Showing 114001 words to 117000 words out of 154131 words

Chapter 39 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

17 Mar 2026

106

ya kalli dukiyar, sannan ya kalli Zayana. A ransa yana cewa,
"Zayana, ashe ma kina taya ni aikin da nake so in yi." Ya gyara tsayuwar sa.. ya furta a fili,

"Zan yi ƙoƙari, Gimbiya.. Amma fa ki sani, idan asiri ya tonu, ni da ke ne a gaban shari'a."

Zayana ta buga tafi, tana jin ta yi nasara.. "Ba zai tonu ba. Tunda kai ne PA, kai ne za ka kai wa ƴan aika wasiƙun. A lokacin za ka cire tawa..."

Ya karɓa sannan ya juya ya tafi..

Can dare tayi wanka cikin sleeping dress tana zaune a tsakiyar gadonta dake sashenta, ta buɗe akwatin zinaren da Zayana ta ba ta. Kyalkyalin duwatsu masu daraja ya cika ɗakin. Ya san cewa waɗannan kuɗaɗen an tara su ne ta hanyar zalunci..

"Zayana, kina tunanin za ki iya sayen ƙaddara da kuɗi?" Ayat ta yi maganar zuci tana murmushin yaƙi...
"Tunda kina da kuɗin banza, to zan taimaka miki wajen rage miki nauyin su ta hanyar kai su inda suka dace."

✨✨

Bayan kwana biyu da maganarta da Inuwa, Maayah ta tafi makaranta cikin wani irin yanayi..
Jikinta ya yi sanyi, kwarjininta na dā ya ragu domin zuciyarta tana cike da fargabar aure da kuma kaunar Inuwa, ga Uncle Jalal da ya sako ta a gaba...
Ta daina hantarar kowa, amma har yanzu akwai ragowar izzah a tare da ita.

Tana zaune a aji, tana tunanin Inuwa, sai ga Uncle Jalal ya shigo. Takunsa kawai ya isa ya sanya ajin yin tsit. Jalal mutum ne mai cikar kwarjini...

Ya tsaya a gaban aji, ya kalli kowa da idanunsa masu kaifi. Kowa ya miƙe ya yi gaisuwa ban da Maayah... Uncle Jalal ne ya watsa mata wata harara guda daya, wadda ta sanya ta rasa natsuwarta, ta miƙe a hankali tana sunkuyar da kanta tare da hadiye miyau.

Can ya mu su alamar su zauna da hannu...sai da kowa ya zauna tukun itama za zamo last ɗin zama kamar yadda tayi last ɗin tashi..

Jalal ya ajiye littattafansa a kan teburi, muryarsa ta daki kowanne lungu na ajin...
"Where is the class Rep?"

Maayah ta ɗago kai da sauri, tana zare ido. Tunda ya ba ta mukamin Class Monitor, rayuwarta ta sauya..

"Je ki nemo min sabuwar marker rubutu yanzun nan," ya fada cikin sanyi na ba da umarni...

Maayah ta tashi tana turo baki, ranta a ɓace. Ita ce gimbiyar da bayi suke yi wa komai, amma yau ita ce take yawo a corridors ɗin makaranta neman marker...

Kuma yanzu Bodyguards ɗin nata Jalal ya hanasu tsayuwa a cikin makaranta, ya sanar cewa zasu iya kawo ta, amma da zaran sun dire ta a cikin makarantar sai kuma su juya sai lokacin tashi yayi...

......Bayan ta dawo, Jalal bai karɓi marken ba sai da ya kalli allo wanda yake cike da rubutun jiya..

"Goge allon nan kafin ki mika min marken," ya faɗa yana gyara zama akan chair.

Maayah ta ɗauki duster din, ta fara goge allon. Hawaye suka fara silalo mata a kunci. Tana gogewa tana kukan zuci, tana ganin kamar Uncle Jalal ya tsane ta ne kawai yake mata wannan walakancin. Tana turo baki, kyakkyawar fuskarta ta ɓaci da ƙura, amma ta kasa musawa domin kwarjinin Jalal ya sha karfinta...

Uncle Jalal ya zauna yana kallonta ta glassin idonsa. A ransa yana murmushi, domin ya san cewa wannan tarbiyyar tana da amfani gare ta kafin lokaci ya kure...

"Idan kika gama, ki buɗe textbook ɗinki shafi na arba'in," ya fada ba tare da nuna tausayi ba, yayin da Maayah take share hawayen dake diga a kan takardarta...

