Showing 1 words to 3000 words out of 133773 words

Chapter 1 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9694

ο»ΏπŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«
( YAR JARIDA )







( A heart touching love story & destiny )








STORY & WRITTEN BY : ANISH








Marubuciyar littafin




TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ




❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯






BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM









PAGE 1 πŸ₯€ ❀






NIGERIA ( KADUNA STATE )












NASSARAWA G.R.A










Wata mota ce fara kal ta karyo wata kwana , glass din ta duka bakake ne ba ka iya ganin wanda ke ciki
Ta na tafiya a hankali kamar wanda ke tukin ya na cikin magagin barci


Sai da ta dauki wajen good five minutes ta na tafiya a haka kafin ta iso bakin kofar wani katafaren gida na ji da gani
Horn a ka danwa gateman din gidan , dan da ga gani wannan gidan da wuya a ce ba gateman


A hankali a ka fara wangale door din gidan
Tun kafin a ida bude kofar gidan , wannan motar ta yi cikin gidan da gudu kamar ba ita ba ce yanzu ke tafiyar nan a hankali


Ya na ganin motar ta shiga , gateman din ya saki dan karamin murmushi sannan ya meda kofar ya like ya zauna saman wata chair da ke bakin kofar gidan


Parking space wannan motar ta nufa , inda ta yi parking geffen wata motar irin ta tak amma ita wannan baka ce


A hankali a ka bude kofar driver sannan a ka kashe motar ,
Slowly a ka ziro kafa guda waje , sanye cikin wasu sneakers pink colour ma su bala'in kyau


Sai da a ka dauki wajen good two minutes kafin a ziro da kafar guda , sannan wata kyakyawar matashiya ta fito da ga cikin motar , sam ba ta da jiki amma ta na da shape kamar coca cola gaba da baya duk a cike su ke


Ta na sanye da wando palazzo black colour da wata t-shirt mai dogayen hannu pink colour , ta na sanye da wani dan karamin hijab fari , hannun ta dauke da school bag ta sunkuyar da kai kassa


A hankali ta sa hannu ta zame hijab din ta , nan take duk jelar gashin ta ta bazun mata ta rufe mata fuska , ta zubo saman shoulder din ta , har zuwa baya


Gashin na ta mai bala'in taushi so smooth , colour din shi blond ne kamar golden
A hankali ta daga kafa ta fara takawa kai a sunkuye , kamar an yi mata dole


Takawa ta ci gaba da yi har ta shigo cikin wani katafaren parlour mai bala'in kyau , komai na cikin shi golden colour ne ban da painting din bango da ya ke fari kal


A hankali ta ci gaba da takowa ta nufi wani stair an mishi kariya da glass


Har da ga kafa za ta haura stair ta jiyo Muryar wata mace ta na fadin " Safa , baza ki yi sallama ba ? "


Wata mace ce zaune saman Royal sofas three seaters , macen ta na da jini a jika dan a kila ba za ta wuce 40 years haka , skin din ta chocolate ne dan ba za ka ce mata baka ba baza kuma ka ce mata fara ba , yanayin jikin ta ya nuna ta na shan hutu kuma ta na kashe wa skin din ta kudi , kamar irin wadanan hamshakan hajiyoyi


Ta na sanye cikin wata gown ta lace pink colour mai ratsin bakin ta yi daurin dan kwalin ta kwanin burgewa


A hankali matashiyar da ta kira da safa ta juyo ba tare da ta dago kai ba ta fara takawa ta dawo cikin parlour din ta zauna geffen matar nan


Murmushi matar ta yi kafin ta kai hannu ta janye mata jelar gashin ta , ta meda ta baya ta daure sannan ta sa hannu ta dago habar ta


Gaskia matashiyar nan kyakyawa ce , fara kal da ita kamar ka taba jini ya fito , amma sam ba ta yi kama da bahaushiya ba , jinin ta ya fi kama da yan China
Ta na da sleeping eyes yan kanana irin na yan China , farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma baki kirin da ita , ta na dogon hanci mai kyau da dan karamin baki , lips din ta pink colour ne masu bala'in laushi , ta na dogayen eyelashes bakake kirin kamar ta saka mascara , fuskar ta a dan cike ta ke hakan ya kara kyawata fuskar ta ta , a shekaru za ta kai 18 to 19 years haka




