Showing 138001 words to 141000 words out of 154131 words

Chapter 47 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

ya kalli Sarki, ya kalli Maayah dake can tana hawaye, sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin girmamawa amma ba tare da nuna tsoro ba. Ya san cewa yau ya kulla abota da mutuwa, amma bai yi dana-sanin kare mutuncin fadar ba...

Taron ya watse cikin firgici da tsegumi. Masu sauƙar Alkur'ani duka sun koma sashensu cikin damuwa, yayin da fada ta ɓarke da wata irin hayaniya ta daban...

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 37

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



A cikin katafaren jirgin Chief Onyx mai ɗauke da fasahar zamani ta Pavilion, shiru ya ratsa cikin jirgin, sai dai kawai sautin injin jirgin dake tashi a hankali. Chief Onyx yana zaune a kan wata kujera ta alfarma, idanunsa a lumshe, yayin da fuskarsa dake sanye da karfen azurfa take haskaka karkashin fitilun jirgin...

Gely tana tsugune a gabansa, hannayenta na robot suna motsawa cikin kwarewa da sanyi. Ta riƙe babban hannun Chief wanda takobin Ayat ya ratsa. Tafin hannun ya tsage, jini mai kauri na digowa, amma Onyx ko kifta ido bai yi ba, kamar ba a jikinsa ake aikin ba.
Gely ta kunna wani haske mai launin shuɗi (Laser treatment) daga yatsunsa, wanda yake bin asalin inda takobin ya yanke jikin. Tana goge jinin da wani lallausan kyalle mai ɗauke da sinadarin kashe kwayoyin cuta.

Gely cikin muryarta mai sanyi irin ta na'ura ta ce,
"Boss, raunin ya ɗan yi zurfi. Takobin yarinyar nan yana da kaifi na musamman. Me ya sa ka bari ta taɓa ka? Da ka ba ni izini da na raba ta da numfashinta tun kafin takobin ya karaso."

Chief Onyx ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli tafin hannunsa dake ta konewa karkashin hasken Gely. Murmushin nan nasa na gefen baki ya sake bayyana...

"Gely, wani lokacin jini yana bukatar ya zuba domin mu tuna cewa mu mutane ne. Yarinyar tana da jini mai zafi... jinin Alhamra ne yake yawo a jikinta. Tana bukatar tarbiyya, amma jarumtarta ta burge ni."

Gely ta kammala ɗinke raunin da wani irin ɗinki na zamani wanda baya barin tabo. Ta shafa masa wani magani mai sanyi, sannan ta naɗe hannun da wani farin kyalle mai ɗauke da tambarin Pavilion...

Chief Onyx ya dunƙule hannunsa don jin karfin dinkin,
"Ina so ki sa ido akan wannan Guard ɗin. Akwai wani abu a tare da shi wanda ya fi karfin kwayar idon mutum. Tsikar jikina ba ta taba tashi a banza ba, kuma bisa alamun ba mutum bane...."

Gely ta ce, "An gama Boss. Na riga na ɗauki hoton kwayar idonsa na tura wa babban kwamfutar Pavilion don bincike."

Chief Onyx ya ƙura wa sararin samaniya ido ta taga, yayin da jiragen suke kutsawa cikin gajimare. Zuciyarsa tana can fadar Alhamra, yana tunanin ɗacin zuciyar Ayat da kuma kwarjinin Inuwa dake taɓa ruhinsa....

✨✨✨

Sarki Nourdeen ya saka ƙaramin Memory ɗin a cikin na’urar kallo ta hologram dake falo ɗinsa. Nan take haske ya bayyana a tsakiyar ɗakin, hoton wani fili mai ɗauke da fasahar zamani ya bayyana.

​A tsakiyar hoton, Ching-Ching ce tana sanye da kayan makaranta mai kalar navy blue and white, fuskarta tana sheki da alamun wayewa da natsuwa. Tana zaune a gaban wasu manyan malaman bincike da malaman addini...

​Bidiyon ya fara nuna yadda ake jifan ta da tambayoyi masu wahala..

​Fannin Kimiyya Malami ya tambaye ta game da tsarin kwayoyin halitta da fasahar makaman nukiliya. Ching-Ching ta amsa da yaren Turanci British Accent cikin kwarewa, tana bayani daki-daki kamar ita ce ta ƙera na'urorin...

