Showing 60001 words to 63000 words out of 154131 words

Chapter 21 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

na gimbiya kuma auta mai ƙaramar shekaru? Shekararta nawa wadda ba ta fi 16 ba? Haba don Allah, me ya sa Abul zai yi mana haka? Me ya sa sai Chingching? Ga ni, ga Maayah, ga Yumna, ga Zayana... me ya sa sai ita wadda ba ta iya komai ba sai shagwaɓa?"....

Kwananta biyu a bata leƙo falonta ba, sannan bata fita wurin aikin tsaro ba a matsayinta na PA Ibrahim..

Tana cikin wannan halin ta ji ƙarar ƙararrawar ɗakinta na tashi. Ta san cewa ba za a bar ta ta ci gaba da zama a haka ba. Ta tashi da kyar, ta murɗa key ta buɗe ƙofar da ta daɗe a rufe tun shekaran jiya...

Uma Saratu, uwar ɗakinta mai kula da ita, ta shigo cikin gaggawa da damuwa...

"Gimbiya lafiya kuwa? Tun kwana uku ake zuwa dubaki amma kin ƙi buɗe ƙofa. Anyi-anyi har an sanar da sarki cewa kin kulle kanki a ɗaki tun safe...

Shima kuma yana fama da alhinin rashin autarsa."..

Ayat, ko a wannan yanayin, ba ta rage izzah da kwarjininta ba. Ta kalli Uma Saratu ta ce..

"Kun san yana cikin alhini, kuma kuka sanar masa batu na?"

Uma Saratu ta yi ajiyar zuciya,

"To ai munga ba lafiya ba. Yanzu fa magariba ake shirin ƙira, kuma tun bayan kwana uku aka ji ki shiru. Ba ci, ba sha, ba walwala..."

Ayat ta ɗan ɗaure fuska,

"Bai kamata kowane abu kuna sanar wa sarki ba. Tunda kun san ina ciki, buɗewa ne ban yi ba, meye amfanin sanar masa?"

"Gimbiya, rai da mutuwa ai ba sa haɗuwa," in ji Uma Saratu cikin rarrashi. "Idan da rai ai ba mu sani ba ko kina halin rashin lafiya."

A lokacin ne Ayat ta kalli Uma Saratu da idanunta waɗanda suka yi jawur saboda kukan da ta sha...

Uma Saratu ta tsorata, "Lafiya kuwa Gimbiya? Ya idanuwanki suka yi jawur haka kamar wuta? Kuka kika yi ne?"..

Ayat ta kasa boyewa, ta furta..

"Ƙanwata ta tafi, ya zan yi da rayuwata?"

Uma Saratu ta yi mamaki, "Amma ta yaya kika san cewa Chingching ba ta nan alhalin kina kulle a ɗaki?"

Ayat ta ce,

"Tin ranar da sarki ya ƙira mu fada yake sanar mana, nasan kinsan da hakan. Hakan ya sa na kulle kaina a ɗaki, ba na son damuwar kowa."..

Uma Saratu ta ji tausayin gimbiyar tata sosai, ta yi mata fatan alheri tare da tabbatar mata cewa kanwar tata za ta dawo lafiya...

Ayat ta buƙaci a haɗa mata ruwan wanka domin ta wanke damuwar dake jikinta. Lokacin da Uma Saratu ta yi kokarin tilasta mata ta fara cin abinci, Ayat ta nuna fushinta..

"Haba Uma Saratu, me ya sa kuke jayayya da ni ne? Idan na ce a min abu kaza sai ku ce a'a. Shin haka ake yi wa sauran gimbiyoyin ne?"

Cikin sauri Uma Saratu ta ba da hakuri, ta shiga haɗa mata ruwan wanka tare da fesa turaruka masu sanyaya rai a ko'ina a cikin bedroom ɗin don gyara yanayin dakin...



A ɗayan ɓangaren masarautar, Gimbiya Maayah tana zaune a cikin katafaren falonta... Kwakwalwarta tana cike da tunani guda biyu, na farko, yadda za ta sake haɗuwa da kyakkyawan jami'in tsaron nan, Inuwa, wanda ya tafi da tunaninta. Na biyu kuma, tana nazarin me ya sa za'a bada Ching Ching a masarautar pavilion?. Duk da ba ta taɓa ganin Chief Onyx ba, labarin kwarjininsa da ƙarfin mulkinsa ya isa ya sanya kowa fargaba...

Duk kwana biyun nan basu san da cewa an riga an tafi da Ching Ching ba domin hatta ma'aikatansu ba komai suke sani game da masarautar ba...