Dan lumshe idanun ta ta yi kafin ta janye kan ta , ta bude idanun ta slowly
Cikin wata zazzakar murya mai cike da nitsuwa ta ce " Momy why did you stop me ? "


Murmushi matar da ta kira da momy ta yi kafin ta ce " Safa , wai me ya ke damun ki ne ? "


Mikewa tsaye Safa ta yi fara takawa za ta bar wajen ta ce " nothing Momy " ta kai karshen ta na hayewa stair


Da kallo momy ta bi har sai da ta ga ta haye stair din sannan ta mike ta nufi dining room da ke fuskantar sofar da ta tashi


Bangaran Safa kuma bayan ta Haye stair din , nan ma wani parlour din ne har da Tv plasma makale a bango , ci gaba da tafiyar ta tayi har sai da ta wuce door biyu ta nufi ta ukun wadda ita ce a karshe


A hankali ta kai hannu ta riko handle din kofar ta murda ta shiga
Wow wata bedroom ce mai bala'in kyau , komai na cikin ta light pink ne , har zuwa bedsheet din saman katafaren bed din dakin


Ta na shigowa ta tila school bag din ta saman wata sofa da ke geffen kofar shigowa
Ba ta rufe kofar dakin ba ta shiga cire kayan jikin ta , daya bayan daya ta na tilawa geffen school bag din ta


Sai da ta rage da ga ita sai pant da bra sannan ta nufi kofar toilet da ke fuskantar katafaren gadon ta




Ta dauki wajen good 40 minutes kafin ta fito da ga cikin toilet , sanye da bathrobe , ba ta tsaya cikin dakin ba ta nufi wata door dan nesa kadan da ta toilet , tsakiyar su kuma wata closet ce wadda a ka daura Tv plasma da sauran abubuwa kamar su books da littafafan ta na karatu


Dressing room ta shiga , sai da ta dauki nan ma wajen 20 minutes kafin ta fito sanye da kananan kaya wando jeans iya cinya pink colour , da shirt fara mai dogayen hannu , ta Rowling din veil din ta a fuska shi ma fari ta yi simple make up sai tashin kamshi ta ke


Wajen sofar da ta ajiye school bag din ta ta nufa , ta dauki bag din ta bude ta ciro wayar ta kira iphone 14 pro max pink colour mai bala'in kyau


Ta na daukar wayar ta meda bag din ta ajiye sannan ta nufi bedside drawer ta bude ta dauki wata face mask baka ta saka


A hankali ta juyo kai a sunkuye ta na latsa wayar ta , ta nufi Tv plasma ta ajiye wayar ta bakin Tv din


Ta dan ja baya kadan ta tsaya , ashe camera din wayar ta kunna , Tiktok live ne ta ke shirin yi


Ta na tsayuwa a wajen live din ya fara yi sannan ta fara magana kamar haka " Assalamualaikum wa rahmatullah , barkan mu da warhaka , ku na tare da abokiyar hirar ku , kamar dai kullum yau friday za mu tatauna a kan matsalolin da su ka shafi society din mu , musaman abun da ya shafi fanin lafya , kafin nan zan fara amsa muku tambayoyin ku kamar kullum "


Ta na gama fadar haka ta karaso gaban wayar ta dan sunkuya ta na karanto sakon comments


A hankali ta ce " okay ga wani nan ya na cewa * Gaskia mu na jin dadin shirin but me ya sa ba ki son nunawa jama'a fuskar ki kullum sanye ki ke da face mask ? * "


Dan murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce " kawai dai na saba da sa face mask din ne idan zan yi video na , amma in sha Allah watarana zan cire shi "


