Showing 42001 words to 45000 words out of 154131 words
Chapter 15 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
sha'awar saye amma duba aljihunsa ke da wuya, sai ya ga kuɗin jikinsa ba zai isa yayi siyayyar da yake so ba. Cikin sanyin jiki ya kawar da kansa ya yi gaba...
Ba tare da ya sani ba, King Diamond yana biye da shi a baya, idanunsa na yawo akan kowane motsi na Ayat, amma sai dai a wannan lokacin bai fito a mai siffar farin gashi ba, ya koma gashinsa irin na ko wani mutum amma yana sanye da fararen kaya domin yana son farin abu a rayuwarsa....
Ganin yadda ta bar wurin mai zaƙin nan cikin rashin nasara, King Diamond ya isa wurin, ya nuna abin sannan ya ciro guda ɗaya daga cikin tsayayyun lu'u-lu'unsa ya miƙa wa mai sayarwa. Mai tallan ya daskare, ya kasa yarda cewa an biya shi da lu'u-lu'u akan kayan zaƙi!..
Inuwa ya cigaba da tafiya har ya tsaya a wurin mai snacks, ya sayi wasu ƴan abubuwa ya cigaba da tafiya. King Diamond ya sake tsayawa a wurin, yana kallon bayanta cikin nazari...
"Tana son cakes ne?..." ya tambayi kansa a hankali. Shi ma ya sayi wasu nau'ukan snacks ɗin, ya sake biyan mai sayarwar da lu'u-lu'u. Mai snacks ɗin ya fara murna da rawa domin abin da aka biya shi ya fi ƙarfin abubuwan da yake sayarwa ninkin-ba-ninki...
Daga ƙarshe Inuwa ya tsaya a wani babban tebur dake cike da littafai. Mai tallan yana ta shela..
"Books for sale! Littafai na tarihin duniya!"
Inuwa ya fara dubawa, can sai idonsa ya sauƙa akan wani littafi mai taken "The Legend of the White Cat."
Wani murmushi na natsuwa ya bayyana a fuskarsa, ya sayi littafin cikin farin ciki ya rungume shi, ya cigaba da tafiya...
King Diamond ya ƙaraso wurin mai littafin, idanunsa suna kallon yadda Inuwa yake tafiya yana rungume da littafin nan...
"Kana son littafai ne, Sir?" Mai littafin ya tambaya cikin girmamawa..
King Diamond bai amsa ba, ya zura wa bayanta ido yana maganar zuciya..
"Me ya sa take farin ciki da sayan littafi kuma? Me yake cikin wannan takardar da ya sa ta murmushi haka?"
Ya ji wani irin shauƙi na son sanin komai game da ita, abin da take so, abin da yake sa ta dariya, da kuma abin da take karantawa a cikin sirri..
King Diamond ya matso kusa da mai littafin, idanunsa har yanzu suna kan Ayat dake ƙoƙarin ɓacewa cikin taron mutane..
Cikin murya mai natsuwa da iko ya yi tambaya..
"Shin kuna da littattafai waɗanda suka fi waɗannan inganci da kuma ƙarancin samu?"
Jin wannan tambayar, mai littafin ya matso kusa da shi cikin girmamawa yana mamakin kwarjinin wannan baƙon mutumin. Ya tambaya,
"Wane irin littattafai ne kake nema waɗanda ba a cika samu ba? Ko irin su Spring palace"...
King Diamond ya ɗan yi shiru sannan ya ce,
"Ko Spring Palace ko Winter Palace, ko ma mene ne... muddin dai ba a cika samun su ba. Kuma dole ne su kasance suna magana ne akan Jin King’s Requite..."
Mai littafin ya jinjina kai, fuskarsa cike da fara'a ya ce.
"Eeee... muna da littattafai akan Requite."..
Daga nan, mai littafin ya buɗe wani akwati na musamman ya ciro wani littafi mai taken..
"Prince Regent’s Requite"
Ya miƙa wa King Diamond littafin yana ƙarin bayani..
"Babban jarumin wannan littafin ba Jin King ba ne, sarki ne shi ma."..
King Diamond ya karɓi littafin, ya bi rubutun dake jikin bangon littafin da kallo. Ta ke ya karanta sunan littafin a ransa..
"An Evilly Charming Emperor’s Requite"
Ma'ana (Sakamakon Wani Mugun Sarki Mai Kwarjini da jan hankali..)..