​Fannin Addini kuwa Wani malami ya nemi ta yi bayanin wasu hadisai da ka’idojin ilimin Mantiq. Nan take ta sauya harshenta zuwa Larabci mai kyan gaske, tana kwararo hujjoji daga litattafan da sarki bai taɓa tunanin yarinya karama kamar ta za ta sani ba.

​Sarki Nourdeen ya daskare yana kallon allon, idanunsa sun cika da hawayen alfahari. Ya ga yadda diyarsa, wadda ya ɗauka tana can tana bauta a matsayin baiwa, ta zama wata kwararriyar malama kuma masaniya a karkashin kulawar Chief Onyx...

​Sarki cikin muryar raɗa ya furta
"Masha Allah... ashe bawan nan Onyx bai yaudare ni ba. Ya mayar da Auta tauraruwa. Wannan ilimin ya wuce tunanin kowa."

​Ya gane cewa Chief Onyx ya ɗauke ta ne ba don wulakanci ba, sai don ya tafi da ita inda za ta samu ilimin da babu shi a Alhamra...

Sarki ya sake tunawa da yadda Ayat ta kusan kashe Chief Onyx da takobi. Ya ƙara jin haushin Ayat a ranta...

"Wannan yarinyar Ayat tana so ta lalata komai! Gata tana can tana zargin Onyx azzalumi ne, alhali gashi ya mayar mata da kanwa sarki-ta-fannin-ilimi. Idan ta kashe shi, wa zai cigaba da rainon Ching-Ching?"

✨✨✨

Sydney...
Sarauniya Ruma tana zaune a cikin babban fadarta. Tana riƙe da wani kofin giya na alfarma, sai ga wani baturen ɗan leken asirinta ya shigo cikin gaggawa, ya zube a gabanta...

​Dan Leken Asirin ya ce,
"Your Majesty... labari ya zo mana daga Alhamra. Gimbiya Zayana tana tsare a Cell yau kusan mako guda. Sarki Nourdeen ne ya sa aka rufe ta, tana cikin kaskanci, ba abinci mai kyau, ga kuma azabar sauraye da kadaici."

​Kofin dake hannun Ruma ya faɗi ya fashe, jan giyar cikinsa ta bazu a kasa kamar jini. Ruma ta mike tsaye, idanunta masu kalar kuliya suka rikiɗe suka koma wani irin kore mai firgitarwa. Wani irin ihu ta saki na ɓacin rai wanda ya sa ɗaukacin dakarun dake wajen ɗakin firgita...

​Ruma cikin muryar dake fitar da hayaki ta ce,
"Nourdeen! Ka taɓa jini na? Ka taɓa guda ɗaya tilo da nake so a duniyar nan? Na gaya maka zan rusa Alhamra idan gashi ɗaya na kanta ya faɗi, ashe ba ka ɗauke ni da gaske ba!"

​Ta fara zagaye ɗakin tana numfashi sama-sama, kissar dake fuskarta ta ɓace, sai mugunta ta bayyana..

​ "Ba zan tafi Alhamra yanzu ba. Ina so Nourdeen ya ji daɗin mulkinsa kaɗan kafin in ruguza masa shi. Amma daga yau, Alhamra ta daina sanin lafiya."

​Ta juya ga babban janar ɗin dakarunta na Sydney..

"Ƙira min dakarunmu na sirri. Ina so a fara gurgunta duk wata mashigar abinci da makami dake shiga Alhamra. Ina so mu fara shakarsu ta tattalin arziki kafin mu shakarsu ta wuya."

​Ta nufi taga, tana kallon birnin Sydney amma tunaninta yana can fadar Alhamra inda Zayana take kuka..

​ "Nourdeen, ka sanya ɗiyata a cell saboda kana tunanin kai sarki ne? To zan nuna maka cewa ni mace ce da nake mulkar sarakuna. Zan sa ka roƙi mutuwa amma ba za ka ganta ba. Zan mayar da fadar Alhamra kango, inda jemage kawai zai rika shawagi. Kuma sai na fito da Zayana da kaina, sannan na sanya ka durkusa a gabanta kana neman gafarar jinin jiki na."

​Ta ciro wani takobi karami na azurfa, ta yanke tafin hannunta kadan, ta bari jinin ya digo a kan hoton Sarki Nourdeen dake kan tebur...

