Showing 105001 words to 108000 words out of 154131 words
Chapter 36 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
tsaye. Takunta na nuna cewa ita asalin sarauniya ce ta jini. Ta zo har gabansa, ta tsaya tana kallon kwayar idonsa..
"Saboda ni kaɗai ce matarka. Zan nemi na biya maka haƙƙinka na ma'aurata, duk da muna ɗaukan lokaci ba mu haɗu ba."
Sarki ya jinjina kai, ya ja dogon numfashi. Akwai nauyi a muryarsa yayin da yake magana..
"Uhm! Kin ƙi komawa cikin masarautata wanda asalin nan ne ya fi dacewa da ke, ko don saboda ƴarki, amma kin zaɓi nan. Hakan ba laifi ba ne don na biyo ki a matsayin miji na kuma karɓi haƙƙina na aurena da ke... Amma babban abinda zai ƙara shiga tsakanina da ke, wanda zai hana na biya miki haƙƙinki a matsayin mata, shine bijire wa Musulunci. Kin yaudare ni, kin karɓi Musulunci saboda ki aure ni, amma bayan haka kika koma addininki."
Ruma ta ɗaga hannu, ta dakatar da shi cikin sauri. Fuskarta ta canza daga murmushi zuwa ɓacin rai na lokaci guda..
"Ka daɗe kana nanata wannan maganar har na fara gajiya. Muna zaune ne a matsayin ma'aurata, ba wai maganar addini ba. Kowa ya riƙe addininsa mana! Kuma ba za ka taɓa barin wannan fadar tawa ba har sai ka biya min haƙƙina na matarka. Kuma muddin ina raye, ba za ka taɓa kasancewa da wata mace ba bayan ni."
Sarki Nourdeen ya zuba mata ido. Ya san halin Ruma, idan ta ƙafe a kan abu, to babu mai iya canza ta. Sun daɗe suna samun matsala akan maganar Musulunci, amma tana amfani da kyawunta da muryarta wajen tursasa shi. Duk da ɗacin ransa akan addini, sarki ya san cewa a fannin sha'awa da biya wa juna haƙƙi, Ruma ta dabance.
Sannan, ya gwammace ta zauna a nan Sydney tana mulkin mutanen mahaifinta, domin muddin Ruma tana cikin fadar Alhamra, to masarautar haukacewa take yi saboda kishinta da muguntar da take yi wa kowa..
Bayan kammala cacar baki akan maganar addini, Ruma ta sauke numfashi, fuskarta ta koma cike da lallausan murmushi mai nuna kissa. Ta matso kusa da Sarki, ta fara shafa ƙirjinsa a hankali da yatsunta masu sanyi, tana lallashi da sarrafa shi yadda ta saba..
Sarki ya zuba mata ido, duk da yana jin shauƙinta na ratsa shi, amma akwai wani abu da yake damunsa. Ya dakatar da hannunta na ɗan lokaci, ya kalle ta sosai.
"Ba ki da labarin Chief Onyx ya ɗauke min Auta? Na ji kin yi shiru ba ki yi min magana a kai ba... ko ba ki damu ba ne?"
Ruma ta yamutsa fuskarta ta nuna rashin damuwa ƙarara, ta janye hannunta daga ƙirjinsa na ɗan lokaci kamar ana maganar abin da bai shafi rayuwarta ba.
Cikin isa da halin ko-in-kula ta ce,
"Ƴarka aka ɗauke, ba ƴata ba. Don haka jininka, jininka ne, bai shafe ni ba. Jinina guda ɗaya ce a masarautarka wato Zayana, kuma ba ita aka taɓa ba balle na yi magana a kai. Saboda haka, wannan damuwarku ce kai da shi... ai ɗan uwanka ne."
Sarki Nourdeen ya ja dogon numfashi, ya ji raɗaɗin kalaman nata. Ya san Ruma ba ta da tausayi, amma bai yi tsammanin rashin damuwarta zai kai ga haka ba, musamman sanin cewa Chief Onyx ɗan uwansa ne kuma babban makiyinsa..
Duk da haka, kwarewar Ruma wajen sarrafa mace da namiji ba ta bar sarki ya tsananta fushin ba. Ta sake matsowa, ta rungume shi, tana busa masa sanyayyar iskar numfashinta a wuya. Ya fahimci cewa tana fama da tsananin shauƙi da kewarsa da ta daɗe tana ciki...
