Showing 21001 words to 24000 words out of 133773 words
shi Safa ta yi kafin ta kauda kan ta gefe ba ta ce mishi komai ba
Kujerar da Haoua ta tashi ya zauna ya na fadin " okay ba komai na zo ne muyi magana a kan abun da ya faru jiya "
Tsaki Safa ta yi kafin ta ce " magana a kan cin amanar kawa ta da ka ke yi "
Yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " to minene a ciki , na ga ai ba ta gan ni ba kin ga ko kin fada mata ba za ta yarda da ke ba , me zai hana ki ba ni dama ke ma , za ki ji dadin taraya da ni tun ranar da na dora ido na saman ki , na ba ni son kowa sama da ke " ya kai karshen ya kai dan yatsar shi ya shafi geffen fuskar ta
A dubu dari Safa ta riko hannun shi , ta murde baya , kafin ta mike ta karaso geffen shi ta tsaya , ta kai hannun ta , ta damko wuyan shi ta baya ta gama kan shi da table din da karfi ta danne
Sannan ta ce " kale ni da kyau ka ga ni , ko wanda ya haife ka na fi karfin shi ba kai ba , wlh dirty boy kamar ya yi kadan ya ce zai taba ni , tun wuri gwara ka fita hanyar Djami idan ba haka ba sai na sa an yi min maganin ka "
Ba ta gama rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar Djamila ta na kiran sunan ta da karfi
Da gudu ta karaso wajen , ta sa hannu ta kwace Mansour da ga hannun Safa ta na fadin " Safa lafyar ki kuwa me ya yi miki da za ki shake shi haka "
Safa ko kallon su ba ta yi , sai ma tattare kayan ta da ta yi ta meda cikin bag din ta , ta rataya ta
Ta na shirin barin wajen ta jiyo Muryar Mansour ya na fadin " baby na sha fada miki , wlh bakin ciki ta ke yi miki , ko yanzu na zo ina tambayar ki ne ta ce min in zauna za mu yi magana ni na dauka wani abu mai mahimanci game da ke ne za ta fada min , wai sai ta shiga ce min wai ta jima ta so na kuma za ta so mu kula alaka bayan idon ki , da na fada mata ni ba zan iya cin amanar ki ba shi ne ta ce sai ta yi duk yadda za ta yi ta raba mu ni da ke da na nuna mata ba ta isa ba shi ne ta hau ni da duka " ya fada ya rike da hannun Djamila
Haoua dai na gefe ta na kallon makirci irin na Mansour ita ta ma rasa bakin magana
Ta na a haka sai ganin Safa ta yi ta kai mishi wani irin wawan bugu a ciki har sai da ya zube saman guyiwowin shi
Zaro idanu Djamila ta yi ta na kallon shi ya na juyi a kassa ya dafe cikin shi
Cikin bacin rai ta daga hannu ta wanka ma Safa mari har sai da veil din ta ya warware ya fadi kassa , wannan Golden hair din na ta ya bazun mata har sai da ya rufe mata fuska
Slowly ta dago kai ta na kallon Djamila , idanun ta sun koma jazir dan bacin rai
Da sauri ta daga kafa ta bar wajen dan ta san in ta ce za ta sa hannu ta rama , to sai dai a dauki gawar Djamila a wajen
Ta na barin wajen Haoua ta riko kafadun Djamila ta na girgiza ta ta ce " ke Djamila da hankalin ki kuwa , yanzu Safa ce wa kan ta ki ka daga hannu ki ka mara saboda wani banzan cen daban , me Safa a ba ta yi mana ba , shi ne yanzu za ki watsa mata kassa a ido , kin fi kowa sanin ko cikin makarantar nan Safa mu biyu kawai ta ke yi wa magana , tsawan shekaru uku yanzu mu na tare da ita , ba ta taba bude baki ta fada mana wata bakar magana , Ki duba tarin dukiyar sa gare su , ki duba fatar jikin ta sam ba irin ta mu ba ce , amma a haka ta dauke mu yan uwan ta , shi ne yanzu dan wannan ya fada miki karya da gaskia za ki daga hannu ki mare ta , kin ba ni kunya Djamila " ta kai karshen ta na sakin ta
Ta juya da gudu ta bi bayan Safa , amma tun kafin ta ida sauko stair ta ga motar Safa ta bar school din da mugun gudu
Tsaki ta ja kafin ta juya ta koma library , ba ta tsaya bin ta kan Djamila ba ta dauki bag din ta , ta bar wajen ita ma
Ta na tafiya Mansour ya ce ma Djamila " kar ki ga laifin su don Allah , ya kamata ki je ki bawa Safa hakurin marin da ki ka yi mata , ko ba komai kawar ki ce , kar ki bari dan soyayyar mu ku rabu please "
Murmushi Djamila ta yi kafin ta ce " shikenan yadda ka ke so haka za a yi , yanzu dai tashi , ka zauna , ka sha ruwa kar a je ta ji maka ciwo " ta kai karshen ta na taimaka mishi ya tashi ya zauna saman chair ya na dafe da ciki sai nishi ya ke kamar wadda ta ke shirin haifuwa
