Showing 120001 words to 123000 words out of 154131 words
Chapter 41 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
Umarni ne daga Sarki, kina bukatar biyo mu yanzu zuwa ɗakin tsaro."
Zayana dake kan dinning zaune ta kifa kanta akan table tana tunanin irin hukuncin da za ta ɗauka akan Ayat...
Jin muryar Master ya sa ta ɗago tare da fito falon, fuskarta yayi jajur saboda marin da Ayat ta mata, abunka da baturen mutum...
ganin yadda Master Ibrahim ya yi mata magana ya sa ta ƙara harzuƙa...
"Who do you think you are? Ibrahim, ka fita daga nan kafin in sa a cire maka wannan kakin sojan naka! You have no right to enter my private section!"
Master Ibrahim ya ce,
"Gimbiya, kiyi hakuri ki biyo mu cikin ruwan sanyi. Umarnin Sarki ne, kuma kin san ba a musa masa. Kin wulakanta shi a fada, kuma yanzu lokacin hukunci ya yi."
Zayana ta kalli Master Ibrahim da waɗannan cat eyes ɗinta, ta ɗauki wata kwalbar turare mai tsada ta kwada masa, amma cikin zafin nama ya kauce...
Ta cigaba da magana
"I am not going anywhere! Idan ka taɓa ni, Mom ɗina za ta sa a datse maka hannaye!"
Ganin ba za ta bi shi ba, ya ɗaure fuska. Ya san idan ya tsaya rarrashi, lokaci zai ƙure..
"Ina neman gafararki Gimbiya, amma aikina zan yi."
Cikin zafin nama, ya nufi Zayana....
Ta fara kai masa naushi da yakushi, tana ihu tana kiran sunan mahaifiyarta. Amma Master Ibrahim ya kama hannayenta ya murde su ta baya cikin kwarewa, sannan ya sa mata ankwa...
Haka Zayana take ta zagi da maganganu..
"Let me go! You filthy soldier! I will kill you! Mimi, call your grandmother!"
Sojojin suka kewaye ta yayin da Master Ibrahim yake jan ta da karfi. Mimi ta biyo su a baya tana kuka tana jifan sojojin da kayan wasanta. Bayin sashen kuwa kowa ya laɓe, suna kallon yadda ake jan babbar Gimbiya kamar kura...
Suna isa kofar Dark Room No. 2, Master Ibrahim ya bude kofar dake fitar da wani irin sanyi da duhu mai ban tsoro..
Ya ce, "Gimbiya, anan zaki zauna har sai ranka ya daɗe ya bada umarnin fito dake. Kiyi tunani akan abinda kika yiwa mahaifinki."
Ya tura ta ciki, ya rufe kofar da wani babban kwaɗo. Sautin kukanta da dukan kofar da take yi ya gauraye wajen, amma Master Ibrahim ya juya abinsa cikin sanyin jiki, yana addu'ar kada mahaifiyar Zayana ta bayyana a cikin masarautar nan....
✨✨✨
Ganin Sarki ya fi ce daga fadar yasa Maayah ta tashi daga ƙasa inda take kuka, ta goge fuskarta, ta gyara mayafinta tana wani yatsine fuska. Ta kalli Uncle Jalal daga sama har kasa, sannan ta koma kan wata kujera ta alfarma ta zauna tana jijjiga ƙafa...
Cikin ƙasaita ta furta.
"To Malam Jalal, ko ince Uncle? Ai kaga nan ba makaranta bace ko? Nan gidan ubana ne, kuma ni ce Gimbiya Maayah. Don haka, kada ka sa ran zan raba kaina da ƙasa ina baka amsa kamar yadda nake yi a aji."
Uncle Jalal ya ajiye littafinsa a hankali, ya zura hannayensa a aljihu yana kallon yadda yarinyar ke kokarin nuna isa, alhalin ko 10+10 ta kasa sani..
Yana murmushi ya furta,
"Zama ko tsayuwa ba shi ne zai baki ilimi ba, Maayah....Kuma idan har baki manta ba, Abul dinki ne ya ce in zama inuwar ki har sai kin san me kike yi. Don haka, mu fara darasinmu na yau."
Uncle Jalal ya yanke shawarar saukowa matakin kwakwalwarta domin ya ga iyakarta..
Ya ce, "To, tunda ke 'yar boko ce, gaya min, Daga ina ruwan sama yake fitowa? Kuma me yake kawo shi?"
