Showing 144001 words to 147000 words out of 154131 words

Chapter 49 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

idanunsa don ganin ko tana bin sa ne a littafin, sai ya ga abin da bai taɓa zato ba.
Maayah ta kasa jure gajiya da raɗaɗin kukan da ta yi, sai kawai ta saki jikinta, ta kwantar da kanta luff a kan faffadan kirjin Uncle Jalal. Ta yi nisa a cikin wani nannauyan barci, har tana sauƙe numfashi ɗaya-bayan-ɗaya cikin nutsuwa...

Uncle Jalal ya daskare. Bai lura da lokacin da kanta ya sauƙa a kirjin nasa ba saboda yadda ya zurfafa a karatun. Ya kasa motsawa gudun kar ta farka, kuma ya kasa tura ta gefe saboda wani sabon yanayi da ya ziyarci zuciyarsa.
Ya fara bin kyakkyawar fuskarta da kallo..

Ya kalli gefen fuskarta da ya kumbura kaɗan kuma ya yi ja saboda marin da ya zabga mata ɗazu. Wani ɗaci ya ji a ransa, yana jin kamar ya yi saurin fushi har yake marinta haka..

Gashin kanta dake sanye da abun roll na sarauta mai sheƙi, ya bazu kaɗan, yana fitar da wani daddadan kamshi mai sanyi wanda ya daki hancinsa, ya sanya shi jin wani irin kasala...

Ya ƙurawa lallausan idanunta dake a lumshe ido. Ko kiftawa baya yi, ya rasa dalilin da ya sa yake kallonta haka, amma ya ji duk fushin da yake yi da ita ya narke, ya koma matsanancin tausayi da kuma wani boyayyen shauƙi wanda ya kashe masa jiki gaba ɗaya.

A lokacin, Uncle Jalal ya gane cewa bayan wannan gadarar da yangar ta Maayah, akwai wani ɓoyayyen abu marar kariya dake bukatar rarrashi. Ya ci gaba da zama a haka, ya barta ta ƙara samun natsuwa a kirjin nasa, yayin da zuciyarsa take bugawa da wani irin sauti daban da wanda ya saba ji..

Ya gyara mata kwanciya a hankali, ya bar kanta ya ƙara nutsewa a kan faffadan kirjinsa. Ya ɗauki Alkur'ani karami ya fara karantawa cikin sanyin murya, yana jin natsuwa na ratsa shi. Sai dai karar wayarsa ta katse wannan shirun...

Yana dubawa ya ga Mom a jikin screen. Tashin hankalin mahaifiyarsa ya bayyana tun daga sautin muryarta daga can gida Nigeria...

"Hello... Hello Son! Kana lafiya? Mun ji labarin kasar Alhamra ba lafiya, ana ta rigima. Son, ka dawo gida ban so na rasa ka, don Allah ka dawo gobe-gobe nan!"

Cikin muryar lallashi ya furta,
"Mom, ki kwantar da hankalinki. Ba wani faɗa ake ba, labari ne kawai ake ta zuzutawa. Babu abin da zai same ni tunda ina da ayar Allah a kusa da ni."

Ta ce, "Son, na ji fa sai sace mutane ake yi, ina jin tsoro sosai."

Uncle Jalal ya ce, "Kar ki damu Mom, waɗanda aka sace ma za su fito da yardar Allah. Ki taya mu da addu'a kawai."

Kafin ya ankara, Mom ta sauya kiran zuwa Video Call. Nan take hoton Mom da kannensa mata guda hudu da suke gefe sunata wasan jife-jife da pillow, dukansu 'yan mata ne... Uncle Jalal ya manta cewa Maayah tana kwance a kirjinsa!..

Mom ta zaro ido tare da
"Yaaa ALLAH! Son, wacece nake gani a kwance a kan kirjinka?!"

Kannensa jin haka suka afko cikin wayar, suna kalle-kalle..

Nan suka fara
"Wow! Masha Allah, kyakkyawa da ita! Uncle, ita ce Auntynmu? Allah tana da kyau sosai, fuskarta kamar ta jaruma!"

Mom ma cikin mamaki ta furta
"Ikon Allah... Son, kamar gimbiya nake gani? Dubi abin sarauta a kanta, ga kayan jikinta na alfarma. Kai Jalal, me kake yi da gimbiya?"

Ƙannensa ba su bar shi ya yi magana ba, suka ci gaba da yaba wurin..

