Showing 126001 words to 129000 words out of 133773 words

Chapter 43 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9707

dalilin hakan ne ma ya sa a ka aura maka ita saboda shi ne burin dan uwan ka na karshe , okay na ji ba ka son ta , ka yi kokari ta samu lafiya ta tuno rayuwarta ta baya , ita da kan ta za ta rabu da kai dan ba kai ta ke so ba , ba dan Fatma ta ce kai ne mijin ta kuma auren soyayya ku ka yi ka San ba abun da zai sa ta yarda da kai , duk wannan kulawar da ta ke nuna maka za ta daina , kuma ni in dai ta ce a raba auren ku , wlh sai ka sake ta dan rainin sens kawai " ya na gama fadar haka ya mike ya nufi hanyar part din shi ya bar Assad da Fatma nan zaune


sai da Musadeeq ya bar wajen sannan Fatma ta mike ta karaso wajen Assad ta kai hannu saman shoulder din shi ta ce " my lion , kar ka takurawa kan ka , na san ka na son ta kamar yadda Amar ya ke son ta , kawai ka kasa jure a ce ta fara soyayya da Amar ne na san ka da zafin kishi , ka saki zuciyar ka , ka juyo soyayyarta kanka tun kafin ta dawo cikin hayacin ta ka rasa ta har abada " ta na gama fadar haka ta janye hannun ta , ta bi bayan mijin ta


shiru Assad ya yi ya kassa cewa komai
sai da ya dan dauki lokaci kafin ya sunkuyar da kai ya fara latsa wayar shi
ya dan dauki lokaci a haka kafin ya kai wayar a kunne babu ki sallama ya ce " Fares , yaushe za ka zo ne ? "


a daya bangaran dan jinkirtawa Fares ya yi kafin ya ce " i'm sorry Sasha , ina ga sai dai na turo assistant din Amar Nurse Lea dan ta kula da Madam , akwai wani taro da gare ni Friday ba zan iya zuwa yanzu ba "


dan jinkirtawa Assad ya yi kafin ya ce " Okay , da ga nan zuwa gobe ina jiran ta "
" okay , but Sasha ina da wata shawara idan za ka saurare ni please " Fares ya fada cikin sanyin murya


" okay " Assad ya fada a takaice


dan jinkirtawa Fares ya yi kafin ya ce " ni da Doctor mun sha haduwa da patient din da su ka ke fama da amnesia , mafi yawwancin lokaci mu kan shawarci familyn su kamar su dinga maimaita wasu action da patient din ke yawwan yi , kamar wani Gym haka i don't know how to explain you that "


cikin nitsuwa Assad ya katse shi da cewa " wasu moments da ya faru cikin rayuwar su ta baya ? " ya fada saboda ya tuno yanzu da ta ce mishi ta ji kamar wata arrow ta wuce ta tsakiyar kan ta lokacin da ta sauke lips din ta saman nashi , kenan ta tuno lokacin da Amar ya taba yi mata kiss lokacin da su ka je prison


da sauri Fares ya ce " yeah , yeah , yanzu for example a ce ta na yawwan yin gym , kamata ya yi ka dinga sa ta ta yin gym a yanzu , hakan zai sa wasu remind su dawo mata sannu sannu "


" okay , ina jiran Nurse din gobe " ya na gama fadar haka ya katse kiran ya tashi a hankali ya nufi stair ya haye
kai tsaye part din shi ya koma , ya na shiga bedroom din shi ya ga babu kowa a ciki


a rude ya fara bin wajen da kallo ya na fadin " Safa where are you ? "
shiru babu motsi kowa
da sauri ya nufi toilet ya tura kofar
cak ya tsaya ya na kallon ta naked tsaye bakin bath za ta shiga


wata irin muguwar bugawa zuciyar shi ta yi nan take jiri ya debe shi ya zube saman guyiwowin shi ya na kai hannu saitin zuciyarshi ya dafe
ba karamar razana ya yi ba ganin ta naked , wannan kyakyawar surar jikinta a waje


a hankali Safa ta juyo ta na ganin shi zube saman guyiwowinshi ta nufo shi ta zube saman guyiwowinta gaban shi ta na fadin " Babe , are you okay ? "


kassa bude idanun shi Assad ya yi , ya na tsoron ya bude ya sake yin karo da wannan surar jikin ta
a hankali ya mike tsaye idanu a rufe ya juya a hankali ya fito toilet din kai tsaye bed din shi ya nufa kamar ya na gani ya haye ya konta








πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«


( YAR JARIDA )













πŸ•ŠπŸ’”( A heart touching love story & destiny ) πŸ’”πŸ•Š














STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸŒΈ








【THE ROYALTY LOVE πŸ•ŠπŸŒΈπŸ’•γ€‘














Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ :FREE BOOK


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀ : PAID BOOK














TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP POSTING ROOM


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054










DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i










DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite












BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM












______________________________________








LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN , COMPLETE KUMA 400


GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❀⚘EXILED PRINCE ⚘❀
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank


IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
Zain (Airtel)
08081129487


sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753








_____________________________________

















ο½› PAGE 37 πŸ₯€ ❀ }


















Safa na ganin ya konta ta juya ta koma cikin toilet din ta ci gaba da wankanta
sai da ta dauki wajen good one hour a ciki kafin ta fito ta na daure da towel a kirjin ta
har za ta shiga dressing room kawai ta tuno ashe ba part din ta ne ba
a hankali ta karaso bakin gadon ta ce mishi " Babe , please ka dauko min kaya a part di na "


a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya sauko da kafafun shi kassa ya mike zaune ba tare da ya ce mata komai ba ya fito part din
ya na fita ta zauna bakin gadon ta na sakin wani dan karamin murmushi


jim kadan ya dawo cikin dakin ya na rike da wata yar box Fara , kai a sunkuye ya mika mata
hannu ta kai ta karba ta na yi mishi godiya kafin ta tashi a hankali ta nufi dressing room , shi kuma ya sa kafa ya fice part din , dama headquater ya ke son tafiya Musadeeq ya tsayar da shi , to yanzu kuma ya kama hanya


jim kadan ta fito sanye da wata gown white color har kassa mai zanen flower multicolore , sai wani dan veil pink color ta yafa shi a kai
kai tsaye part din ta baro ba ta tsaya neman shi ba , a haka ta sauko parlourn kassa
nan ta tardo Rahaf da Sohan zaune , ko wane ya na faman latsa wayar shi


a haka Safa ta karaso cikin parlourn ta na fadin " har kun dawo ? "
a tare ita da Sohan su ka dago kai su ka kalle ta kafin su sakin wani dan karamin murmushi a tare su ka ce " Hi sister "


a hankali Safa ta karaso cikin parlourn ta zauna geffen ta na fadin " Hi ! ina ku ka baro Sahan ? "


" wai ya tafi yin barci " Rahaf ta ba ta amsa
" barci warhaka ? " Fadin Safa


a hankali Rahaf ta matso kussan Safa ta ce mata " ina big bro ya yi ne wai ? "
daga mata kafadu Safa ta yi allamun ba ta sani ba
a hankali Rahaf ta juya nan idanun ta su ka sauka kan Sohan da ke ta faman sakin wani cool murmushi shi kadai


hannu Rahaf ta kai ta tabo Safa ta na nuna mata Sohan da kai
slowly Safa ta juya ta kalli Sohan , wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " Sohan , me ka ke yi wa wannan murmushin kai kadai ? "


a hankali Sohan ya dago kai ya na kara fadada murmushin shi ya ce " nothing sister , kawai dai wata fan di ta mu ke chating da ita , she is so funny "


dan tabe baki Rahaf ta yi ta na fadin " toooo , yanzu kai har wata fan gare ka ? "


