Showing 3001 words to 6000 words out of 133773 words
:
ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL πππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE 2 π₯ β€
Kallon ta da kyau momy ta yi , ta na shirin magana wayar Safa ta fara ringing
Hannu Safa ta kai ta dauki wayar ta na kallon screen din
Nan ta ga bakuwa number ce ke kiran ta
A hankali ta dago kai ta kali momy kamar ita ce ta kire ta sannan ta dawo da kallon ta kan wayar kafin ta daga kiran ta kai wayar a kunne ta na sallama
A daya bangaran kuma sai da a ka amsa mata sallamar ta sannan a ka daura da cewa " ina magana ne da Abokiyar hira ? "
Kallon momy ta yi ta na zaro idanu ta na tambayar kanta ya a ka yi ya samu number din ta
Cen kuma sai ta bude baki a hankali kamar ba ta son maganar ta ce mishi " e ita ce "
" yawwa barkan ki da wannan lokacin , ki na magana ne da shugaban gidan Tashar Tauraruwa da ke nan Abuja , na kira ne saboda ina yawwan kallon shirin ki saman kafofin yada zumunta , so zan so na baki damar ki yi aiki a tare da mu , zan turo miki duk karin bayani da ki ke bukata a Text da kuma adress din seat din mu , idan kin amince sai ki tardo ni gobe a office di na misalin karfe 10 na safe , nagode " ya na gama fadar hakan ya katse kiran ba tare da ya jira amsar ta ba
Baki saki ta ke kallon momy ta na zaro idanu ta rasa magana
" lafya wanene ya kira ki ? " momy ta tambaya ta na tsare ta da idanu
Wata yar siririyar kara ta saki ta na fadawa jikin momy ta rungume ta ta na fadin " momy , shugaban gidan Tashar Tauraruwa ne ya kira ni , ya ce in na shirya in aiki tare da su "
Cike da murna momy ta rungume ta ta na jerowa Allah godiya , dan ta san shi ne babban burin yarinyar ta ta
Sai da su ka ida rungumeΒ²n su sannan su ka raba jiki cike da zumudi mama ta ce " yanzu yaushe za ki je , a ina gidan tashar ya ke ? "
" gobe momy ya ce zai turo min adress din su , sai na tarda shi babban offishin su wajen karfe 10 na safe ya min sauran bayani "
" alhamdoulilah , abu ya yi kyau gaskia , amma fa ni ban san a wace jaha babban offishin su ya ke ba "
Ta na shirin mike wa ta ce " a Abuja ya ke momy "
Cak ta tsaya sakamakon hannun ta da momy ta yi
Da sauri ta juyo ta na fadin " minene momy ? "
Mikewa tsaye momy ta yi , duk yanayin fuskar ta ya sauya kamar wadda a ka turowa sakon mutuwa
" Safa, Abuja fa ki ka ce ? "
" e momy Abuja " ta fada cikin ko in kula
Sakin hannun ta momy ta yi kafin ta ce " Safa kin shirya komawa Abuja bayan duk abun da ya faru .. ."
