Showing 90001 words to 93000 words out of 133773 words
aiki na ne , a haka mu ka ci gaba da yin shopping din a tare mu na tafe ta na yi min hira a kan ta , bayan mun Kamala mu ka je reception na ce ta bari zan biya amma fir ta ki ta ce ita za ta biya saboda irin al'herin da na yi mata ba za ta iya bari na biya ba , haka mu ka shiga jayaya da ita har dai na hakura na bari ta biya , da ga haka mu ka baro Mall din amma kafin nan sai da ta karbi number ta , ta ce min za ta dinga kira na mu gaisa , da ga haka mu ka yi sallama , sannu sannu mu ka fara sanin juna ta na sake min , mu na wassa da dariya , mu na haduwa bayan na sauka da ga aiki , mu tafi shan coffee ko shan ice cream , wani lokaci ma mu tafi kallon film har soyayya ta shiga tsakanin mu , soyayya mai karfi yadda ko kwana ba ma iya yi ba mu ga juna ba , a haka har na Kamala aiki na a China , na komo Nigeria ko bankwana ban yi mata ba , amma tun bayan dawowa ta ba abun da na ke tunani sai ita na kassa barci , na kassa cin abincin har jinya na yi a Asibiti , family na ba rokon da ba su yi min ba na fada musu abun da ke damu na amma fir na ki yarda , a haka har na share wajen two months , a cikin na ukun na yanke shawarar komawa China dan na gan ta , sai dai ko da na koma china na neme ta na rasa , ashe bayan komawa ta Nigeria ita da familyn ta sun koma UK da zama , babu yadda na iya na kama hanya na dawo Nigeria inda na sake kontawa sabon ciwon , na rashin ta a kusa da ni , dan duk duniya ita kadai ce macen da na taba fadawa kalmar so yanzu kuma ga shi mun rabu , sannu sannu har sai da na share one year a haka , a cikin shekarar ba yin da ahali na ba su yi da ni ba a kan na yi aure ko zan samu saukin abun da na ke ji duk da ba su san abun da ke damu na ba , amma na ce ba na so saboda mace guda na ajiye wa gurbin mata a waje na kuma bayan ita babu wadda zan bawa , kawai watarana na je Hospital sai secretary di ta ta ce min na yi bakuwa , amma ta ce ta tafi an jima ta dawo , kawai na ce mata okay , after some hours ta dawo ta ce min guest di ta ta dawo kuma ta na son gani na yanzu , da ya ke a lokacin saura 30 minutes na sauka sai na ce mata kawai ta shigo , ba musu ta je ta ce ma bakuwar na ce za ta iya shiga , Jim kadan na ga an turo kofar office di na a shigo , lokacin da ta shigo kai na ya na sunkuye na ce mata ta zauna , ba musu ta karaso ta zauna ta na kallo na da murmushi a fuskar ta , sai na tambaye ta abun da ya kawo ta waje na sannan na dago kai , ina ganin ta na ji zuciya ta ta buga da karfi tamkar a mafarki haka na ke ganin ta wani kyawatencen murmushi ta sakin min ta daga min hannu ta ce HI , mamaki ne ya hana ni magana kawai na tsaya ina kallon ta babu ko kiftawa , ganin yadda na tsare ta da idanu ya sa ta cewa DEAR BA KA GANE NI BA ? ban san lokacin da wasu hawaye su ka zubo min ba , da gudu na tashi na je na rungume ta cikin fitar hayaci kamar wani ya ce zai kwace min ita , kin san abun da ya faru , ashe lokacin da na dawo da ga China bayan na je neman ta a lokacin ita ma ta je nema na kawai dai mun yi crossing ne ,
inin ranar a tare mu ka share shi , amma na fada mata ba zan iya ci gaba da soyayya da ita saboda ita ba musulma ba ce , ni duk na manta da wannan tun farkon soyayyar mu sai a lokacin , ta yi kuka kamar za ta hadiye ran ta , amma haka na danne mu ka rabu da juna , a tunani na ta koma UK a ranar ashe ba ta koma ba , washe gari early ina shigowa office ita ce guest na farko da ta zo waje na , na roke ta ta tafi saboda ba za mu iya kasance wa a tare ba tun farko laifi na ne da na manta ita ba musulma ba ce , haka ta dinga yi min magayi ta na kuka a kan kar na rabu da ita , har ta ba ni labarin auren da a ka yi kokarin yi mata bayan komawar su UK amma ta cere , har ciwon zuciya ya kamata ta shiga doguwar suma na sati biyu , ba za ta iya jure rayuwa babu ni ba , duk da ni ma ba zan iya rayuwa babu ita ba amma haka na danne zuciya ta na ce mata ta yi hakuri ba zan iya zama da ita ba , da ga haka na tashi zan bar mata office din saboda ba zan iya jure ganin hawayen ta ba , har na kai bakin kofar na jiyo Muryar ta ta na cewa ta yarda za ta karbi addini na , in har ta hakan ne kadai za mu iya kasancewa a tare na takaice miki labarin , momyn ki ta karbi kalmar shahada a ka daura mana aure , da farko familyn mu sun ki yarda saboda launin fatar mu , amma da mu ka nuna musu mu na son junan mu su ka yarda da auren mu , amma duk wannan abun familyn momyn ki ba su San cewa ita musulma ce a yanzu kuma na sauya mata suna na saka mata MRS MARWA ABDOUL KARIM , My Twinkle , My first lady , the love of My life " ya kai karshen ya juyawa ya kali Twinkle