Gashi yau har mako guda da faruwar haka amma banda Ayat babu wanda ya sani a cikin gimbiyoyi...

Tana zaune ta ƙura wa plasma ɗinta ido, amma ba kallon take yi ba, tunani ne ya yi mata yawa.

Mama Liyatu, uwar ɗakinta, ta shigo falon a guje, fuskarta cike da tashin hankali...

"Gimbiya Maayah mun shiga uku!" ta faɗa cikin rawar murya...

Maayah ta juyo a slow cikin fushi, ta katse ta cikin gadara..

"Kin shiga uku dai ke kaɗai! Amma kada ki sake sako Maayah a cikin shiga uku, na gaya miki. Faɗi abin da za ki faɗa."..

Mama Liyatu ta sunkuya, "Allah ya ba ki haƙuri. Amma na zo na sanar da ke cewa Sarkin Pavilion ya tafi da Auta Chingching a matsayin baiwarsa."...

Maayah ta zaro ido cikin mamaki na ɗan lokaci,

"What?! Shi sarki yana ina aka yi hakan?"

"Sarki yana wurin amma bai iya cewa komai ba," in ji Mama Liyatu...

Maimakon Maayah ta nuna damuwa ko tausayi ga ƙanwarta, sai ta ɗaga kafaɗa cikin ko-o-ho ta ce..

"Alright. Shi sarki bai iya cewa komai ba, to ni me zan yi a kai? Yanzu dai sarki ya nuna cewa kwarjinin da yake da shi ya tashi a aiki ke nan, tunda har zai ji fargabar tunkarar Sarkin Pavilion har ya iya tafiya masa da ɗiya a matsayin Maid. To lallai wannan sarautar ta faɗi ƙasa!"

Ta kalli Mama Liyatu cikin ƙasƙanci, "Kinga Mama Liyatu, ba na son damuwa. Ki tashi ki ba ni wuri."

Mama Liyatu ta miƙe jiki a sanyaye ta bar falon, tana mamakin irin zuciyar Maayah. Ita kuwa Maayah, tana ganin ta fita, ta ci gaba da kallon Plasman ta, ta kawar da zancen Chingching daga ranta kamar ba abin da ya faru, burinta kawai shi ne yadda za ta sake ganin Inuwa...



A cikin daren nan, a ɗayan bangaren sashen gimbiya Yumna...

Wata matashiyar ma'aikaciya siririya wacce aka fi sani da 'Yar mitsila tana gudu tana cilla sirarrun sawayenta a guje...

Ta bankaɗo babban ƙofar falon tana kwala ƙira cikin ɗakin...

"Gimbiyata Yumna! Gimbiyata Yumna!! Gimbiyata Yumna kina inaaaa?..."

Ba tare da jiran izini ba, ta haura saman bedroom ɗin Yumna ta tura kofar ta shige. Tana shiga ta tarar da Gimbiya Yumna a kan sallaya tana sallah...

'Yar mitsila ta samu wuri ta zauna zaman jiran ta, tana haki...

Yumna ta idar da sallar, ta ɗaga hannu ta yi addu’o’i, sannan ta shafa fuskarta..

Ta juyo tana murmushi duk da cewa ƙiran Ƴar mitsila ya ɗan tsorata ta, ta ce..

" 'Yar mitsila, dodo ne ya koro ki ko ya ya?"

'Yar mitsila ta gyara zama,

"Labari da ɗumi-ɗuminsa nazo miki da shi! Nima sai yanzu nake tsintar labarin nace da dukkan alamu baki sani ba, bari nazo in shafa miki..."

Yumna ta yi dariya, "Shafa min naji kawataaaa..."

'Yar mitsila ta fara zayyano mata..

"Wai wani sarki ne mai kwarjinin bala'i ne ya ziyarto cikin masarautar nan. Ban ganshi ba amma ance da na ganshi to zan yi sumar tsaye! Kaiii Aradu ya ninka sarki kyan yanayi, ko dan shi ɗin ɗan matashin saurayi ne oho..."

Yumna ta ce "To pah, wani irin sarki ne haka? Sarkin ina ne?"

'Yar mitsila ta yamutsa fuska tana kokarin tuno sunan,
"Aradu ni ban riƙe sunan ba amma dai kamar Sarkin Pa, Pa, Pabi... Pabimila... ko dai Pabiliya? Yawwa yawwa Pabiliya!"

Yumna ta yi murmushi, "Wai Sarkin Pavilion kike nufi?"

'Yar mitsila ta zabura, "Yauwa ehhh shiii!"