Maayah ta danyi shiru, ta kalli silin din fadar, sannan ta taɓe baki cikin rashin sanin komai da kuma nuna ilimi...
"Wannan ai tambayar yara ce. Ruwan sama a tankin gidanmu yake fitowa! Idan aka bude fanfo a sama, shi yasa yake zuwa. Kuma idan hadimai sun manta basu rufe ba, sai ayi ta ruwa kenan har sai ya cinye ƙananun flowowi 😏...."
Ita kanta bata sani ba amma ta faɗi haka ne don ta ƙular da shi...
Uncle Jalal ya runtse idonsa na dakika biyar, yana neman hakurin da zai cigaba da wannan zama.
Ya ce, "To, bar batun tankin ruwa. Gaya min, ina ne babban birnin kasar Saudiyya...?"
Maayah ta hure iska daga bakinta, tana wasa da zoban hannunta...
"Saudiyya kuma? Ai tana nan, ƙasar su mahaifiyar Ayat da Ching Ching ne... Na taɓa jin ana cewa can ne ake sayo turaren wuta, yanzu haka ƙamshin turaren da kake ji a fadar nan, na Saudiyya ce, to Saudiyya tana karkashin wannan masarautar tamu ne. Birnin kuma sunansa Birnin Turare..."
Wannan karon kam ta zaƙe, tsakaninta da Allah take gaya masa gaskiyar saudiyyar da ya tambaye ta..
Uncle Jalal ya matso kusa da ita, ya kura mata ido yadda ta ji jikinta ya danyi sanyi, amma ta dake ta ƙara gimtse fuska...
A hankali ya furta
"Maayah, kin san me nake gani idan ina kallon kwayar idonki? Ba girman kai nake gani ba, wani ƙaton duhu nake gani na jahilci wanda kike son rufe shi da gadara. Amma ki sani, muddin ina nan, sai na fasa wannan duhun. Yau zan barki ki tafi ki huta, amma gobe... gobe zamu fara da koyon haruffan 'A, B, C' da kuma 'Alif, Ba, Ta'. Kuma za ki rubuta su a gaban kowa...."
Maayah ta miƙe tsaye cikin fushi,
"Ni ce zan rubuta Alif Ba? Wallahi ka da ka kuskura! Ni ba 'yar Nursery bace! Kuma idan ka matsa min, zan ce wa Abul duka na kake yi!"
Uncle Jalal ya yi murmushi kawai, ya juya ya bar falon, ya bar ta da huci tana buga kafa a ƙasa...
✨
Uncle Jalal ya nemi izinin ganin Sarki domin ya sanar da shi tafiyarsa. Sarki ya ba da izinin ya same shi har can sashensa na musamman. Jalal ya shiga, ya zauna a babban falon Sarki, falon da aka ƙawata shi da duk wata daular duniya..
Ba jimawa, Sarki ya sauƙo daga saman bene, ya zauna fuskarsa cike da mutuntawa...
Bayan gaisuwa, Uncle Jalal ya dubi Sarki cikin natsuwa ya ce..
"Ranka ya daɗe, zan wuce, amma kafin nan ina neman wata alfarma. Shawarwari ne akan Maayah, idan har ana son ta sauƙo da kanta ƙasa, to dole sai an kiyaye wasu abubuwa. A koda yaushe tana ganin kanta a sama ne saboda waɗannan zabga-zabgan mutanen da ke kewaye da ita... Motoci manya guda biyar ne ke rakata makaranta, kowa yana mata abin da take so, shi ya sa ba ta ganin kowa da mutunci."
Ya gyara zama ya ci gaba..
"Alfarmar da nake nema ita ce, a kullum zan riƙa zuwa har masarautar nan na ɗauke ta mu tafi makaranta tare a motata. Sannan akwai lokutan da zan riƙa zuwa ina koyar da ita a gida. Kuma gaskiyar magana, dole sai an mata repeat ɗin aji, an dawo da ita baya. Tana SS3 amma koda rubutu ba ta iya ba? Idan kuma ta je jami'a fa?"
Sarki ya jinjina kai, maganar ta ratsa shi...
"Wannan batun naka gaskiya ne," in ji Sarki cikin damuwa.. "Mahaifiyarta ta dage ne akan sai an kai ƴarta makaranta domin ta yaƙi jahilci. Mahaifiyar Maayah a baya malamar jami'a ce dake ƙasar Mumbai, har ta samu lambobin yabo masu yawa a fannin ilimi. Ina jin shakkar ranar da za ta ga ƴarta a haka. Na yi mata alƙawarin zan kai mata Maayah hutu nan ba da jimawa ba, amma yanzu na fara karaya. Domin na tabbata idan na kaita a haka, mahaifiyar za ta binciki ƙwaƙwalwarta ta ga babu komai."