A wannan daren, dukkan wata takaddama ta addini da ta siyasar masarauta aka ijiye ta a gefe. Fadar ta yi tsit, sai dai ƙarar iska dake kaɗawa a waje. A cikin wannan babban sashi na Sarauniya Ruma, sarki ya kasance da matarsa a matsayin ma'aurata, inda suka nuna wa juna shauƙi da aka daɗe ba a yi ba.
Duk da sarki ya san cewa gobe idan ya tashi, matsalolin Alhamra suna jiran sa, amma a daren nan, ikon Ruma da kyawunta sun yi nasara akan duk wani damuwarsa...
Bayan gari ya waye, sarki yana shirin barin Sydney don komawa Alhamra.. Ruma tana kwance tana kallon sa yayin da yake shirin sa na sarki..
Ta furta "Nourdeen, ka tabbatar ka kula da Zayana. Idan na ji wani abu ya same ta, zan iya rusa Alhamra don ganin na maido ta nan."
Sarki bai ce komai ba, ya gyada kai kawai, ya fice daga sashen ya bar ta a nan tana mulkan mutanenta na Sydney, yayin da shi kuma ya nufi filin jirgi don fuskantar rikicin da ya bari a gida...
Bayan jirgin Sarki ya tashi daga Sydney, ya ba wa matuƙan jirgin umarnin sauya hanya.
Ya dai sanar wa Ruma cewa zai koma Alhamra amma a zahiri ba Alhamra zai koma ba..
Kai tsaye Indiya dake birnin Mumbai ya nufa.
A nan, Sarki yana da wani katafaren gida wanda aka gina shi cikin sirri, kewaye da lambuna masu ban sha'awa, nesa da idon duniya..
Wannan gidan shi ne Zindanin Zinariya na Sarauniya Hibba... Hibba mace ce kyakkyawa, fara ce mai kalar jinin Indiya, tana da dogon gashi baƙi wanda yake sheƙi, da idanuwa masu zurfi dake nuna tsantsar baƙin ciki..
A zamanin da Hibba take Alhamra, fadar ta zama tamkar filin daga. Hibba ba ƴar sarauta ba ce, amma tana da jinin girman kai na ƴanci.
Ruma tana so ta mulki Hibba kamar baiwa..
Hibba kuma ta nuna mata cewa ita ma mace ce mai matsayi a gaban Sarki..
Hakan yasa jininsu bai haɗu da Ruma ba..
Ta rabu da sarki sakamakon rashin zaman lafiya..
Ruma ta tsane ta sosai, hakan yasa kullum faɗa ita da Ruma a masarautar Alhamra..
Kullum Ruma tashin hankalinta shine Sarki ya saki Hibba..
Ruma har sawa take akai mata farmakin kisa, sau biyar ana zuwa kasheta amma take tsira daƙyar..
Anan ne ta tayar wa Sarki hankali akan ya sake ta bazata iya zama a kashe ta ba..
Domin lamarin Ruma yafi ƙarfinta..ba za ta iya kishi da ita ba...
Don kare rayuwarta, Sarki ya shirya wasan kwaikwayon cewa ya sake ta, sannan ya ɓoye ta a Mumbai. Ruma tana tunanin ta yi nasara, ashe Sarki har yanzu yana tare da matarsa ta uku....
🥀
Sarki ya shiga gidan shiru, ya tarar da Hibba a cikin lambu tana kallon faɗuwar rana. Ta ji takun takalmansa, amma ba ta juyo ba. Ta san shi ne...
Sarki ya furta
"Hibba, ina fatan kina lafiya?"
Hibba ta juyo, fuskarta ba annuri. Kyawunta ya ƙara fitowa duk da ramar da ta yi saboda damuwa..
"Lafiya? A cikin wannan kurkukun da ka gina min? Ka raba ni da ƴata Maayah, ka raba ni da kowa, ka mayar da ni tamkar gawa mai numfashi don kawai kana tsoron Ruma."
Sarki ya matso kusa da ita, yana ƙoƙarin taɓa hannunta amma ta kauce.
YA ce, "Na yi hakan ne don in kare rayuwarki, Hibba... Ruma mace ce mai haɗari..."
Cikin ɗacin rai ta ce,
"To idan har ba za ka iya kare ni a matsayin sarki ba, me ya sa ba za ka sake ni ba? Na gaji, Nourdeen! Na gaji da wannan rayuwar sirrin. Ka sake ni, in tafi in yi aurena cikin kwanciyar hankali, in samu rayuwar da nake so."
