Showing 15001 words to 18000 words out of 133773 words

Chapter 6 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9697

taba ganin wata mai irin wannan face din , amma ke ba cikakiyar yar china ba ce ko "


Yar dariya Safa ta yi kafin ta ce " doctor kowa tambayar da ya ke min , ke ba cikakiyar bahaussa ba ce ko ? Yau ku kuma kun tambaye ni , in ni ba cikakiyar yar china ba ce "


" kin fi kama da mutanan china , fiye da haoussa wan shi ya sa , amma ke da ga gani an san ba yar Africa ba ce "


" to , mahaifiya ta dai yar china ce , mahaifi na ne bahaushe " Safa ta fada ta na komawa wajen ta ta zauna


Gyada kan ta Doctor ta yi kafin ta ce " Okay , bani number din ki , duk shawarar da na yanke zan fada miki " ta kai karshen ta na mikawa Safa wayar ta


Karbar wayar Safa ta yi ta saka mata number din ta , ta mika mata wayar sannan ta kali su Haoua ta ce su tashi su tafi su na yi wa doctor din sai an jima su ka ficewar su


Bayan sun baro Hospital din cikin motar Safa
Kai tsaye wani kyakyawan Restaurant su ka tafi
Cikin restaurant din su ka shiga a tare , su ka nufi VIP space saboda Safa ta ce ba ta son hayaniya idan ta cin abincin


Su na zama wani server ya nufo su dan ya dauki order din su
Nan kowace ta fadi abun da ta ke so da bai wuce ice cream ba
Ya na daukar order din su ya juya ya bar wajen , sannan su ka fara hirar su


Su na tsaka da hirar su Safa ta dago kai ta kali kofar shigowa Restaurant din
Nan take yanayin face din ta ya sauya , ta na zaro idanu


Kallon ta da kyau Haoua da Djamila su ka yi , kafin su juya su kali inda ta ke kallo dan sun bawa kofar baya amma ba su ga komai ba


A tare su ka juyo su na kallon Safa har su na hada baki wajen tambayar ta lafya
Da sauri ta ce musu " no ba komai , wani abu ne na tuno kawai "


Okay su ka amsa mata a tare kafin su ci gaba da hirar su dai'dai lokacin da server din ya kawo musu order din su


Sai da su ka Kamala shan ice cream din su , su na hirar su amma hankali Safa ya na nesa
Sai da su ka Kamala sannan Safa ta kira server ta ba shi card din ta ta ce su fida kudin su


Jim kadan server din ya dawo ya na fadin " madam card din ta ki shiga "
Cike da rudu Safa ta ce " What ? Kamar ya , ku sake gwada mana "
" sau uku muna saka ta amma ta ki kamawa " server din ya fada


Ta na shirin magana wani dattijo ya karaso wajen, ya na sanye da manyan kaya na shada green colour da gani ba na arziki ba ne


Sallama ya yi musu kafin ya ce " yan mata lafya me ya faru "


Kallon sama da kassa Safa ta yi mishi kafin ta ja dan siririn tsaki ta kauda kai gefe , ta kai hannu cikin bag din ta ta ciro wayar ta


Contact ta shiga ta dibo number din momy ta dana mata kira
Ringing biyu ta yi momy ta dauka ta na mata sallama


Amsa sallamar Safa ta yi kafin ta dora da cewa " momy what happiness why my card ? Mun sayi ice cream server ya ce ta ki kamawa "


A daya bangaran momy ta ce " sorry my daughter , wlh mantawa na yi ban fada miki ba , bank din sun yi sabin card so wannan ba ta aiki yanzu , mantawa na yi ne ban baki sabuwar ba , ta na cikin drawer di na , amma turo min account number din su sai na tura musu kudin su " ta na gama fadar haka ta katse kiran


Dan tsaki Safa ta ja kafin ta mikawa server din wayar ta , ta ce " ka saka account number din ku , da kuma kudin ku za a turo muku "


