Showing 24001 words to 27000 words out of 154131 words

Chapter 9 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

"Da gaske nake mana Gimbiya. Tun ɗazu yake can ya shimfiɗa dadduma yana duba littafansa."

Yumna ta miƙe da sauri, ta umarci bayin su gama shiryata cikin gaggawa. Allah ya jarrabe ta da tsananin son wannan Malamin nata, wanda yake koyar da ita karatun boko da na Larabci a wani tsararren lambu dake gefen sashenta...

Malamin, wanda kyakkyawan Balarabe ne mai farar fata da dogon hanci, yana da sanyi da sauƙin kai. Sai dai babban abin tashin hankalin shi ne, shi kansa Malamin bai sani ba cewa Gimbiyar dake koyon karatu a hannunsa tana ƙaunar sa fiye da komai. A wurinsa ita Gimbiyarsa ce mai girma, a wurinta kuwa shi ne rayuwarta...

Yumna ta isa lambun, ta tadda Malam zaune a kan dadduma, ya sa fararen kaya ya naɗa rawanin Larabawa. Ta ƙaraso tana tafiya a hankali don kada ya fahimci yadda take jin nauyinsa..

"Assalamu Alaikum, Malam. Ina fatan ban daɗe ba?"

Ya ɗago ya kalle ta da idanunsa masu kwarjini, sannan ya yi murmushi mai sanyi
"Wa'alaikumussalam Gimbiya Yumna. A'a, yanzu ma na ƙaraso. Ki zauna mu fara da karatun Larabcin tukunna kafin mu koma na Turanci."

Yumna ta zauna a kusa da shi, ƙamshin turaren sa ya fara buge ta. Ta buɗe littafi amma idonta yana kan yatsunsa dake nuna mata haruffan...

"Gimbiya, wannan kalmar ana ƙiranta 'Al-Hubb'. Kin san ma'anarta kuwa?"

Yumna ta kalli Malam, fuskarta ta yi jawur, ta ce a ranta

"Kamar ka san abin dake cikin zuciyata..." Amma a fili sai ta ce "A'a Malam, meye ma'anarta?"

Cikin muryar natsuwa ya ce,
"Ma'anarta ita ce Soyayya. Ita ce jigon rayuwa."

Yumna ta sauƙe ajiyar zuciya, tana kallon kyakkyawar fuskar Malamin da take matuƙar so, yayin da asalin soyayyar take a ɓoye a tsakaninsu.

A cikin masarautar Alhamra, kowace Gimbiya tana da nata malamin da yake zuwa har sashenta don koyar da ita, domin kiyaye mutuncinsu da kwarjininsu...

Malam ya lura da yadda Yumna take ta murmushi tun farkon zaman, ya gyara zama sannan ya kalle ta cikin natsuwa ya ce..

"Sarkin murmushi, idan kin gama murmushin, sai ki sanar da ni a wace ayar kika tsaya a karatunmu na Kur'ani. Kin san mun yi nisa sosai."

Yumna ta ɗan sunkuyar da kanta, tana jin wata irin kunya mai daɗi. Ta buɗe babban littafin dake gabanta sannan ta ce..

"Malam, mun kusan kammala suratul Baƙara gaba ɗaya. Na kusa na yi sauƙar Alkur'ani mai girma."

Malam ya jinjina kai cikin gamsuwa da farinciki, ya ce..

"Haka ne Gimbiya. Kin mayar da hankali sosai a kan karatu, kuma hakan babban abin alfahari ne. Yanzu sauran mana shafi uku kacal mu kammala wannan surar. Yanzu za ki iya karanta min daga inda muka tsaya, sai na ƙara miki wani karatun ko?"

Yumna ta gyara zama, ta nutsu, sannan ta fara karatun cikin muryarta mai sanyi da zaƙi wadda take sa natsuwa a zuciyar duk wanda ya ji ta. Karatun nata ya fito ne daki-daki, ba tare da kuskuren tajwidi ko na haruffa ba...
Yayin da take karantawa, Malam ya zuba mata ido, yana sauraron yadda haruffan suke fita. Duk da cewa malami ne shi, a wannan lokacin ya ji wani irin kwarjini da natsuwa sun mamaye shi. Ya fara jin cewa wannan ɗalibar tasa tana da wani sirri na musamman dake sa karatun nata ratsa ko'ina.
Ita kuwa Yumna, tana cikin karanta kalmomin Allah, amma a gefen zuciyarta tana jin daɗin yadda Malam yake sauraronta cikin kulawa. Lambun ya yi shiru, sai sautin muryarta da kukan tsuntsaye dake rera waƙa a saman bishiyoyi....