Jin kalmar "Aurena", sai idanun Sarki Nourdeen suka sauya launi. Wani irin kishi mai zafi ya lulluɓe shi. Ya damƙi kafaɗunta, yana kallon cikin idanunta da wani irin kwarjini na tsoro..
YA furta,
"Kada ki sake furta wannan kalmar! Ba za ki taɓa zama da wani namiji ba bayan ni. Muddin ina numfashi, ke tawa ce, ko a cikin sirri ko a fili. Babu wani namijin da ya isa ya kalle ki balle ya taɓa ki!"
Hibba ta fashe da kukan takaici...
"To me kake so da ni? Ka hana ni ƴata, ka hana ni rayuwa. Maayah tana can tana girma ba tare da uwa ba, tana koyon muguntar Ruma da ƴarta..."
Sarki ya jawo ta jikinsa ya rungume ta da ƙarfi, duk da tana tirjiya. Ya fahimci cewa kishinsa da son da yake mata sun zama masifa gare ta. Amma ba shi da niyyar sakinta...
(WANI SANAR WA A WAƊANNAN LOKUNAN KASANCE DA MATANSA, SARKI NOURDEEN ASALIN SIFFARSA TA MUTUM YAKE, BA WANNAN FUSKAR ZAKI....)
Sarki ya kwana a ƙasar Mumbai, yana ƙoƙarin rarrashin Hibba, amma zuciyarta ta riga ta bushe. Tana tunanin yadda za ta kuɓuta daga wannan ramin da aka binne ta da rai...
A gefe guda, sarki yana tunanin yadda zai kwashe duka matan nasa ya dawo da su fada guda ba tare da an zubar da jini ba.. Amma babban abin tsoronsa.
Idan Ruma ta gano yana tare da Hibba, to Alhamra za ta kone kurmus!...
Bayan babban kishi da cacar baki da aka yi, sarki ya yi amfani da hikima da muryarsa mai sanyi wajen rarrashin Hibba.. Ya san inda yake taɓa zuciyarta. Ya rungume ta, yana raɗa mata kalaman da suka nuna cewa duk abin da yake yi, yana yi ne don ya kare rayuwarta daga kaidin Ruma..
A hankali, taurin zuciyar Hibba ya narke. Ta sani cewa tana matuƙar son Nourdeen, kuma kishinsa ma wata alama ce ta yadda yake daraja ta.
Don nuna ta haƙura, ta shiga kicin ɗin gidan wanda aka ƙerawa ado da kayan marmari. Ta haɗa wa sarki girkin Indiya na musamman..
Biryani mai ɗauke da ƙamshin kayan spices na asali...
Sai Butter Chicken mai gardi da laushi..
Samosas da Chutney Don buɗe abinci...
Sarki yana zaune a kan dinning, yana kallonta cikin alfahari. Hibba tana sanye da wata doguwar rigar Indiya (Sari) kalar ja, wadda ta ƙara fito da asalin kyawun jikinta..
Sarki ya jawo ta ta zauna kusa da shi, yana ciyar da ita tana ciyar da shi. Duk wata damuwa ta sarauta da damuwar Ruma suka fita daga kansu...
"Hibba," sarki ya faɗa cikin muryar sha'awa,
"ba za ki san yadda nake ji ba idan na tuna kina nan a fake. Ke ce numfashina na sirri."
Hibba ta yi murmushin kunya, ta kishingiɗa a kafaɗarsa...
"Nourdeen, burina ɗaya ne, mu zauna tare ba tare da tsoron kowa ba. Amma a daren nan, kai nawa ne ni kaɗai."
Daren ya ja, gidan ya yi tsit sai ƙamshin turaren wuta dake tashi. Sarki da Hibba sun koma babban ɗakin kwananta. A nan, sun rayu kamar wasu sabbin ma'aurata. Ba batun sarsuta, ba kuma sarauniya, sai dai Nourdeen da Muheebban sa...
Sun gudanar da darensu cikin tsantsar soyayya da nuna wa juna shauƙi..
Wannan daren ya zama tamkar maganin raɗaɗin ƙuncin da Hibba take ji na zama ita kaɗai, sannan ya ƙara wa sarki ƙarfin gwiwar cewa dole ne ya samo hanyar da zai haɗa iyalinsa wuri guda nan gaba...
Washegari da safe, bayan sun yi karin kumallo cikin nutsuwa, sarki ya yi wa Hibba ban-kwana da alkawarin zai dawo nan kusa, kuma zai yi ƙoƙarin kawo mata Maayah su gaisa a asirce...