Sarki ya kalli Jalal sannan ya furta
"Shi ya sa yanzu, ko me kake buƙata, indai za ka dawo min da ƙwaƙwalwarta, to na amince. Ba ni da burin kaita jami'a yanzu, ina jiran ne ta kammala SSCE sai na musu aure gaba ɗaya, amma yanzu komai ya dawo baya... Jalaludden, zan ninka maka kuɗaɗen da ake baka a makaranta sau biyar don ka gyara ta. Za ka riƙa zuwa kana mata home lesson, sannan ka dage mata a makaranta. Idan ta ƙi ba ka haɗin kai, na ba ka izinin ka bulale min ita."
Uncle Jalal ya girgiza kai cikin nuna rashin kwaɗayin abin duniya...
"Zan yi iya ƙoƙarina Ranka ya daɗe. Amma ba na buƙatar kuɗin da za ka ƙara min don kawai kana so na gyara ƴarka. Nima ina so na gyara ta ne ta zama abin misali a fannin ilimin boko da na Arabic."
Sarki ya yi murmushi, ya tambaye shi, "Daga ina kake? Wato kai ɗan ina ne?"
Uncle Jalal ya amsa.
"Ni ɗan Nigeria ne, daga yankin Borno State. Kuma a nan ina zaune ne a The Royal Palace Hotel..."
(Wani babban hotel ne mai tsada da kwarjini a birnin Alhamra)..
Daga nan, Uncle Jalal ya yi sallama da Sarki ya miƙe ya fice daga sashen, ya bar Sarki cikin tunanin yadda wannan malamin zai fara jujjuya Maayah....
GA TAMBAYA
SHIN WANI SCENE NE YA FI BURGE KU?
ZAYANA KO MAAYAH?....
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 3️⃣3️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Bayan ya dawo daga masallacin dake can gefen babban filin fadarsa, iskar asuba mai sanyi tana bugun fuskarsa. Chief Onyx ya shigo babban falon inda ya tarar da Gely, PA ɗinsa kuma tsararriyar Robot mai basira, tana hidimar haɗa karin kumallo cikin natsuwa..
“Good morning, Boss,” Gely ta gaishe shi da muryarta mai sanyi da madaidaicin sauti.
Chief ya amsa a nutse, ya zare agogonsa na alfarma ya ajiye, sannan ya tambaya, “Shin Ching-Ching ta tashi ta yi sallah?”
Gely ta gyara tsayuwa, “Eh Boss, ta tashi ta yi sallah, amma ta koma bacci saboda yanayin sanyin safiyar.”
Chief ya ɗan yamutsa fuska, ya bayyana asalin Boss ɗin nasa...
“Jeki tashe ta yanzun nan. Yau za ta fara zuwa makarantar The Royal Valorant Academy... Bayan kin tashe ta, ki zo ki karɓi jakunkunanta da sabbin kayan makaranta da litattafan da na haɗa mata. Komai ya zama ready.”
Yana hawa saman ɗakinsa bai fi mintuna biyar ba, agogonsa mai tsadar gaske dake ɗauke da fasahar zamani ya fara girgiza a hannunsa. Gely ce ke kiransa ta na’urar sadarwa..
“Boss... akwai matsala. Ching-Ching ba ta da lafiya.”
A ruɗe Chief ya sauƙo ƙasa, har yana kusa tuntuɓe a kan matakala. Ya garzaya zuwa ɗakin Ching-Ching, ya tarar da ita kwance, duk da sanyin A.C dake ratsa ɗakin, jikinta duk ya jike da gumin wahala..
“Mene ne ya faru da ita?” Chief ya tambayi Gely cikin murya dake nuna damuwa..
Gely ta duba bayanan dake cikin na’urarta ta lafiya, ta ce, “Na gama bincikar jikinta. Mararta ce ke mata ciwo sakamakon First Period da za ta fara. Yau ne karon farko da ta zama budurwa.”
Chief ya zaro ido, a ɗan ruɗe... “Kina nufin... yanzu jini yana kan zuba mata ne?”