Aji ya yi tsit, kowa ya maida hankali. Uncle Jalal ya fara darasin sa, yana tafiya yana zazzage tambayoyi da turanci. Abin sha'awa, kowanne dalibi idan ya tashi, magana yake yi cikin kwarewa da harshen Turanci kamar dan Jami'a. Suna fito da hujjoji da tambayoyi masu zurfi dake nuna cewa lallai kowa ya haɗiye karatun...

Uncle Jalal ya gyada kai, yana jin dadin yadda daliban nasa suke da kwakwalwa. Amma duk wannan bajinta da ake yi, Maayah tana zaune ne can baya, kanta a sunkuye tana wasa da gefen skirt ɗinta dake short ne...

Uncle Jalal ya tsaya kusa da teburinsa, ya gyara tsayuwa sannan ya ƙira sunanta cikin natsuwa..

"Maayah, me kika gane game da bayanin da na yi yanzu? What is your take on this topic?"

Maayah ta ɗago kai, ta kalle shi da idanun nan nata dake cike da shagwaba da kuma ruɗani..
Ta yi shiru, ta kasa cewa uffan. Duk ajin suka juyo suna kallonta. Wannan ba sabon abu bane, domin Maayah ba ta taɓa bada amsar tambaya ba, kuma ba ta taɓa ɗaga hannu ta yi tambaya ba...

A kallon Uncle Jalal, Maayah ce kadai jahila a cikin ajin dake neman ɓata masa kokari...

Ganin ba ta da niyyar magana, ya tako har zuwa mazauninta. Ya miƙa hannu ya ɗauko jakartar makarantar ta, ya buɗe ta gaban kowa. Ya fara fito da littattafanta daya bayan daya.
Ya bincika na Turanci, ya bincika na Lissafi, da na computer sai ya iske abin takaici. Wasu littattafan fanko ne babu rubutu ko daya. Wadanda kuma take da shi, rubutun babu fasali, gurgwaye ne kamar na yara 'yan Nursery dake koyon rike fensir. Rubutun nata ba shi da tsari, kuma bai fi na darasi biyu ba a duk semester din, nan ma ba complete ba.

Uncle Jalal ya jefa littattafan akan teburin natan, ransa ya ɓaci sosai...

"Maayah! Me kike zuwa yi a makarantar nan?" Ya daka mata tsawa wadda ta sa duk ajin suka razana..

"Ina sauran rubutun malaman? Na bada note kusan guda goma, amma ke naki bai fi na darasi biyu ba, kuma ko shi din ma ba a kammala ba!"

Ya nuna littafin da rubutun nursery dake ciki. "Duba irin rubutunki, shin hakan ya dace da daliba a wannan matakin? Kullum kowa yana fahimtar darasi amma ke kina nan kina wasa da lokaci. Idan kika sake zuwa ajina gobe ba ki kammala wannan note din ba, to lallai za ki fuskanci hukuncin da ba ki taba gani ba a makarantar nan!"

Maayah ta rasa inda za ta sa kanta don kunya da takaici. Ta turo baki, hawaye suka fara sintiri a fuskarta. Ta ji kowa a ajin yana kallonta a matsayin jahila, alhalin ita a gida ita ce gimbiya mai kowa da komai..

Ta kalli Uncle Jalal cikin kiyayya da kuma tsoro, tana mamakin yadda mutumin nan yake da kwarjinin da har yake iya daka mata tsawa a gaban mutane. Ta sunkuyar da kanta tana goge hawaye, tana jin duniyar ta yi mata zafi....

Uncle Jalal ya tsaya dambar a gabanta, hannayensa a dunkule, idanunsa suna huda zuciyarta...

"Dakata tukunna," ya faɗa cikin muryar da ta sa kowa a ajin ya daskare..

"Ta yaya ma kike rubuta jarrabawa? Na duba kundin sakamakon makarantar nan, naga dukkan sakamakonki kina cin first position... A kowace jarrabawa tun da kika fara makarantar nan, ke ce kike ɗaukar ta ɗaya."

Ya yi wata dariyar raini wadda ta fi ciwo fiye da dukan bulala...

"Oh! Na gane. Saboda duk sauran malaman da har shi kansa Shugaban makarantar tsoronki suke yi, ko? Ba kya rubuta komai a jarrabawa, hasali ma ba kya zama a ɗakin rubuta jarrabawar, amma kuma a baki First Class!"

Uncle Jalal ya buga teburin dake gabanta, "Wannan cin mutuncin ilimi ne! Wannan rashin adalci ne ga waɗannan ɗaliban dake zaune suna ta faman karatu dare da rana. Amma tunda yanzu ina nan, naga yadda za ki samu sakamako ba tare da kin rubuta jarrabawa da hannunki ba. Ko ke ɗiyar Sarki ce, ko ɗiyar wane ne, a ajina dukiya da sarauta ba sa ba da sakamako, sai ƙwaƙwalwa!"....