Sarki Nourdeen ya bar Mumbai cikin sirri, maimakon ya nufi Alhamra, sai ya nufi ƙasar Saudiyya...
Wannan ziyarar ita ce tafi kowacce ciwo a zuciyarsa, domin yana zuwa ne domin ya ga matar da kowa ya ɗauka ta mutu shekaru goma sha shida da suka wuce.
Wannan ita ce Sarauniya Ayshert, mahaifiyar Ayat da Ching-Ching. Ita ce matar sarki ta biyu...
Tun lokacin da aka yi mata tiyata aka cire Ching-Ching daga cikinta saboda rashin lafiya, Aysh ba ta sake farfaɗowa ba. Labarin da aka yaɗa a Alhamra shi ne ta rasu a lokacin haihuwa, aka yi mata jana'iza ta ƙarya. Amma a zahiri, Sarki ya kaita Saudiyya ne wurin kakanta, wani babban malami mai ilimin addini da magungunan gargajiya, don ya kula da ita...
Sarki ya isa gidan tsohon malamin dake kusa da garin Madina. Gidan yana cike da nutsuwa da ƙamshin turaren miski da karatun Al-Kur'ani dake tashi...
Ya shiga wani babban ɗaki mai haske, inda ya tarar da Sarauniya Aysh kwance a kan gado. Shekaru goma sha shida ke nan tana kwance a matsayin Living Ghost wato Gawa mai rai...
Idanunta a rufe suke, numfashinta a hankali yake fita, amma jikinta bai ruɓe ba, kuma tana nan da kyawunta na asali, sai dai ramar da ba a rasa ba...
Sarki ya zauna a gefen gadon, ya kama hannunta wanda yake sanyi ƙalau...
Cikin muryar kuka ya furta..
"Aysh... har yanzu ba za ki tashi ba? Shekaru goma sha shida ke nan. Ƴarki Ayat ta girma, tana kama da ke sosai... Ching-Ching ma yanzu ta zama budurwa, amma ba su san kina raye ba. Kowa yana tunanin kin bar duniya."
Tsohon malamin ya shigo ɗakin, ya dafa kafaɗar Sarki..
Ya ce, "Sarki Nourdeen, jinyar Ayshert ba ta likitoci ba ce kawai. Mun yi dukkan gwaje-gwaje, kwakwalwarta tana nan garau, amma akwai wani abu da ya riƙe ruhinta. Wannan suma ce ta shekaru (Long-term Coma) wadda ilimin duniya bai kai ga gano maganinta ba. Sai dai mu ci gaba da addu'a."
Sarki ya zuba wa matarsa ido. Yana jin zargin cewa wannan jinyar ta Aysh ba ta Allah ba ce kawai. Yana tunanin ko akwai sa hannun wani wanda ya yi amfani da wani irin guba ko asiri da ya daskare kwakwalwarta a ranar da ta haihu..
Kuma daman kafin ta haihu tana fama da matsanancin jinyar da har yasa akayi mata tiyata saboda ba za ta iya yunƙurin haihuwa ba..
A yanzu, Aysh tana nan tana numfashi, amma ba ta san me yake faruwa a duniya ba....Ba ta ji kuma magana..
"Zan yi duk abin da zan iya don ganin kin farfaɗo. Amma kafin nan, zan koma Alhamra in ga yadda zan cigaba da tsare yaran da kika bari..."
A cewar sarki yana zub da hawaye...
Bayan ya kammala ziyarar ban-tausayi a Saudiyya, sarki ya shiga jirginsa na ƙarshe wanda zai kai shi Alhamra. Wannan karon, fuskarsa ta zama tamkar dutse, babu wani shauƙi, sai fushinsa na taɓa masa iyali da akayi...
Daidai karfe biyu na rana, sararin saman Alhamra ta cika da sautin injin jirgin sarki. Tun kafin ma ya sauka, an riga an baza jami'an tsaro na musamman a ko'ina...
A kofar fita daga filin jirgin, wasu jerin gwanon motoci ne bakake, kirar Rolls Royce da Mercedes-Maybach, wadanda suka sha bakaken gilashi, suke jiran sa. Mazajen masarautar sanye da bakaken kayan sarauta da rawuna wadanda suka rufe rabin fuskarsu, suka jera don taryen sa...
Yana fitowa daga jirgin, iskar Alhamra ta bugi fuskarsa. Ba tare da sakin fuska ba, kuma bai kalli kowa ba. Tafiyarsa kawai tana nuna cewa akwai nauyi a zuciyarsa...