"Kaiii Uncle! Dubi wurin da kake, tsatstsarren lambu ne mai furanni masu kyan gaske. Gaskiya Uncle, ba don ana faɗa a can ba, da yanzu na taho ziyara. Garin ya tsaru!"

Uncle Jalal ya ji kunya ta kama shi, ga shi ya rasa yadda zai yi bayani ga Mom ɗinsa dake ta zargin wani abu daban. Shi kuma ya san halin Mom da ƙannensa, idan ya bar su, za su iya kai dare suna surutu...

Cikin sauri ya furta "Yanzu tunda kun ganni na sanar da ku ina lafiya, sai an jima."

Kit! Ya yanke wayar kafin su ƙara wani surutun. Ya sauƙe numfashi, yana jin ɗacin yadda suka ganshi a haka...

Ya sake mayar da kallonsa kan Maayah, wadda ko motsi ba ta yi ba. Tana nan cikin bawan barcinta, ba ta san kishin-kishin ɗin da aka yi a kanta daga Nigeria ba...
Uncle Jalal ya yi murmushi mai ciwo, ya ci gaba da karanta Alkur'aninsa, yayin da yake jin ɗumin kanta a kirjinsa yana ƙara masa wani irin nishaɗi da bai taɓa ji ba...

Wannan karan kam, Mom ba za ta kyale shi ba! Bayan ’yan mintuna kaɗan da yanke wayar, sai ga saƙo ya shigo ta WhatsApp daga wurin Mom. Uncle Jalal ya zaro ido ganin har saƙon voice note ta turo...

Uncle ya rage ƙarar wayar yadda Maayah ba za ta ji ba, sannan ya danna play...

"Jalal! Kana jina? Wato ka kashe min waya don kada in tambaye ka gaskiya ko? To uwar kowa ce uwar kowa, wallahi na gani da idona. Yarinyar nan ba ’yar kowa ba ce, kowa ya ganta ya san jinin sarauta ne. To ina so ka sani, duk ranar da za ka taho hutu, kada ka kuskura ka taho ba tare da ita ba. Ko da kuwa sarki ne ubanta, ka ce masa Mom ta ce tana son ganinta. Kuma gobe zan ƙira ka mu ƙarasa maganar, ka shirya bayani!"

Uncle Jalal ya dafe kansa, yana murmushin yaƙe. Ya san Mom, idan ta ƙafe akan abu, to magana ta ƙare. Ya kalli Maayah dake ta sharar barci, ya raɗa mata a kunne cikin wasa...

"Ke dai kina nan kina barci, ba ki san ruhinki ya riga ya koma Nigeria ba."

A hankali Maayah ta fara buɗe idanunta. Ta ji wani irin ɗumi da lallausan ƙirji dake ɗauka yana hawa. Da farko ta ɗauka a gadonta take, amma kamshin turaren Uncle Jalal da sautin karatun Alkur'aninsa da yake yi a hankali suka dawo mata da hayyacinta...

Ta zabura ta miƙe zaune, tana goge idanunta, fuskarta cike da kunya da kuma mamaki...

"Uncle... barci na yi?"

Ya rufe Alkur'aninsa, ya kalleta da wani kallo mai cike da ma'ana..

"Barci ma kuwa.. Kin yi barci sosai, har ma kin yi baƙi daga Nigeria."

Maayah ta yamutsa fuska tana mamaki...
"Nigeria? Me kake nufi?"

Uncle Jalal ya sauya salon maganar zuwa mai muhimmanci don kada ta gano abin da ya faru a waya..

"Maayah, gidajen rediyo da gidajen jaridun duniya duk sun ɗauki labarin abin da yake faruwa a Alhamra. Tun daga Nigeria har zuwa Turai, kowa ya sani cewa ana sace mutane a nan. Mom ɗina ma ta ƙira tana neman in dawo gida..."

Maayah ta sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannunta. Tausayin kanta da na garinsu ya sake kama ta...

Ya furta a hankali
"To Uncle, me ya sa ba ka tafi ba tunda ta buƙaci hakan? Kowa yana gudun Alhamra yanzu."

Uncle cikin muryar lallashi ya ce,
"Zan iya barin karatun naki a rabi ne? Kuma na gaya mata akwai wata 'yar karamar gimbiya dake buƙatar kariya ta, shi ya sa zan tsaya."

Maayah ta ɗago ta kalle shi, wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta. Ta manta da marin da ya yi mata ɗazu, yanzu kawai tana jin daɗin kalaman sa.

