Showing 150001 words to 153000 words out of 154131 words
Chapter 51 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
zan bari a fada tana da ikon yin magana da aikata komai kamar ke, don haka ki saki ranki ki yi yaƙin nan don mutanenki."
✨✨✨
Iya makarantar ne kawai ya rage ba'a rufe ba saboda Examination amma an bada tsaro na musamman sosai...
Shiru ne ya ratsa babban Exam Hall na makarantar Royal International Academy. Sautin agogon dake jikin bangon ɗakin kawai kake ji yana bugawa..
tik-tok, tik-tok, tamkar yana ƙirga sauran lokacin da ya rage wa ɗaliban...
Maayah tana zaune a tsaka-tsakiya, sanye da uniform makarantar... Duk da kyawun fuskarta, yanzu fuskar ta nuna tsantsar firgici... Ta ƙura wa takardar jarrabawar ido, tambayoyin suna yi mata gizo kamar yaren jinnu...
Iya abin da ta rubuta shi ne sunanta, SHAHZADI MAAYAH MUHAMMAD NOURDEEN...
Ta daɗe tana kallon takardar, tana son tuno da abin da aka koyar musu, amma kwakwalwarta ta ƙi bata haɗin kai. Sauran ɗaliban dake ɗakin, waɗanda a baya ita ce take nuna musu izza, kowannensu kansa yana ƙasa yana rubutu ba kakkautawa. Malaman dake zagayawa kuwa, duk da cewa tsoronta suke ji a baya, yanzu suna wucewa ne ba tare da sun kalleta ba, domin sun san mulkin Master of Discipline wato Uncle Jalal ya riga ya kawar da tsoron fada a makaranta...
A can gefe guda, a cikin ofishinsa, Uncle Jalal yana zaune, idanunsa kyam akan jadawalin jarrabawarsa domin ko wani malami da darasinsa...
Wata zuciyar kuma tana hasasho masa Maayah a hall duk da cewa akwai wani boyayyen tausayinta da yake ji a duk lokacin da yake mata darasi a gida, musamman yadda take zubar da hawaye idan ya tsawata mata amma a makaranta, shi ne katangar ƙarfe..
Lokaci guda, Uncle Jalal ya miƙe, ya nufi hall ɗin jarrabawar. Takun takalmansa ya sanya kowa a ɗakin ƙara nutsuwa. Ya shigo cikin takunsa na isa, ya fara zagaya teburan ɗaliban...
Ya iso daidai teburin Maayah. Ya tsaya cak, inuwarsa ta rufe takardar jarrabawar tata. Maayah ta ji wani irin Shock, ta kasa ɗagowa ta kalle shi...
Uncle Jalal ya sunkuyo daidai kunnenta, muryarsa can ƙasa cike da gargadi...
"Gimbiya Maayah... saura minti goma sha biyar... Shin sunanki ne kadai kika koya a duk zaman da kike a aji?"
Maayah ta ɗago idanunta da suka rine da kwalla, ta kalli Uncle Jalal cikin yanayin roko...
"Uncle... kaina ciwo yake yi, na kasa tuno komai."
Uncle Jalal bai nuna alamun tausayi ba, ya gyara tsaiwarsa yana kallon agogonsa...
"Nan ba gida ba ne, kuma ni ba Uncle ɗinki ba ne a nan. Ni malamin jarrabawa ne. Idan baki rubuta komai ba, za'a raba miki takardar 'F' ɗinki a gaban kowa, sarki ya gani."
Ya matsa daga gefenta, ya cigaba da zagawa yana cewa, "Sauran dalibai...saura minti goma! Duk wanda bai gama ba ya hanzarta."