Ba tare da ɓata lokaci ba, ya karanta ɗan taƙaitaccen bayanin farko da na ƙarshe dake cikin saƙon siyan littafin, yana ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa Ayat take sha'awar irin waɗannan labaran. Ya ji wani irin murmushin gefen baki ya subuce masa, yanzu ya fara gano hanyar da zai bi ya shiga zuciyarta ta hanyar abubuwan da take so...
King Diamond ya buɗe shafin farko na littafin, idanunsa suna yawo akan kalmomin da aka rubuta da fasaha. Ya furta a hankali,
"Alƙawarin rayuwa?... haka sarakuna suke biyan sakamakon soyayya."
Mai littafin ya gyaɗa kai cikin gamsuwa, ya ce, "Haka ne, ka gane ma'anar kenan."..
Wani sanyayyen "Ohhh!" ya fito daga bakin King Diamond, yayin da wani haske ya ratsa ƙwaƙwalwarsa..
"Ashe shi ya sa ba ta taɓa gaya min ba duk da lokacin da muka ɗau a wancan lokacin..." Ya fara fahimtar cewa Ayat tana ɓoye abin da yake ranta ne saboda kunya ko kuma girman abin da take ji...
Mai littafin ya yi murmushi, ya ƙara da cewa,
"Ai tana da kunya ne.... Ya kamata ka kasance mai nuna himma da ƙwazo wajen neman soyayyarta."
Ya ƙarasa maganar yana ɗan dariya, yana ƙarfafa wa King Diamond gwiwa...
King Diamond bai sake cewa uffan ba, ya tsaya kawai yana kallon mai littafin da wani kallo mai zurfi. Sannan ya sanya hannu cikin aljihunsa, ya ciro ƙarin wasu lu'u-lu'u masu tsada, ya miƙa wa mutumin a matsayin lada...
Mutumin ya karɓi diamonds ɗin hannunsa na rawa, ya shiga murna da farin ciki maras iyaka, domin wannan abin ya fi ƙarfin duk wani littafi da ya taɓa sayarwa a rayuwarsa..
King Diamond ya juya ya bar wurin yana rungume da littafin An Evilly Charming Emperor’s Requite a ƙirjinsa. Yanzu ya sami makamin da zai yi amfani da shi wajen narkar da zuciyar Ayat.. zai koyi yadda ake zama sarki mai jan hankali wanda zai iya sadaukar da komai don masoyiyarsa....
Daga kasuwa kai tsaye masarautar ta nufa, a bakin gate ta tarar da master Ibrahim..
Ta ƙarasa tana dariya, ta gaishe shi..
Master ya ce, "ina ka je?..."
Inuwa ya ce, "na shiga kasuwa ne.."
Ibrahim ya sauƙe idonsa akan littafin da ke hannunsa ya karɓa yana faɗin "wannan fa? Kaima kana son karanta littafan almara ne...?"
Inuwa ya jinjina kai tare da faɗin "Eeee! Master..."
Ya jinjina kai sannan ya ba shi umarni da ya shiga...
Yana hanyarsa ta koma wa sashensa sai kwatsam ya haɗu da wasu jami'an da ya gane su, sune masu tsokanarsa...
Nan suka dakatar da shi suna faɗin "Ya Ɗan ƙwaƙur ya akayi ne..."
Ɗaya daga ciki ya make mazauninsa tare da faɗin
"Ɗan ƙwaƙur mai manyan ɗuwawu...burgeni suke saboda mata ne masu irin shape ɗin ɗuwawun nan..."
Ɗaya ya ce, "ai tin da yana da ɗuwawu to bazai rasa nonuwa ba, mu ji su..."
Ya kai hannu yana shirin taɓa su, Ayat tayi saurin ja da baya..
Tana shirin bin ta gefensu ta wuce suka riƙo ta, suna faɗin...
"Muna son yau mu ji ya girman zarman lulunka yake, mun ji labarin kana neman mata..."
Ɗaya ne ya kai hannunsa da sauri wurin gabanta, ya yi nasarar canke wa, da sauri Ayat ta ja da baya...
Mutumin ya zaro ido cikin izgilanci yana faɗin "kaiii ya ban ji komai ba, Ɗan ƙwaƙur ko dai har yanzu kaciyar takan bata girma bane, kuma da haka kake biyan buƙatarka a wurin mata?...."
Sauran ma hannu suka kai zasu taɓa su ji, kawai suka ji an riƙe hannunsu tare da murɗawa...