Ya kalli yadda idanunta suka cika da kwalla, ya sauƙe nannauyan numfashi. Ya gane cewa ba rashin son karatu ne ke damunta ba, illa dai nauyin kwakwalwa da kuma halin da ta tashi na rashin uwa da kuma ko in kula da mahaifinsu...

Uncle Jalal ya gyara zama, ya miƙa hannu ya ɗauko littafin dake gabanta, ya kalle ta cikin natsuwa...

"Maayah, ki saurare ni da kyau. Rayuwa ba ta tsaya kawai akan kyau ko gadara ko zama a cikin wannan garden ɗin ba. Duniya tana canzawa, kuma ilimi shi ne kaɗai hasken da zai taimake ki ki mulki kanki kafin ki mulki wasu. Ki duba yadda kowa yake takama da ke, idan baki da ilimi, gobe idan ba kya karkashin inuwar sarki, yaya zaki kare mutuncinki?"

Maayah ta fara girgiza kanta, hawaye suka fara sintiri a kuncinta, muryarta tana rawa. .

"Uncle... kana ganin bana son yi ne? Wallahi ina so, amma bana fahimta! Komai kake faɗa ji nake yi kamar a mafarki. Kwakwalwa ta bata ɗauka, Uncle na gaji, na gaji da jin kaina yana min ciwo duk sanda nake son haɗa waɗannan haruffan..."

Ta fashe da gagarumin kuka, ta boye fuskarta a cikin tafukan hannunta..

"Kowa yana ganin ni jaka ce, ko Abul idan yana maganar ilimi sai dai ya ƙira sunan Ayat ko Yumna da Ching-Ching... Uncle, idan har ban fahimta ba yanzu, yaushe zan fahimta?"

Ganin kukan nata ya tsananta, Uncle ya ji wani irin tausayi ya sake ratsa shi. Ya ɗauko lallausan tissue ya miƙa mata, sannan ya yi magana cikin sanyin murya..

"Shiru... ya isa haka. Ba jaka bace ke. Kowa da irin gudunsa, wani sai an bi da shi a hankali sannan yake gane abu. Ni ba zan taɓa barin ki ba har sai kin iya... Ko da haruffa biyu ne zamu riƙa koya a rana ɗaya, zan yi haƙuri da ke. Amma kada ki sake cewa baki da amfani, domin wanda ya iya barci a ƙirjin malaminsa ba tare da tsoro ba, yana da babban rabo a zuciyar malamin."

Maayah ta tsagaita kukan ta ɗago tana kallonsa da jajayen idanu, tana mamakin kalaman ƙarshe da ya faɗa. Ta ji wani irin kwarin gwiwa ya ziyarce ta...

✨✨✨

VIP Ward, Pavilion International Hospital...

2:30 na dare.

​Cikin dare, duk asibitin ya yi tsit. A cikin ɗakin Chief, Ching-Ching ta tana gadon Chief, ta tura kanta cikin faɗaɗɗen ƙirjinsa, Tana ta sharar bacci, har tana ɗan minshari kaɗan-kaɗan..

​Chief Onyx kuma yana nan idonsa biyu, yana danna wayarsa cikin natsuwa, kansa yana ɗan sarawa saboda dambarwar hayani..
​Domin shi sam baya son hayaniya tinin kansa yake hau ciwo..

​Kwatsam! Ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali. Dr. Sophia ce ta lallaɓo, tana sanye da ƙananun kayan ta, idanunta sunyi ja saboda kishi.. Ganin Ching-Ching a inda take mafarkin kasancewa ya sa jinin jikinta tafasawa...

​Ba tare da tsoro ba, Sophia ta ƙarasa gadon. Cikin zafin rai ta cafko rigar Ching-Ching, ta ɗage ta sama, ta cillar da ita ƙasa a kan carpet...
Ching-Ching dake baccin wahala sai kawai ta juya ta ci gaba da baccin a ƙasa, tana tunanin ko mafarki take yi ta faɗa daga gado..

​Sophia ta hau gadon da sauri, ta ture wayar Chief, sannan ta kwanta a daidai saitin da Ching-Ching take, ta dora kanta a kirjinsa...

​Chief Onyx ya zaro ido, ya tashi zaune kaɗan yana kallon Sophia cikin mamaki da bacin rai..

​Cikin tsawa ya furta...

"Are you stupid, Sophia? What the hell do you think you're doing? Get off my bed right now!"

​Itama cikin nata Turancin tana huci ta ce,
"No, Onyx... I won't, This girl has no right to be here.. I was here first.. I am the one who knows how to heal your heart and your body.. I'm not leaving you for a child..."

