Showing 141001 words to 144000 words out of 154131 words

Chapter 48 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

da kike gani a matsayin tsoro… alhali kuwa tsari ne.”

Idanunta suka ɗan haɗe...
“Ruma ba mace bace mai sauƙi. Amma ba duk abin da kuke tunani bane gaskiya.”

Ya shafa fuskarsa tare da faɗin
“Kuma akwai wasu abubuwa… da lokacin su bai yi ba....”

Ayat ta ɗan sauke numfashi, zuciyarta tana cike da sha’awar sani...
Idanunta sun yi haske kamar tana ƙoƙarin fahimtar duk wani sirrin da mahaifinta ya ɓoye tun da farko..
Ta miƙe, ta kalli Sarki Nourdeen cikin natsuwa, muryarta cike da tambaya..

“Abul… ka riga ka gaya min game da Ruma da Aysh. Amma yanzu ina son sanin wani abu… Hibba, mahaifiyar Maayah… Me ya sa aka raba ku da ita? Me ya sa aka ɗauke Maayah daga hannunta? Shin akwai wani abu da ya faru da ya tilasta hakan?”

Sarki ya tashi tsaye tare da gyara alkyabbarsa. Ya kalli Ayat da wani irin kallo mai cike da sanyi da tsoron abin da gobe za ta haifar...

​ "Gimbiyata, gaskiya tana da ɗaci.... Idan har kika san cikakkiyar gaskiyar abin da ya faru tsakanina da Hibbah... watakila ba za ki sake kallona da irin idon girmamawa da kike kallona yanzu ba. Gwara mu bar labarin a haka yanzu."

​Bai jira amsarta ba, ya juya ya nufi Bedroom ɗinsa, ya bar Ayat nan zaune tana kallon inuwarsa, yayin da zuciyarta take cike da dar-dar...


✨✨✨

​Gari ya waye ba tare da haske ba, domin gajimare ya rufe sararin samaniya. Tun kafin sallar asuba, aka fara jin koke-koke da hayaniya a kofar fadar Alhamra...

​Dubunnan talakawa ne suka taru a bakin babban gate din fadar. Fuskokinsu cike da hawaye da ɓacin rai.

​Wani bawan Allah yana kuka tare da faɗin
"Ina yarona? An sace min yaro a tsakiyar dare!"

​Wata mata ta ce, "Mijina ya fita bai dawo ba, an neme shi an rasa!"

​Wani dattijo shima ya ce,
"An sace Ƴata! Sarki ya fito ya gaya mana abin da yake faruwa!"

​Jami’an tsaro sun yi katanga da jikinsu, suna tura mutane baya don kada su afka cikin fada. Sarki Nourdeen yana tsaye a saman bene na fadar, yana kallon mutanen nan, yana jin wani irin tashin hankali. Ya san wannan aikin Ruma ne, ta fara cika alkawarinta na sanya masa zazzabi....

​A gefe guda kuma, Ayat ba ta iya zama shiru ba. Tana ɗakinta ta yi shigar Inuwa. Ta gyara kakin jami'an tsaro dake dauke da tambarin Royal Guard, ta sanya gemu da saje na jabu waɗanda suka sauya fuskarta gaba ɗaya, ta rufe kanta da rawani...

​Ta bi ta wata boyayyar hanya ta fita har zuwa bakin gate, inda ta haɗu da sauran sojojin da suke tsaron kofar fadar...

​Inuwa tana tsaye, riƙe da makami, tana kallon talakawan dake kuka a gabanta. Duk da tana shigar namiji, zuciyar Ayat ta mace tana tafasa da tausayi...

​Ta ga wata yarinya ƙarama tana kuka tana neman mahaifinta...

​Ta ji kukan wata uwa dake roƙon a cece mata ɗanta..

​Inuwa A ransa ya ce,
"Me Ruma take taƙama da shi ne? Ina sojojin da Abul yake gadara da su? Gashi ana taɓa talakawa marasa laifi saboda rikicin manya. Allah Ka kawo mana dauki...."

​Duk da cewa an tsare kowace gimbiya a sashenta, Zayana tana can a Cell ta ji labarin abun da ke faruwa a can waje da hanyar guard dake kula da ita... Ta yi murmushin mugunta tana kallo gabanta... tare da maganar fili

"Na gaya muku... Mummy ba ta wasa. Wannan farkon wasan ne kawai. Idan ba a fito da ni ba, kowa a Alhamra sai ya gwammace ya mutu."