Waiwayowan da zasu yi sai suka ga Master Ibrahim ne, haka gaba ɗaya ya riƙe hannunsu su ukun ya fara muɗewa, ihu suka shiga yi suna bashi haƙuri..
Shi kuwa sai da ya ji hannunsu yayi ƙaƙasss kafin ya sakar musu, ya juya zai kalli yanda Inuwa ya ke akan su bashi haƙuri sai ya ga bata nan, tin zuwan Ibrahim ta sulale ta gudu...
Babu wanda yasan hanyar da ta bi, ta shiga private garden yanda hanyar sirrinta yake wurin koma wa part ɗinta...
King Diamond yana tsaye a bayan masarauta, inda hasken dake jujjuya aljani ya zamar da shi toka yake ta walƙiya. Ya san idan ya yi ƙoƙarin shiga da jikinsa to rayuwarsa za ta shiga haɗari...
Ya kalli ledar da yake ɗauke da Sugar-coated Haws da kuma sauran snacks ɗin da ya saya mata a kasuwa..
"Aayat..." ya raɗa sunanta a cikin zuciyarsa, yana amfani da igiyar jinin dake tsakaninsu..
Maimakon ya shiga, sai ya yi amfani da wata tsohuwar dabara..
Ya ajiye ledar kyaututtukan a ƙasa, sannan ya yi wasu kalaman tsafi waɗanda suka sanya kyautar ta zama tamkar shadow...
Ledar ta zama Inuwa wanda ba'a iya ganin ainahin ledar, don haka hasken tsaron masarautar ba zai iya gano ta ba...
Ya tura wa Ayat saƙon hoto a cikin zuciyarta na inda ya ajiye kyautar daidai jikin taga na ɗakinta...
Ayat tana zaune a ɗakinta, tana ƙoƙarin buɗe littafinta na White Cat wanda ta saya a kasuwa, ga kuma hawaye a fuskarta na baƙin cikin abinda jami'an nan sukayi mata. Nan take ta ji wani irin bugun zuciya, sannan ƙamshin Sugar-coated Haws ya bugi hancinta, ƙamshin da ta ji a kasuwa lokacin da take son saye..
Ta ɗaga kai sai ta ga wani abu yana walƙiya a jikin tagarta. Ta matso kusa sai ta ga wani leda mai kyau dake lulluɓe da wani sanyayyen haske mai launin diamond...alamun an masa garkuwa ne..
Tana taɓa ledar, sai hasken ya ɓace, ledar ya zama na gaske a hannunta.... Tana buɗewa, sai ta ga duka abubuwan da take sha'awa a kasuwa..
Sugar-coated Haws masu zaƙi..
Cakes da Snacks masu daɗi..
Kuma a ƙasan ledar akwai wata ƴar takarda da aka rubuta..
"Sakamakon sarki ba ya karewa a baki kawai. Ki ji daɗin zaƙin da kika rasa a kasuwa.".
Ayat ta daskare, gabanta ya faɗi. Ta san babu kowa a masarautar nan da ya ga lokacin da ta so sayan waɗannan abubuwan sai shi. Tsoro da wani irin shauƙi suka gauraye ta..
Ta zauna a gefen gadonta, tana kallon tarkacen zaƙi da snacks ɗin dake gabanta. Ƙamshin Sugar-coated ɗin nan yana ratsa hancinta, yana tunatar da ita daidai lokacin da ta tsaya a kasuwa tana sha'awa amma ta kasa siya..
Ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki. Zaƙin ya narke a harshenta, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta. Amma duk da daɗin, hannunta yana rawa..
Ta lumshe idanu, tana jin yadda zaƙin yake ratsa ta. A ranta tana tunanin..
"Wane irin aljani ne wannan? Ta yaya ya san abin da nake so? Kuma ta yaya ya keta wannan katangar haske da kowa yake tsoro?"..
Domin a saninta dai akwai wani hasken shocking a kewaye da masarautar nan saboda aljanu..
Tsoro ya fara ba wa shauƙi fili. Ta san cewa shingen masarautar Alhamra ba abin wasa ba ne, an ƙirƙire shi ne don ya raba jiki da ran duk wani aljani da ya yi gigin kusantowa. Amma shi, ya tsallake shi kamar iska, ba ma don ya kai hari ba sai don ya ba ta kyautar abin zaƙi...
Ta sake karanta ƴar takardar dake hannunta..
"Sakamakon sarki ba ya ƙarewa a baki kawai..."
