Showing 72001 words to 75000 words out of 133773 words
iya iskancin ki na dame shi na shanye za ki san assalin wacece ni "
Bari na leko mana Twinkle mu gani
Bayan ta Haye stair kai tsaye part din ta ta wuce , ta na shiga ta yi zaman ta a parlour ta dauki remote ta kunna Tv , dama ita ba ma'abociyar hayaniya ba ce kullum ta na cikin part din ta sai in Daddy ya zo sun sauko a tare
Ta na haka Daddy ya turo kofar dakin ya na sallama
Ba tare da ta juyo ta kaleshi ba ta amsa mishi sallamar shi kassa kassa
Cikin parlourn ya karaso ya zauna geffen ta cikin sanyi murya ya ce " lafiya ki ka taho nan , wai me ya sa ba ki son zama tare da yaran nan ne "
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " tsawon shekara 13 kennan ina zaune cikin gidan nan , babu wanda ya taba bude baki ya yi min gaisuwar mutunci bayan Sami , kuma a haka ka ke son na zaune da su "
Hannu ya kai ya riko nata ya na fadin " ki yi hakuri kin ji , nan gaba komai zai zo karshe "
" tabass komai zai zo karshe " ta fada cikin zuciyar ta
A fili kuma ta ce " A'a Abban Noor , yaran duk kai ka ba su dama su na yin abun da su ke so cikin gidan nan , tun farko da ka na tsawa tar mu su da hakan ba ta faru ba "
" wai me ki ke nufi , wani abu su ke yi ne wanda ban sani ba "
" ni dai ba za ka ji mutuwar sarki a baki na ba , amma ka je za ka gani nan gaba " ta na gama fadar haka ta janye hannun ta , ta tashi ta shiga bedroom din ta
Da kallo ya raka ta har sai da ta shiga sannan ya mike ya fice part din shi kuma
* WASHE GARI
* KADUNA ( G.R.A )
* SAFA 💋
A hankali ta fara motsi ta na kokarin tashi , ta na karanto kalmar shahada ,
Slowly ta ware idanun ta , ta na kallon ceiling din dakin ,
Sai da ta dauki lokaci a hakan kafin ta mike zaune a hankali
Ta na zama kan ta ya yi mata wata muguwar sarawa har sai da ta dafe shi da hannu guda ta na fadin " Wayooo Allah kai na "
Ta na gama fadar haka ta janye hannun ta sannan ta sauko da kafafun ta kassa sannan ta sauko da ga saman gadon ta mike tsaye ta fara takawa
Ta na tafe ta na tangal tangal kamar yar maye har dafe bango ta ke yi amma a haka ta sauko stair ta na kiran sunan Amar
Ta na shigowa parlourn har ta yi gaba za ta fita ta jiyo Muryar mutane a bayan ta
Cak ta tsaya ta juya slowly a tunanin ta Amar ne
Amma sai ta ga wasu samari biyu zaune saman sofa , rike da wayoyin su
, kamin su daya tak kamar ka tsaga kara , launin Skin din su dukka fara ce amma ba fari cen sosai ba , su na da dara daren idanu , farare kal , kwayar cikin su kuma baka ce kirin har wani kyali ta ke yi , ga dogon hanci mai kyau kamar pencil , sai dan karamin bakin su , da lips din su pink colour ma su bala'in laushi da ga gani ,
a takaice dai kamanin su daya da Amar & Assad , sai dai daya ya na da wani piercing a kunnen shi na dama ya saka wata yar jewel ta Diamond
Dayan kuma ya na da kontancen saje baki kirin ya konta mishi lufff gwanin burgewa
Kare musu kallo da kyau Safa ta yi babu ko kiftawa a hankali ta bude baki slowly ta ce " Amar ? " ta fada dan sun yi mata mugun kama da Amar ga shi ta na dan jin jiri ba ta iya tantance abun da ke gaban ta
Mai piercing din ne ya amsa mata da cewa " no ba shi ba ne , My name is Sohan , and him Sahan " ya fada mata da turanci
Ya na gama fadar haka wata kyakyawar budurwa ta fito da ga kitchen ta na rike da tray , shekarun ta sun zo daya da na Safa , ta na fadin " Sohan , wai ina Chefs su ka yi ne , kitchen din ba kowa da na shiga " ta fada ta na karasowa cikin parlourn ta ajiye tray din hannun ta saman table din tsakiya
Ta na ajiyewa ta dago kai ta kali Safa ta na murmushi ta ce " Hi "