Yayin da sarki Nourdeen ya samu nasarar lallashin talakawa su koma gida har zuwa washegari...

*OTHER SIDE*

Binciken sirri na King Diamond ya kai shi ga gano asalin ƙasar Pavilion. Wani gari ne da mahaifinsu ya assasa tun ba mutane, amma yanzu cikin shekaru 33, ya zama gari mafi kyan gaske a duniya..

Babu ginin ƙasa ko ɗaya, ko’ina gine-gine ne na gilashi wato skyscrapers masu kallon sararin sama, suna sheƙi karkashin hasken rana...

Sararin samaniyar garin cike yake da kananan jirage Drones masu sanya idanu, waɗanda ba sa bacci don kare ƙasar daga kowane irin farmaki...

Pavilion ta zama matattarar masu neman ilimin kimiyya da addini daga sassan duniya daban-daban, sakamakon kokarin Chief Onyx...

King Diamond ya gano cewa ɗan uwansa ba sarki ne kawai ba, babban masanin kimiyyar kwamfuta ne da geography... Ya kera dakarun Robots dubun-dubatar waɗanda suke gudanar da ayyukan tsaro da na yau da kullum. Gely ma ɗaya ce daga cikin manyan robots ɗin da ya ƙera da kansa...

A ɗaya bangaren kuma, King Diamond yana zaune a tsakiyar fadarsa, karkashin ruwan Power Pool dake fitar da haske mai launin shuɗi. Damuwa ta lulluɓe shi, yayin da yake kallon kansa a cikin ruwa...
Tambayar Da Ba Ta Da Amsa...

"Me ya sa?" Ya faɗa cikin muryar da ta girgiza ɗaukacin fadarsa...

"Me ya sa a cikin mu tagwaye, aka zaɓe ni domin in zama silar sadaukarwa ga duniyar aljanu? Me ya sa aka bar Ra'ees yana mulkar mutane da hasken rana, ni kuma aka turo ni cikin wannan duhun tun ina yaro?"

Baƙin ciki ya tsaya masa a makogwaro. Ya ji an yi masa wariyar jini.... Ganin yadda ɗan uwansa yake rayuwa cikin duniyar mutane, yana taɓa su, yana magana da su, yayin da shi kowa yake gudunsa ko tsoronsa saboda shi Aljani ne...

Idanunsa sun koma ja saboda fushi da raɗaɗi..

"Mahaifina ya sadaukar da ruhina domin ya samar da iko da kariya da mulki...Ya mayar da ni makamin kare dangi, ya hana ni jin ɗumin rayuwar ɗan Adam..."

✨✨✨

Hamadar Desert Oasis
Wato wurin HUTAWAN ZAKI Chief onyx...

Can nesa da hayaniyar gari, a wani wuri na musamman a cikin Pavilion City, Chief Onyx ya ja layin hutawa. Wurin ya haɗu da ni’imar hamada da kuma kyan wani kogi dake ratsawa a gefe. Nan ne mazaunin dabarunsa, inda babu mai isa sai da izininsa...

Chief ya baje kayan wasannin motsa jiki, akwai teburin Snooker, akwai Handball, da kuma babban teburin Foosball wanda ake tura ƙananan ƴan ƙwallo da sanda... Bayan ya kammala ɗan motsa jiki, ya ɗauki bindigarsa ya fuskanci Target Board...wurin atisayen harbi...

Pat! Pat! Pat! Duk harbin da yake yi, a tsakiyar jan ɗigon yake fita...

Chief ya ajiye bindigar, ya nufi wani babban dogon madubi na hangen nesa (High-powered Telescope)...

Ya ƙanne ido ɗaya, yana kallon kyawun sararin samaniya da kuma abubuwan dake nesa da sauran mutane..

A gefensa kuma, Bodyguards ɗinsa suna tsaye kamar wasu mutum-mutumi... Kowannensu sanye da baƙin gilashi, bindigunsu a shirye, fuskokinsu ba sa nuna alamar wasa. Iskar sahara tana kaɗawa, tana hura rigar Chief...

Yana cikin karkata Telescope ɗin, kwatsam! Wani harbi marar sauti wanda ake ƙira da Silencer shot ya fito daga can nesa, inda maƙiyi ya fake...

Harsashin ya samu Chief Onyx a kafaɗarsa ta dama...
Ba tare da ya nuna raki ko ya faɗi ba, Chief ya saki Telescope ɗin, ya dafe damtsensa yayin da jini ya fara ɓulbulowa ta cikin rigarsa. Idanunsa suka rine suka yi ja, ya zama kamar zaki da aka harba...