Bangaran Safa kuma , ta na barin school din kai tsaye gida ta nufa
Ta na shiga gidan ba ta tsaya wani bata lokaci ta tila bag din ta tsakiyar parlourn , ta Haye stair kai tsaye gym ta shiga ba tare da ta saka gloves ba , ta kama bag din boxing ta fara kai mata uban duka da hannayan duka biyu
Sai da ta dauki wajen Good one hour ta na abu guda ba tare da ta sani ba
Sai da ta gaji iya gajiya sannan ta bari ta fito gym din ta shiga bedroom din ta
Kai tsaye toilet ta wuce
Jim kadan ta fito sanye da bathrobe ta wuce dressing room
Ba ta dauki wani lokaci ba ta fito sanye da wata gown zuwa cinya , navy blue mai bala'in kyau ta saki wannan golden hair din ta har tsakiyar bayan ta , sai tashin kamshi ta ke
Bedroom din baki daya ta fito , a hankali ta ke tako stair din ta sauko kassa , nan ta ga bag din ta tsakiyar parlourn
Daukar bag din ta yi ta ajiye saman sofa kafin ta nufi dining room ta shiga kitchen ta na sallama kassa kassa
Nan ta isko Balki ta na girki
Karasowa cikin kitchen din ta yi ta na fadin " Balki ina kayan da na ce ki sayo min "
A razane Balki ta juyo ta na kallon ta , dan ta san da wuya Safa ta dawo wannan lokacin
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " sannu da dawowa madam , na sayo duk abin da ki ka bukata bar1 na dauko miki su " ta kai karshen ta na nufar wajen Drawer na sama ta bude ta fido wani carton madaidaici ta ajiye saman wata table
Karasowa wajen Safa ta yi kafin ta bude carton din ta fara fido abun da ke ciki daya bayan daya ta na ajiyewa saman table din ta fara aikin ta
After some hours
Konce Safa ta ke saman doguwar sofa , ta daura hannun ta daya saman forehead din ta , dayan kuma ta na danna remote ta na sauya chanel
Ta na a haka ta jiyo wayar ta ta na ruri allamun shigowar sako
Dan karamin murmushi ta yi kafin kai hannun ta , ta ajiye remote din saman table ta dauki wayar ta
Kallon screen din ta yi ta na karanto sakon * Good morning Miss Safa * shi ne abun da ke rubuce
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta yi reply da * Good morning Mister Musadeeq *
Sai da a ka dauki lokaci kafin ta ga an yi mata reply * me ki ke yi da wayar ki a wannan lokaci , ko ba cikin aji ki ke ba π€π€ *
Dan karamin tsaki ta ja ta na kauda kai gefe sannan ta meda wayar saman table ta ajiye ta dauki remote ta ci gaba da sauya chanel
Ta dan jima a haka kafin wayar ta ta yi ruri allamun shigowar sako , amma ba ta duba ba
Jim kadan wani sakon ya kara shigowa , yanzu ma ba ta duba ba sai ma lumshe idanun ta da ta yi allamun barci ta ke ji
Ba ta jima ba da lumshe idanun ta wayar ta ta fara ringing
A hankali ta bude idanun ta, ta kai hannu ta dauko wayar ta na kallon screen din
Sai da kiran ya tsinke , ba ta daga ba ta na kallon screen din har wani ya sake shigowa
Sai da ya kusa tsinkewa sannan ta dauki kiran ta sa wayar a Hand free ta ajiye ta saman chest din ta , sannan ta kai hannu ta dauki remote ta na yin sallama a hankali
Sai da a ka dauki lokaci kafin a amsa mata sallamar ta cikin wata zazzakar Sexy voice cike da nitsuwa , da ga jin wanda ya amsa sallamar nan ba ya son yawwan magana
Dan karamin murmushi ta yi jin wannan Muryar ta shi ba karya ta yi mata dadi
Cen kuma sai ta ce " Mister Musadeeq lafya ka kira ni "
Yanzu ma sai da a ka dauki wajen good five minutes kafin a ce " please yi magana da turanci ba na jin haoussa " ya fada da turanci
Dan zaro idanu Safa ta yi cike da mamaki ta ce " ba ka jin haoussa amma ka a yi amsa sallama ? "
Shiru ba a amsa mata ba
" da kai na ke magana " ta sake fada jin an yi mata shiru
Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " ni musulmi ne shi ya sa "
" ahhh , kenan kai balarabe ne " ta fada cikin zolaya
" cikaken bahaoushe ne ni " ya ba ta amsa cikin sanyi
Dan zaro idanu Safa ta yi ta na fadin " what ? Bahaoushe fa kuma ba ka iya haoussa ba , no gaskia ba zai yi yu ba , ban yarda da hakan ba "
Shiru ya yi bai ce mata komai ba , ita ma ba ta ce mishi komai ba har sai da su ka dauki wajen ten minutes a haka kafin ta jiyo sexy voice din shi ya na fadin " ban taso cikin haoussawa ba "