hararrar ta Sohan ya yi ya na fadin " ina ruwan ki malama ? ni tsaran wassan ki ne ? " ya fada cikin tsare gida


wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " Allah ba ka hakuri "
bai ce mata komai ya tashi ya nufi stair ya haye ya bar su nan


wata yar karamar dariya Rahaf ta yi ta na raka shi da kallo har sai da ya haye sannan ta juyo ta kalli Safa
ta sunkuyar da kai ta na rike da hannayan ta da allamun ta tafi duniyar tunanin ta
a hankali Rahaf ta dafa shoulder din ta ta na fadin " sister ki na lafiya kuwa ? "


a hankali Safa ta dago kai ta saki wani dan karamin murmushi ta na gyada mata kai allamun Eh
" no , ga damuwa nan a tattare da ke , akwai abun da ke damun ki ? za ki iya fada min kin sani ko ? " Rahaf ta fada cikin sanyin murya


dan jinkirtawa Safa ta yi kafin ta ce " please Rahaf fada min gaskiya , wai auren soyayya mu ka yi ni da yayanki ? "


dan zaro idanu Rahaf ta yi ta na kallon ta , ta rasa me za ta fadawa Safa , doctor ya fada musu kar wanda ya fada mata rayuwar ta ta baya za ta iya samun matsala , ita kuma ta na jin yaunin ta yi wa Safa karya
ta yi nisa duniyar tunanin ta , ta jiyo Muryar Safa ta na fadin " Rahaf ki ban amsa mana "
a hankali Rahaf ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " auren soyayya ku ka yi mana sister , me ki ka gani ? "


" nothing , kawai na ga yanayin da yayanki ke yi min magana kamar ba ya so na , ko dan na manta rayuwar mu ta baya , na manta abubuwan da ya ke so da wanda ba ya so shi ya sa ya sauya min haka " ta fada cikin raunin murya


cikin sigar rarrashi Rahaf ta ce mata " ni dai na san big bro ya na matukar son ki , kar ki manta tare ku ka yi accident din , a ranar da ki ka farka , a ranar shi ma ya farka , kuma kalma ta farko da ya furta shi ne where is my Safa ? " ta fada duk da ta san ba haka nan ne ba
ranar da Assad ya farka , da sunnan Amar a bakin shi ya farka


wani dan karamin murmushi Safa ta saki ba tare da ta ce komai ba
ganin yadda ta saki murmushi ya sa Rahaf cewa " kar ki damu , in sha Allah komi zai koma kamar da farko , ki bar duba sauyawar da big bro ya yi lokaci guda haka please , ki na sakawa ranki damuwa for anything , big bro ya na son ki , fiye da rayuwarshi kuma na san ba abun da ba zai iya yi a kan ki ba , kawai ki dan ba shi lokaci ya dawo dai'dai kin ji my lovely sister ? "


wani cool murmushi Safa ta sakin mata kafin ta ce " shikenan , na gode da kwarin guyiwar da ki ka ba ni "


wani kyawatencen murmushi Rahaf ta saki kafin ta ce " shikenan yanzu tashi mu tafi , kin ga lokacin sallat ya yi "
da to kawai Safa ta amsa mata kafin ta mike a tare ita da Rahaf su ka koma part din su , kowace ta nufi bedroom din ta , su ka shiga toilet
Rahaf ta yi wanka sannan ta dauro Alwalla , Safa kuma Alwalla kawai ta yi ta fito ta nufi daddumar ta , ta fara gabatar da sallarta , ko da ta Kamala sai da ta zauna ta na karanto addu'a , sannan ta shiga karatun kur'ani har lokacin Sallar Isha ya zagayo sannan ta tashi ta gabatar da ita bayan ta Kamala kuma ta zauna saman gadon ta , ta yi zugum waje guda kamar mai tunanin wani abu