Cikin murya mai amo da juriya ya ce,

“KADA KU BAR SHI! Ku kamo ko wanene!”

Nan take ayarin tsaro suka rarrabu. Wasu suka kewaye shi tare da bashi kariya, wasu kuma suka zura a guje da motocinsu zuwa inda akayi harbin..

An garzaya da Chief cikin motarsa ta alfarma wanda harsashi ba ya ratsawa...

Duk da jinin dake zuba, Chief yana zaune ne daram, fuskarsa ba ta nuna alamar rauni ba. Jajirtaccen namiji, mai jure azaba...

Yana magana ta cikin na’urar sadarwa..

“Ko wanene ya yi wannan, ya sani ya taɓa wutar da za ta ƙone shi.”

Ayarin motocin suka nufi babban asibitin sirri na Pavilion. Ko da suka isa, Chief Onyx ya fito da kansa, yana takawa cikin natsuwa duk da jinin dake fita. Likitoci suka yi kansa cikin gaggawa.
A lokaci guda, labari ya isa makaranta inda Ching-Ching take....wasu bodyguards da suke tsaronta acan ne suka ɗauko ta tare da nufo wa asibiti...

✨✨

Special VIP Ward, Pavilion International Hospital

Chief Onyx yana kwance a kan gadon asibiti, an cire masa harsashin kuma an fara yi masa ɗinki. Duk da irin wannan azaba, ko motsa fuska bai yi ba, yana kallon silin ɗin ɗakin cikin natsuwa.
Kwatsam! Sai aka ji wani ihu daga corridor, irin ihun da Chief ya riga ya sani...

Ching-Ching ce.
Ta faɗo ɗakin tana kuka, har tana tuntuɓe da carpet, Gely tana biye da ita tana ƙoƙarin riƙe ta...

"WAYYOOO UNCLE! Wayyo Allah na, an kashe mana kai! Uncle dama ka bari ni aka harba, tunda ni dama jini na riga na saba da shi a kwanakin nan! Me ya sa za su harbi namijin da yake da mata mai juna-biyu a hannunsa?.....Dama ni aka harba ba kai ba..."

Ta faɗa a kan gadon tana ƙanƙame ƙafarsa, tana kuka kamar ranar zai mutu...


Chief cikin murya mai rauni ya daka mata tsawa...

"Ching-Ching! Ya Isa haka! Harbi ne a kafaɗa, ba mutuwa zan yi ba. Sannan ya isa haka, kukan nan naki ya fi harbin ciwo."

A daidai wannan lokacin, Dr. Sophia, wata kyakkyawar likita mai dogon gashi da farar riga, ta ƙaraso kusa da Chief don duba saitin ɗinkin. Ta rusuna tana tattaɓa kafaɗarsa cikin kulawa...

Dr. Sophia ta ce,
"Chief, please stay calm, I just need to check the dressing..."

Ching-Ching ta tsagaita kukan lokaci guda. Ta ɗago kanta, ta kalli yadda likitar take taɓa kafaɗarsa, nan take idanunta suka sauya kala. Ta miƙe tsaye tana turo baki...

"Ke! Maza matsa daga nan! Ke ma so kike ki taɓa shi ki ɗauki ciki? Ko ba ki ga ni yadda na zama ba ne? Maza matsa ni zan wanke masa ciwon da kaina!"

Dr. Sophia cikin mamaki ta ce,
"Excuse me? I am a doctor, and I'm just doing my job."

Ching-Ching ta ce,
"Aikin me? Aikin shafa kafaɗar mutane? Uncle, kalle ta, har wani lumshe ido take yi tana taɓa ka! Gely, maza ba ni ruwan zafi da auduga, ni zan yi masa komai. Ba ma buƙatar wannan likitar mai gashin doki!.."

Ching-Ching ta ƙwace audugar dake hannun Dr. Sophia, ta fara ƙoƙarin matsa wa Chief kafaɗa...

Duk juriyar Chief sai da ya kanne ido yana faɗin

"Washhh! Ching-Ching, za ki ɓalla min ƙashi ne? Ki bari likitar ta yi aikinta!"

Tana turo baki ta ce,

"A'a Uncle! Ita fa kallo na take yi kamar tana so ta sace ka. Ni dai na gaya maka, duk macen da ta sake taɓa ka a asibitin nan, to za mu raba juna-biyun nan da ita...! Kuma ma, me ya sa kake kallonta? Ko tafi ni kyau ne don tana da farar riga?"