Maayah ta ji kamar ƙasa ta tsage ta haɗiye ta. Kalmomin Uncle Jalal sun kasance masu zafi... Ta saba da ganin kowa yana rawar ƙafa a gabanta, amma wannan malamin ya fito da kuskurenta a gaban kowa..
Hawaye suka fara zubar mata gwanin ban tausayi. Tana turo baki, tana jin wani irin takaici na yadda asirinta ya tonu. Sauran ɗaliban suka fara raɗa-raɗa a tsakaninsu, wasu suna kallonta cike da tausayi, wasu kuma da mamakin yadda ashe First Class ɗinta na jabu ne...

"Daga yau," Uncle Jalal ya ci gaba da faɗa, "Ba ke ce za ki riƙa fita ɗauko min marker ba. Domin wannan ma alƙali ne na ƙarya. Za ki zauna a nan, ki kammala duk notes ɗin da kika bari. Kuma gobe, zan baki jarrabawa ta musamman a ofishina don in ga abin da kika sani."

Ya juya ya bar mazauninta, yana tafiya cikin takunsa na isa, ya ɗaga hannu yana faɗin...
"Class dismissed!" ..

✨✨

Fadar ta yi shiru, sai kamshin turaren da ya gauraye ko'ina. Sheikh Shureim, kyakkyawan Balarabe mai cikar kamala da haiba, yana zaune cikin ladabi a gefen Sarki akan ƙaramar sofa na baƙi...

Fararen kayan sa da jajurwar fuskarsa sun ƙara masa kwarjini.
​Sarki ya gyara zama, fuskarsa cike da annuri..

"Alsheikh Shureim, shin ya koyarwarku take gudana? Ko dan Ina da tabbaci akan Gimbiyata Yumna."

​Sheikh ya sunkuyar da kansa, ya amsa cikin muryarsa mai daɗi..

"Ranka ya daɗe akanta nazo magana. A yanzu haka, Gimbiya Yumna ta kammala haddar Alkur'ani mai girma har sau biyar. Ta haddace hadisan Manzo (S.A.W) da sauran litattafan fikihu."

​Sheikh ya ci gaba, "Ta aiko ni ne ta roki alfarma, tana son gudanar da gagarumar walima a masarautar nan. Amma tana son a bincika idan akwai sauran Gimbiyoyin da suka haddace Alkur'ani domin su gudanar da walimar tare."

​Sarki ya sake murmushi mai ƙayatarwa, sai dai abin mamaki a yanzu babu fuskar zakin nan, asalin kamanninsa ne,
Ya ji daɗin wannan albishir domin sai hamdala yake tayi...

"Masha Allah! Wannan ita ce kyauta mafi girma da ɗiya zata ba mahaifinta."

Nan take ya bada umarnin a ƙira masa dukka Gimbiyoyin masarautar ba tare da bata lokaci ba.

​A lokacin ne motar jami'an tsaron Maayah ta shigo masarautar daga makaranta. Aka tsaida su aka gaya musu sakon Sarki. Maayah ta firgita, ta yi saurin goge hawayen dake fuskarta na takaicin Uncle Jalal...

​"Wayyo kar dai maganar auren ne?..." ta faɗa tana turo baki, zuciyarta na bugawa. Ita ce ta farkon shiga fadar, tana taku ɗaya-ɗaya har ta samu waje ta zauna, tana kokarin boye idanunta dake jawur.

​Ba a daɗe ba, sauran Gimbiyoyin suka fara isowa. Zayana ta shigo cikin takun gadara. Sai kuma Ayat ta bayyana, a yau ta yi sa'a tana matsayinta na Gimbiya ba Inuwa ba. Ta zauna cikin sanyi da nutsuwa, fuskarta a rufe da siririn mayafi...

An buƙaci ganin malaman dake koyar da yaran gaba ɗaya dake ko wace gimbiya da malaminta...

​Malaman gida suma sun iso...

​Malamin Ayat shiru-shiru mai yawan nazari da nuna Dattaku...

Sai ​malamin Zayana wanda kullum take bashi wahala...

​Sai kuma Sheikh Shureim dake zaune gefe ɗaya, idanunsa a kasa.

​Daga ƙarshe, Gimbiya Yumna ta shigo. Ta sha bamban da sauran, fuskarta tana fitar da wani irin haske na tarbiyya da karatun Alkur'ani. Tana shigowa, idanunta suka sauka akan Sheikh Shureim. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, tana jin wani daɗi dake gauraye da kunya na cewa "Ga masoyina, ga kuma abin alfaharina."