Da sauri Safa ta katse ta da cewa " don Allah momy kar ki ce a'a , ai ba wajen ba zan sauka so kar ki damu , na san dalilin da ki ke jin tsoron , amma wannan abun ya riga da ya wuce , su je su suka sani , wlh har ga Allah ni ban rike wannan abun ya rai ba , please momy don't stop me , kin fi kowa sanin shi ne babban buri na a rayuwa , kar ki hana min shi " ta kai karshen ta na marairaice fuska
Komawa saman sofa momy ta yi ta zauna ta dan sunkuyar da kai kafin ta ce " ni da kai na bazan so na hana ki ba my jewel , yanzu in su ka dauke ki aikin shikenan kin koma Abuja da zama , ni babban abun da ke damu na , in kin je a ina za sauka , ko cikin gidan mu na cen ke kadai za ki zauna , ina tsoron wani abu ya zo ya cutar da ke , ga shi bazan iya barin aiki na ba na biki " ta kai karshen kamar ta yi kuka
Da sauri Safa ta tsuguna gaban ta , ta riko hannuwan momy ta ce " my momy, ki kontar da hankalin ki ba abun da zai samu na , ni fa ba yarinya ba ce , kuma na san shirin da zan haska sau daya a sati ne za a yi shi , so kin ga ranar ne kawai zan tafi Abuja , sauran rananakun ina nan tare da ke , kuma ga Balki nan, ga Snoopy duk tare za mu tafi a ranar kar ki damu don Allah ba abun da zai same ni momy da yardar Allah "
Dago kai momy ta yi ta kali Safa ta na sakin murmushi ta ce " ke duk yadda za ki yi ki samu abun da ki ke so kin sani " ta kai karshen ta na dan bugun ta a kumatu
Yar karamar dariya Safa ta yi ta na daga ma momy gera
Da sauri ta mike ta nufi stair ta na fadin " momy na tafi ni in shirya kaya na , na san yau da wuya in yi barci " ta kai karshen ta na Hayewa stair
Da kallo momy ta bi ta ta na murmushi har sai da ta Haye stair din sannan ta ce " ki dai yi a hankali , ya Allah na roke ka ka tsare ta da ga sharin wannan mutun , ya Allah kar ka sa ta tafi gidan nan " ta fada cikin raunin murya kafin ta mike ta nufi stair ita ma
Washe gari
Misalin karfe 6 na safe
Tsaye su ke cikin parlour din su , momy na rungume da Safa kamar wadda za ta yi tafiya ta har abada
Sanye ta ke cikin wando palazzo navy blue , da T-shirt Fara dai'dai cibiya , ta daura wata jacket navy blue ita ma , ta yi Rowling veil din ta white colour a kai , ta na rataye da wata yar karamar bag white colour , ta yi kyau over , duk da ba ta yi wani ado ba , lips din ta kawai ta shafawa gloss
Sai da ta gaji sannan Safa ta yi kokarin raba jikin su ta na fadin " momyyy ya isa haka kar na je na yi late , na dawo fa "
Murmushi momy ta yi kafin ta kai hannayan ta duka biyu ta talabo face din Safa ta kai bakin ta , ta manna mata kiss saman forehead din ta
Murmushi mai dan sauti Safa ta yi kafin ta ce " shikenan momy zan iya tafiya yanzu "
Jinjina mata kai momy ta yi kafin ta ce " e za ki iya tafiya , ki kula min da kan ki kin ji , Allah ya kiyaye hanya , sai kin dawo "
Da amine ta amsa mata kafin ta juya ta fara takawa za ta bar falon ta na fadin " sai na dawo momy "
Da kallo momy ta rakata ta na murmushi har sai da ta ga ta fita parlour din sannan ta juya ta Haye stair
Safa kuma , ta na fitowa ta nufi parking space , har za ta shiga motar ta ta jiyo kukan Snoopy
Wani cool murmushi ta saki kafin ta juyo ta kaleshi ta ce " ka na zuwa mu tafi ? "
Gyada mata kai ya yi ya na haushi
Da sauri ta ce mishi " shiiiiiiiiii kar momy ta ji " ta kai karshen ta na nufar geffen mai zaman banza ta bude mishi kofar
Da gudu ya nufe ta ya shiga motar ya na haushi ,