Maayah ta ji zuciyarta tana dukan uku-uku. Ta kalli bayan Uncle Jalal, tana jin wani irin shauƙi na ƙiyayya da kuma sha'awar yadda yake nuna mata rashin tsoro. Ta ɗauki alkalaminta, hannunta yana rawa, ta fara kokarin zana duk abin da ya zo mata a rai, ko da kuwa ba shi ne amsar ba, don gudun kada Uncle Jalal ya kunyata ta a gaban mutane...
A ƙarshen hall ɗin, Uncle Jalal ya juyo ya kalle ta. Kwayar idonsu ta sarƙe. Shi ma ya ji wani irin tausayi ya ziyarci ransa, ganin yadda take ta faman kokawa da alkalami, amma dole ya danne domin ya mayar da ita mutuniyar kwarai...
Bayan ya fita zuwa ɗakin jarrabawa na gaba, Ɗakin ya ɗan yi sanyi. Maayah ta ƙura wa takardarta ido, tana jin tamkar kanta zai rabe biyu...
Sadiq wato saurayinta na wasa wanda take aikansa ya siyo mata abu, yana zaune a kujera ta kusa da ita, ya kammala nasa rubutun tsaf. Ya lura da yadda Maayah take zufa, duk da sanyin dake ɗakin..
Sadiq ya yi mata ɗan tari na ƙarya. Maayah ta ɗago idanunta da suka rine..
Ya yi mata nuni da idanu akan ta miƙo masa nata booklet ɗin, shi kuma ya miƙa mata nasa wanda ya riga ya kammala amsoshin. Cikin sanɗa da sauri, suka yi musayar takardun a karkashin tebur..
Wani malami dake zagayawa ya gansu, amma ganin Maayah ce, gimbiyar da kowa ke shakka, sai ya ɗauke kansa kamar bai gani ba, ya cigaba da takunsa..
Ta fara acting...Ta duƙufa tana kwaikwayon rubutu, amma hannunta yana rawa. Tana rubuta haruffa marasa ma'ana a gefen takardar Sadiq, tana yawan ɗagowa tana kallon ƙofa..
Kwatsam! Sai ga Uncle Jalal ya dawo ajin. Ya shigo da wani irin kwarjini, ya tsaya a gaban class ɗin yana bin kowa da kallo ɗaya bayan ɗaya. Idanunsa masu kaifi suka sauƙa akan wani ɗalibi dake can baya yana satar amsa a karkashin tebur...
Uncle Jalal ya nufe shi gaba-gaɗi...
"Give me that!" Ya daka masa tsawa da turanci. Ya fizge takardar, sannan ya karɓe booklet ɗin dalibin ya yaga shi gida biyu...
"Get out of my class. Now!"
Bayan ya gama zagayawa, ya nufi hanyar fita, amma wani abu ya tsaya masa a rai. Ya juyo ya kalli Maayah. Ya lura da yanayinta, bata danna biro kamar yadda mai rubutu yake yi, kuma yawan ɗagowan da take yi tana kallonsa ya ba shi shakku...
Ya tako a hankali har ya iso gefenta. Ya tsaya kyam, ya zuba mata ido...
"Anya kina da gaskiya kuwa, Gimbiya?" ya faɗa cikin muryar raɗan nan tasa mai tsoratarwa...
Maayah ta daskare. Ta kasa magana, sai dai kawai ta zuba wa booklet ido...
Uncle ya sa hannu ya janye littafin. Ya buɗe shafin ƙarshe, ya ga har tambaya ta karshe an amsa ta..
"Yanzu a fitar tawa har kika kai ga tambaya ta karshe?"
Cikin zargi ya buɗe shafin ƙarshe na takardar. Nan take ya ga rubutun daban ne, rubutu ne mai ɗaukar hankali, ba irin na Maayah dake tangal-tangal ba. Ya sake juyo da shafin gaba don ganin sunan dake kai...
ABUBAKAR YUNUS...
Zuciyar Uncle ta buga. Ya kalli Sadiq, sannan ya kalli Maayah wadda ta riga ta fara hawaye. Sadiq kuwa ya gama kiɗimewa, numfashinsa yana fita da sauri-sauri...