​Ta gaishe da mahaifinta, sannan ta zauna kusa da Aunty Zayana...

​Sarki ya kalli Gimbiyoyin nasa guda huɗu da suka hallara...
"Na ƙira ku ne domin na ji labari mai daɗi daga bakin Sheikh Shureim game da Yumna. Tana son yin walimar saukar Alkur'ani, kuma tana son wacce ta haddace a cikinku ta fito su yi tare."

​Sarki ya kalli kowacce ɗaya bayan ɗaya.. "Zayana? Maayah? Aayat? Shin akwai wacce ke da haddar Alkur'ani a cikinku?"

​Zayana ta kau da kai, Maayah kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta tana tunanin notes din Uncle Jalal... Sai Ayat ce kadai ta ɗanyi motsi, amma ba ta ce uffan ba...

Bayan tambayar Sarki, Malam Mubarak ya yi murmushi mai cike da alfahari, ya gyara zama...

"Ranka ya daɗe, tabbas Gimbiya Aayat ma ta haddace Alkur'ani mai girma da wasu daga cikin litattafan Manzo Allah (S.A.W). Dalilin da ya sa kuke ganinta tana ba ni hutu ne saboda ta kammala komai, tana tilawa ne kawai a kowane lokaci."

(A ranta, Ayat ta sauke ajiyar zuciya, domin ta san dalilin dakatar da shi shine don ta samu sararin fita a matsayin Inuwa, amma hakan bai hana ta kasancewa mai kwazon karatu a ɓoye ba).

Sarki ya jinjina kai, fuskarsa cike da mamaki. "Masha Allah! Amma batun boko fa?"

Malam Mubarak ya ci gaba, "Alhamdulillah! Ta ƙware a Turanci da rubutu. Ta bitar darussan kimiyya irin su Physics, Chemistry, Maths, har ma da fannin tattalin arziki (Economics). Ta hadiye duk wani fanni da ake koyarwa."

Sarki ya kalli Ayat da matsanancin farin ciki..

"Daman burinta ta zama likita tun tana ƙarama, ashe har kin shirya."

Ba zato ba tsammani, Ayat ta ɗaga kai ta cikin mayafinta, muryarta a sanyaye cikin natsuwa...

"Abul... yanzu na fasa zama likita."
Fadar ta ɗauki shiru. Sarki ya zaro ido, "Me ya sa? Bayan kin gama tattara duk darussan fannin kin karance su?"

Ayat ta yi murmushin nan nata na shagwaɓa wanda Sarki ba ya iya musa mata duk mayafi ya rufe...

"Abul, ni yanzu Criminology nake so. Burina shi ne in zama Sojan Sama wato Air Force Officer..."

Sarki ya kalli 'yarsa kamar bai taɓa ganinta ba. "Kina Gimbiya? Kuma matar wani nan gaba? Kuma da wannan rufin fuskar koda yaushe za ki yi aikin soja? Wannan wane irin buri ne Ayat?"
Ayat ta ɗan matso kusa da mahaifinta cikin sigar lallashi da shagwaɓa..

"Abul, please mana. Duk wanda zan aura ai zai bar ni in yi abin da nake so. Kuma duk sanda na zama sojan sama, to zan yaye wannan mayafin in sanya kakin soja. Batun gimbiyanci kuma... uhmm uhmmm," ta turo baki tana dariya.

Duk waɗanda ke fadar suka daskare.
Sheikh Shureim ya ji jiki ya yi sanyi ganin yadda 'yar Sarki ke da babban buri na jarumta..

Maayah ta daina kukan zucin da take na Uncle Jalal, ta tsaya tana kallon Ayat da mamaki, tana tunanin yadda za a yi mace ta zama soja..

Sarki kuwa ya rasa abin da zai ce, domin ya san tauri da kaifin zuciyar Ayat idan ta sa abu a gaba.

Sai kawai ya juya kansa a hankali zuwa ga Gimbiya Zayana, muryarsa a nutsuwa yake furta wa Ayat...
“Bari na koma ga ƴan'uwanki kafin na dawo gare ki...”

Sarki ya kalli Zayana, ya tambaye ta game da nata karatun. Zayana ta yi shiru, tana wasa da zoban hannunta cikin ko-oho..

Da Sarki ya kalli Malam Mahmud,
“me zaka iya cewa ga me da Zayana?”

Malam Mahmud ba tare da ya kalli idon Zayana ba, balle ya damu da kwarjininta ko matsayinta..