✨✨✨

A sashen Chingching, baccin daɗi take sha, domin ita a rayuwarta ba abin da take so irin bacci...
Altine ta shigo ɗakin, ta daɗe tana jijjiga ta..

"Gimbiya, tashi Malam ya zo yana jiran ki!"

Chingching ta turo baki, ta koma ta nade a cikin bargo. Sai da aka sha fama da ita, kafin Altine ta samu ta sanya mata dan madaidaicin hijab dinta. Ganin yadda Chingching ta ki takawa da kafarta, dole Altine ta goyo ta a bayanta har zuwa lambun da Malam ke jira...


Malam dake ustaz ne mai kamala da uban gemu mai tsawo da sheki, ya gyara zama bayan an dire Chingching a dadduma. Ya kalle ta ya ce..

"Gimbiya, a ina muka tsaya da karatunmu?"

Chingching ta kalli fuskar Malam, ta yi fari da ido ta ce.
"Malam ai mun tsaya a wurin da Malam ya aske gemunsa!"

Malam ya ji tamkar ya nitse, ya kalle ta cikin mamakin shiriritar dake kanta..

"Kur’ani nake tambayarki Gimbiya, ba zancen gemuna ba. A ina muka tsaya?"

Ta yamutsa fuska, "Yoo Malam ni na manta, gaya min farkon sa."

Malam ya girgiza kai, "Ba kina Suratul Anbiya'i ba?"

Ta jujjuya idanu tamkar mai tunani, daga bisani ta ce,

"Ehh, haka ne ashe!"

"To karanta min daga inda kika tsaya," in ji Malam..

Chingching ta sake cewa,
"Me ma farkon ayar?"

Bayan Malam ya karanto mata farkon ayar, sai Chingching ta tashi ta daka wani tsalle na farinciki tana ihu, sannan ta dawo ta zauna. Abun mamaki tana farawa sai ta karanta karatun tsaf, babu gyara ko guda ɗaya duk da shiriritar dake kanta...

Malam ya yi murmushin jindadi, ya bude shafin littafin don ya kara mata karatu....
Yana fara karantawa, ita kuma Chingching ta ƙura wa gemunsa ido. Gemun yana ta motsi sama da ƙasa yayin da Malamin yake karatu, gashi yana ta sheki...

Chingching ta fara dariya ƙasa-ƙasa. Duk sanda Malam ya sunkuyar da kansa yana karatu, sai ta kai hannu tana shirin taɓa gemun. Da zarar Malam ya ɗago kai, sai ta janye hannunta da sauri tamkar ba ita ba. Haka ta yi ta yi, tana wasan ɓuya da gemunsa.
Ana karshe ne, tana ganin Malam ya nutsu a cikin karatun, sai ta kai hannu ta damƙe gemun gaba daya ta jawo shi da karfi!..

Malam ya saki wata irin kururuwa, jikinsa ya ɗauki rawa..

"Ke meye haka! Sake min gemu! Nace ki sakar min gemu kar ki cire min! Baki da hankali ne? Zaki cire min gemu! Innalillahi wa inna ilaihir raji'un... Kin kashe ni!"

Ta saki gemun, ta faɗa ƙasa tana kwashewa da dariya. Ta riƙe cikinta tana birgima a kan dadduma, har hawaye ya fara zubo mata tsabar dariya...

Malam ya zauna cikin kalar tausayi, yana shafa gemunsa dake masa zafi, yana kallon yadda wannan yarinyar take tamkar ba ta san zafin da ya ji ba. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, har zuciyarsa ya ji ya gaji da koyar da ita, domin kowace rana da nata sabon iskancin take zuwa...

Bayan Chingching ta gama dariyar ta gyara zama tana kallon Malamin cikin yanayin natsuwa na karya, ta ce,

"To Malam, mu ci gaba mana..."

Malam ya sauƙe ajiyar zuciya, amma saboda tsaro sai da ya sanya hannunsa na hagu ya danne gemunsa sosai, gudun kada ta sake damƙe shi. Ya fara karanta mata ayoyin Kur'ani cikin muryar raɗa, yana sa ido a kanta.

Chingching tana sauraron karatun kamar wata shiryayya, har Malam ya fara tunanin yau ta nutsu. Kwatsam! Sai idonta ya sauƙa a ƙasan hantsar wandonsa. Sakamakon yadda Malamin ya naɗe ƙafafunsa a kan dadduma, rigarsa ta ɗan janye, sai ga hantsar wandonsa ya yage ta ciki, inda wani abu ya ɗan fito ya yi ƙulƙule...