Uncle Jalal ya tsaya kyam a gefen Maayah, inuwarsa ta mamaye teburinta, wanda hakan ya sa numfashinta ya kusa tsayawa...Ya sanya dogayen yatsunsa ya janye booklet ɗin a hankali..
Maayah ta kalli Sadiq da gefen ido, shi ma Sadiq ya riga ya daskare, zufa tana keto masa ta ko'ina duk da sanyin AC dake ɗakin..
"Ina kika samu wannan dabarar, Maayah?" Uncle Jalal ya faɗa cikin murya mai sanyi mai cike da ɓacin rai...
Maayah ta yi tsuru-tsuru, muryarta tana rawa..
"Uncle... rubutu na ne, kawai na yi sauri ne shi ya sa ya canza."
Wani murmushin takaici ya subuce wa Uncle...
"Sauri? Sauri har ya mayar da sunanki Abubakar Yunus?" Ya ɗaga littafin sama yadda kowa zai gani, sannan ya kalli Sadiq wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa yana rawar jiki...
"Abubakar Yunus! Tashi tsaye!" Muryar Uncle Jalal ta daki bangon ɗakin kamar ƙarar tsawa...
Sadiq ya miƙe tsaye jikinsa na kyarma...
"Sir... dama... dama taimaka mata zan yi..."
Uncle Jalal ya taka zuwa gaban Sadiq, ya raba shi da booklet ɗin dake gabansa, wanda kusan babu komai a ciki sai sunan Maayah...
"Taimaka mata? Shin kai ne Sarki da zaka bayar da tallafin maki a ɗakin jarrabawa? Ko kuma ka ɗauka dokokina na wasan yara ne?"
Ya juyo kan Maayah, wadda hawaye suka fara wanke mata fuska..
"Gimbiya Maayah, kin nuna min cewa duk kokarin da nake yi a gida asara ne. Kin gwammace ki yi sata da sunan wani namijin, maimakon ki faɗi da mutuncinki."
Ɗakin ya yi shiru, sauran daliban suna kallon ikon Allah. Malami na farko da ya share su kuwa ya ɓuya a can gefe yana zaro ido...
Uncle Jalal ya yage booklets guda biyun a gaban kowa, fatsa-fatsa!...
"Kuje ku fita daga ɗakin nan! Maayah, Abubakar, kun faɗi wannan darasin... Kuma ina tabbatar muku, sai na sanar da Minister da kuma Mai Martaba Sarki abin da kuka aikata yanzun nan."
Maayah ta fashe da kuka mai karfi.
"Don Allah Uncle Jalal! Kada ka gaya wa Abul, zai iya min kowane hukunci!"
Uncle ya nuna musu ƙofa da yatsa, idanunsa sun yi ja tsantsar ɓacin rai. "Fita! Tun kafin in rasa natsuwata a kanku!"
Bayan sun fita..
Maayah bata wani tsaya ba domin daman Uncle Jalal ne mai zuwa ɗaukanta a gida idan an tashi kuma ya mayar da ita.. Ya dakatar da kawota a tsararrun motoci sama da biyar da bodyguards saboda a tunaninsa hakan zai sa tana yawan ji da kai..
A wannan lokacin haka take takawa tana tafiya a hankali, ba'a san ta fita ba ma...
Kawai tafiya take tana hawaye, a tunaninta ta gama amfani yanzu..
Ba wai gida ta nufa ba, kai tsaye cikin daji tayi..
Tana tafiya hankalinta ya gama fita daga jikinta..
Bayan sa'o'i guda..
Kowa ya fito a exam, Sadiq ya samu Uncle a office Yana ta roƙonsa amma Uncle yace,
"ai ya riga ya faɗi a wannan exam sai dai ya kiyaye zuwa next.."
Sadiq yayi magiyar har ya haƙura..
Ya fita..