β–ͺMISALIN KARFE 11 NA DARE


β–ͺASSAD πŸ₯€


tsaye ya ke saman balconyn part din shi , da ga shi sai short da singlet ya na rike da glass dauk da juice a ciki hannun shi guda rike da wayarshi , ya meda shi bayan
ya na kallon yanayin garin , specially da ya ke ta balconyn ka na iya ganin Swimming pool da kuma garden
ga kuma yanayin garin a irin wannan lokacin wani sanyi a ke na musaman mai dadi ga shi yau har da wata yar snow a ke yi
irin wannan yanayin ya na mugun tayar mishi da sha'awa , that's why ma ya ke rike da juice din lemon ya na sha


ya na a haka kawai ji wayar shi ta fara ringing , a hankali ya zagayo da hannunshi ya na kallon screen kafin ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ba tare da ya ce komai ba


ban san ko da wa ya yi magana kawai sai ji na yi ya ce " no , ku meda tafiyar Friday " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran , sannan ya dago glass din hannun shi a hankali ya kai a baki ya dan surbi juice


ya na a haka kawai ya ji an rungume shi ta baya
ba karamar razana ya yi ba , bai san lokacin da ya saki wayar shi kassa ta fadi , cikin irin wannan yanayin da ya ke ciki a yanzu , ko yatsa a ka daura saman shi zai iya samun matsala


da sauri ya ajiye glass din hannun shi saman table din geffen shi ya riko hannayan ta ya juya ya na kallon ta
sanye ta ke cikin wasu kananan kayan barcinta , rigar ko gama rufe cibi ba ta yi ba , ta na ganin ya juyo ta saki wani cool murmushi
ta na shirin magana ya riga ta cewa " what are you doing here ? "


cikin shagwaba ta ce mishi " kamar ya me na ke yi a nan ? wajen ka na zo mana " ta kai karshen ta na zagayo da hannayan ta a kugunshi


da sauri ya sa hannu ya raba ta da jikin shi ya tura ta baya kadan ya na fadin " please get out ! "


nan take yanayin face din ta ya sauya , ta marairaice mishi fuska ta na fadin " kamar ya na fita ? no , ni wlh babu inda zan je yau a nan zan kwana " ta kai karshen ta na nade hanayan ta a kirji ta kauda kai geffe


shi dai ba zai iya kwana da ita ba daki guda , bare kuma har yanzu ya na jin kan shi a hannu idan ta kwana tare da shi da wuya ya jure bai taba ta ba
wata irin gigitaciyar tsawa ya daka mata ya na fadin " i say get out ! "


har wata yar razana ta yi ta na kallon shi , nan take idanun ta su ka ciko da ruwa kamar za ta yi kuka ta ce mishi " shikenan zan tafi , zan tafi har abada yadda ba za ka sake gani na a kusa da kai bare ka ce na tafi " ta na gama fadar haka ta juya da sauri ta koma cikin bedroom din ta baro part din ta na hawaye


da kallo ya raka ta har sai da ta fita part din sannan ya ja wani dan karamin tsaki ya juya ya dauki glass din shi na juice ya na fadin " Amar , me na yi maka da za ka ba ni wannan punishment din ? " ya kai karshen ya na jan wani dan tsaki , ya na ci gaba da shan juice din shi


ya na tsaye a haka kawai ya ga Safa ta shigo garden ta na tafiya da sauri ta na hawaye
wani dan karamin tsaki ya yi kafin ya ce " me kuma ta ke shirin yi ? " ya fada kassa kassa
haka ya tsaya ya tsare ta da ido har ta karaso bakin pool ta tsaya
slowly ta dago kai ta kalli saitin balconyn , su ka yi ido hudu
sai da ta dan dauki lokaci su na kallon juna cikin ido babu ko kiftawa kafin ta dawo da kallon ta kan pool din
a hankali ta daga kafa ta tsunduma cikin pool din nan , ruwan sun yi mugun sanyi kamar ice


tsayewa ya yi ya na kallon ta ko ajikin shi bai ma san da ita a wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login