Ba ta gama rufe bakin ta ba wani comments ya shigo
Shi ma a fili ta fara karanto shi kamar haka " please ko za mu iya sannin sunnan ki , na duba duk chanel din ki akiyar hirar ku ne ke sama "


Girgiza kai ta yi kafin ta ce " i'm sorry gaskia bazan iya fada ba , tambaya da ga babyn baban ta , ta ce shin ke cikakiyar bahaussa ce , na ji haussar ta ki kamar ta wanda ke koyo "


Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " no ni ba cikakiyar bahaussa ba ce , ruwa biyu ce ni , mahaifina a bahaushe "


Ta na gama fadar haka sabon comments ya shigo " Gaskia shirin ki ya na da dadi , amma zan so in san aikin jarida ki ke yi ko shi ya sa ba ki son ki gwada mana face din ki dan kar mu gane ki a bakin aikin ki ko ? " ta karanto a fili


Yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " no gaskia ni ba yar JARIDA ba ce , amma karatun na ke yi , asali ma ina cikin shekara ta karshe , shikenan tambayoyin sun isa haka , yau za muyi magana ne a kan ciwon da ya shafi kwakwolwa , yau kuma ina tare da doctor Sadeeq "


Ta kai karshen ta na daura hannun ta saman wayar ta yi yan dane dane sai ga call ya shigo


Daukar call din ta yi ta na yin sallama a daya bangaran ma amsa mata sallamar ta a ka yi duk da ta na cikin live din


" Doctor Sadeeq barkan ku da zuwa filin abokiyar hirar ku nagode sosai da ka karbi invitation di ta "


A daya bangaran kuma doctor Sadeeq ya ce " ni ne da godiya , ina yiwa ma su kallon mu barka da warhaka "


Ya na gama fadar haka comments kalla kalla su ka fara shigowa


Ba ta bi ta kan comments din ba ta ce " mu na godiya doctor , kamar dai kullum one minutes gare mu , tambaya ta ta yau zan so ka yi wa masu kallon mu ba ya ni a kan abun da ya safi ciwon kwakwolwa "


" okay ! Da farko dai suna na Doctor Sadeeq , likitan kwakwolwa a babban Hospital na birnin kaduna , shi ciwon kwakwolwa ya na da makasudi daban daban , amma ma fi yawan cin abun da ke hadasa shi , When you receive a blow to the head or body, your brain moves inside your skull. This movement can cause brain damage, such as a concussion. A concussion causes changes in the way you think and feel, which can lead to amnesia or a short-lived coma or even madness if the concussion is not treated well , zan so na kara jan hankalin ku a kan ciwon tapin hankali , mafi yawwan cin abun da ya ke hadasa shi , ciki har da ta'amali da miyagun kwayoyi ma su karfi , zan so na muku karin bayani a kai amma lokaci bazai isa ba , sai mun hadu da ku next week " ya na gama fadar haka ya kashe kiran


Ya na kashe kiran safa ta ce " mun gode sosai doctor , to yan uwa kun dai ji abun da doctor ya fada , mu daina anfani da muyagun kwayoyi , basu da kyau kuma illa ne a rayuwar mu , sai mun hade sati mai zuwa inda za muyi magana a kan ciwon da ya shafi mata , abokiyar hirar ku ce ke ce muku mu hadu a sati na gaba "


Ta na gama fada haka ta sa hannu ta kashe live din sannan ta dauki wayar ta , ta cire face mask din ta ta ajiye geffen Tv
Sannan ta fara warware Veil din ta tila saman sofa sannan ta fara takawa ta bar dakin




Parlour na kassa ta sauko ta na tafe ta na latsa wayar ta , har sai da ta karaso wajen doguwar sofa sannan ta haye ta konta


Ta na kontawa wata yan mata ta fito da ga cikin dining room rike da tray dauke da fruits da glass sai kwalin juice


Saman table din tsakiyar falon ta ajiye tray din sannan ta ce " sannu da fitowa , hajiya ta ce na fada miki ta fita in an jima za ta dawo "


Ba tare da ta kale ta ba ta ce " shikenan " ta fada a takaice
" ko zan kawo miki lunch din ki ne ? " yarinyar ta fada ta na kallon face din ta