da sauri ta fada jikin shi ta rungume shi tsam ta na fadin " Ina mutuwar son ka ka sani ko ? " ta fada kamar za ta yi kuka
a hankali ya zagayo da dayan hannun shi a bayan ta ya kai lips din shi saman forehead din ta ya manna mata kiss sannan ya ce " Ina mutuwar son ki ni ma baby "
kamar da ga sama su ka jiyo Muryar wani saurayi bakin kofar shigowa parlourn ya na fadin " and me ? Who loves me ? "
wata yar karamar kara Safa ta saki kafin ta diro da ga saman cinyar his excellency ta nufi saurayin nan da gudu ta na fadin " Aryan , Aryan ! "
ta na karasowa wajen shi ya sa hannayan shi biyu ya daga ta sama ya juya da ita cikin parlourn kafin ya ce " My Puppy , Na yi kewar ki over "
saurayin kyakyawan gaske ne , Fari kal da shi kamanin shi daya tak da Safa ya na kama da yan china , sai dai ya so ya yi jinin Hausawa , a shekaru ba zai wuce 15 years , kunsan yadda yaran turawa ke da saurin tassowa , Idan ka gan shi sai ka ce ya kai shekara 20 , ga shi kuma ya da tsayi da murdaden jiki , gashin kan shi golden ne kamar na Safa shi ma , mai mugun laushi ya daure shi a baya
ya na sanye da wani Jeans White color da T-shirt Navy blue , kafafun shi cikin wasu sneakers farare kal su ma ya hadu over
Sai da ya gama juyawar shi sannan ya tsaya , ya ce ma Safa " Na yi kewar ki sosai da sosai "
wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Aryan amma tare za mu koma Moscow ? "
" Yeah tare za mu koma " ya fada ya na fara takawa ya nufi sofa ya zauna
tsuke fuska Twinkle ta yi ta na cewa " Yanzu Marwan ba za ka gaishe ni ba "
wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya sauke Safa ya tashi ya nufi Twinkle ya rungume ta ya na fadin " na yi kewar ki over My momy "
rungume shi ta yi ita ma ta yi ta na fadin " ni ma na yi kewar ka sosai my boy "
a hankali ya raba jikin shi da nata ya na shirin magana His excellency ya kai hannu ya murde mishi kunne ya na cewa " Yanzu tsakani da Allah Marwan me na fada maka ? ba cewa na yi ba ka jira zan je na dauko ka ? "
" ashhhhh Daddy please let me da zafi wlh , kuma na yi wajen one hour da jirgin mu ya sauka na yi ta jiran ku amma ba ku zo ba , shi ya sa na taho na yi muku surprise "
sakin kunnen shi His excellency ya yi ya na cewa " ba za ka kira ni ba ? shikenan yanzu tafi ka yi wanka ka zo ka ci abinci "
" Okay dad " ya fada a takaice kafin ya juya ya mikawa Safa hannu
da gudu ta karaso wajen shi ya sa hannu ya daga sama ya daura saman kafadar shi ya nufi stair ya na fadin " Daddy ka sa a kawo min kayana bedroom di na "
ya kai karshen ya na fara taka stair , a nan ma wani dan karamin parlour ne , komai na cikin Pink color ne , ga wasu Door guda hudu a jere
kai tsaye Door ta biyu ya nufa , ya tura kofar ya shiga ya na sallama kassa kassa
wani kyawatencen parlour ne , ya kawatu da kayan more rayuwa har da fridge komai na cikin Milk color ne , da ga gani wajen kullum cikin Shara da guga ya ke
kai tsaye Door din da ke fuskantar kofar shigowa parlourn ya nufa , ya tura ta
nan kuma wani kyawatencen bedroom ne , komai na ciki Milk color ne , da wani Royal bed Fari kal shinfide da wata bedsheet Milk color mai mugun kyau , gadon ya na fuskantar wasu door guda biyu a tsakanin su kuma akwai wani dressing room dauke da kwallaban Perfume da lautions
a geffen door ta farko akwai wata Sofa three seaters , sai wata one seater a geffen ta
ga wani Chinesse carpet Fari kal gaban ta , saman shi akwai wata yar karamar Table ta glass dauke da flowers irin na decoration haka
cen bayan gadon akwai wata yar table , dauke da books da wata yar karamar laps kamar bedside lamps , sai wata yar chair din ta kamar office haka
a geffen ta Table din akwai wani Wall na zalar glass , an rufe shi da wasu curtain white color su ma abun dai Masha Allah
kai tsaye saman gadon ya sauke Safa sannan ya kai hannu cikin aljihun shi ya fido wayoyin shi ya ajiye saman bedside drawer
ya na shirin magana wata Maid ta shigo janye da trolley biyu ta na sallama
dan runsunawa ta yi ta na cewa " barka da zuwa yallabai "