Ba musu ya karba ya koma wajen biya dan bai San account number din ba


Ya na barin wajen Dattijon da ke tsaye kan su ya ce " yan mata ina muku magana kun kyale ni "


Hararrar shi Safa ta yi kafin ta ce " please sir , get out of my sight "
Kallon ta Haoua da Djamila su ka yi har su na hada baki wajen cewa " pretyy yi a hankali mana "
Wani mugun kallo Safa ta wurga musu har sai da su ka shanye sauran maganar ta su


Murmushi mai dan sauti dattijon nan ya yi kafin ya ce " haba yan mata, taimakon ku ne kawai na zo in yi "


Sunkuyar da kan ta safa ta yi kafin ta dago ta kaleshi ta na sakin wani dan iskan murmushi ta ce " uncle mun gode , amma ba ma bukata " ta na gama fadar haka ta mike ta nufi reception


Da sauri Haoua da Djamila su ka mike su ka bi bayan ta , su ka bar shi nan a tsaye
Wayar ta ta karba sannan su ka fice restaurant din baki daya cikin motar su


Su na saman hanya Djamila ta kali Safa ta ce " pretty, na minene za ki wa dattijon nan haka taimakon mu ne kawai ya zo yi "
[17/08 Γ  23:34] MEERAHπŸͺ·πŸ©·:




πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«
( YAR JARIDA )





















( A heart touching love story & destiny )






















STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘β€














Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀

( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯


















TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i














TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY






BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
























PAGE 6 πŸ₯€ ❀
























Ta na ci gaba da tukin ta , Ba tare da ta kale ta ba Safa ta ce " wane taimako kuma "


Haoua ce ta karbe zancen da cewa " Haba Safa ki rage wannan rashin yarda da mutanan na ki , yanzu inda momy ba ta karbi account number din su ba ta turo musu kudin , kin san fa ba za su bar mu mu tafi ba , ko ba komai idan mun ma dattijon nan magana a hankali zai taimaka mana , dan da ga gani ya na da kirki , kin san fa mu ko kashe mu za a yi ba mu kudin biyan ice cream din nan , dan ni ko kudin kati ba ni da "


Yar karamar dariya Safa da Djamila su ka yi kafin Djamila ta riga Safa cewa " ke kudin katin ma ki ke nema , ni yau din nan Always di na su ka kare , ga shi ko dubu daya ba ni da a jiki na , Allah ta ki mai sauki ce , ke pretty da dai kin hakura ya taimaka mana ga shi yanzu kin janyo mana asara "


Dariya sosai Safa ta yi har da bugun steering motar ta
Hararrar ta Haoua da Djamila su ka yi kafin Djamila ta ce " kin ga ko wlh abun da ke gama ni da ke kenan komi sai ki meda shi abun dariya "


Tsagaita dariyar ta Safa ta yi kafin ta ce " okay na ji Haoua ta ce ba ta da kudi , ba matsala na san ba ta da mashinshi ni amma ke fa ina wanda ki ke kira da baby , ba ya baki komai kenan " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya dai'dai lokacin da ta yi parking motar ta bakin kofar gidan su Djamila


Tsaki Djamila ta ja kafin ta bude kofar ta sauko da ga cikin motar
Har ta nufi cikin gidan Safa ta ce ta tsaya , ba musu ta dawo geffen Safa ta tsaya
Ta na tsayuwa Safa ta bude wani locker a cikin motar ta fido bandir din kudi dan dari biya biyar ya kai dubu dari biyu ta bawa Djamila
Cike da murna Djamila ta karba ta na yi mata godiya kafin ta juya ta shiga cikin gidan su ita kuma Safa su ka yi gaba


Su na tsaka da tafiyar su Haoua ta kali Safa ta ce " yanzu pretty dama ki na da kudi cikin motar ki , shi ne da card din ki ta ki kamawa ba ki zo kin dauke su kin biya ba ? "


Sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " ba ni son taba su , sai in ya zama urgent ne na ke daukar su , wannan dan karamin abu ne shi ya sa na kira momy "


