Showing 75001 words to 78000 words out of 133773 words
ta juyo ta kali cikin parlourn
ta na zaune saman sofa three seaters , ga kuma Sami zaune ta sofar da ke geffen ta , ya tsare Safa da ido
ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta juya ta koma cikin parlourn ta zauna saman sofar da ke fuskantar ta shi
ta na shirin magana momy ta riga ta cewa " da ga ina ki ke Safa "
dan karamin tsaki Safa ta yi ta na kauda kan ta gefe ta ce " ba ga ni na dawo ba "
" kin san fa mun damu a kan ki , har kiran ki na yi amma wayar ki ta na cikin bedroom din ki " Sami ya fada cikin sanyi murya
a hankali ta juyo ta kale shi kafin ta kali momy ta saki wani karamin murmushi ta ce " i'm sorry , mu na tare da doctor ne "
" shikenan , tashi ki je ki yi wanka sai ki sauko mu yi breakfast " momy ta fada
gyada mata kai kawai Safa ta yi kafin ta tashi ta nufi stair ta Haye
sai da ta Haye sannan momy ta kali Sami ta ce " me ka ke jira har yanzu ba ka tafi ba "
cikin ko in kula ya ce mata " saman kan ki na ke ne , kin ga ko wlh ki bar shiga harka ta ko kuma na fashe kwalbar "
cike da rudu momy ta ce mishi " wace kwalbar kuma ? "
yar karamar dariya Sami ya yi kafin ya ce " za ki sani nan gaba , gobe zan zo mu tafi wajen dan uwan ta , gobe ne birthday din shi "
a dubu dari momy ta mike tsaye cike da bacin rai ta ce mishi " in dai na isa da ita to babu inda za ta je , ni dama na san ba banza ka zo gidan nan ba , wlh ba bu inda Safa ta je , musaman wannan wajen "
mike wa tsaye Sami ya yi ya karaso gaban ta ya tsaya ya na kallon cikin idanun ta ya ce " Ni kuma zan gwada miki ba ki isa ba da ita , wannan asirin da ki ke boye mata tsawan shekaru , ya kusa zuwa karshe , Dan uwan ta ne , kuma sai ta je ganin shi "
" Sami fice min da ga gida , Kuma kar ka sake zuwa gidan nan , dan ba al'heri ba ne gare ta , tsawan shekaru sai yau ka tuno da ta na da dan uwa bayan kun raba ta da shi "
cikin konciyar hankali ya katse da cewa " kun dai raba ta da shi , kar ki manta duk abun da ya faru da su da hannun ki a ciki , ke da wancen yayan na ki da na ke kira uba , a tare ku ka yi musu yankar baya , duk ranar da ta gano abun da ki ke boye mata sai ta tsane ki fiye da makiyin ta "
" sami ya ishe ka haka , kar ka manta ni fa kanwar mahaifin ka ce , kuma cikin gida na ka ke "
" correction , cikin gidan Safa na ke , ko kin dauka ban da masaniya a kai , ki fara kirga lokacin da ya yi miki saura , nan gaba kadan za ki je in da ku ka aika Uncle Abdoul Karim , ba gidan yari ba , no afterlife "
ya na gama fadar haka ya saki wani cool murmushi ya fara takawa ya nufi kofar fita parlourn ya fice
da kallo ta raka shi har sai da ya fita , sai cika ta ke ta na batse wa allamun ya bata mata rai sosai
shi ko Sami ko ajikin shi ya shiga motar shi ya bar gidan
bangaran Safa kuma kai tsaye bedroom din ta ta wuce ,
ta na shiga ta sa hannu ta zuge Zip din Abayar ta har kassa sannan ta cire abayar ta tila saman sofa sannan ta nufi toilet
After some minutes ta fito sanye da bathrobe ta nufi Dressing mirror din ta , ta dauki lotion din ta , ta dawo bakin gadon ta , ta zauna sannan ta fara shafawa
sai da ta Kamala sannan ta tashi ta meda lotion din saman dressing mirror din
ta bude closet na kassa ta ciro Hairdryer ta fara Busar da gashin ta