Ya na shiga ta rufe kofar ta zagayo geffen driver ta shiga ta tada motar su ka bar parking space , a hankali ta nufi babbar gate
Ta na isa ta danna horn , da gudu gateman ya fito da ga dakin shi ya bude mata babbar gate
Babu ko sallama ta danna hancin motar saman titi da uban gudu ta bar gidan
A haka su ka kama hanyar Abuja , ita da Snoopy , su na tafe su na hira
Duk duniya ba wanda Snoopy ke yarda da shi kamar Safa , sai momy shi ma dan ya na jin tsoron ta
Snoopy shi ne babban abokin Safa tun ta da yar shekara hudu momy ta sayo mata shi lokacin ya dan jinjirin shi dan ya dunga debe mata kewa , a tare su ka taso kamar abokai duk abun da ta fada mishi ya na ji , ita ma kuma ta na gane abun da ya ke fada , dan wani lokaci har zaune ta ta saka shi a gaba su yi ta hirar su kamar da mutun ta ke maganar
After some hours
Misalin karfe 10 dai dai Safa ta shigo garin Abuja , ba ta tsaya ko ina ba sai babban offishin Tashar Tauraruwa , dan tun lokacin da su ka ida magana da shugaban , ya turo mata adress din
Ga Dukan allamu ta san garin Abuja dan ba ta tsaya tambayar kowa hanya ba
Misalin karfe 10 da rabi na safe ta shigo cikin babban offishin su
Kai tsaye parking space ta nufa ta yi parking , sannan ta kashe motar , ta bude bag din ta , ta fido face mask baki ta saka sannan ta fito , ta zagayo ta budewa Snoopy kofa ya diro kassa sannan ta rufe kofar ta nufi hall din shiga office din , Snoopy na biye da bayan kamar bodyguard
Duk inda ta wuce sai an bi ta da kallo ita da Snoopy , tafiyar ta su gwanin burgewa wani har wayar shi ya ciro ya yi musu pic
Safa kuma ba ta tsaya ko ina ba sai Reception , ta na zuwa ta sanar da receptionist cewa ta da meeting da shugaban su
Kare mata kallo da kyau matar ta yi da ga kassa har sama kafin ta ce " kamar na taba ganin ki ? "
Da sauri Safa ta girgiza mata kai ta ce " no wannan shi ne karo na, na farko da shigowa Abuja , please ko zan iya tafiya karfe 10 mu ka yi da shi "
" e ya sanar da ni , za ki iya tafiya , office din shi shi ne mai door ta glass da ga karshe , mu je na raka ki "
" nagode amma yi zaman ki " Safa ta fada a takaice kafin ta kali Snoopy ta ce " Snoopy mu tafi " ta na gama fadar haka ta yi gaba ta bar wajen Snoopy na biye da bayan ta
Receptionist ta na sha ruwan mamaki ganin ta tare da kare ita ta dauka da yaro ne ta ke tafe
Safa kuma tafiyar ta take yi kamar ba ta san da mutane a wajen ba
Sai kai kawo su ke yi ko , kowa sai bin ta ya ke yi da kallo ita ko ajikin ta
( Kun san yadda yanayin gidan Chanel ya ke ba sai na fada muku ba so kowa ya yi tunanin yadda office din zai kasancewa thanks )
Sai da ta yi yar tafiya kafin ta karaso office din shugaban su ,
Kamar dama jiran ta ya ke , ta na yin knocking na farko ya bata izinin shigowa
A hankali ta tura kofar ta shiga ta na yi mishi sallama , Snoopy na biye da bayan ta
Ya na ganin ta ya saki wani cool murmushi ya na amsa sallamar ta kafin ya daura da cewa " sannu da zuwa ga waje nan zaune "
Ba musu ta tako izuwa chair din da ke gaban desk din shi ta zauna
Da gudu Snoopy shi ma ya karaso ya Haye gudar chair din
Hararrar shi Safa ta yi ta na shirin magana Shugaban ya riga ta cewa " na san ba sai na yi miki dogon baya ni ba, duk wasu bayanai , na tura miki su ta text , yanzu tambaya ta a nan shi ne , kin shirya aiki da mu ? "
" yes, dalilin da ya sa ma na zo " ta fada cikin turanci