Chingching ta zaro ido, ta dafe baki tana faɗin,

"Ah ah ahh ahhh! Me zan gani haka?!"

Malam ya tsagaita da karatun, ya ɗago yana kallonta cikin shakku..

"Meye ya faru kuma Gimbiya?"

Ta duƙar da kanta tana maƙale dariya, "Ba... ba komai Malam, ci gaba kawai."

Malam ya ci gaba da karatu, amma ina! Chingching hankalinta ba ya kan karatun, tana ta leƙe-leƙen wannan wurin da ya yage. Dariyarta ta fara cin ƙarfinta, tana ƙoƙarin danne ta amma abin ya faskara. Lokaci guda ta fashe da wata mahaukaciyar dariya tana karkarwa..
Ta miƙe tsaye tana zagaye daddumar, tana ihu tana dariya har tana neman faɗuwa. Malam kam ya kusa fashewa da kuka tsabar takaici. Ya ce.

"Wai me yake faruwa ne? Idan ba kya son karatun, sai na tashi na tafi na bar miki fadar!"

Cikin dariya da gurguwar magana, Chingching ta dawo ta zauna, tana faɗin

"Yooo Malam, ina karatu zai yiwu ina hango ɗan tulu a tsakiyar wandonka... Kuma wandon ya yage!"

Malam ya firgita, ya yi maza ya gyara zamansa yana rufe wurin. Chingching ta ƙara kwashewa da dariya..

"Malam! Maganin meye ne sa tumatur a tsakiyar wandonka ta ciki? Na ga ya yi ƙulƙule kamar tumatur, kamar kuma dankali... Kai, dankali ne ma! Wallahi dankali ne!"

Malam ya ga cewa idan ya ƙara minti ɗaya a wurin, to mutuncinsa zai zube ƙasa warwas. Ba tare da ya ce uffan ba, ya kwashe littafinsa da sauri-sauri, ya miƙe ya fara sauri yana ficewa daga sashen...

Chingching tana biye da shi da dariya tana kwala masa kira

"Malam mai ɓerarren wando! Ga kuma ƙaton dankali a ciki! Malam ya ɓoye dankali a wando!"..

Ta zube a ƙasa tana dariya sosai, yayin da Altine dake gefe ta rasa ko za ta yi dariya ko za ta yi kuka saboda kunyar abin da Auta ta yi wa ustaz....


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

⚠️ SANARWA⚠️

Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 9️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*


Ba zato ba tsammani sararin samaniyar Alhamra Kingdom ya sauya launi... Wata irin nutsuwa ta ba-zata ta mamaye garin, nutsuwar da ta fi karfin hankali...Tsuntsayen da suke ta rera waƙa a saman bishiyoyi duk sun yi shiru tamkar an zare musu rai... Iskar dake kaɗawa ta tsaya cak. Mutanen gari ne suke ta rarrabe idanu, kowa ya ji a jikinsa cewa akwai wani abu mai nauyi dake tunkaro su...

​Daga can nesa aka fara jin wani irin tafiya na musamman, kwatsam sai ga jerin motocinsa sun bayyana a ƙofar gari.. Motoci ne bakake wuluk waɗanda babu irinsu a faɗin duniya, sheƙinsu kaɗai ya isa ya makantar da idon da ya ƙura musu...
​Ba mutum ɗaya ba, ba goma ba motocinsu sun fi hamsin, suna taho wa a jere tamkar kyanwar daji...
A cikin kowace mota, akwai zafafan Bodyguards sanye da baƙaƙen kaya irin na jami'an tsaron Amurka... Fuskokinsu a murtuke, idanunsu sanye da bakaken gilashi, ba sa kallon dama balle hagu...

​Wannan runduna ta Pavilion Kingdom ba wasa ta zo yi ba. A hannun kowane soja dake kan motocin, akwai wasu zafafan bindigu waɗanda kallo ɗaya zaka yi musu kasan cewa na zamani ne. Ga wasu dogayen takuba a kugunsu masu sheƙi tamkar madubi, waɗanda ke nuna cewa idan aka zaro su, to jini ne kawai zai mayar da su dauɗarsu...

​Duk waɗanda suka kalle su a cikin garin Alhamra, sai da ya daskare a inda yake. Waɗanda suke jin labarin Pavilion kawai a matsayin tatsuniya, yau sun ga zahiri.. Kowa ya tsorata, tsoron da ya sa numfashi ma ya zama wahala.

Kai tsaye ​rundunar ta shine cikin babban masarautar, sun jeru tin daga bakin fada har zuwa babban gate...