ba tare da ya juyo ba ya ce mata " yawwa kai mu su dressing room " ya fada ya na kokarin cire watch din hannun shi
da to ta amsa mishi kafin ta ja trolley din ta nufi door ta biyu ta shiga
ta na shiga , kuma ta fito sannan ta karaso geffen Marwan ta ce " Sir ku na bukatar wani abu ne ? "
" no za ki iya tafiya " ya fada ya na zama bakin gado ya kai hannu ya fara cire sneakers din shi
" Puppy , tashi mu tafi ko ? " ta fada ta na mikawa Safa hannu
noke mata kafada Safa ta yi kafin ta konta saman gadon ta juya mata baya
wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya ce mata " don't worry za ki iya tafiya kawai "
" okay sir " ta fada ta na dan runsunawa kafin ta juya ta fice abun ta
ta na fita Marwan ya mike tsaye ya ce ma Safa " Puppy , zan shiga wanka , kar ki yi min barna kin ji ko ? na san halin ki "
" Aryan , don't forget I'm an angel , babu abun da zan yi "
" hmmmm na ji madam , ke dai kawai na tardo kin taba min kaya , ba zan ba ki gift din ki ba " ta fada ya na fara takawa ya nufi door ta farko
da sauri Safa ta mike zaune ta na fadin " da gaske Aryan ka kawo min gift ? "
" bari na fito ki gani " ya fada ya na shiga toilet din ya janyo Door
sai da ya dauki wajen good one hour cikin Toilet din kafin ya fito sanye da bathrobe , bai bi ta kan Safa ba ya wuce dressing room
ya na shiga ko wayar shi ta fara ringing
da sauri Safa ta mike zaune ta kai hannu ta dauki wayar ta jingina bayan ta a jikin forehead din gadon ta dauki kiran sannan ta kai wayar a kunne ta na fadin " Hello "
Shiru ba a amsa mata ba , a hankali ta sauko wayar ta ga kalli screen din ta ga kiran bai katse ba
sai ta meda wayar a kunne ta sake cewa " Hello ! Here the earth , is There anyone ? "
sai da a ka dauki wajen Two minutes kafin ta jiyo wata Zazzakar sexy voice cike da nitsuwa a ka ce mata " where is Aryan ? "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " me za ka ba ni idan na fada maka ? "
ta na gama fadar haka ta ji an kwace mata wayar ,
da sauri ta juyo ta na kallon Marwan tsaye bakin gadon sanye da wasu pajama blue ma su mugun kyau
" me na ce miki ah ? "
" but Aryan , ba abun da na yi fa yanzu na dauki wayar , kuma tambaye shi ba abun da na ce mishi " ta fada cikin shagwaba
bai ce mata komai ba ya kai wayar a kunne ya ce " Hi guy , how are you ? "
a daya bangaran kuma a ka ce mishi " who is she ? "
murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya ce " ina ruwan ka uban tambaya , where is Doctor ? " ya fada da turanci
dan jinkirtawa ya yi kafin ya amsa mishi da cewa " Ya na barci " ya ba shi amsa da turanci shi ma
" Gaskiya Doctor ya ji dadin rayuwar shi , har ya samu damar yin barci "
" na ga kai har damar komawa gida ka samu "
" Hmmm na ji shikenan , tell me How are you , ya jikin naka ? "
" Fine , yaushe za ka dawo ? "
wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya ce " har ka fara kewa ta kennan ? "
wani dan karamin tsaki mutumin nan ya yi kafin ya katse kiran ba tare da ya ce komai ba
sauko wayar Aryan ya yi ya na yar karamar dariya kafin ya kai hannu ajiye ta saman bedside drawer , kar ku manta duk maganar nan da su ke da turanci su ka yi ta
[20/09 Γ 23:47] MEERAH πͺ·π©·:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
πΈπ ( A heart touching love story & destiny ) ππΈ
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ππΈ
γTHE ROYALTY LOVE ππΈπγ
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ :FREE BOOK
β€β EXILED PRINCE ββ€ : PAID BOOK
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
πππππππ
https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
ππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
___________________________________________
LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN β€βEXILED PRINCE ββ€
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
ππππ
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πππππ
Zain (Airtel)
08081129487
sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753
___________________πππππππππ____________________
ο½ PAGE 27 π₯ β€ ο½
a hankali Marwan ya juyo ya kali Safa ya ce " mu je ki ga surprise din ki ? "
da sauri ta Haye saman bayan shi ta na fadin " yeah , yeah , mu je na gani , I hope chocolate ne dayawa "
yar karamar dariya ya yi ya na mikewa tsaye da ita a bayan shi ya ce " sannu ke