Showing 153001 words to 154131 words out of 154131 words

Chapter 52 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

mayar da kan ka bawan mace maimakon Sarkinmu!"

​Ko wani shugaba da abinda yake faɗi...

​King Diamond ya tsaya daram, gashinsa na yawo a iska, idanunsa na shuɗi sun yi jawur saboda bacin rai...

​Ya furta cikin ƙwarin gwiwa

"Ina amfanin mulki idan ba zan iya kare abin da zuciyata take so ba? Ayat ba mace bace kawai, ita ce inuwar da take sanyaya min zafi na tsawon shekarun baya...."

​Azazil ya ce,
"Hukuncinmu ɗaya ne! Ko dai ka yanke alaƙa da ita yanzu, ko kuma mu kwace duk Ikon Sarauta dake tattare da kai. Idan muka janye wannan ikon, ba za ka iya bace-wa ba, ba za ka iya ba ta kariya ba, kuma ba za ka iya yin aiki da ikon mu ba...."

​King Diamond ya yi murmushin rainin wayo sannan ya ce,

"Kuna tunanin ikon da nake da shi ne yake sa ni faɗa? A'a. Zuciyata ita ce babban ikona. Ko da za ku janye komai, zan tafi wurinta a matsayin kowane irin hali. Idan har kariya ta tana nufin zan zama mazauni a duniyar mutane, to na shirya!"

​Majalisar ta yi kukan ruri, hasken ɗakin ya fara dishi-dishi da wani irin walƙiya...

​Azazil cikin ɓacin rai ya furta

"Ka zaɓi kaddararka. Daga daren yau, mun janye kashi saba'in na ikonka. Ba za ka iya keta hazo cikin sauƙi ba, kuma duk raunukan da za ka ji a duniyar mutane, za su zama raunuka na haƙiƙa a jikinka. Ka zama tamkar mutum mai ɗan karamin ikon aljani."

​King Diamond ya ji yadda karfin dake jikinsa yake raguwa, ya ji nauyin jikinsa ya ƙaru, amma bai nuna tsoro ba...

​Sai ma cewa da yayi..

"Ku kwace duka idan kuna so. Amma ku sani, ko da hannu ɗaya zan yi faɗa, ba zan taɓa barin Ayat ta zama ganima ga kowa ba..."

Sauran Aljanun suka furta
"Akwai sauran hukunci zuwa gaba..."

Daga nan duk suka ɓace..domin sun san shi da masifar taurin kai da kafiya akan abu...


Bayan wasu sa'o'i yana zaune yana faman saƙe-saƙen zuci...
Kodayake an rage masa kashi saba'in na ikonsa, amma ragowar kashi talatin ɗin sun isa su girgiza duniya...Abokinsa Prince Zarith yana gefensa, yana ta faman zazzaga surutu..

​ "King, ka saurare ni! Wannan yarinyar bil'adam za ta zama silar rugujewar ka. Ka barta tayi rayuwarta ita kadai, domin babu aure a tsakaninku...kar ka zo kayi biyu babu, ka ceci kanka daga fushin dattijan aljanu!"

​King Diamond ya yi banza da shi, idanunsa suna kallon sararin samaniya. Tunaninsa ɗaya ne...

"Ta yaya zan samar da Ayat ta biyu wadda za ta zauna a fada ba tare da an gane ba?..."

Lokaci guda, fuskar ɗan uwansa, Chief Onyx wato Ra'ees ta faɗo masa a rai...

Onyx kaɗai ne yake da fasahar da za ta iya ƙera Robot wanda zai yi kamanin Ayat ɗari-bisa-ɗari...

​Ba tare da cewa uffan ba, King Diamond ya miƙe, hasken shuɗi ya gauraye jikinsa. Zarith ya saki baki yana kallo, sai kawai ya ga Diamond ya ɓace kamar walkiya...

​Bai sauƙa a kowane lungu ba sai a gaban katon babban gate ɗin masarautar Pavilion City...

Wani birni ne da aka gina shi da gilashin da ba ya fashewa, cike da fasahar da ta wuce tunanin ɗan Adam...

Wannan ne karon farko da zasu yi face to face tin yarinta kuma akan wani aiki..

Duk da a cikin zuciyar King Diamond bai so ya je wurinsa ba domin yana tunanin ai bai damu da shi ba...
Shima Chief onyx Yana ganin tunda King Diamond aljan ne ai zaifi neman yadda yake ya neme shi amma bai damu da shi ba..
Sai kowa ya sharar da kowa saboda kowa a cikinsu yana fama da girman kai da jiji da kai...