Yumna ta yi salati, "Subhanallahi! Me ya kawo shi kuma? Shi da na ji labarin duk sanda ya zo masarautar nan to yaƙi ne zai tashi, innalillahi..."

Ta nuna kamar bata san shi ba...balle ta nuna sun san juna...

'Yar mitsila ta karkaɗe hannu,

"To yanzu dai ba yaƙin bane. Ya zo ya cicciɓi autarku Chingching ya tafi da ita, wai zai mayar da ita bazawararsa!"

Yumna ta dafe ƙirji tana zaro ido cikin gigita,

"Yaaa ALLAH! Bazawara kuma? Ya tafi da ita?"

'Yar mitsila ta ci gaba da zugawa,

"Ahh to! Ance saurayi ne bai taɓa yin aure ba, kuma ya zo ya ɗauki yarinya to me kenan? Kumaaa ance mace da namiji in sun haɗu shaidan ne a tsakiya... to kinga bazawara kenan zai mayar da ita, kuma ya fake da wai wai wai 'yar aikinsa..."

Hawaye suka cika idanun Yumna, ta dakatar da 'Yar mitsila cikin rawar murya..

"Kinga ya isa haka! Wannan ba labari mai daɗi ba ne ai. Kuma ki daina cewa zai mayar da ita bazawara, ba haka ba ne a ransa. Shi fa na ji labarin dan uwanmu ne, ba zai cutar da ita ba... kawai ki tashi ki tafi, zan yi addu'a."..

'Yar mitsila ta miƙe tana ƙunƙuni,
"Ah to! Yanzu ai ba'a maganar ɗan uwantaka, shaiɗan ba ruwansa da wannan..."

Daga nan ta fice daga ɗakin...

Tana fita, Yumna ta fara wasu zafafan hawaye, tana tausayin 'yar kanwarsu Chingching da aka kai wata duniya daban...

Ta wani ɓangaren kuma tana ganin ai duk jini ɗaya ne, kuma tana da yaƙini akan Yayanta, zai kula da ita sosai..



A cikin sashen Gimbiya Zayana, komai a gyare yake tamkar kana cikin birnin Sydney...

Zayana tana zaune a kan kafet mai laushi tare da ɗiyarta Mimi, tana koya mata rubutu. Zayana na sanye da riga marar nauyi, gashinta ruwan zinare ya bazu a bayanta..

Suna tsaka da hakan, wata baiwar part ɗin ta shigo tana haki, ta durƙusa a gabansu tana ƙoƙarin daidaita numfashinta don faɗin labarin da ya firgita masarautar...

Mimi, ganin ma’aikaciyar ta kasa magana sai haki take, sai ta ɗauki kofin ruwan juice ɗin da suke sha, ba tare da wata fargaba ba, ta watsa wa matar a fuska..

Baiwar ta zabura ta dafe fuskarta, ruwan lemon yana ɗiga daga jikinta. Zayana ta kalli Mimi da idanunta masu kalar na kyanwa (cat eyes), ta tambaye ta cikin yaren Turanci..

"What did you do that for?"

Mimi ta turo baki, cikin muryar yara mai cike da raini ta amsa da Hausa..

"Naga ta ƙi nutsuwa ne shi yasa na watsa mata lemon."

Maimakon Zayana ta tsawatar mata, sai kawai ta yi murmushin jin daɗi, tana jin daɗin yadda Mimi take nuna gadara. Ta kalli baiwar ta ce,
"Lafiya?"

Baiwar ta share fuskarta, muryarta na rawa ta ce,

"Chief Onyx ne ya tafi da Chingching can yankinsa a matsayin baiwarsa."

Zayana ta gyara zama, fuskarta a washe da annuri,

"Hakan ya min daɗi sosai! Ashe ba maganar yaƙi ne ya kawo shi ba?. Let me call my mom, zan sanar da ita kayataccen albishir, ta sauƙe makamanta kawai tunda ba matsayina aka taɓa ba."

A wajen Zayana, damuwar kanwarta ba komai ba ce, muddin ita tana cikin ƙoshin lafiya, to komai ya tafi yadda ake so...

Ta kori matar da hannu, amma matar na shirin tashi, Zayana ta daka mata tsawa...

"Ke ƙazama! Haka zaki bar min wannan jikar ruwan juice ɗin da aka watsa miki a wurin?"

Matar ta koma da sauri, ta cire dankwalinta ta fara gogewa tana kuka kasa-kasa. Tana gamawa ta gyara wurin tas, Mimi ta kalli fuskarta, sai ta sake dauko ragowar juice ɗin dake cikin kofin, ta sake karkaɗe shi a dai-dai inda matar ta gama gogewa...