​Chief ya ce,
"We are over Sophia... You destroyed everything with your crazy jealousy years ago. This is a hospital, not a drama club..."

​Ta ce,
"Call it whatever you want... I am staying right here. If you want me out, call the security to carry me like a criminal..."

​Chief ya yi barazana, ya yi faɗa, ya yi harara, amma Sophia ta yi biris. Ta kankame hannunsa, ta lumshe ido tana hawaye. Chief ya gaji, ya san cewa Sophia idan kanta ya ɗauki zafi, to ba ta ji, ba ta gani...

​Daga karshe Chief ya yi dogon nishi, ya ajiye wayar ya kalli silin. A haka bacci ya kwashe su, Sophia tana kankame da shi a kan gado, Ching-Ching kuma tana sharar bacci a ƙasa tana mafarkin tana cin naman kaza a cafeteria...

​Asubar fari, anata ƙiraye-ƙirayen sallah.. Ching-Ching ta fara buɗe idonta tana miƙa. Ta kalli kanta a ƙasa, sannan ta ɗaga kai ta kalli gadon...
​Ganin Sophia a makale da Chief, idon ya fito waje kamar an danna mata allura...

​Ta zabura ta miƙe, ta nufi kanta da ihu..

"Wayyoooo Uncle shi kenam ka mata ciki wallahi...na shiga uku na lalace, wannan jarababbiyar likitar arniya, sai da kika lallaɓo cikin dare kika zo? Mai son maza kawai...."

Chief yana mata alamun ta rage murya a asibiti suke amma Ching-Ching ba ji ba gani...

Ching-Ching ba ta tsaya wata-wata ba, ta haura kan gadon ta fara ƙoƙarin tura Sophia, yayin da Sophia ita ma ta ƙanƙame hannun Chief kamar na gadon gidan ubanta...

"Ki sauƙa, mai son maza kawai, ai ba shi bane kaɗai namiji ga can bodyguards ɗinsa kije ki zaɓi ɗaya mana...ki sauƙa kar ya miki ciki..."


Dr. Sophia tana tunkuɗa Ching-Ching itama tare da faɗin

"Stay away, you brat.. Ni ce na fi cancanta in kasance a nan. Get off before I inject you with something that will make you sleep for a week!"

Chief Onyx ya tashi zaune cikin matsanancin raɗaɗin ciwon kai, fuskarsa ta kumbura kamar gajimaren hadari tsabar fushi...

Ya daka musu tsawa
"Ya isa haka!!! Sophia, sauƙa daga gadon nan! Ching-Ching, sauƙa ke ma!"

Ganin Sophia ta ƙi sauƙa, yasa Chief ya danna ƙararrawar gaggawa. Nan take Security guda biyu suka faɗo ɗakin...

Cikin murya mai sanyi cike da umarni ya furta,
"Take her out. Now!"

Jami'an tsaron suka kama Sophia. Tana kuka tana mutsu-mutsu, har suka kai ta bakin ƙofa. Ta tsaya, ta kalli Ching-Ching wadda take washe haƙora tana yi mata gwalo...

Dr. Sophia cikin zafin rai da ihu, ta ce,
"Kada ki yi murna yarinya. Kina tunanin ke ce a zuciyarsa? To ki sani, Chief Onyx yana da wani sirri a ɓoye. Baya taɓa barin mace ta shiga ransa don akwai wani hoto a cikin locket ɗin sarƙar da yake sawa a wuyansa... hoton macen da ya fi kowa so ce a duniya, kuma ba ke ba ce!"

Ta faɗa tana kuka, jami'an tsaron suka ja ta waje.

Ɗakin ya yi tsit. Ching-Ching ta daina gwalo, ta juya tana kallon Chief Onyx da wani irin kallo na tuhuma. Ta matso kusa, idonta ya sauƙa akan wuyan Chief inda take ganin sarƙar zinare a ɓoye cikin rigarsa..

Cikin muryar shagwaɓa amma akwai kishi a ciki ta furta
"Uncle... dama kana da wata macen a cikin sarƙa? Ka nuna min! Idan ba haka ba, zan fasa ɗinkin kafaɗarka in zuba masa gishiri!"

Chief Onyx ya dafe kansa, ya san cewa maganar Sophia ta dasa wa Ching-Ching wani sabon tsimi...

Ya ce, "Kada ki saurari Sophia, Ching-Ching. Surutu take yi kawai saboda kishi."