Slowly Safa ta bude bakin ta ta ce " Sannun ki , please ina Amar ya ke ? "
Wani kyawatencen murmushi Yarinyar nan ta saki kafin ta matso gaban Safa ta na fadin " You are his girlfriend ? "
" Rahaf ina ruwan ki da ita " Sohan ya fada cikin tsare gida
Slowly Sahan ya mike tsaye ya karaso gaban Safa ya tsaya
Sai da ya kare mata kallo da kyau sannan ya saki wani cool murmushi ya ce " Sister please samu waje ki zauna tun dazu ki na tsaye "
ta na shirin magana Amar ya sauko da ga Stair ya na sanye da Trouser navy blue da T-shirt white color kayan sun yi mugun kama shi
ya na tafe ya kai a sunkuye ya na latsa wayar shi
sai da ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofa sannan ya dago kan shi ya na shirin magana idanun shi su ka sauka kan Safa da ke tsaye kamar ice
wani cool murmushi ya saki kafin ya mike tsaye ya karaso gaban ta murya kassa kassa ya ce " ya ne baby har kin tashi "
tsuke fuska ta yi ta na kallon cikin idanun shi ta dunkule hannun ta ta kai mishi wani mugun bugu a ciki har sai da ya saki wata yar karamar kara ya dafe cikin shi da hannayan shi biyu
Wani irin murmushi ne Sohan da Sahan su ka saki a tare har juya wa su ke su kali juna su na son su yi dariya amma ta ki fitowa
Rahaf ita dai kallon su ta ke baki sake
sai da ya dan dauki lokaci kafin ya janye hannayan shi ya gyara tsayuwar shi ya kali Safa ya ce " me na yi miki za ki min irin wannan bugun "
" ban sani ba , ni na ce ka ba ni maganin barci " ta fada cikin tsare gida
dan zaro idanu ya yi ya na fadin " ta ya a ka yi ki ka san maganin barci na ba ki "
murguna mishi baki ta yi ba tare da ta ce komai ba ta na kauda kai gefe
yar karamar dariya Amar ya yi kafin ya zagayo da hannu shi saman shoulder din ta ya na murmushi ya ce " shikenan i'm sorry , yanzu bari na gabatar miki da brothers di na , Jiya bayan kin yi barci su ka zo , wanna Twins ne , wassiq & Wassif "
da sauri Sohan ya katse shi da cewa " correction , Sohan & Sahan , why kullum ka ke son sauya mana suna "
" ku dai ku ka sani , wannan kuma autar mu ce Rahaf , Family wannan kuma Sunan ta Safa , Your futur sister-in-low " ya kai karshen da harshen Rassian
dan karamin murmushi Safa ta yi ta na kallon su ba ta da ce komai ba
a tare Sohan da Sahan su ka kali junan su baki sake , Rahaf kuma ta saki wani kyawatencen murmushi ta nufi Safa ta rungume ta ta na yar karamar dariya
dan bubuga bayan ta Safa ta yi da ga nan su ka raba jikin su ta na fadin " barka da zuwa cikin familyn mu "
dan gyada mata kai Safa ta yi kafin ta juya ta kali Amar ta wurga mishi hararra sannan ta ce " ni na tafi gida " ta fada ta na shirin juyawa
da sauri Rahaf ta ce " no tun yanzu , ba za ki tsaya mu yi breakfast ba "
dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " kar ki damu zan dawo da yamma "
"okay , ina jiran ki " Rahaf ta fada ta na komawa saman sofa ta zauna
juyawa Safa ta yi ta nufi door din fita ta fice , Amar na biye da bayan ta , har sai da ya kai bakin kofar gidan su sannan ya juya ya koma na su gidan
ya na shigowa parlourn ya tardo su Rahaf su na breakfast
bai bi ta kan su ba ya nufi stair ya Haye ya nufi part din Assad
ta kassan ido Sohan da Sahan su ka raka shi har sai da ya Haye sannan su ka bushe da dariya a tare
hararrar su Rahaf ta yi ta na fadin " to why did you laugh ? "
tsagaita dariyar su , su ka yi sannan Sohan ya ce " Doctor fa ya fada Love , ki na ji fa cewa ya yi Futur sister-in-low "
hararrar kassan ido Rahaf ta yi mishi ta na fadin " and so what ? She is beautiful kuma sun dace da juna "