Chief ya runtse ido, ya dafe kansa da hannu guda..

"Gely, don Allah ki fitar da ita kafin ta ƙarasa kashe ni. Maƙiyin da ya harbe ni bai kai wannan yarinyar haɗari ba."

Ching-Ching tana shirin sake fashewa da kuka tana faɗin

"Yanzu Uncle korata kake yi? Bayan kasan halin da nake ciki? To gaskiya ni nan zan kwana, kuma zan riƙa duba duk macen da ta shigo, sai na ga takardar shaidar cewa ba ta da sha'awar riƙe hannun mutane!"

Yayin da Ching-Ching take faman danna wa Chief kafaɗa cikin rashin ƙwarewa da tura baki..

Chief ya ɗaga kansa, idonsa ya sarƙe cikin na Dr. Sophia..

Idanun Sophia sun yi jawur saboda wani baƙin ciki da kishin da suka ninka na Ching-Ching sau dubu..

Sophia ba kowa ba ce illa tsohuwar budurwar Chief. Sun yi soyayya mai zafi tun lokacin da ya taɓa yin wani haɗari a baya, ita ce take zuwa har cikin fada tana ba shi kulawa... Amma kishinta ya yi yawa irin overdose ɗin nan, har ta kai ga tana kishin iskar da take bugunsa, hakan ya sa suka rabu...

Amma kallon da suke yi wa juna yanzu? Akwai sauran burbuɗin soyayya wanda ake ƙira da love residue dake yawo a iska...

Ching-Ching ta lura da yadda suke kallon juna. Ta ga yadda idon Sophia ya canza, ta kuma ga yadda Chief ya yi sanyi. Nan take ta ƙara danna masa kafaɗar da ƙarfi!

Chief ya furta "Auuu! Ching-Ching! Za ki cire min kafaɗar ne?!"

Tana shirin kuka cikin shagwaɓa ta ce,

"Kyale ni Uncle! Matsawa nake yi don jinin ya koma zuciyarka, don na ga kamar kallon wannan likitar yana sa zuciyarka bugawa da sauri. Ke kuma Likita, me kike kallo haka? Ko ke ma kin san cewa idan kika daɗe kina kallon namiji haka shima yana kawo ciki?"

Dr. Sophia ta goge wani ɗigon hawaye dake neman fito mata, ta ƙaraso kusa da gadon, ta yi banza da Ching-Ching kamar ba ta wanzu ba. Ta sa hannu ta riƙe ɗayan hannun Chief na hagu wanda ba shi da ciwo...

Cikin muryar kuka da rawar murya..ta ce,

"Onyx... har yanzu baka canza ba. Kullum cikin haɗari kake. Kuma har yanzu baka koyi yadda zaka zaɓi mutanen dake kusa da kai ba. Wacece wannan yarinyar da take neman ƙarasa ka?"

Ching-Ching ta ajiye audugar hannunta, ta ɗora hannu a ƙugu ta ce,

"Iyeeee? 'Onyx'? Sunan da kika kira shi kenan? Lallai ma wannan likitar! To ki sani, ni ce Future Mother of his Baby koda kuwa ta hanyar taɓa hannu ne..! Kuma ki sake shi yanzun nan, karki goga masa tsofaffin ƙwayoyin cutarki..."

Chief Onyx ya ji ciwon kafaɗarsa ya ragu, amma na kansa ya ƙaru. Ga Sophia dake kuka tana kallonsa da tsohuwar soyayya, ga kuma Ching-Ching dake shirin kai wa Sophia dambe...

Chief ya ce,
"Sophia, ya isa haka. Kin san me ya sa muka rabu a baya, kishinki zai iya lalata komai..."

Sophia ta ce, "Amma kalli wannan yarinyar! Ta yaya zaka bar ta tana danna maka rauni? Ni ce na san yadda jikinka yake, Onyx! Ni ce na san inda yake maka ciwo!"

Ching-Ching ta tura baya da ƙarfi sauran kaɗan Sophia ta faɗi tana faɗin

"Ƙarya kike yi! Ni na fi sani! Har ma na san cewa idan ya ɓata rai, hancinsa yana yin girma! Kuma ke Likita, idan baki fita ba, zan ƙira Gely ta ɗaga ki ta jefar da ke ta taga, don kishina ni Original ne, naki kuma na Expiring date ne!"

