Chief Onyx ya yi abin da ya fi kisa muni,"
sarki ya faɗa a ransa...

Sarki ya kalli Tafida, amintaccensa wanda suke zaune a falon sirri. Ba kowa a wurin don haka maganar sirri ce ta musamman..

"Tafida, wace shawara kake da ita? Kwanaki sun ja, kuma Chief Onyx yana jiran mu,"
Sarki ya faɗa cikin muryar damuwa..

Tafida ya gyara zama, ya dube sarki ido-da-ido..

"Ranka ya daɗe, abu ɗaya nake tunanin shine mafita... Me zai hana ka kai masa Yumna?"

Sarki ya ɗago a ruɗe, zuciyarsa ta buga.

"Yumna kuma? Kana nufin Yumna ɗiyar da kowa ya ɗauka tawa ce?"

Tafida ya jinjina kai, "Tabbas. Shi Chief Onyx bai san ta ba, tun tana ƙarama rabonsa da ita. Ba zai taɓa gane cewa ƙanwarsa bace ta jini. Idan ma mugunta yake son yi wa 'ya'yanka, to sai dai ya yi wa ƙanwarsa a rashin sani. Kuma tunda ita tafi kowa sanyi da biyayya, zata iya zama da shi ba tare da ta jawo maka matsala ba."..

Sarki ya jinjina kai, ransa ya ɓaci da tunanin yadda zai kalli Yumna ya ce ita zai kai...

"Amma Tafida, kowa ya ɗauka 'yata ce. Babu wanda ya san cewa ba daga cikina ta fito ba. Idan na ba shi ita, ba ka ganin wata rana gaskiya zata fito?"

Tafida ya yi murmushin kwantar da hankali.

"Ranka ya dade, wannan shi ne asirin da zai kare ka. Ta zama personal maid ɗinsa, amma a asali ita kanwarsa ce. Idan ya cutar da ita, ya cutar da jininsa. Idan ya so ta, ya so kanwarsa. Kuma hakan zai sa ya daina neman sauran 'ya'yanka."

Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya gamsu da wannan dabarar koda yake zuciyarsa tana masa nauyi..

"Shikenan Tafida. Shirya yadda za a sanar da ita, amma kada wani ya san asalin gaskiyar nan."..

Tafida ya ce,

"Baza'a sanar da ita ba, kawai za'a kaita a matsayin bata san meke faruwa ba, da zaran an kaita acan zata ji dalili..."


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment

*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

⚠️ SANARWA⚠️

Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 1️⃣6️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Bayan sati biyu na jinya a ƙasar Indonesiya, Maayah ta dawo Alhamra cikin ƙoshin lafiya, Kowa ya yi murnar ganinta amma murnar ta fili ce, domin a zuci kowa akwai abin da yake saƙawa. Sarki Nourdeen ya shigo ya nuna farin cikinsa, duk da cewa ransa rabi yana kan shirin tura Yumna Pavilion ne...

Maayah tana zaune a kan kujera ta alfarma, tana nuna isa, yayin da Yumna take zaune a gefenta tana mata hidima...

Sai ga Gimbiya Ayat ta shigo, sanye da riga ta alfarma wadda aka ƙawata da zaren zinare, kanta rufe da mayafi mai tsada wanda ya fito da kyan idanuwanta domin tana rufe da rabin fuska ne kamar yanda ta saba. Saratu tana biye da ita a baya tana taku cikin ladabi. Babu wanda zai kalle ta ya yi tunanin ita ce wannan dakare wato Inuwa...

Ta samu wuri ta zauna kusa da gadon Maayah,

"Sannu da dawowa Maayah. Allah ya ƙara miki lafiya. Yi haƙuri da baki ganni ba kafin ku tafi, jikina ne ya ɗan yi tsami a lokacin."

Maayah ta gyara kwanciya tana yatsina fuska.
"Ba komai Ayat. Na san ai ke baki cika son shiga harkar mutane ba, sai dai idan abin ya shafi Chingching..."