Hamdala ya yi kafin ya daura da cewa " gaskia na ji dadin haka , i'm sorry na manta ban yi presenting kai na ba , my name is Moutalab ni ne mai kula da wannan gidan tashar, a kan shirin da za ki haska kuma na ba ki dama ki zabi duk sunnan da ki ke so da kuma yadda za a gudanar da shi , idan kin gama tunani a kai sai ki yi min magana ta yadda zan rubu contract din mu kin ga shikenan da kin yi sign sai ki fara aiki "
" da so samu ne , na ci gaba da shirin da na ke yi Friday na abokiyar hira , saboda dayawa sun sanni a matsayin hakan kun ga idan na ci gaba da gudanar da shi a nan , Tashar za ta samu ma su kallo dayawa musaman Followers di na "
Jinjina kan shi ya yi kafin ya ce " gaskia shawarar ki ta yi kyau , yanzu next week za mu fara gudanar da shirin kenan "
" idan Allah ya kai mu da rai da lafya , sai mu fara " ta kai karshen ta na mikewa
Da sauri ya taro ta da cewa " but ba ki fada min sunan ki ba , ban ga kuma face din ki ba , sannan zan so mu je na gabatar da ke ga sauran mutanan gidan "
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanu ta a hankali ta bude
Sannan ta sa hannu ta zame face mask din ta, ta na kallon shi ta ce " my name is Safa "
" Masha Allah " ya furta cikin zuciyar shi ya na kare mata kallo kamar zai cinye ta
Sai da ya dauki lokaci kafin ya mike tsaye ya fara takawa ya yi gaba zai fice office din ya ce " okay Safa , mu je ko ? "
Ba musu ta bi bayan shi, car za ta fita ta juyo ta kali Snoopy ta ce " Snoopy let's go "
Dan haushi ya yi kafin ya diro da ga saman chair din ya bi bayan ta
Sai da su ka dan yi tafiya kafin su iso wani babban parlour dan cike da mutane , dan yanzu lokacin break ne kowa ya na nan
Moutalab na shigowa wajen da sallama duka su ka yi shiru su na amsa mishi sallamar shi
Safa na biye da bayan shi ita da Snoopy kowa sai kallon ta ya ke dan ba karamin kyau ta yi musu
Su na shigowa wajen Moutalab ya ce " na ji dadin ganin ku a nan duka , na zo na gabatar muku da new member din mu , na san dayawa cikin ku sun san ta a matsayin Abokiyar hira ku na kallon Chanel din ta saman tiktok da sauran su , yau dai ta zamo yar gidan za ta fara aiki tare da mu ranar Friday , miss Safa bismillah " ya kai karshen ya na nunawa Safa geffen shi
Murmushi ta yi kafin ta tako ta tsaya geffen shi , sannan ta ce " Hi everyone ! Fatan na same ki cikin koshin lafya ? "
Da sauri wata da ga cikin ta karaso ta mika mata hannu su ka gaissa ta na fadin " Hi ! Sannun ki da zuwa gaskia na ji dadin ganin ki , sisters di na kullum sai sun yi min maganar ki , ashe ba banza ki ke boye fuskar ki ba , you're so beautiful "
Dan sunkuyar da kai Safa ta yi ta na murmushi kafin ta ce " nagode " kassa kassa
Kallon daya da ga cikin su Moutalab ya yi kafin ya ce " Nabil , zo ka gwada mata office din ta, da wajen daukar shiri , miss Safa sai mun hadu Friday " ya kai karshen ya na kallon Safa kafin ya juya ya bar wajen
Wanda ya kira da Nabil ne ya karaso gaban ta ya tsaya ya na murmushi ya ce " sannun ki ni dai sunana Nabil , your futur best friend , mu tafi ko "
Gyada mishi kai ta yi kafin ta juya ta na shirin bin shi sai ta tsaya ta kali gefe da gefen ta ga Snoopy ba ya nan
A razane ta fara bin wajen da kallo ta na kiran sunan shi
Kallon juna su ka shiga yi kowa na tambayar kan shi wanene Snoopy kuma
" wanene Snoopy ? " Nabil ya tambayeta
" My dog , tare mu ka shigo nan , ina kuma ya yi " ta fada kamar za ta yi kuka
" I'm sorry amma ke