Ga kuma King Diamond yana jin haushinsa yadda ya wulaƙanta Ayat a walimar sauƙar al'kur'ani su...

​King bai zo da sauƙin kai ba... Yana takowa, wata irin ƙaƙƙarfar guguwa mai ɗauke da sanyi da ƙura tana biye da shi, tana kakkarya duk abin da ya yi yunkurin tare shi...

Bodyguards ɗin Chief Onyx, dakarun zamani masu ɗauke da makaman lantarki, suka fara yo kansa...

"Tsaya a nan! Waye kai?...!"

​King Diamond bai ko kalle su ba. Wannan guguwar dake biye da shi ta riƙa ɗaukar bodyguards ɗin tana sama da su, tana buga su da ƙasa. Yana tafiya yana ratsa cikin dogayen gine-ginen gilashin fadar. Duk da cewa gilasan Pavilion an kera su ne da gilashi masu bala'in ƙarfi, amma kwarjinin King Diamond ya sanya su fara faffashewa ɗaya-bayan-ɗaya...

​"PHAS! PHAS! PHAS!" Sautin fashewar gilashin yana tashi kamar ƙarar bindiga...

​A can cikin babban falon masarautar, Chief Onyx yana zaune a kan kujerarsa ta alfarma. Gaban faffaɗan allon Plasma dake nuna podcast na duk abin da yake faruwa a bakin gate...

​Yana kallon yadda wannan guguwar take tunkaro shi. Ya ga wani matashi mai farin sumar gashi da idanun shuɗi, wanda kamaninsa da nasa kusan iri ɗaya ne, yana take duk dakarunsa...

Ko kiftawa Onyx baya yi, kuma bai nuna alamar tsoro ba, duk da yadda gine-ginen falon nasa suke girgiza..
​Onyx ya gyara zama, idanunsa suka yi walwali da wani boyayyen sirri. Ya san wannan ba kowa bane face ɗan uwansa, tagwayensa, wanda duniya ta raba su shekaru 23 da suka wuce...

Wasu robots ne kala-kala suka shigo falon da Chief yake suna sanar dashi irin ta'adin da wani Jinn yake musu..

Abinda Chief ya furta cikin rashin damuwa shine
"Ku bar shi ya ƙaraso..."

Ya ƙarasa maganar tare da ɗaukan lemon juice ya kurɓa...
Yana sanye da silver mask ta gefen fuska wanda yake rufe sirrin kamanninsa..

​King Diamond ya isa ƙofar falon ƙarshe, ya sanya kafarsa ta dama ya buga ƙofar, guguwar dake bayansa ta haɗiye ɗaukacin hasken falon...

Sun faɗo cikin duhu, kuma babu wani haske da zai iya bayyana yadda za su fita...


ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!!
ALHAMDULILLAH!!!

​📢 EXTRACT: DOMIN CIGABA DA BOOK TWO!

​Anan muka kawo ƙarshen Book One. Shin yaya za ta kasance tsakanin manyan tagwayen nan biyu a masarautar Pavilion?

Shin Inuwa (Ayat) za ta iya jure wa yaƙin dake jiran ta?

Ko kuwa ya zata kasance da Uncle Jalal da Maayah a cikin kogon can mai zurfi?

*SHIN WANI SCENE NE YAFI BURGE KU KO YA KWANTA MUKU A RAI?*

_CHING-CHING— CHIEF ONYX—GELY.._

_AYAT—KING DIAMOND._

_MAAYAH—UNCLE JALAL_

To fa ga kuma Zayana har yanzu a Cell, sarki kuma yana son kawar da tsoron Ruma a zuciyarsa ta hanyar cigaba da tsare Zayana...

​Domin samun cigaban wannan labari a Book Two, ga yadda tsarin yake:

​Paid Group (Page by Page): N500 kacal.

​Full Document (Bayan an kammala): N700 kacal.

​Kada ku bari a ba ku labari, domin Book Two ya fi komai zafi!

*MASU KARATU, KU SHIRYA DOMIN BOOK TWO YA FI WANNAN ZAFI DA TASHIN HANKALI!....*

_BAYAN SALLAH ZA'A ƊORA DAGA YADDA AKA TSAYA GA WAƊANDA SUKA YI PAYMENT..._

Za'a fara saka sunaye a list tun yanzu.
Da zarar lokaci ya yi, za a ɗora kai tsaye.

ACCOUNT DETAILS:

Opay / Palmpay
9065443871
Asma’u Muhammad Auwal

📩 Tura shaidar biya + sunanki domin a saka ki/ka a list....


*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login