"Requite..." ta maimaita kalmar a hankali. Ta tuna littafin da ta gani a kasuwa mai magana akan wannan kalmar. Ashe shi ma ya karanta abin da nake karantawa? Ko kuma shi ne asalin jarumin da littattafan suke magana a kansa?..
Wani irin murmushi mai tattare da fargaba ya subuce mata. Ta ji kanta a matsayin wata ganima da babban sarki yake nema, amma ba ta san ko za ta buɗe masa ƙofa ko kuma ta ƙara ƙarfafa shingen zuciyarta ba...
Yayin da take cin sauran cakes ɗin, ta ji wani irin bugun zuciya na daban. Ta san yana nan kusa, tana jin sa a cikin jinin dake yawo a jikinta. Wannan Blood Bond ɗin ya zama tamkar rediyo dake nuna mata cewa ba ita kaɗai ba ce...
Sai da ta gama cinye abubuwan tass sannan ta miƙe ta nufi taga, ta kalli hasken masarautar daren dake waje. Hasken tsaron masarautar yana ta walƙiya a nesa..
"Kayi kuskure idan kana tunanin za ka iya mallake ni da waɗannan kyaututtukan," ta raɗa wa iska, kodayake tana sane da cewa zuciyarta ta riga ta fara karɓar saƙon sa......
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣5️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Bayan kwana biyu.
Sarki Nourdeen ya ba da umarni na gaggawa, inda ya buƙaci ganin dukkan jami'an sojojinsa da dakarun tsaro. Nan take kowa ya halarta, kowa ya jera a layin da ya dace a babban ƙofar fadar. A cikin dakarun har da Inuwa, wacce take tsaye tana nazarin yanayin da ake ciki..
Abin da ya fi ba kowa mamaki shi ne fitowar sarki. A wannan karon, Sarki Nourdeen ya fito ne tare da fadawansa da tafidarsa, amma babban abin al'ajabin shi ne Sarki ya cire sirrin dake rufe da fuskarsa, ya fito a asalin siffarsa...
Duk ma'aikatan ciki har da waɗanda suka daɗe a fada, babu wanda ya taɓa ganin fuskar sarki haka fili sai a yau. Da farko da yawa sun ɗauka ba sarkinsu ba ne, sai da suka ji sautin muryarsa da irin izzar da yake magana da ita, sannan kowa ya tabbatar cewa lallai Zakin Alhamra ne.
Sarki ya kalli dakarunsa, fuskarsa a murtuƙe cikin tsananin damuwa. Ya yi jawabi mai zafi..
"Na tara ku ne don in sanar da ku cewa masarautar nan tana fuskantar barazana. Ina umartarku da ku ƙara sa ido fiye da kowane lokaci. Kada ku yarda wata baƙuwar fuska ta shigo cikin masarautar nan ba tare da izini ba. Mutanen Pavilion suna shiri ne na musamman don ƙwace mana ikonmu da mutuncinmu."
A ransa, sarki ya riga ya gama yanke hukunci. Ba zai bayar da ko ɗaya daga cikin ƴaƴansa ba.
Ya gwammace ya fuskanci yaƙi da Chief Onyx da ya amince da wannan cin fuskar na mayar da gimbiya ƴar aiki...
Bayan sarki ya kammala jawabin ya koma cikin fada, dakarun kowa ya kama gabansa cikin fargaba..
Amma Inuwa ta shiga wani dogon tunani. Ta tsaya a inda take, tana maimaita sunan a ranta.
"Pavilion..."
Wace irin daula ce wannan da har mahaifinta, sarki mai iko, zai fito ya nuna fuskarsa fili sannan ya nuna tsoronsu haka? Zuciyarta ta gaya mata cewa akwai wani babban sirri dake ɓoye tsakanin Alhamra da Pavilion...
✨✨
A can daular Pavilion, yanayin ya sha bamban da fargabar dake cikin Alhamra. Wurin shakatawa private pool na Chief Onyx wuri ne dake cike da natsuwa, inda ruwan ke sheƙi ƙarƙashin hasken lantarki na zamani.
Chief Onyx yana cikin ruwan, ya nitse gaba ɗaya har zuwa ƙasan pool ɗin. Ya kwanta a can ƙasa tamkar ba ya buƙatar numfashi, idanunsa a rufe yana dogon nazari. Ruwan yana kewaye faffaden ƙirjinsa da kuma dogon gashinsa dake yawo a cikin ruwan...
Ga kowa, wannan lokaci ne na wanka da hutu, amma ga Onyx, lokaci ne na tsara dabarun da za su girgiza duniya...