Mimi ta yi dariya tana nuna matar da yatsa, "Ki sake gogewa, har yanzu akwai datti."

Zayana ta saki wata 'yar dariya mai sauti tana kallon yadda matar take ƙara ninkewa tana goge wurin cikin kaskanci...

"Goge da kyau ƙazama, sannan ki ɓace mana da gani kafin na sa a miki hukunci," in ji Zayana...

Matar ta gama tana karkarwa ta fice, yayin da Zayana ta dauki wayarta don kiran mahaifiyarta Ruma, tana farincikin cewa rigimar Pavilion ba za ta shafe ta ba tunda an tafi da Chingching...



A duniyar King Diamond ganin abokinsa Prince Zarith ya fara magana akan golden armor, hakan yasa ya ƙudiri cewa zai je ya ɗauko duk da wurin na da haɗari...

Ya bayyana a gaban ƙofar kogon, idanunsa na haske da jarunta duk da cewa ya san tsafe-tsafe ne ke gadin wurin. Masu gadin, ba mutane ba ne, wasu halittu ne masu siffar dabba amma da ran aljanu suka far masa lokaci guda...

Diamond bai yi ƙasa a gwiwa ba. Da dantsensa mai ƙarfi ya riƙo takobinsa da ya bayyana cikin iska..
Lokaci guda ya dinga raba kawunansu, jini na fantsama a jikin bango..

Kowane sara ɗaya, mutuwa ɗaya. Bayan dogon faɗa da ya bar shi da fuskarsa cike da jini da gumi, ya yi nasarar kawar da su gaba ɗaya..

A tsakiyar ɗakin, can bisa wani dakalin dutse, Golden Armor yana sheƙi, yana haskaka duhun kogon..

Diamond ya taka a hankali, ko da yake numfashinsa na fita da sauri saboda gajiya. Ya sa hannu ya damƙi armor...

A take, wata irin tsawa ta ratsa kogon. Cire sulkun daga inda yake ya zama silar rugujewar duk tsafin da ke riƙe da dutsen kogon..

Ƙasan kogon ya fara tsagewa, manyan duwatsu daga silin ɗin kogon suka fara fadowa. Diamond ya yi ƙoƙarin tsallakawa waje, amma babban dutse ya daki kafaɗarsa, ya ji ƙarar karyewar ƙashi. Kafin ya kai ga fita, sauran silin ɗin wurin ya rufo kansa da wani irin mugun ƙarfi...

Ƙura ta turniƙe wurin, ƙarar rushewar ta cika dajin. King Diamond ya ɓace a cikin baraguzan duwatsun, rungume da Golden Armor, yayin da jini ke malala daga raunukan da ya ji. Shiru ya biyo baya, sai hayaki da ƙurar duwatsun da suka binne shi....



Maayah tana tsaye a gaban babban madubi a ɗakin shiryawarta. Ta sanya kayan makarantar amma nata ya sha bamban da na kowa, an ɗinka shi da wani tsadadden yadi mai sheki, an goge shi ya fito da layin guga raɗau. Tana sanye da farar riga, kyakkyawa mai dogon hannu, da pleated red skirt wanda ya tsaya daidai gwiwarta. Ta ɗaure gashinta wanda aka sanya masa wani ribbon na alfarma mai kalar zinare...
Da haka take barin gashin ba rufe wa, a makarantar ba'a saka hijab, akwai jar hula mai kalar skirt wanda aka tanada wa musulmai, Christian kuma babu komai, itama Maayah bata wani sanya hula, lokaci lokaci take sakawa...

Tana sanye da takalman fata baƙaƙe masu sheki (designer loafers) da safa fara tass. Kamshin turarenta ya cika ko’ina, kamshi ne mai karfin da ke nuna cewa na masu kuɗi ne. Ta rataya karamar jakar makarantar ta a kafada ɗaya, fuskarta babu ko murmushi, sai wani kallo na rainin wayo...

Tana fitowa daga sashenta, bayi da hadimai kowa sai sunkuyar da kai yake yi. Ba ta ko kallon gefen kowa. A harabar fadar, jerin motoci biyar bakake (Black SUVs) suna jiran ta, kofofin a buɗe. Tana shiga daya daga ciki, motocin suka lula zuwa makaranta...

Kamar kullum, isar Maayah makaranta tamkar isar wata shugabar ƙasa ce..

Motocin suka raba tsakiyar makarantar, dalibai suka tsaya suna kallo. Da zarar motar ta tsaya, bodyguards hudu sanye da bakaken kaya da bakaken tabarau suka fito da sauri. Ɗaya ya buɗe mata ƙofa, ya kare mata kai...