Can motoci ne suke zuwa ɗaukan ɗalibai dake duk makarantar na ƴaƴan masu kuɗi ne....kuma an ƙara kafa tsaro saboda yanayin garin bashi da kyau sai satar mutane ake..
Uncle ya fito daga office ya tambaya ina Maayah akan zai kaita gida shi kuma sai ya wuce...
Amma an dudduba ko ina ba'a ganta ba..
Sai Sadiq ne da zai tafi motarsu tazo ɗaukansa yake sanar wa cewa Maayah fa ta daɗe ta fita daga makarantar...
A take Uncle Jalal ya ƙira wani jami'i mai tsaron get ɗin fada ya tambaya cewa Maayah ta iso kuwa?
Aka sanar da a'a.
Nan Uncle Jalal ya ɗauki superbike ɗinsa ya fita daga makarantar a ɗari...
Yana fita ya bi hanya amma bai ganta ba..yana ta tambaya amma babu wanda ya ganta..
Ya shiga tashin hankali..
Ya juma yana neman ta amma bai sameta ba, ya ƙara ƙiran fada akan ta isa, aka nasar da a'a...
Ya bi hanya yana tambaya, har ya haɗu da wani dattijo...
"Baba, ko ka ga wata ɗaliba ta wuce nan?"
Dattijon ya nuna masa can cikin kurmi. "Na ga wata yarinya tana kuka ta nufi wancan jejin."
Uncle Jalal bai tsaya wata-wata ba, ya murɗa wutar mashin ɗin, ya lulƙa cikin jejin. Yana ta gudu, yana kewayawa tsakanin bishiyoyi har sai da ya iso wani fili mai faɗi. A can gabansa, ya ga ramin da kowa ya sani, babban rami ne mai gudun ruwa a ƙasa, wanda idan mutum ya faɗa, ba za a taɓa samun gawarsa ba..
Ya hango Maayah tsaye a bakin ramin, tana ta maganganu cikin kuka...
Iskar dajin tana kaɗawa da ƙarfi, tana tura kukan Maayah zuwa cikin ramin dake gabanta... Ruwan dake karkashin ramin yana gudana da wani irin sauti mai ban tsoro, yana jiran duk abin da zai faɗo masa..
Tana tsaye a bakin rami, uniform ɗinta yana kaɗawa cikin iska da sumar gashinta duk da akwai hula akai....
"Gwara na mutu kowa ya huta!" ta faɗa cikin kuka mai cin rai. "Na gaji da wannan rayuwar ta kunya. Abul ya tsane ni, Uncle Jalal shima ya tsane ni.. Babu amfanin rayuwata!"
Ta rufe idanunta, ta sanya ƙafa ɗaya tana shirin tura kanta cikin ramin. A daidai lokacin da take jin jikinta yana neman tafiya...
"Maayah!" Wata murya ta daka mata tsawa, muryar da ko a cikin mafarki ta ji ta, ta san ta Uncle Jalal ce.
Ba ta ko juyo ba, ta ƙara zamar da ƙafarta..
"Kada ka matso! Ka bar ni na huta!"
Kafin ta samu damar sakin jiki, Uncle Jalal ya daka wani uban tsalle daga kan mashin ɗinsa. Cikin zafin nama irin na jarumai, ya damko damtsen hannunta da wani irin ƙarfi, ya juyo da ita baya da karfin tsiya..
Saboda gudun da ya kwaso, sai da suka faɗi ƙasa tare, yana kanta, numfashinsa yana fita da sauri-sauri, idanunsa sun yi jawur tsabar tashin hankali...
Ya miƙe tare da ita, ba tare da ya ba ta damar yin magana ba, ya daka mata wata uwar tsawa..
"Ke wace iriyar wawiya ce?! Mutuwa kike nema?!"
Sai kawai ya ɗauke ta da wani lafiyayyen mari..