Gely ta yi ɗan murmushi na inji. “Wannan ba abin damuwa ba ne Boss, dabi’ar kowace mace ce. Shekarunta sun kai yanzu. Abin da ake buƙata shi ne abin tare jinin don kada ta ɓata jikinta...”
“Okay... Stay here!” Chief ya juya da sauri ya fita, ya shiga motarsa ya nufi babban shago cikin gaggawa..
Bayan ya dawo, ya miƙa wa Gely wata baƙar leda. Gely ta buɗe, ta kalli abin ciki sannan ta kalli Chief da mamaki..
“Boss... wannan ai Pampers ne na jarirai, na tarewa yara kashi ne... Wancan kuma Pad ne na mata.”
Chief ya shafa kansa cikin jin kunya. “Yanzu dai ya jikinta? Wancan kiyi amfani da wanda ya dace.”
Kafin Gely ta kai ga amsawa, sai suka ga Ching-Ching ta buɗe ido tana rarraba su...
“Fitsari zan yi...” ta faɗa cikin murya mai rauni, ta miƙe ta shiga toilet...
Shiru na ɗan lokaci... can kuma sai aka ji wani firgitaraccen ihu! “WAYYOOO!”
Ta fito a guje tana ihu, fuskarta cike da firgici. Chief ya cafko ta da sauri kafin ta fice daga ɗakin, ta ƙanƙame shi tana kuka da ƙarfi..
“Wayyo Allah, Uncle! Na mutu na lalace! Jini! Jini! Wallahi na ji ciwo a ɗuwawu naaa! Wani ya soka min wuƙa ban sani ba!”
Ta cigaba da kwarara surutai, tana ƙara matse Chief, fuskarta ta yi ja saboda tsoro. Chief Onyx wanda damuwa ta lulluɓe shi, sai da ya ji dariya na neman kufce masa saboda jin abin da ta faɗa..
“Yi shiru, babu wanda ya soke ki,” ya faɗa yana ƙoƙarin danne dariyarsa, yayin da yake shafa kanta don rarrashi. “Ƙaruwa kika yi, kin zama budurwa.”
“A’a Uncle! Jini ne fa! Na mutu, kaga yadda yake zuba!” ta ƙara sa da ihu, tana ɓuya a ƙirjinsa.
Bayan an gama wannan guje-guje na firgici, Chief Onyx ya samu nasarar dawo da Ching-Ching kan gado. Ya zauna a gefenta, ya sa hannunsa duka biyu ya kamo nata, yana kallon yadda take kuka tana shashsheka kamar wadda aka yi wa mutuwa...
“Yi shiru na ce miki, babu wani abin tsoro,” Chief ya faɗa cikin muryar lallashi, yana ƙoƙarin danne dariyar da take taso masa duk lokacin da ta ambaci ciwon ɗuwawu...
Chief Onyx ya gyara zama, ya dube ta da idon gaske don ya yi amfani da damar ya ba ta ilimin zamantakewa, amma cikin sigar tsoratarwa irin ta manya...
YA ce murya ƙasa-ƙasa
“Saurara min nan Ching-Ching. Daga yau fa kin zama babbar mace, ba yarinya ba. Kuma ki buɗe kunnenki da kyau, daga yau, kada ki kuskura ki bar wani namiji ya taɓa ki. Ko hannunki namiji ya riƙe, to fa za ki iya ɗaukar ciki nan take!”
Ching-Ching ta zaro ido, ta daina kukan lokaci guda. Ta kalli hannunta ta kalli na Chief dake riƙe da nata.
Sai kuma ta turo baki ta ce,
“Da gaske Uncle? Yanzu kenan zan iya haihuwa? Amma gaskiya ni bana son jinin nan, jini ne he kace wanda aka yanka akuya!”
Ta ƙara sautin kukan, “Kaiii nifa ban yarda ba! Dole wani ne ya zo ya caka min wuƙa a wurin fitsarina don mugunta. Ko ma hala Gely ce ta soka min!”
Gely, wadda ke tsaye kamar gunki a gefe, ta juya kanta zuwa ga Ching-Ching, idanunsa na Robot suna ba da hasken bayani,
"Ni ban taɓa taɓa ki da wani abu mai kaifi ba, Shugaba Ching-Ching... Wannan tsari ne na halitta.”
Ching-Ching ta harare ta duk da yanzu suna shiri, ta ce, “Rufe min baki! Ke dake da hannun ƙarfe ai ba kya jini. Ni dai Uncle kaji na gaya maka, wanda ya yi min wannan muguntar sai na rama...”