kamar da ga sama ta jiyo a na yi mata gyara murya
a razane ta dago kai ta juya ta kali kofar shigowa dakin , ta ga ba kowa ta kauda kan ta ta na bin dakin da kallo ba ta ga kowa ba a ciki
juyawa ta yi ta ci gaba da busar da gashin ta
ba ta yi one minute ba ta ji an sake yi mata gyaren murya
ba ta juya ba ta ci gaba da aikin ta , a haka a sake yi mata gyaren murya har sau biyu amma ba ta tanka ba
sai da ta Kamala sannan ta meda Hairdryer wajen shi , ta nufi dressing room ta shige
jim kadan ta fito sanye da wata gown sky blue , ta sha stone da ga sama har kyali ta ke yi , ta na da wani belt fari da ga tsakiya amma ba ta kai kassa ba , da kadan ta wuce Guyiwa
ta saki wannan golden hair din na ta , ya zubo mata har saman shoulder , sai tashin fitinannan kamshi ta ke yi
dressing mirror din ta ta nufa , ta dauki wani lips balm pink colour ta shafawa lips din ta sannan ta ajiye shi
maimakon ta fice dakin sai ta nufi window ta janye curtain din ta bude ta
sai ga Amar ta bayan Window din
daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " lafiya ka biyo ni , ba ka san hanyar daki na ba da za ka tsaya a nan "
wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya dago hannun shi ya mika mata wata Rose ya na fadin " wannan ne na zo kawo miki "
kallon rose din Safa ta yi , ba ta san lokacin da wani cool murmushi ya subce mata
a hankali ta kai hannu ta karbi rose din murya kassa kassa ta ce mishi " Thanks "
ba ta gama rufe bakin ta ba kawai sai ji ta yi ya diro cikin dakin
a razane ta dago kai har sai da ta dan yi baya kadan
a hankali ya daga kafa ya matso kusa da ita ya na kallon cikin idanun ta
baya ta fara yi ta na kallon cikin idanun shi ita ma ta bude baki a hankali ta ce mishi " let's go now "
a hankali ya gyada mata kai kafin ya saki wani dan karamin murmushi ya kai hannu ya karbi rose din da ya ba ta , ya soka ta cikin gashin ta ya ce " haka ya fi kyau " ya na gama fadar haka ya raba ta geffen ta ya fice dakin
dan juyawa kadan ta yi ta na kallon shi har sai da ya fice dakin
a hankali ta fara takawa ita ma ta nufi dressing mirror ta tsaya ta na kallon kan ta
wani cool murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta taba rose din nan da ya saka mata a gashi
a hankali ta juya ta fara takawa ta fice dakin ita ma
tun da ta fara tako stair , ta hango Rahaf Zaune saman sofa ta na sanye da wani mini skert zuwa guyiwa pink colour da wata t-shirt white color ta saki gashin ta ita ma , sai kamshi ta ke yi
Safa na ganin ta , ta saki wani cool murmushi ta karaso cikin parlourn
da sauri Rahaf ta mike ta na murmushi ta ce " i'm sorry na zo ba da sanin ki ba "
Safa ba ta ce mata komai ba har sai da ta karaso cikin parlourn sannan ta zauna saman sofa ta na fadin " kar ki damu dama na gaji da zama ni daya cikin gidan "
komawa geffen ta Rahaf ta yi ta zauna ta na fadin " Ke da dama ke daya ce , ni fa cikin gidan ni kadai ce mace duk maza ne , shi ya sa na ga ba zan iya zama da su , da Doctor ya ce min gidan ku shi ne wanda ke fuskantar na mu , kawai na taso na taho "
dan karamin murmushi Safa ta yi ta na shirin magana Snoopy ya shigo parlourn da gudu ya na haushi
ya na zuwa ya Haye jikin Safa ya rungume ta ya na ci gaba da kukan shi
yar karamar dariya Safa ta yi ta na fadin " Baby ya isa haka , ni ma na yi kewar ka sosai "