"Wannan shi ne alkawari na na jini. Masarautar Alhamra za ta zama makabarta muddin diyata ba ta fito ba cikin kwana ɗaya ba... amma kafin nan, zan fara aikewa Nourdeen da sakonni da zasu sanya shi zazzabi."

Bayan kwana ɗaya..

Sarki Nourdeen yana zaune a babban falonsa, yana duba wasu takardu sai ya ji wani irin sauti Buzzzzz... a bakin tagarsa. Wata karamar na'ura ce mai kalar azurfa, wadda aka kera ta a siffar tsuntsu, tana shawagi a iska.
​Sarki ya mike da sauri. Ya gane wannan fasahar, ta fadar dake Sydney ce. Na'urar ta shigo dakin, ta sauka a kan teburinsa, sannan ta bude wani dan karamin Screen na hologram.

​Fuskar Sarauniya Ruma ta bayyana a jikin hasken. Idanunta dake zubar da wutar fushi..cike da izza da sanyi mai ratsa kashi..

"Nourdeen... Na gaya maka kada ka taba jini na. Na gargade ka cewa muddin gashi ɗaya na kan Zayana ya faɗi, to masarautarka ta zama kango. Yau kwana shida diyata tana cikin cell cikin azaba, tana shan azabar da ko bawan da ka fi tsana bai cancanta ba."

​Sarki ya tsorata, ya fara zazzaro idanu. "Ruma... ta yaya kika sani?" ya fada a ransa...

​Ta ci gaba da magana kamar tana ganinsa...
"Kada ka damu da yadda na sani. Ka sani kawai cewa, daga daren yau, barci ya tafi daga idanunka. Zan fara shakƙun tattalin arzikin Alhamra tun daga Sydney har zuwa sauran kasashen duniya. Idan har Zayana ba ta fito daga wannan cell din ba cikin sa'o'i ashirin da hudu ba, to zan aiko maka da kawunan jakadunka guda 50 dake nan Sydney a matsayin kyautar karin kumallo'."

Daga nan ​hoton ya ɗauke,

​Sarki Nourdeen ya zauna a kan kujerarsa, gumi ya fara keto masa duk da sanyin dake ɗakin. Ya san Ruma mace ce mai cika alkawari, musamman idan aka taɓa Zayana. Idan har ta fara gurgunta kasuwancinsa a Sydney, Alhamra za ta shiga matsin lambar da zai iya jawo bore daga talakawa...

​Yana magana shi kadai.. "Yanzu idan na fito da Zayana saboda tsoron Ruma, zan zama rago a idon mutane. Idan kuma na bar ta, Ruma za ta rusa min masarauta. Me zan yi?"

A wannan lokacin, Master Ibrahim ya tura kofa ya shigo, fuskarsa cike da damuwa.

"Ranka ya daɗe, na zo ne in sanar da kai cewa yanayin cell ɗin Zayana ya ƙara muni. Tana kuka tana kiran mahaifiyarta, kuma na lura wasu bakaken tsuntsaye na na'ura suna kewaye da bangaren kurkukun. Akwai abin tsoro a iska."

Sarki Nourdeen ya kalli Master Ibrahim, ya kalli hoton Ching-Ching dake allon, sannan ya kalli rubutun TICK-TOCK na Ruma dake kan tebur..

Sarki ya aika master zuwa can sashen Ayat domin ya ƙira masa ita...

Master Ibrahim ya isa sashen Ayat. Bayan ya isar da sakon Sarki, suka nufi sashen Sarki Nourdeen tare...

Bayan ta shiga katafaren falon Sarki, ta iske shi zaune cikin tunani. Ta zube ta gaishe shi cikin girmamawa, fuskarta dauke da alamun marin da Onyx ya yi mata duk da tana cikin niƙab..

Sarki ya ce,
"Ayat, ki tashi ki zauna. Ga wannan bidiyon, ina so ki kalla kiga abin da idonki ya kasa gani a fili. Ina zuwa, bari in sallami bakin dake falo."

Ayat ta ƙura wa allon hologram ido. Ganin Ching-Ching ya sanya zuciyarta narkewa. Ta ga kanwar tata tana sanye da tufafin makaranta masu kyau, tana amsa tambayoyi cikin kwarewa da kwarjini. Wani dadi ne ya mamaye Ayat ganin cewa kanwarta ba baiwa bace, tauraruwa ce dake haskaka...
Hawaye suka fara wanke mata fuska, hawayen farin ciki da kuma kewar rashin kasancewa kusa da ita.