Yayin da ayarin motocin sarki suke ratsa cikin gari zuwa babban gate na masarauta, garin ya yi tsit tamkar an cinye mutane..
Masu sayar da kaya sun rage sautin muryarsu...
Cikin masarauta bayi da ma’aikata sun raɓe a jikin bango, kowa ya sunkuyar da kai. Ba a jin komai sai sautin takalman sojoji da kakarar motoci a kan kwalta...
Kowa ya san cewa sarki ya daɗe bai yi tafiya mai tsawo haka ba, kuma dawowarsa tana nufin za a yi bincike a kan komai...
Sarki ya isa babban falonsa na taro... Ya cire babban rigarsa ya mika wa bawan dake tsaye kusa da shi. Ya zauna a kan karagar mulki, idanunsa suna kallon kofar shigowa...
Cikin murya dake amo "Ina suke? Ina gimbiyoyin masarautar nan?..."
Ko hutawa bai yi ba balle ya yi tunanin cin abinci..
Tin a cikin jirgi na dawowa ya canza fuskarsa zuwa ta zaki..
Sai ga Mama Liyatu ta shigo ta durƙusa tana miƙa gaisuwa ..
Sannan ta ɗora da faɗin..
"Ranka ya daɗe, suna nan suna jiran izinin shigowa. Amma... Gimbiya Maayah ba ta nan, tana can makaranta, kuma an ce akwai matsala tsakaninta da wani sabon malami..."
Sarki ya buga hannun kujerarsa. Gwam! Sautin ya ratsa ko'ina a falon...
"Ban zo nan don jin labarin malami ba. Ina son ganin kowa a gabana yanzun nan. Idan har sirri na ya fara fita tun ina raye, to lallai masarautar nan tana bukatar gyara mai zafi."
Ko wani Hadimi ya je sashen gimbiyoyi domin sanar dasu cewa Sarki ya dawo kuma yana buƙatar sanya su a idanuwansa...
A yayinda Ayat take shigar Inuwa a matsayin PA tana tare da Master Ibrahim domin ba shi wasu bayanai...
Lokacin da aka je sanar wa ko wace gimbiya..Ayat ƙirjinta ba ƙaramin bugawa yayi ba..
Kuma ga Master Ibrahim ya riƙe ta..basu gama tattaunawa ba....
TILL NEXT TIME...
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 3️⃣0️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Da zarar Ching Ching ta faɗo daga sama, Chief Onyx ya cafke ta a hannunsa cikin firgici..
Jikinta ya yi sanyi, numfashinta yana fita da ƙyar, jini kuma na zuba daga bakinta..
“Ching Ching… Ching Ching!”
ya ƙira sunanta da ƙarfi, amma babu amsa..
Gely ta matso kusa da su, fuskarta cike da nadama da tsoro. Idanunta shanye kamar mai jin bacci lokacin da ta ga yadda jinin ke ƙara fita...
“Boss… dole ne mu tafi asibiti yanzu nan,” ta faɗa cikin rawar murya..
Chief Onyx bai tsaya jayayya ba. Yana ɗauke da Ching Ching a hannunsa kamar jaririya, ya fice da sauri daga ɗakin... Siren na gaggawa ya fara ƙara a cikin harabar fadar, motocin tsaro suka fara motsi da kansu, suna sarrafa kan su, jira suke kawai a shige su, su fara tafiya...
Cikin mintuna kaɗan, sun shige cikin motar gaggawa mai sauri ba tare da masu tuƙa su ba. Kawai iya rubutu yayi a allon gaban motar ta ciki, ya rubuta yanda zai kai su.. shi kuma yana ɗauke da Ching Ching akan cinyarsa, idonsa a kanta kamar zai iya dawo da ranta da kallo kaɗai...
Motar ta ratsa titi cikin gudu, hasken ja da shuɗi na walƙiya...
Pavilion babban birnin zamani ya bayyana da fitilunsa masu sheƙi, amma a zuciyar Chief Onyx babu komai sai tsoro..
“Ki jure… ki jure Ching Ching,” ya faɗa a hankali, murya tana karyewa. “Ban gama dake ba… ba zan bar ki ba.”
Bayan sun isa Babban Asibitin Pavilion, likitoci da nas-nas suka ruga suna tura gadonta zuwa sashen gaggawa. Chief Onyx ya dakata a jikin ƙofar.. Yana kallon ciki dake glass door ne...
Gely ta iso daga baya, ta tsaya nesa tana kallonsa. A karo na farko, ta ga Chief Onyx cikin tsoro da tausayi..
A ta ciki