a hankali Snoopy ya sauko da ga jikin ta ya koma geffen kafar ta ya zauna ya na fido harshe waje ya na girgiza bindin shi
" na ki ne ? " Rahaf ta tambaye ta
a hankali Safa ta gyada mata kai allamun eh
dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " ya na kama sosai da na Big bro ...... "
cikin nitsuwa Safa ta katse ta yi da cewa " Rex ? "
" eh , bayan Doctor da Big bro ba ya yarda da kowa , ga shi kuma da mugun Fada "
a hankali Safa ta gyada kan ta kafin ta juya ta kali Snoopy ta ce " Je ka kira min Balki "
ta na gama fadar haka ya tashi da gudu ya juya ya nufi dining room ya wuce kitchen
bai yi one minute ba da shiga ya dawo da gudu ya nufi hanyar fita parlourn
da kallo Safa da Rahaf su ka raka shi har sai da ya fita
ya na fita Balki ta fito da ga kitchen , ta karaso cikin parlourn ta na sallama
amsa mata sallamar ta su ka yi a tare sannan Safa ta daura da cewa " Yawwa Balki , kayan da na yi cake da su last time ni ke son ki fido min "
" Madam cake za ku yi ne ? " Balki ta tambaye ta
" eh ko ki na da ja ? " Safa ta fada cikin tsare gida
dan karamin murmushi Balki ta yi ta na dan sunkuyar da kai ta ce " Dama dama , mommm "
cikin nitsuwa Safa ta katse ta da cewa " Dama dama me? ki yi maganar ki kawai "
" dama momy ta ce kar na bar ki , ki shiga kitchen in dai cake za ki yi "
a hankali Safa ta mike tsaye ta fara takawa ta nufi kitchen
da sauri Balki ta sha gaban ta , ta na fadin " don Allah madam ki yi hakuri , wlh idan momy ta ji na bar ki kin shiga kitchen za ta iya sallama ta " ta kai karshen kamar za ta yi kuka
" idan ki ka hana ni shiga kitchen din nan a bakin aikin ki Balki "
wasu yawu Balki ta hadiye , ta na fa cikin tsaka mai wuya , idan ta ki a bakin aikin ta in kuma ta bari a bakin aikin ta shi ma yanzu ya za ta yi.
ta yi nisa cikin tunanin kawai sai ji ta yi Safa ta raba ta geffen ta ta wuce ta bar ta nan nan tsaye
Safa kuma har ta kai cikin dining room ta tsaya ta juyo ta kali Rahaf ta ce mata " i'm sorry zan yi wani dan aiki ne , jira ni ina zuwa "
a hankali ita ma Rahaf ta mike ta na murmushi ta ce " Shikenan mu je na taya ki " ta kai karshen ta na fara takawa ta nufi dining room din
Safa dai ba ta ce mata komai ba su ka juya su ka shiga kitchen din a tare
su na shiga su ka fara aikin a tare , ita ma sai Rahaf ba baya ba ta iya cakes , haka su ka kama su ka yi kayan su cikin konciyar hankali su na hira
sai wajen karfe 1 na yamma su ka Kamala su ka fito da ga cikin kitchen , Rahaf ta tafi gidan su Ta sake kayan ta , ta yi sallat , Safa kuma ta Haye bedroom din ta , ita ma ta yi wanka ta sauya kayan ta , ta yi sallat da ga nan sai barci
a takaice dai inin ranar Safa da Rahaf a tare su ka yi shi , ita Rahaf ba ta jin dadin zama cikin maza shi ya sa ta ke tahowa wajen Safa , saboda ita a matsayin sister-in-low ta dauki Safa
Safa kuma ba ta da matsala da zuwan da Rahaf ke yi wajen ta , dama ba ta jin dadin zama cikin gidan ita dai , yanzu ta samu Abokiyar hira
a tare su ka yi zaman su cikin gidan , har wajen karfe 10 na dare su na tare su na hirar su , sai wajen karfe 11 sannan Rahaf ta tashi ta koma gidan su
*WASHE GARI ⛅⛅
Misalin karfe 6 na safe kamar dai kullum Safa ta shirya za ta tafi Abuja dan yin daukar shirin ta