Jinjina kan ta Haoua ta yi kafin ta juya ta kali titi , da ga haka ba wanda ya sake cewa wani abu har su ka karaso gidan su Haoua


Ta na shirin sauka Safa ta tsaida ta , sannan ita ma ta ciro kudi ta ba ta dubu dari biyu
Murmushi Haoua ta yi kafin ta karba ta na yi mata godiya


Jinjina kan ta Safa ta yi kafin ta juya da kyau ta na kallon Haoua ta ce " Haoua ba zan miki karya ba , ke da Djami ku kadai ne friends ni a rayu kuma Allah ya sani da zuciya daya na ke zaune da ku "


Da sauri Haoua ta katse ta da cewa " na sani pretty , mu ma haka zalika da zuciya daya mu ke zaune da ke , kar ki yi tunanin mu na biye miki ne kawai saboda abun hannun ki , wlh Allah ne shaida "


Dan lumshe idanun ta Safa ta yi kafin ta bude su slowly ta ce " Haoua na sani , amma zan so wani lokaci idan na fada muku wani abu ku yarda da ni , kin san ke na fi sabawa da ita saboda duk cikin mu kin fi mu nitsuwa , amma Haoua zan so ki san , na je gariruwa daban daban , na yi yawwan bude ido har wajen Africa na ga abubuwa dayawa da ku ba ku ga ni ba , dalilin da ya sa a ba ni saurin yarda da mutun , amma sai ki ga kamar girman kai ne , wlh ba hakan nan ba ne , Haoua dattijon nan da ku ke cewa ya taimaka mana wlh ba dattijon arziki ba ne , ke ba ki jin a na maganar sugar Daddy to irin su wannan , da mun ba shi dama wlh zai kai mu ya baro shi ya sa ya yi mishi hakan , na san ba laifin ku ba shekarun shi ku ka kalla "


Riko hannun ta Haoua ta yi kafin ta ce " gaskia , mu ma mun yi ganganci ba mu San mutun ba kawai sai mu yarda da shi "


" please Haoua duk lokacin da ku ke da bukatar kudi , kar ku je nema wajen wanda ba familyn ku ba , ko da cikin familyn ku ne ku dinga duba ma su halin kirki , ke kar ma ku tambaya , ki kire ni kai tsaye ko da million ne wlh ni zan iya ba ku "


Murmushi Haoua ta yi kafin ta ce " mun gode da irin wannan kulawar da ki ke ba mu Safa , wlh ban taba tunanin haka irin ku su ke ba , na yi tunanin ke ma wariyar launin fata za ki gwada mana " ta kai karshen cikin zolaya


Yar karamar dariya su ka yi a tare kafin Safa ta ce " mahaifi fi na fa bahaushe ne , ta ya zan nuna wariyar launin fata "


" e fa haka ne ni na ma manta " ta kai karshen ta na yar dariya
" okay ya isa akwai abun da zan fada miki , na san ke za ki saurare ni shi ya sa na fara kai Djami gida dan mu samu mu yi maganar "


Juyowa Haoua ta yi ta na kallon Safa kafin ta ce " maganar minene za ki yi min "


Dogon nunfashi Safa ta ja ta na saukewa a hankali kafin ta ce " na san maganar da na yi miki dazu a library a kan Mansour za ki yi tunanin ina kishin su ne shi da Djami "


Da sauri Haoua ta katse ta da cewa " no no wlh ba haka ba ne k......"