Ta ƙara shige tsakanin Chief da Sophia, ta ƙara tura Sophia da baya da ƙarfi, ta koma ta laɓe a ƙirjin Chief ta bangaren da ba shi da ciwo...

"Uncle, ko ka kore ta, ko kuma in sa maka kuka yanzu in tada dukkan asibitin nan!"....

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 39

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*




Halin da ake ciki a Alhamra ya kai maƙura, domin fargaba ta cika zukatan talakawa yayin da aka rasa inda mutane suke ɓacewa...
Sarki Nourdeen yana can yana faman sintiri a fadarsa, yana ta ƙiran lambar Ruma amma "not reachable", bai sani ba cewa Sarauniyar tana wasa da hankalinsa ne da gangan..

A cikin wannan yanayin ne Uncle Jalal ya iso fada domin koyar da Maayah.

Ma’aikatan fada sun riga sun san darajar Uncle Jalal a matsayin malamin gimbiya, don haka aka ba shi damar wucewa har zuwa babban sashen Maayah. Aka kai shi har cikin lambunta, wanda yake cike da furanni masu kamshi da korayen ƙananun bishiyoyi... Aka shimfida masa wata dadduma ta alfarma, mai laushi da tsada...

Uncle Jalal ya zauna ya baje littattafansa, yana jiran gimbiya. Amma Maayah, wadda take ta gadara da son jan aji, ta bar shi zaune na tsawon awanni biyu. Tana can ɗaki tana gyara kwalliya, tana cewa a ranta,
"Ai shi ma dole ya san ya zo wurin gimbiya...."

Bayan lokaci mai tsawo, Maayah ta fito tana taku ɗaya-ɗaya, tana yauƙi da yanga kamar yadda ta saba. Ta ƙaraso garden ɗin tana tauna chewing gum, tana busawa yana fashewa a fuskarta..

Ta tsaya a gaban Uncle Jalal wanda ransa ya riga ya ɓaci, tana tauna gum ɗin nan tana wani kalle-kalle. Ganin rashin kunyar ta yi yawa ne yasa bai yi wata-wata ba, ya miƙe tsaye tare da zabga mata wani lafiyayyen mari wanda ya sanya kanta juyawa...

Nan take chewing gum ɗin ya faɗo daga bakinta, ta dafe kuncinta wanda ya yi jawur, hawaye suka fara sintiri akan fuskarta...

Cikin kuka da shagwaba ta ce,
"Uncle Jalal... jan aji fa nake maka... me ya sa za ka mare ni?"

Ya zaro idanu, yana huci saboda raɗaɗin abin da yake faruwa a garin Alhamra da kuma halin ko-in-kula na Maayah..

"Ina kika ga ajin da za ki ja? Wawiya kawai! Garinku yana cikin tashin hankali, ana sace mutane ana sace kananan yara, kowa yana kuka, amma ke kina nan kina wani jan aji da nuna isa? Ke wace irin mutum ce da ba ta san ciwon kanta da na al'umma ba?"

Ya ci gaba da balbale ta da faɗa, yana nuna mata cewa mulki ba hauka ba ne, sannan ya zauna ya nuna mata wurin zama...

Ta zauna tana shasshekar kuka, tana goge hawayenta da bayan hannu. Duk gadarar nan ta tafi, yanzu tana jin tsoron Uncle Jalal fiye da kowane lokaci...

Ya buɗe littafin, ya ajiye a gabanta, ya fara nuna mata alphabets ɗaya bayan ɗaya..

"Karanta wannan! Kada ki kuskura ki sake min wasa. Alhamra tana bukatar shugabanni masu tunani, ba gimbiyoyi masu tauna chewing gum ba."

Maayah ta sunkuyar da kai, tana bin haruffan da yatsanta, muryarta na rawa tana biyo karatun. A karon farko, ta gane cewa rayuwar fada ba kawai yanga ba ce, akwai darasi mai tsanani dake jiranta.

Lambu ya yi tsit, sai sautin tsuntsaye dake kuka a hankali da kuma ƙamshin fure dake tashi. Uncle Jalal ya dukufa, yana nuna mata yadda ake haɗe Sentences a harshen Turanci.. Muryarsa tana fita cikin natsuwa, yana kokarin ganin ta gane dukkan bayanan da yake mata.

Yana cikin bayani, sai ya ji shiru, babu amsar Eh ko Na gane... Ya dakata da maganar, ya sauƙar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login