kamar dai wacen karan yanzu ma tare da Amar su ka tafi dan yau shi ne special guest din ta , tun safe ta ke sakin murmushi ita da kan ta , ta rasa na minene
shi dai Amar kallon ta kawai ya ke bai ce mata komai ba , da allamun akwai abun da ya shirya mata
AFTER SOME HOURS
Misalin karfe 10 dai'dai motar su ta shigo garin Abuja , kai tsaye Gidan Tashar Tauraruwa su ka wuce
kamar dai kullum yau ma an yi duk shirin da ya dace ita kadai a ke jira da doctor Amar
ta na shigowa Building din ta ci karo da Mutalab a reception ya na jiran ta
ya na ganin ta ya saki wani kyawatencen murmushi ya nufe ta da sauri cike da zumudi ya ke cewa " Safa , ina doctor Amar din ya ke , tun dazu na ke jiran ku "
cikin fara'a Safa ta ce mishi " Kar ka damu a tare mu ke ai "
a hankali Mutalab ya leka bayan Safa , ya ga ita kadai ce , sai wannan saurayin da ta zo da shi Last Friday , ya na tsaye bakin reception ya na latsa wayar shi
dawo da kallon shi Mutalab ya yi kan Safa ya ce " Safa yo ai ni ban ga kowa ba "
" bai ga kowa ba " Safa ta maimaita cikin zuciyar ta kafin ta juya a hankali
ta na ganin Amar tsaye ta saki wani cool murmushi ta ce mishi " Doctor karaso mana "
slowly Amar ya dago kan shi ya kale ta , ya yi dan karamin murmushi sannan ya meda wayar shi cikin aljihun shi , ya karaso geffen ta ya tsaya ya na tambayar ya a ka yi
" nothing ! Mr Mutalab , ga Doctor Amar Musadeeq " ta fada ta na nunawa Mutalab Amar
baki sake Mutalab ke kallon shi , " Last Friday ba tare ku ka zo ba ? " ya tambaye ta cike da rudu , in har shi ne doctor Amar kuma last Friday a tare su ka zo why ba a yi shirin tare da shi ba , ita ce tambayar da ta tsaya mishi a rai
Dan karamin murmushi Safa ta yi , ita ta ma rasa abun da za ta ce mishi
shi dai Amar tsaye ya ke kamar gunki , ko motsi ba ya yi
sai da Mutalab ya kare wa Amar ka kallo da kyau sannan ya ce musu za su iya tafiya a na jiran su , da ga haka ya juya ya bar wajen
ya na barin wajen Safa ta riko hannun Amar ta ce " mu ta fi ko ? " ta fada ta na dan karamin murmushi
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya bi bayan ta su ka bar wajen
kai tsaye lift su ka nufa , su ka shiga , kai tsaye sai Etage din da a ke daukar shirin
su na zuwa duk an yi wasu shirye shiryen da su ka dace , safa da doctor kawai su ke jira
duk mutanan wajen babu wanda bai yi mamakin ganin Amar ba , musaman Nabil da Yasmina
Nabil da kan shi ya zauna tare da Amar last Friday , har hira sai da su ka yi , sai ga shi ya dawo yau a matsayin doctor Amar
mutumin da babu wanda bai san shi ba a duniya saboda kwarewar shi wajen aiki , Da uwar dukiyar da ya tara , sai ga shi yau cikin Nigeria , kuma tashar su ita ce ta farko da za ta fara haska shi cikin Tv
Safa dai da Amar ko ajikin su , a haka a ka shirya wajen su ka hau plateau din , su ka zauna saman chair din su
su na zama mai kula da camera ya daga Murya ya na fadin " 1 , 2 , 3 Action "
ya na gama fadar haka a fara daukar shirin , Safa ta saki wani cool murmushi ta na fadin " Assalam alaikum ma su kallon mu , barkan mu da wannan lokacin , kamar dai ko wace Friday , ku tare da Safa a cikin shirin mu na Abokiyar hira da tashar Tauraruwa ke haskawa , a yau ina tare da special guest , Doctor Amar Musadeeq , na san dayawa cikin ku sun San shi , amma ba