Ya fara ƙiƙƙina, murya tana rawa..
"Ranka ya daɗe... a gafarce ni. Gimbiya Zayana ko izu biyu ba ta kai ba. Idan na je koyar da ita, wulaƙanta ni take yi ta kore ni, har tana cewa ba ta son sake ganina."

Sarki ya ji wani zafi ya ziyarci zuciyarsa. Ya fara mata faɗa mai ratsa jiki, yana tuna irin taurin kan mahaifiyarta da ya shafi rayuwar Zayana...


“Zayana! Har yanzu baki gane darajar abin da kike yi ba? Al-Kur’ani ake magana, kalmar Ubangiji! Ke kuma kina raina malaminki, kina kore shi kamar bawa? Wannan wace irin tarbiyya ce?”

Zayana ta ɗaga kai cikin izzah, idonta babu ko ɗigon nadama..

Sarki ya cigaba,
“Na ba ki malamai, na ba ki lokaci, na ba ki duk abin da ’ya mace za ta nema amma ke kina zaɓar girman kai akan ilimi! Kina son ki zama me? Sarauniya marar addini?”

Nan take Zayana ta yi dariyar raini, ta matso gaba kaɗan..

“Abba, ka daina min wannan wa’azin. Ba kai ne ke zaune a zuciyata ba, don haka ba ka san abin da nake ji ba.”

Sarki ya harara ta, muryarsa ta ƙara tsananta.
Ya ce,

“Ke fa ’yata ce! Zan gyara ki ko kin so ko ba ki so! Addini ba zaɓi ba ne a wannan fadar!”

Zayana ta ɗaga hannu alamar dakatar da shi, muryarta mai sanyi amma kalmomin suna yankar zuciya... Ta ce

“Gyara? Kai fa kana ƙoƙarin mallaka ne, ba tarbiyya ba. Kana son mu zama yadda kake so, ba yadda muke ba.”

Sarki ya daki ƙasa da ƙafa cikin ɓacin rai tare da faɗin

“Zayana! Ki kula da bakinki! Ina magana da ke a matsayin uba da sarki!”

Ta kalleshi kai tsaye, ba tare da tsoro na,

“Ni kuma ina sauraronka ne a matsayin mutum, ba gunki ba. Idan tarbiyya ta tilas ce, to ka sani zuciya ba a tilasta mata gaskiya.”

Shiru ya sauƙa na ɗan lokaci...
Sarki ya yi kamar zai sake magana.
Sai Zayana ta ƙara da murya mai kaifi..

“Za ka iya min hukunci, sannan ka iya yi mun tsawa, amma ba za ka taɓa sa ni in zama abin da ban yarda da shi ba.”

Nan take ta juya, ta ɗaga habarta cikin izzah.
“Na gaji da zaman fadar nan...”

Ta fice daga fadar ba tare da waiwaya ba.
Tana takun gadara, ta bar kowa cikin mamakin rashin tarbiyyarta.

Sarki ya tsaya cak, kalamanta suna maimaituwa a kansa kamar sara..

Ayat ta kalli bayan Zayana, ranta yana suya. Ta ji zafi yadda Zayana ta wulaƙanta mahaifinsu a gaban malamai. A ranta take cewa,

"Zayana, akwai ranar da za ki san kuskurenki." Amma sarki ya danne tasa damuwar ya kalli Maayah, wadda hankalinta yake wani wajen...

Tun farko ya lura hankalinta ba ya nan gaba ɗaya. Kamar akwai wani abu mai nauyi da ke damunta.
Cikin murya mai ɗan tsauri..

"Ke kuma fa? Ko ke ma rashin kunyar za ki tsaya min?" Sarki ya tambayi Maayah.

Maayah ta girgiza kai a hankali. Ta ɗago idonta ta kalle shi, murya a sanyaye ta furta.

"Duk lalacewar tarbiyyata, ba zan yi musayar yawu da kai ba, Abul.... Ko da naman jikinmu kake yankewa kullum, hakan ba zai sa mu ƙi ka a matsayin uba ba.”

Sarki ya ji sanyi a ransa, "Allah ya miki albarka ƴata. Yanzu ke kin haddace?"

Maayah ta gyara zama, ta ce cikin ƙwarin gwiwa,

"Abul, ban haddace duka ba, amma na kusa... domin yanzu haka ina Suratul Musa."

😨😨😨!!! Fadar ta ɗauki shiru. Malamai suka zaro ido, Sarki ya daskare...

Ayat, duk da baƙin cikin Zayana da ke ranta, ta kasa riƙe dariya, sai da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login