Ita ma katse ta Safa ta yi da cewa " please saurare ni , ni ba kishin su na ke ba asali ba ban taba jin irin wannan emotion ba cikin zuciya ta , wlh Djami ta fi karfin Mansour , ba dan komai ba saboda shi ba mutumin arziki ba ne , Haoua , lokacin da muke restaurant na gan shi ya shigo restaurant din tare da wata yan mata ya na rike da ita a kugu , mu na yin ido hudu da shi ya juya su ka bar restaurant din kafin ku juya sun bar wajen , shi ne da ku ka tambaye ni na ce ba komai "


Zaro idanu Haoua ta yi ta na kai hannu ta toshe bakin ta
A hankali ta sauko shi ta na kallon Safa ta ce " yanzu da gaske ki ke , kam in haka ne ko Mansour ya cika dan iska , kar ki so ki ji in ya na ce ma Djamila ita kadai ce ya ke so , wai ita kadai ce macen da ya fara so dan ko a gida kowa ya san ba ya wa mata magana "


Murmushin takaici Safa ta yi kafin ta ce " Haoua wannan karan shi ne na uku ina ganin shi tare da yan mata daban daban amma shi sai yanzu ya gan ni , kuma kowa ne lokaci yan matar da ga ganin ta ba ta arziki ba ce dan kayan jikin su ma ya isa ka gane yan iska ne , ba banza na ke ce miki bai konta min a rai ba "


Jinjina kan ta Haoua ta yi kafin ta ce " gaskia dole mu raba wannan yaron da Djamila , idan ba haka ba zai lalata mata rayuwa, wlh ta sha fada min , wai ya ce mata su tafi gidan su ta ga yan uwan shi amma kullum sai ta ki "


" Haoua, Djamila fa ta na mutuwar son Mansour so ko kin fada mata ba yarda za ta yi ba amma , zan fada miki abun da za mu yi magriba ta gabato zan koma gida "


" okay sai mun yi waya " ta kai karshen su na rungumar juna kafin ta sauko da ga motar ta shiga gidan su , Safa kuma ta tada motar ta ta bar wajen da gudu


Cikin kankanin lokaci ta isa gida , ba ta tsaya batta lokaci ba ta wuce kai tsaye bedroom din , ta yi wanka , ta yi Alwalla , sannan ta fito ta shirya cikin Abaya baka ta yi Rowling veil din ta sannan ta nufi sallayar ta ta yi sallat
Bayan ta Kamala sallar ta , ta zauna ta na karatun Alkur'ani , har sai da a ka yi kiran sallar isha sannan ta tashi ta yi sallar


Bayan ta Kamala sallat ta tashi da ga saman sallayar , ta koma cikin dressing room
Jim kadan ta fito sanye da kananan kaya pink colour , wando ya tsaya a iya cinya da riga ta dan wuce cibiya mai shilalen hannu


Parlourn din kassa ta sauko kai tsaye , ta na tafe ta na latsa wayar ta , har sai da ta iso wajen doguwar sofa ta zauna


Ta na zama ta ajiye wayar shi geffen ta sannan ta shiga kwallawa Balki kira


Da sauri Balki ta fito da ga cikin kitchen din ta karaso gaban ta ta tsaya ta na fadin " ga ni madam , ki na bukatar wani abu "


Kallon ta Safa ta yi ta na fadin " Dauko min notebook da paper , zan rubuta miki wasu ingredients , gobe ina son ki je market ki sayo min su "


Da to Balki ta amsa mata kafin ta juya ta nufi closet din kassan Tv ta bude wani locker ta fido notebook da pen , ta karaso ta bawa Safa


Karba ta yi ta fara yin rubutu sannan ta mikawa Balki ta ce " kar ki batar da paper din nan kin ji ko "


Da to Balki ta amsa mata kafin ta dauki notebook din ta meda wajen shi sannan ita ta koma kitchen


Ta na shirin daukar wayar ta , ta jiyo sallamar momy
Juyowa ta yi ta kali momy ta na amsa mata sallamar ta kafin ta kauda kan ta ta dauki wayar ta ta gyara ta konta saman sofar


Sofar da ke geffen ta momy ta zauna ta na fadin " kin dauki card din ki , kar na manta yanzu ma "


Shiru Safa ta yi ta na ci gaba da latsa wayar
Murmushi momy ta yi kafin ta kai hannu ta shafi kan ta ta na fadin " na ji yi hakuri wlh mantawa na yi "


" uhmm " ta fada a takaice ba tare da ta kale

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login