Ayat ta kalleta cike da mamaki a ranta tace, "wato yanzu an daina respect, ba Auntyn ma..."

Zayana ta tura ƙofa ta shigo kamar iska, sanye da wata riga 'yar kanti dake nuna asalin jinin baturiya. Ta kalli Ayat ta taɓe baki, sannan ta kalli Maayah...

"Oh... ashe duk an taru a nan? Maayah, naga kin dawo kina taku kamar ba ke ce kika kusa zama gurguwa ba. Amma dai ina fata jinyar Indonesiya ta rage miki wannan girman kan, ko kuwa?"

Maayah cikin zafi ta ce,

"Zayana, idan girman kai gado ne, ai na gada ne. Kema kinsan cewa ko ana ruwa ana iska, ni ce gimbiya ta musamman a masarautar nan, dube ni jinin Hindu.... Kuma naga har yanzu baki daina sanya waɗannan kayan turawan naki ba marasa lissafi kamar wata Christian, ko kina nufin baki ɗauki kanki a matsayin 'yar masarautar Alhamra ba ne?"

Zayana ta kalli Ayat duk da baƙin cikin da Maayah take ƙunsa mata

"Ke kuma Ayat, kullum kina nan cikin shiru-shiru kamar ruwan sanyi. Amma kowa yasan ruwan sanyi shike cin uwar tulu. Me kike ta saƙawa a ranki ne da har kike wasu maganganu a ranki?"...

Ayat ta ɗago idanunta masu kaifi ta kalli Zayana..

"Kin san me take faɗa a raina kenam? Zayana, shiru na ba tsoro ba ne, kuma magana ta ba sirri ba ce. Kawai dai na fi son in ga mutum ya yi magana cikin hankali maimakon ya dinga surutu kamar mahaukaci... Ke kullum burinki ki ga kin ɓata wa kowa rai, amma ki sani, kyan mace ba a tsayin riga yake ba, a natsuwar zuciyarta yake."

Maayah ta katse su da cewa,

"Dakatar da wannan surutun..!
Zayana, kada ki zo nan ki nemi raina mana hankali. Idan mahaifiyarki tana da iko a ƙasarsu, nan Alhamra ce......Kuma Ayat kada ki yi mana wani bayanin natsuwa, domin natsuwar mace ita ce ta san yadda za ta kula da ƙannenta, ba wai ta keɓance kanta kamar wata mayya ba."..

Zayana ta yi dariya ta rainin wayo..

"Lallai Maayah, kinsan yadda ake jifan magana. Amma fa karki manta, a cikinmu duka, ni ce mahaifina yake tsoro. Don haka kowa ya kiyayi harshensa, domin kalma ɗaya zan faɗa, gobe ku tsinci kanku a gidan kurkuku!"...

A gefe guda, Yumna tana zaune tana kallon yayyen nata. Zuciyarta tana mata zafi. Su suna faɗa akan iko da nuna isa, amma ita tana jin wani irin kewa aranta... Ta kalli Ayat, ta kalli Maayah, sannan ta kalli Zayana. Ta yi tunanin cewa wata rana fa bazasu kasance da juna kamar haka ba, sai sunyi kewar junansu...

Yumna cikin sanyin murya ta ce,

"Aunty Zayana, Aunty Ayat, don Allah ku bar wannan maganar. Muna farin cikin dawowar Aunty Maayah ne, kada mu sanya taron ya zama na kuka.".

Maayah ta ce,
"Ke dai Yumna yi shiru. Shirun naki ne ya sa kowa yake raina miki hankali a gidan nan!"..

Zayana ta tsaya na takaitaccen lokaci, ta kai wa Yumna wani irin kallo na alfarma.

"Ke kin ciri tuta, Yumna... Saboda kina ba ni darajata kuma kina girmama ni, don haka ke tawa ce. Sauran kuma, sai dai su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login