Dukan farko ya sauƙa a kuncinta na dama. Maayah ta daskare, idanunta suka zaro waje...
Na biyun ya biyo baya. Waɗannan lafiyayyun marukan suka sa kanta juyawa, kukan ma ya tsaya mata a makoshi... Ta kalli Uncle ta ga yadda jikinsa yake rawa, ba na fushi kaɗai ba, har da na tsoron rasa ta...
"Kin san abin da kika kusan yi wa kanki kuwa? Kin san tashin hankalin da kika sanya ni?" Muryarsa ta dashe, yana sake damko kafadunta...
"Idan kin faɗi jarrabawa, wannan dalili ne na kashe kanki? Me ya rage miki a duniya idan rayuwar taki ta ƙare a nan?"
Maayah ta dube shi, hawaye masu zafi suna kwarara. "Amma ai ka ce na faɗi... ka ce zaka gaya wa Abul..."
Uncle ya rungume ta da karfi lokaci guda, rungumar da ta nuna tsantsar tausayi da ƙauna, saɓanin dukan da ya yi mata yanzun nan...
"Ba zan taɓa barinki ki mutu ba a wannan yanayin Maayah. Ko da kuwa zan koya miki darasi ne amma kada kiyi tunanin na mutuwa ne. Kin nuna min yau cewa ba ki san darajar kanki ba..."
Bayan marukan da ya zabga mata, Maayah ba ta daɗe cikin hayyacinta ba. Wani irin hauka ya ƙara turnuke ta, ta fusge kanta daga rungumar tasa, ta juya da gudu ta nufi bakin ramin tana kuka...
"Ka kyale ni! Mutuwa nake so!"
Uncle ya ƙara daka wani uban tsalle ya sake cabko ta a daidai gaɓar ramin...
Saboda ƙarfin gudun da ta ɗauka da kuma nauyin jikinsa da ya faɗa kanta, sai suka rasa daidaiton sawunsu. Nan take suka fara gangarawa daga kan tudun zuwa wani gangaren mai ban tsoro...
Dake wurin sai kayi a hankali, saboda tudu da gangarensa, da kuma ramuka da yawa..
"Wayyoooooo!" Maayah ta sake wani irin ihu mai ban tsoro wanda ya karaɗe jejin...
Sunka fara gangarawa suna juyawa, wani lokacin Maayah a ƙasa, wani lokacin Uncle Jalal. Cikin zafin nama, Uncle ya sa hannuwansa duka ya kankame ta, ya danne kanta a kirjinsa don kare ta daga buguwa da duwatsu..
Maayah kuwa ta sa hannu ta damke gaban rigarsa, tana kuka da ihu yayin da suke ƙara nisa cikin gangaren...
Basu tsaya ko'ina ba sai ga su Giffffff! sun faɗa cikin wani babban kogo mai zurfi wanda ciyayi da kananan kofofin ruwa suka kewaye..
Shiru ya biyo baya. Maayah tana kwance a saman kirjinsa, idanunta a rufe ta riga ta suma saboda tsananin firgici...
Uncle Jalal ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya, jikinsa duk ya yi tsami, rigarsa ta yage a wasu wuraren. Ya yi kokarin tashi, ya juyar da ita daga kansa ya kwantar da ita a kan rantsatstsen korayen ciyayin dake cikin kogon...
"Maayah! Maayah!" ya fara jijjiga ta, muryarsa tana rawa. Ya kalli kyakkyawar fuskarta wadda ƙura ta ɓata, ya ji wani irin tausayi ya ziyarci ransa. Ya taɓa wuyanta ya ji jini yana bugawa, nan ya san tana raye...
Ya ɗaga kansa ya kalli saman kogon da suka faɗo. Ya ga nisan wurin ya fi karfin a iya takawa a hau, kuma babu wani abu da za a iya kamawa. Ya duba ko'ina, sai sautin ruwan dake gudana a cikin kogon yake ji. Sun tsinci kansu a inda ba su taɓa tsammani ba...