" Duk da haka nan mom and Dad din ka su na jin haoussa , why ba su koya maka ba " ta kai karshen ta na sauko da kafafun ta kassa ta mike zaune
Yanzu ma sai da ya dauki lokaci kafin ya amsa mata da cewa " sun so su koya min , amma na ki "
" Why ? "
" zan kira ki an jima " ya na gama fadar haka ya katse kiran ba tare da ya jira amsar ta ba
Kallon screen din ta yi , ba ta san lokacin da wani cool murmushi ya subce mata ba , ko ba komi ya iya magana , kuma ya na da nitsuwa
A hankali ta koma jikin sofar ta konta , ta na jin yanayi mai dadi na ziyartar ta lokaci guda a haka har lokacin sallat ya yi ta tashi ta koma bedroom din ta
[21/08 Γ 22:40] null:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH πͺ·π©·
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
πππππ
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
πππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
π²π²π²π²π²π²π²π²π²π²π²π²
DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION
( D.A.W.A )
π²π²π²π²π²π²π²π²π²π²π²π²
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE 8 π₯ β€
βͺABUJA ( KUJE PRISON )
βͺMARWANπͺ·
zaune ya ke saman wani banci cikin harabar prison din , ya daga kai sama ya lumshe idanu , ya saki wani cool murmushi
Ya na a haka Bachir ya yi mishi sallama ya na fadin ya yi bako
Ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " Bachir , na fada maka in dai wacen mutumin ne , ku daina barin shi ya na shigowa "
" No Sir ba shi ba ne , ina ga wanda ka ce zai fitar da kai da ga gidan nan ne "
Murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya sauko da kan shi slowly ya bude idanun shi ya kali Bachir ya ce " no ba shi ba ne "
Ya kai karshen ya mike tsaye ya fara takawa ya yi gaba , da sauri shi ma Bachir ya juya ya bi bayan shi su ka nufi dakin da a ke kawo ziyara
Bakin shi dauke da sallama cen kassan makoshi ya shigo dakin , ya nufi chair ya zauna ya jingina a bayan ta ya saka hannayan shi a aljihu ya na sakin wani makirin murmushi , ya na kallon wanda ya zo ganin shi
Wani cool murmushi Sami ya saki kafin ya ce " Bro ya ka ke ? "
" kamar yadda ka ga ni ban mutu ba " ya fada a takaice
Kara fadada murmushin Sami ya yi ya na fadin " haba bro , da ga tambaya "
" to ina lafya , shikenan ? "
" haka ya kamata ka ce "
" na ji fada min , me ya kawo wa je na yau , ko ka zo ne ka yi min dariya kamar yadda ka saba " ya kai karshen ya na daga mishi gera guda
A tare su ka bushe da dariya kafin Sami ya ce " kai bro wai har yanzu ba za ka daina wannan tsagar da ka ke ba ? "
Tsagaita dariyar shi Marwan ya yi kafin ya ce " To ya ka ke so na yi , kun kawo ni gidan tantirai dole na koyi tsaga , yanzu fada min ya su momy su ke ? "
Murmushi mai dan sauti Sami ya yi kafin ya ce " su na nan lafya , ka San wani abu ma ? "
Girgiza mishi kai Marwan ya yi allamun a'a
" kawo kunnen ka ka ji " ya fada ya dan gusowa
Ba musu shi ma Marwan ya matso ya mika mishi kunne shi sannan Sami ya rada mishi wani abu
Ban san abun da ya fada mishi ba , kawai sai ganin shi na yi ya saki wani cool murmushi har sai da ya lumshe idanun shi slowly ya bude su
Komawa su ka yi su ka zauna saman chair din su , su na kallon juna an rasa me cewa wani abu
Sai cen kuma Marwan ya ce " wlh Sami ka cika dan sa ido "
Dariya sami ya yi ya na mikewa tsaye ya ce " dole na sa ido mana , mu na nan sake da ba ki , sai dai kawai mu ji an kawo mana katin aure , ni zan tafi sai na dawo " ya kai karshen ya na barin dakin
Dan karamin murmushi Marwan ya yi kafin ya juyo ya kali Bachir ya ce " wlh kayi hankali da yaron nan mugun sa ido gare shi " ya kai karshen ya na mikewa tsaye ya fara takawa ya bar dakin
Bin bayan shi Bachir ya yi ya na yar dariya , ya rasa dalilin da kullum ya ke bala'in son Marwan kamar yan uwan shi na jini
βͺUK ( LONDRES )
βͺMisalin karfe 10 na dare
wani tanpasheshen parlour ne mai bala'in girma da kyau , Parlourn ya na da bala'in haske duk da cikin dare ne
Wani Chandelier ne fari kal mai bala'in kyau ga haske kuma sai ka rantse da Allah da rana ne
Komai na cikin parlourn da ga Red sai white colour ne , gaskia ya hadu iya haduwa dan da ga gani ba kananan kudade a ka kashe cikin gidan ba ki daya
A hankali ya ke tako stair din