Babban jami'in dake jagorantar aiken ya fito, ya shige cikin fadar sarki ya miƙa wata wasiƙa mai ɗauke da tambarin Pavilion, wani tambari mai kwarjini da firgitarwa...

​A cikin fada, Sarki Nourdeen ya miƙe tare da karɓan wasikar da hannu biyu, amma yana buɗewa idanunsa suka firfito, hannunsa ya fara karkarwa. Sakon a gurguje yake amma yana da nauyin dake iya rushe masarauta...

_​"Ina nan tafe. Zan shigo ƙasarka ta Alhamra City nan ba da daɗewa ba. Lokacin cika yarjejeniyarmu ya yi."_

​Sarki ya sulale ya zauna a kan kujerarsa ta sarauta, gumi ya fara keto masa duk da sanyin dake wurin.. Tsoronsa daya shine yarjejeniyar Sirri dake tsakaninsa da Pavilion. Lokaci ya yi, kuma Sarkin Pavilion ba ya yafe alkawari...

​Ya kalli fadawansa waɗanda kowanne ya zama mutum-mutumi saboda tsoro. Idan har waɗannan ma’aikatan aike ne kawai kwarjininsu ya kai haka, ina ga shi kansa Ogan? Mutumin da sunansa kaɗai ke sanya sarakuna su rasa baccinsu..

​Masarautar Alhamra ta shiga cikin duhu, kowa ya san cewa babban yaƙi ko babban canji yana nan tafe...


​A sashen Gimbiya Aayat, tana zaune a babban falonta cikin shigar alfarma na sarauta, tana cin fruits a nutse tana ƙoƙarin danne damuwar takurar da ma'aikatanta suke mata... Kwatsam, sai ga wani ma'aikacinta ya shigo a guje, ko neman izini babu jikinsa na rawa tamkar wanda aka yi wa bushara da mutuwa..

​"Ya ke Gimbiyata, a gafarce ni! Wannan yanayin na yau ya girgiza kowa, hatta sarki kansa!"..

​Ayat ta ji gabanta ya faɗi... Idan har mahaifinta, babban zaki na Alhamra ya girgiza, to lallai al'amarin ba karami ba ne. Cikin dake wa ta ce, "Me yake faruwa?"

​"M... mu... mutanen Pavilion Kingdom ne suka zo!"

​A zabure Ayat ta miƙe, tana zazzaro manyan idanunta...
"Pavilion Kingdom?"
Ta maimaita cikin rawar murya. "Shi da ake jinsa a cikin littafin almara da labaran tsoro, yau ya tabbata a cikin wannan masarautar?"
Zuciyarta ta fara bugawa da sauri, tana tunanin ko wane irin asiri ne ya kusa bayyana haka...

✨✨✨

​A can ɓangaren Gimbiya Maayah, tana kan electric treadmill tana gudu sosai. Gumi ya jiƙe mata jiki, gashinta ya bazu a baya.. Ba wai don lafiyar jiki kaɗai take wannan gudun ba, tana gudu ne don ta tsira daga tunanin Inuwa da kuma damuwar dake cunkushe a zuciyarta.
​Kowane taku dake bugawa a kan injin, tamkar yana rage mata zafin kishin dake ranta ne. A kan wannan injin, Maayah ba gimbiya bace, mace ce kawai dake neman sauƙi a cikin azabar tunani.

​Tana tsaka da wannan gudun, sai ga Mama Liyatu ta shigo wurin a guje, tana ƙwala kira..

"Gimbiya! Gimbiya!! Gimbiya!!!"

​Maayah ba ta ko kalle ta ba, ballantana ta amsa, tana jin daɗin yadda gudun yake ɗibar mata kewa. Amma jin furucin Mama Liyatu na gaba ya sa jinin jikinta daskarewa..

"Kin ji labarin mutanen PAVILION KINGDOM sun shigo cikin masarautar nan kuwa?!"

​Jin sunan Pavilion, Maayah ta firgita, ta nemi ta tsaya cak cikin tsoro, ta manta cewa tana kan injin dake gudu a kan high speed. Ba ta danna maballin dakatarwa ba, nan take injin ya wurgar da ita sama, tayi gaba ta faɗo ƙasa da ƙarfi!

Wani uban ƙara ya fito daga bakinta yayin da bayanta da ƙunkuminta suka daku a kan tattausan darduma mai tauri.. Faɗuwar ba ƙarama bace, domin numfashinta ne ya kusa ɗaukewa na ɗan lokaci..

​Mama Liyatu ta kwala ihu, ta yo kanta da gudu tana kiran sunanta. Maayah tana kwance tana murƙususu, azabar dake jikinta ta haɗu da tsoron jin sunan Pavilion ya sanya ta rasa inda za ta sa kanta..