Tana cikin wannan yanayin, sai idonta ya sauka akan wata na'ura dake gefe wadda take ta haske. Ta taɓa na'urar, sai kawai hoton Sarauniya Ruma ya bayyana, muryarta tana maganar barazanar rusa Alhamra idan ba a fito da Zayana ba.
Daidai lokacin, Sarki Nourdeen ya tura kofa ya shigo. Ganin Ayat tana kallon sakon sirri na Ruma, sai ransa ya baci lokaci guda...

Cikin tsawa da bacin rai ya furta
"Wa ya ba ki umarnin taɓa wannan? Wace irin yarinya ce ke da ba ki da iyaka?"

Ayat ta zabura ta mike, jikinta yana rawa. Ta durkusa har kasa tana kuka.

"Abul, don Allah ka yafe min. Ban taɓa da nufin bincike ba, shauki ne ya kaini. Kuma... Abul, na zo ne in roki gafararka akan abin da na yi a filin taron sauka. Na wargaza taron murnarmu, na sanya ka cikin kunya a gaban baki. Ka yafe min don Allah."

Sarki ya sauke wani nannauyan numfashi, ganin diyar tasa tana kuka ya sanya tausayinta ya ratsa shi. Ya zauna a gefenta, ya dafa kafadar ta.

"Ayat, ki kalla ki gani. Ilimin da Ching-Ching take samu a can Pavilion, babu shi a nan. Onyx ba azzalumi bane kamar yadda kike tunani, kawai dai salon mulkinsa ne ya banbanta da namu. Dole ne ki koyi rage zafin rai. Zafin rai baya taɓa haifar da Ɗa mai ido, sai dai ya janyo wa mutum nadama."

Ya ci gaba da magana cikin muryar uba..

"Duba abin da kika janyo yanzu. Saboda zafin ranki yasa kowa yabar taron cikin baƙin ciki...Dole ki riƙa amfani da hankali fiye da zuciya. Kiyi amfani da wannan ilimin da kika samu na Alkur'ani wajen taɓa zuciyarki da rahama."

Ayat ta jinjina kai, tana jin kalaman mahaifinta suna shiga cikin jinin jikinta. Ta gane cewa yanzu Alhamra tana bukatar haɗin kai, ba gaba ba...

Bayan Ayat ta share hawayenta, sai ta gyara zamanta, ta ƙura wa Sarki Nourdeen ido, idanun dake cike da ɗimbin tambayoyin da suka daɗe suna cin zuciyarta tun tana yarinya.

Ayat ta sauƙe numfashi, muryarta a sanyaye ta fara jefar da tambayoyin...

"Abul, ka gafarceni, amma yau ina son sanin gaskiya. Na daɗe ina jin sunan Sarauniya Ruma, na san ita ce mahaifiyar Zayana, amma tun da na tashi a fadar nan ban taba ganin fuskarta ba, balle mu haɗa ido hudu. Me ya sa kake takun saka da ita? Shin akwai sauran aure a tsakaninku, ko kuwa kun raba gari ne gaba ɗaya? Idan kuwa kun rabu, me ya raba ku har kuka kasa zama inuwa daya?"

"Tambaya ta biyu Abul,... Me ya sa kake rayuwa kai kaɗai a matsayin gwauro a wannan katon fadar? Kowace masarauta da kake gani a duniya, sarki yana da mata, yana da sarauniyoyi dake rage masa zafi da damuwa, amma kai ka zaɓi zama kai kaɗai. Shin ko akwai wani boyayyen abu ne da ya sanya ka tsani zama da mace a matsayin mata a fada?"

"Me ya sa Ruma take da iko haka akan ka? Na ga yadda kake shiga tashin hankali a duk lokacin da maganarta ta taso. Shin akwai wani abu da take riƙe wa wanda ya fi karfinka ne, ko kuma soyayyarta ce har yanzu take maka raɗaɗi a zuciyarka?

Falon ya yi tsit, karar agogon bango kawai ake ji Tik.. Tik... Sarki Nourdeen ya kawar da kansa gefe, ya kalli taga yana kallon sararin saman Alhamra. Wani irin nannauyan numfashi ya sauƙe wanda ya nuna cewa tambayoyin Ayat sun sosa masa inda yake masa ciwo...