Chief Onyx ya girgiza kai, ya da fa kuncinsa yana kallon wannan dambarwar..
DAga bisani ya ce,
“Ban da surutu. Sannan kuma tun da jinin nan ya zo, duk abin da kika yi na rashin jin magana, za a fara rubuta miki zunubi. Mala’iku sun shirya takarda yanzu...”
Ching-Ching ta tsaya cak, ta yi tunani na daƙiƙa biyar. Sai kuma ta washe haƙora, ta matso kusa da Chief har tana gogar hancinsa...
“To Uncle, tunda kace idan namiji ya taɓa ni zan yi ciki... yanzu kai ai namiji ne, kuma kana ta riƙe ni. Kenan yanzu zan haifi baby Chief?”
Chief Onyx ya ji gabansa ya faɗi, ya ji kamar ya tashi ya gudu...
“A’a! Ni... ni daban ne! Ni ai Uncle ɗinki ne.”
Ta ce, “Hmm! Uncle ne ko baban baby ne? To ni dai gaskiya idan zan haihu, ba zan haifi baby boy ba, sai baby girl kamar niiii...”
Chief ya tashi tsaye yana gumi, ya kalli Gely..
. “Gely, koya mata yadda za ta yi amfani da kayan da na kawo. Ni dai zan fita, kafin wannan yarinyar ta haukatani da maganganunta.”
Yana fita, ya ji ihun Ching-Ching daga ciki.. “Uncle! Zo ka tafi da Pampers ɗinka, ni ba jaririya ba ce!”..
Washegari da komai ya lafa...
Chief ya tambayi Gely game da school ɗinta tinda tana wannan yanayin...
Gely ta sanar cewa "ba matsala zata iya zuwa, saboda da haka mata suke rayuwa a cikin jini kuma babu mai gane wa..."
A lokacin ya sanar da a shirya ta..
Bayan wasu mintuna Ching Ching ta wankanta tayi brush...
Tana zaune a gaban babban madubin dake dakinta, Gely ta gama baje basirarta na Robot. Ta gyara mata gashinta, ta yi masa wani irin lallausan design a gaba wanda ya fito da tsantsar kyan fuskarta. Ta saka mata kyakkyawan uniform ɗin The Royal Valorant Academy, riga fara mai dogon hannu, da tie dake wuyanta, sannan aka dora mata ɗan short riga mai kalar navy blue da ya tsaya dai-dai gwiwarta...
A karshe, aka dora mata hular beret mai launin rigar din. Ching-Ching ta goya jakar makarantarta a baya, ta fito kyakkyawa kamar balarabiya, sai dai tana turo baki alamar ba ta saba da wannan shigar ba...
Suna saukowa falon a jere ita da Gely, Chief Onyx ya dago kansa daga jaridar da yake karantawa. Ya tsaya turus, idonsa ya kasa ɗaukuwa daga kan Ching-Ching. Gaba daya kyan da tayi yanzu ya ninka na baya sau goma
Duk da kyan da ta yi, abu daya ne ya sa Chief ya dafe kai....Tafiyarta.
Ching-Ching ta fara takowa, amma kafafunta a ware suke, ba sa haɗuwa. Tana tafiyar ne kamar agwagwa, tana wani nishi-nishi...
Cikin mamaki ya tambaye ta “Meye haka kuma? Wane irin tafiya ce wannan? Kin kakkarya ƙafafun ne?”
Ching-Ching ta tsaya tana hararar sa daga baki har hanci,
“Yooo! Baka ga abinda aka danna min a gaban mafitsara na bane? Taya zan iya tafiya normal kuma?”
Chief ya ce, “Kowace mace idan tana cikin wannan yanayin ai tana sa Pad, kuma tana tafiyarta normal ba tare da kowa ya gane ba. Maza gyara tafiyar nan!”
Tana turo baki ta ce,
“A’a Uncle! Ni nawa daban ne, ƙarami ne ai! Kuma haka kawai sai in bari wurin ya yi ta ji min ciwo a cinyoyina? Ni dai haka zan tafi, idan kaga dama ma ka turo ni a wheel-chair!”
Chief ya girgiza kai, ya san idan ya tsaya ja-inja da ita to ba za su bar gidan ba yau. “Muje to. Idan aka fara miki dariya a makarantar ai dole zaki gyara da kanki.”
Ching-Ching ta kalli kanta a madubin falon, ta kalli rigar din dake iya