Tana taku cikin natsuwa, Robot ɗinsa ta shigo sashen pool ɗin. Ta tsaya a gefen ruwan, idanunta na karatu da binciko dukkan motsin dake kewayenta. Ba tare da ɓata lokaci ba, ta fara magana da muryarta mai sanyi dake ɗauke da hujjoji..
"Chief, bayanan da na tattara daga Alhamra sun tabbatar da cewa Sarki Nourdeen ya janye yarjejeniyarsa. Ya tara dakarunsa ya ba su umarnin ƙara tsaro, kuma ya nuna cewa ba zai bayar da ko ɗaya daga cikin ƴaƴansa ba. Ya zaɓi yaƙi maimakon biyayya."
Duk da wannan babban labarin dake nuna cin amana, Chief Onyx bai ko motsa ba. Ya ci gaba da kwanciya a ƙasan ruwan na wasu daƙiƙoƙi. Labarin bai girgiza shi ba domin dama ya san halin raunin zuciya na Sarki Nourdeen...
A gare shi, Alhamra tamkar ƙanƙarar dake narkewa take, ba ta da abin da Pavilion take da shi ninkin-ba-ninki... Ko a yau yaso a fara yaƙi, ya san cewa rushe Alhamra abu ne na mintuna, ba ma sa'o'i ba...
Can sai ya fara fitowa daga cikin ruwan a hankali. Yayin da fuskarsa ta bayyana a saman ruwan, gashinsa ya jiƙe ya kwanta a kafaɗunsa, sai ya yi wani irin la'anannen murmushi. Murmushi ne mai cike da ma'anoni dubu na rainin wayo, na jiran lokaci da kuma na muguntar da zai yi wa duk wanda ya yi tunanin zai iya yaudararsa...
Bai furta ko kalma ɗaya ba, amma murmushin ya riga ya faɗi komai.. Wasa ya ƙare...
Chief Onyx ya miƙe tsaye ya fito daga cikin pool ɗin, ruwa yana ta zuba a jikinsa tamkar wani dodo da ya fito daga teku. Ya kalli Robot ɗinsa da idanuwansa waɗanda suka sauya launi saboda jin shirin yaƙi..
Ya tsaya yayin da Robot ɗin take miƙa masa wani babban farin towel don ya busar da jikinsa. Ba tare da ya kalle ta ba, ya ce.
"U. Nourdeen ya zaɓi hanyar da zata kai shi ga halaka. Tunda ya fasa yarjejeniyar, to mu ma za mu nuna masa cewa Pavilion ba ta magana sau biyu. Ki fara shirin Cyber-Attack..."
Nan take Robot ɗin ta fara latsa wasu na'urori dake jikin hannunta. A cikin daƙiƙu ƙalilan, duk hanyoyin sadarwa na masarautar Alhamra suka fara samun matsala. Na'urorin tsaro na fada CCTV suka fara daukewa, sannan hasken wutar lantarki na wasu sassan fadar ya fara dishi-dishi. Wannan shi ne shirin farko na durƙusar da masarautar ta hanyar fasaha kafin ma a kai ga amfani da takobi...
Bayan nan, Chief Onyx ya ba da umarnin tura wasu tsuntsayen na'ura Drones waɗanda aka ƙera su daidai da siffar tsuntsayen gaske amma suna ɗauke da na'urorin leken asiri da makaman guba...
"Ina son ganin kowane lungu da saƙo na Alhamra," in ji Chief Onyx. "Dole ne in san inda ya ɓoye ƴaƴan nasa. Musamman wadda zuciyata take gaya min cewa ita ce mabuɗin wannan masarautar."..
✨✨
A can Alhamra, Inuwa dake zaune a gefen titi masarautar tana tunani, kwatsam sai ta ga wasu tsuntsaye guda biyu sun gilma ta kanta. Sai dai takunsu da sautin fikafikansu ya bambanta da na tsuntsayen da ta saba gani. Zuciyarta ta buga, ta miƙe ta fara bin su da kallo.
A lokaci ɗaya, duk kofofin zamani na fada suka daina aiki, hakan ya jefa jami'an tsaro cikin ruɗani...
Master Ibrahim ya fito yana ta tsawa, "Me yake faruwa? Me ya sa injinanmu suka tsaya?"....
Ayat tana tsaye a tsakiyar harabar fadar, idanunta sun yi jawur tamkar na mace-macen daji. Ta ga yadda ɗaya daga cikin tsuntsayen na'urar yake