​Duk girman kan Maayah da izzarta, yau gwiwoyinta sun yi sanyi. Zuwan mutanen Pavilion ya canja komai a cikin mintuna kalilan....

✨✨

​A sashen Gimbiya Yumna, tana tsaye a cikin kitchen tare da wasu ma'aikatanta, domin Yumna mutum ce mai sauƙin kai da son mu’amala da na ƙasa da ita. Tana tsaka da yanka kayan marmari a kan tray, tana murmushi, sai ga wata baiwa ta shigo falon kitchen ɗin a guje tana haki.

​"Gimbiya kallo ya barki! Yau mutanen Pavilion Kingdom ne suka zo cikin masarautar nan!"

​Wani irin bugawa zuciyar Yumna ta yi, ta ji wani jiri ya ɗibe ta. Ba ta san lokacin da wuƙar hannunta ta suɓuce ba, ta yanke mata yatsa. Jini ya fara zuba amma Yumna ba zafin yankan take ji ba, zafin sunan da ta ji ne ya ratsa kowane sashi na jikinta. Ta ajiye wuƙar, ta juyo idanunta tab da hawaye. Hawaye ne na farin ciki da tsofaffin tunani dake ƙoƙarin dawowa...

​Ganin yadda take kuka, sai baiwar ta ƙara da cewa..

"Amma Gimbiya, mutanensa ne kawai suka zo, shi Sarkin Pavilion bai bayyana kansa ba, saƙo kawai suka kawo."

​Nan take farin cikin Yumna ya dashe, murmushin dake ƙoƙarin bayyana ya koma ciki. Ma'aikatan suka zagaye ta cikin damuwa, suka ɗauki auduga da magani suka treat ɗin yatsarta da ta yanku, sannan suka raka ta har bedroom ɗinta don ta huta.

​Bayan ma'aikatan sun fita, Yumna ta tabbatar ta kulle ƙofar ɗakin. Ta nufi wani sashe na drawer ɗinta dake ɓoye a gefe guda, ta buɗe ta da rawar hannu. Ta zaro wani ƙaton hoto wanda aka adana shi da matuƙar kulawa..
​Hoton wani tsararren sarki ne, kyakkyawa na gaske, fari mai kwarjini, sanye da kayan sarauta waɗanda aka ƙera su da gold.
A gefen damansa akwai wani kyakkyawan yaro, haka a gefen hagunsa akwai wani yaron, twins ne maza waɗanda kyawunsu ya kusan ninka na mahaifinsu...
​Amma babban abin da ya sa Yumna fashewa da kuka shi ne hoton wata ƙaramar yarinya, wacce ba za ta wuce shekara biyu ba, tana zaune a kan cinyar sarki a tsakiya. Wannan yarinyar ba kowa bace face ita kanta Yumna...

​Yumna ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, kukan da ta daɗe tana tura shi a can ƙasan zuciyarta. Ta fara shafa fuskokin twins ɗin da mahaifin dake cikin hoton da yatsunta dake ɗauke da bandage..

​"Kun kusa dawowa? Ko kuwa ni ce zan dawo gare ku?"
ta faɗa cikin muryar kuka.
​Ta ɗaga hoton ta rungume shi a ƙirjinta tana jin tamkar tana rungumar mutanen dake cikinsa ne. Wannan hoton shi ne kaɗai dangantakarta da asalin inda ta fito..

✨✨✨

Sashen Gimbiya Zayana

Lokacin da aka sanar mata, ta tsorata amma bata nuna hakan ba, ta yanke hukuncin zuwa yanda suke tayi ido huɗu da su....

A koda yaushe zuciyarta tambaya take waye Pavilion king? Meyasa yake ɓoye kansa sai dai labarinsa..

Saboda tsoron da ma'aikatanta suke basu sanar mata cewa shi bai zo ba, iya mutanensa ne...

Yayin da Gimbiya Zayana take takawa cikin fadar, idanun kowa na kanta. Wata baiwa mai suna Ladi ta yi kuskuren ƙura mata ido na wasu daƙiƙoƙi. Zayana ta tsaya cak, ta juyo a hankali, idonta ya sauƙa kan baiwar..

​“Ke,”

Zayana ta furta da murya kamar sauƙan aradu...

“Idan kina da abin faɗa, ki faɗa. Idan kuma kallon kike, ki tabbatar kallo ne na ƙarshe.”

​Ladi ta durƙusa da sauri, jikinta na rawa. “Af...afuwa nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login