Ta ce, "A'a! Nima ina da kishin overdose! Nuna min hoton nan, ko kuma in fara ihu daga nan har zuwa fada.."

Ya fara tunanin wani irin abu ne haka kamar Ching-ching ta fara soyayya da shi...a cikin ransa ya furta "impossible, zan cire miki soyayyar nan domin a tunaninsa ba ta kai yin soyayya ba, kuma abin raini ne ya rasa da wanda zai yi soyayya sai da kwailar yarinya kamar Ching-ching, haka ya ƙarisa yana girgiza kai alamun hakan bazai taɓa yu wa ba...

Ya gaji da surutun Ching-Ching, ya san muddin bai ba ta abin nan ba, ba za ta bar shi ya huta ba. Ya cire sarƙar daga wuyansa, ya miƙa mata ita cikin natsuwa..

"Gashi, amma karki taɓa buɗewa. Sirri ne na rayuwata. Idan kika buɗe, raina zai ɓaci sosai."

Ching-Ching ta karɓa, tana washe haƙora. "To Uncle, na ji, ba zan buɗe ba."
Amma a zuciyarta cewa take, Yanzu ma zan ga shegiyar...

Tana fita daga ɗakin, ta nufi wani lungu inda Gely take tsaye tana jiran umarni. Ching-Ching ta fito da sarƙar, locket ɗin yana sheƙi. Ta yi ƙoƙarin ɓallewa da farce, amma abin ya faskara...

"Lallai ma Uncle, ashe ya rufe shi da ƙarfi haka? Gely! Zo nan! Yi amfani da waccan Laser ɗin idonki ki fasa min wannan abun, mu ga Arniyar da take ciki! Ina so in ga wacce take takara da ni a zuciyar Uncle!"

Gely ta kunna idonta, wani jan haske ya fito. Cikin daƙiƙa biyar, locket ɗin ya buɗe kyam...

Ching-Ching ta matso kusa, tana zazzaro ido, tana shirin so ta ga wata kyakkyawar budurwa ce a ciki... Amma tana kallon cikin locket ɗin, sai ta tsaya cak...
Wani kyakkyawan hoton mace ne, mai fuskar natsuwa da kamala... Idanunta irin na Chief ne, kwarjininta kuma ya nuna cewa ita ma daga zuri'ar sarakuna take. Ba kowa ba ce illa Mahaifiyar Chief Onyx...

Ta sauƙe ajiyar zuciya, ta kalli Gely..
"Iye? Gely, ashe ba budurwa ba ce? Wannan ai kaman Uncle take yi! Ashe tsohuwa ce? Haba, dama na sani, Uncle ba shi da sauran taste na irin waɗancan mutanen."

Gely tana binciken bayanan hoton ta ce,

"Scanning... This is Queen Zeenat, the late mother of Chief Onyx. Accuracy 100%."

Ching-Ching ta rufe locket ɗin, ta fara rarraba ido. A maimakon ta ji daɗi, sai kuma kishi ya sake dawowa ta wani fannin..

"Amma duk da haka Gely, me ya sa zai sa hoton wata mace a wuyansa ni kuma bai sa nawa ba? Ni ma ai nan gaba mahaifiyar jariransa zan zama! Gaskiya Gely, dole yanzu mu nemo hoto na, mu maƙala a ɗayan gefen, ko don ya riƙa ganina kusa da zuciyarsa!"

Tana cikin wannan maganar, sai ta ji muryar Chief a bayanta, ya fito daga ɗakin jinya yana takawa a hankali...

"Ching-Ching! Me kuke yi a nan?"..

Ya ƙaraso wurin, idanunsa suka sauƙa akan locket ɗin da har yanzu hayakin Laser ɗin GELY yake tashi a jikinsa. Ya ga hoton mahaifiyarsa a buɗe. Nan take fuskarsa ta sauya, kwarjininsa ya ninka sau goma, wani irin sanyi mai ban tsoro ya ziyarci wurin.

Cikin muryar dake nuna tsananin ɓacin rai ya furta

"GELY... ina umarni na yake? Na ce karki taɓa barin kowa ya taɓa wannan sirrin. Amma yau kin zama 'yar amshin shatan yarinya mara hankali?"

GELY ta tsaya cak, idanunta suka yi ja Error Mode...tare da faɗin

"Warning... Conflict of commands. Primary user override..."

Chief ya darara mata tsawa da
"Yi mun shiru! Daga yau, duk wani System Access da kike da shi a matsayin mataimakiyata, na soke shi. Kin zama tsohon ƙarfe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login