Ya juyo ya kalle ta, idanunsa sun canza launi, sannan ya gyara zama domin fuskantar wannan daddadan labari na baya wanda ya binne shi tun kafin Ayat ta san kanta....

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 38

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Falon ya yi tsit kamar an tsaida lokaci.
Ƙarar agogon bango kawai ake ji…
Tik… Tik… Tik…

Sarki Nourdeen ya jingina da kujera, idanunsa sun yi nisa da falon kamar yana kallon wani zamani da ya dade da wucewa.
Sai ya sauƙe numfashi mai nauyi..

“Ayat…” muryarsa ta fito a sanyaye, “ba komai bane yake da sauƙin faɗi.”

Ya ɗan lumshe idanu.
“Rayuwata ba ta fara a matsayin Sarki ba. Na fara ne a matsayin saurayi mai buri… wanda bai san cewa soyayya na iya zama tarkon da mutum zai gina da hannunsa ba.”

Ya ɗago ya kalli Ayat kai tsaye.
“A lokacin, mulkin Alhamra yana hannun Yayana. Ni kuma ina ƙasar Australia, birnin Sydney. A can ne na haɗu da Ruma.”

Ya ɗan murmusa, murmushin da bai kai zuci ba...

“Ruma ba mace bace kawai. Ita ɗin ‘yar Sarkin Sydney ce. Mai ƙarfin hali, mai girman kai… kuma mai son mallaka.”

Ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Ta kamu da sona fiye da yadda nake zato. Mahaifinta ya matsa min, siyasa ta shiga ciki. A wancan lokacin na ɗauka soyayya ce kawai… ban gane cewa siyasa ta fi soyayya ƙarfi ba.”

Ya ɗan matsa gaba.
“Na aure ta. Duk da cewa iyayena ba su so. An riga an yi min alkawarin wata yarinya tun ina ƙarami.”

Idanunsa suka sauya...
“Amma na bijire.”
Ya sauke numfashi..
“Domin ta aure ni, ta nuna ta musulunta. Amma bayan biki ya wuce… abubuwa suka canza.”

Shiru ya sake lulluɓe falon.
“Ta haifi Zayana. A lokacin na yi zaton komai zai daidaita. Amma na fara gane cewa Ruma ba ta iya rabon zuciya. Ita tana so ne ta mallake ni gaba ɗaya.”

Ya ɗan ja numfashi.
“Bayan rasuwar mahaifina, na dawo Alhamra. Na cika alkawarin da aka min na yarinta na auri Aysh.”

Fuskar Sarki ta sauya gaba ɗaya...

“Aysh…”

Sunan ya fito daga bakinsa kamar addu’a...
“Ita ce mace mafi hakuri da na taɓa sani. Ta zo fadar nan ba tare da gardama ba. Ta girmama Ruma.... duk da cewa ita ce halalina na farko a asali.....mahaifiyarku. Ita balarabiya ce ta asali, jininmu ɗaya. Amma shigowarta gidan nan ya tadda wutar jahannama daga wurin Ruma."

"Ruma ta ɗauka an wulakanta ta. Ta yaya baturiya, sarauniyar Sydney, za a yi mata kishiya? Amma Aysh... mace ce mai matuƙar haƙuri. Ta ɗauki Ruma a matsayin Yayarta, tana girmamata, tana mata biyayya duk da wulakancin da Ruma take nuna mata. Hakurin Aysh ne ya sa Ruma ta sauƙo har aka samu zaman lafiya na ɗan lokaci.."

Ya lumshe ido...
“Lokacin da aka haife ki, Ayat… na ji kamar Allah ya bani wata sabuwar dama.”
Sannan ya buɗe idanu..

“Amma kishi… kishi ba ƙaramin abu bane.”
Ya yi shiru. Kamar mai nazari.

Ayat ta lura da hannunsa na ɗan rawa...

Ya ci gaba da faɗin
“Kin tambaye ni dalilin da yasa nake zama ni kaɗai a wannan fadar…”

Ya yi murmushi mai ciwo.
“Bayan rasuwar Aysh… zuciyata ta daina amincewa da zaman lafiya. Na ga yadda kishin mata ke zama wuta da ke cin komai.”

Sai ya ɗan kalli taga.
“Na zaɓi zama gwauro ba don babu mata ba… amma don na gaji da wutar da nake kunna da kaina.”

Ya juya ya kalle ta.
“Amma ki sani, Ayat… akwai abubuwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login