Ya koma ya zauna kusa da ita, ya zuba mata ido yana kallon yadda ƙirjin ta yake sama da ƙasa saboda numfashi...
Sanyin kogon ya fara ratsa ƙashinsa, ga daddaɗan sautin ƙananan koguna dake gudana a cikin kogon. Ya kalli Maayah, fuskarta ta yi fari saboda firgici da kuma sanyin dake ƙoƙarin shiga jikinta..
Ya rarrafa ya isa bakin ɗaya daga cikin ƙananan kogunan, ya tsoma hannunsa cikin ruwan mai sanyi kamar ƙanƙara. Ya dawo kusa da ita, ya fara yayyafa mata ruwan a fuska, sannan ya sa tafin hannunsa yana shafa fuskarta a hankali..
"Maayah... Maayah, ki tashi..." ya furta cikin muryar raɗa..
Maayah ta fara motsa idanunta, a hankali ta buɗe su. Abu na farko da ta gani shi ne fuskarsa da take kusa da tata, idanunsa cike da damuwar da ba ta taɓa gani ba. Ta rintse idanun ta ta sake buɗewa, tana jin sanyin kogon yana sa jikinta rawa..
"Uncle..." ta furta cikin muryar da ba ta fita sosai.
Ba tare da ya ce uffan ba, ya sa hannu ya janyo ta jikinsa, ya rungume ta da ƙarfi domin ya ba ta ɗumin jikinsa.... Ba ta yi musu ba, ta ƙara shigewa jikinsa tana kuka ƙasa-ƙasa, tana jin yadda bugun zuciyarsa yake dukan ƙirjinta..
Wannan sanyin ya sa duk wani girman kai ya kau, ya bar gurbinsa ga buƙatar kariya.
Ta ɗago ta kalli saman kogon da ya yi nisa...
"Ba za mu iya fita ba, ko? Mutuwa za mu yi a nan?"
Uncle Jalal ya ƙara ƙanƙame ta, ya duba ƙwayar idonta...
"Ba za mu mutu ba Maayah. Muddin ina raye, ba zan bar komai ya same ki ba. Wannan wurin zai zama sirrinmu, babu wanda zai san me ya faru a nan."
Maayah ta kalli yadda rigarsa ta yage, ta kai hannunta ta taɓa inda ya ji rauni a kafaɗa. "Ka ji ciwo saboda ni..."
A take Uncle ya ji wani irin shauƙi ya ziyarci ransa. Ya kalli leɓunanta dake rawa saboda sanyi, sannan ya kalli idanunta... A wannan lokacin babu malami ko gimbiya, sai mutum biyu da ƙaddara ta haɗa a cikin kogon ƙasa...
✨✨✨
Bayan King Diamond ya dawo da Ayat ɗakin baccinta, ya sumbace ta a goshi a matsayin alkawarin kariya, sannan ya ɓace...
Amma yana isa duniyar aljanu, bai tarar da natsuwa ba.. Manya-manyan majalisar aljanu sun taru a kewayen Power Pool, idanunsu suna hura wuta...
Dattijon cikinsu, wanda ake ƙira da Azazil, ya tako gaba, muryarsa tana girgiza duwatsun fadar.
Azazil ya ce,
"King Diamond! Ka ƙeta dokar da aka kafa dubunnan shekaru. Ka sanya jininmu da na bil'adama ya gauraya ta hanyar shauƙi da musayar jini..... me ya sa kake ɓata lokacinka akan mace 'yar ƙasa, wadda numfashinta yake ƙarewa cikin kiftawar ido?"
Wani Aljanin ya ce,
"Mun ga yadda kake shige mata, kusancinku yayi yawa sosai....har ta kai ga a kwanaki kana kwana da ita a matsayin kuliya...Sannan ka kawo ta kana koya mata sirrin yakinmu! Ka