A hankali Safa ta juyo ta kali yarinyar ta saki dan karamin murmushi ta ce " kar ki damu Balki , idan na bukata na ce ki kawo min "


Jinjina mata kai balki ta yi ta na dan murmushi ta juya za ta koma kitchen
Har ta yi dan nisa ta jiyo Muryar Safa ta na kiran ta


Ba musu ta dawo ta tsaya gaban ta ta na fadin " ga ni madam "


Mikewa zaune Safa ta yi , ta ajiye wayar ta gefe ta na kallon Balki ta ce " in tambaye ki wani abu ? "


"E madam ina jin ki " ta fada cikin girmamawa
" na san da ga kauye, momy ta kawo ki , lokacin da ki ke cen wane ciwo ne ki ka fi yawan ganin mata su na yi "


" gaskia madam ban sani ba saboda ba na yawwan zuwa likita , amma watarana mun ta ba yin wani zama a kan cutar yoyon fitsari "


Jinjina kan ta Safa ta yi kafin ta ce " minene yayan fitsari kuma ? " ta tambaya cikin kwarbabar haussar ta


Yar dariya Balki ta yi kafin ta ce " madam ba yayan fitsari ya ke ba yoyon fitsari , wani ciwo ne da mata ke kamuwa da shi lokacin haihuwa haka , sai ta dinga yin fitsari ba tare da ta sani ba "


Murmushi Safa ta yi kafin ta ce " okay Balki na gode sosai za ki iya tafiyar ki "


Da to Balki ta amsa mata sannan ta juya ta koma dining room ta shiga kitchen


Ta na shiga , Safa ta fara jiyo kukan wani kare
Dan karamin murmushi ta saki kafin ya juyo da kan ta ta kali kofar shigowa falon


Dai dai lokacin da wani katon kare ya shigo falon da dan gudu
Karen fari ne ya na dan digon brown kadan , ya na da gashi sosai


Da gudu karen ya nufe ta ya fada jikin ta ya na haushi kwarai
Rungume karen nan ta yi ta na fadin " Snoopy , ina ka je ne haka tun dazu na dawo amma ban gan ka ba ? " ta kai karshen ta na sakin shi


Kamar ko ya san abun da ta fada sai ya sauka da ga jikin ta ya konta kassan carpet ya na marairaice fuska kamar mutun


Da sauri ta ce " a'a Snoopy , me kuma ya faru ko dai ba ka ci abincin ka ba ? "


Haushi ya yi mai dan karfi ya na fido harshe waje


" to minene ah ko dai wani ya taba min kai " ta tambaye shi ta na kai hannu ta fara shafa kan shi


Yanzu ma haushi ya yi mata mai dan sauti
Ta na shirin magana ta jiyo Muryar momy ta na sallama


Kallon kofar shigowa ta yi ta na murmushi ta amsa sallamar ta
Murmushi ita ma momy ta yi ta ci gaba da takowa ta karaso cikin parlour din ta zauna geffen Safa


Kallon Snoopy ta yi kafin ta ce " Snoopy tashi ka je wajen Bello maza "
Dan karamin gunguni ya yi , shi wai babu inda zai je


Ganin haka ya sa momy matse fuska ta ce " wlh in ba ka tashi ba sa......"
Ba ta karasa maganar ta ba ya tashi ya yi waje da gudu dan ya san halin momy , yanzu nan za ta bashi KASHI in ya ki fita


Ya na fita Safa ta kali momy ta ce " haba momy me kuma ya yi miki "


Tsuke fuska momy ta yi cikin tsare gida ta ce " ba na son shirme kin ji ni ko


Shagwaba fuska Safa ta yi ta ce " shikenan na ji momy , amma fa gobe week-end kar ki manta to "
Kallon ta da kyau momy ta yi ta na shirin magana wayar Safa ta fara ringing
: TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY












πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«

( YAR JARIDA )








( A heart touching love story & destiny )










STORY & WRITTEN BY

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login