Maayah ta fito daga motar cikin taƙama. Ta tsaya na sakanni kaɗan, ta gyara tsayuwar jakarta, sannan ta sanya baƙi tabarau. Ta fara tafiya, bodyguards biyu a bayanta, biyu kuma a gaba suna share mata hanya...

Ɗaliban da ke magana duk suka yi tsit. Waɗanda ke wasa suka dakata. Duk wanda idonsa ya sarƙe da nata, sai ya saurin kawar da kai don tsoron kar ta ce yana kallonta da yawa..

Tana tafiya ne kamar ba ta san taka ƙasi. Ta isa corridor din ajinsu, sai ga Hafsat yar President ta taho da sauri da fara’a..

"Good morning Maayah! Kin zo yau da wuri."

Maayah ta tsaya, ta rage tsayin tabarunta kaɗan ta kalli Hafsat, sannan ta gyaɗa kai kawai ba tare da ta ce komai ba...

"Hafsat, ki tabbata kinyi min ajiyar bayanan darasin farko, ba na son surutu yau," abin da Maayah ta faɗa kenan cikin muryar isa, sannan ta wuce ta bar Hafsat a tsaye tana murmushin ƙarfin hali...

Maayah ta zauna a mazauninta na musamman wanda babu wanda ya isa ya taɓa. Malamin lissafi ya shigo, amma ko kallonsa ba ta yi ba, ta buɗe littafinta tana dubawa. Ko da malamin zai yi tambaya, baya kallon bangarenta don gudun ɓacin ranta, domin kowa ya sani, Maayah ba ɗaliba ba ce kawai, ita Gimbiya ce wacce dokar makaranta ba ta hau kanta yadda ta hau kan kowa ba...

An shiga darasin English Literature. Sai dai a wannan karon, ba tsohon malamin da aka saba gani ba ne ya shigo, sai wani sabon malami, Mr. Collins, wanda ya fito daga ƙasar waje kuma bai san matsayin Maayah ba sosai...

Maayah tana zaune, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana danna wayarta ta iPhone, abin da aka haramta wa kowane ɗalibi a makarantar.

Mr. Collins ya tsaya a gaban aji, ya kalli kowa sannan idonsa ya sauƙa kan Maayah. Ya murtuƙe fuska...

"Ke kuma wace ce? Kuma me ya sa kike danna waya a lokacin darasi na? Ajiye wayar nan yanzu ki tashi tsaye!"...

Aji ya yi tsit. Sauran ɗaliban har da Hafsat suka fara zare ido, wasu suna kallon juna cikin fargaba. Maayah ba ta ko ɗaga kai ba, balle ta nuna ta ji me yake faɗa. Ta ci gaba da abin da take yi...

Mr. Collins ya fusata, ya taka har gaban teburinta, ya buga teburin da ƙarfi...

"Ba da ke nake ba? Na ce ki ba ni wayar nan kuma ki fice daga ajina!"

A hankali, Maayah ta ajiye wayar akan teburin. Ta ɗago kanta a hankali, idanunta cike da izzah da wani irin kallo na rainin wayo da isa. Ba tare da ta tashi tsaye ba, sai ma ƙara gyara zama da ta yi...

"Shin ka san wacece kake yi wa ihu?" Maayah ta tambaya cikin sanyin murya mai cike da kwarjini da barazana...

Mr. Collins ya nuna ta da yatsa,

"Ban damu da ko wace ce ke ba! A nan, ni ne malami, ke kuma ɗaliba ce. Fita waje!"

Maayah ta yi ɗan gajeren murmushi na mugunta, sannan ta yi wa ɗaya daga cikin bodyguards ɗinta da ke tsaye a bakin ƙofar aji alama da yatsa...

Nan take bodyguard ɗin ya shigo ciki cikin takunsa na ƙasaita. Maayah ta kalli malamin, ta ce.

"Ba na son ganin fuskarsa a cikin wannan makarantar nan da minti biyar. Kuma ka gaya wa shugaban makaranta ya neme ni don ya ba ni haƙuri akan wannan ɓata lokacin da aka yi min."..

Malamin ya tsaya baki buɗe, yana shirin yin magana sai bodyguard ɗin ya dafa kafaɗarsa, ya dube shi cikin wani irin kallo na kashedi...

"Sir, mu tafi, kafin ranka ya ɓaci," in ji bodyguard ɗin.

Maayah ta sake ɗaukar wayarta, ta ci gaba da abin da take yi kamar ba komai ya faru ba. Hafsat ta saci kallonta, ta girgiza kai cikin tsoro da mamakin yadda Maayah take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login