yar karamar dariya Sahan ya yi kafin ya ce " ni ba abun da ya burge ni sai bugun da ta yi mishi a ciki , da ga gani ba karamin bugu ba ne " ya kai karshen ya na sake bushewa da dariya
" Ko ni bugun da ta yi mishi ya burge ni , babu shiri kawai sai da ya ji abu " Sohan ya fada shi ma ya na yar karamar dariya
hararrar wassa Rahaf ta musu , ta san halin Sohan da Sahan , ba kananan mugaye ba ne in su ka yi niya
yar karamar dariya ita ma ta yi kafin ta ce " wlh ku dai ba ku da kirki yanzu doctor ku ke wa wannan abun "
" kin ga ko fadi gaskia ke ma sai da ki ka yi dariya cikin ran ki " Sohan ya fada ya na daga mata gera guda
yar karamar dariya ta yi ta na fadin " shikenan eh na yi dariya , but duk cikin soyayyar ce , ba ka yadda su ka dace da juna kamar Romeo & Juliet "
" it's true gaskia sun dace da juna " Sohan da Sahan su ka fada a tare da ga haka ba wanda ya sake cewa komai har su ka Kamala breakfast din su
* AMAR 🤙
da sallama a bakin shi ya shigo parlourn part din
Assad ya na zaune saman sofa ya na faman latsa laptop din shi , da ga shi sai short da singlet ya na shan iska
karasowa geffen shi Amar ya yi ya zauna ya na fadin " My General aikin me ka ke tun da safe haka "
shiru Assad ya yi bai ce mishi komai ya na ci gaba da aikin shi
sai da su ka dauki dan lokaci ba wanda ya sake cewa komai kafin Amar ya bude baki ya ce " Gobe Birthday din Aryan "
wannan karan sai da ya dan dauki lokaci kafin ya bude bakin shi a hankali ya ce " I know "
" and ? har yanzu ba ka samo inda ya ke ba , ina kewar dramar nan ta shi sosai " Amar ya fada ya na dan karamin murmushi
ajiye laptop din shi saman table Assad ya yi , sannan ya jingina bayan shi a jikin forehead din sofar ya juyo slowly ya kali Amar ya ce " har yanzu ina bincike , amma duk prison Nigeria ban samu me sunan Aryan ba "
gyara zaman shi Amar ya yi ya juyo su na fuskantar juna ya ce " why ba za mu tambaye ta ba , tun da har mu na da tabbacin dan uwan ta ne , na san ba za ta rasa sanin inda ya ke , kuma na san ita ma ta na son a fitar da shi da ga wajen nan , ko dan haka za ta ba mu hadin kai "
shiru Assad ya yi kamar mai tunanin wani abu
cen kuma sai ya ce ma Amar " no ba za ta fada ba , Tabass ta san inda ya ke , amma ba za ta iya fada mana ba , kuma ita da kan ta ba ta zuwa inda ya ke "
" Assad , dole akwai wanda ya ke hana ta zuwa wajen shi "
" may be matar da ta ke tare da ita "
" why , ka ke tunanin haka ? "
dan jinkirtawa Assad ya yi kafin ya ce " i don't know , kawai matar nan ba ta konta min a rai ba , she is so suspect , abun da na sani His excellency ya na da wani babban yayan bayan ita , na san ba zai rasa family ba , to ya na ina , why ba ya zowa duba ta , tun da har yarinyar Kannen shi ce , dole akwai wata a kassa , akwai wani abun da matar nan ke boyewa "
shiru Amar ya yi kamar mai tunanin wani abu ya daga kan shi sama
da sauri ya sauko shi ya matso kusan Assad ya ce " Assad , Shekaran jiya , ba na fada maka momy ta kira ni ta ce na je gaishe da mijin sister din ta da ke a Abuja "
a hankali Assad ya gyada mishi kai allamun Eh
" yawwa , gidan da mu ka je , na ga wata matar kamanin ta sak da Miss Safa , har da wata yar yarinyar a shekaru za ta kai 13 haka ita ma ta na kama sak da Miss Safa "
daga mishi gera guda Assad ya na fadin " And ? "
" And she call her Momy "
" Momy ? ka na nufin mahaifiyar ta ce "
" ga Dukan allamu , Ta na kiran ta da momy ga shi kuma su na kama tak tak kamar an tsaga kara , har kuka sai da Miss Safa ta yi da ta baro matar nan , sai da na tambaye ta in ta san su amma ta ce ba za ta iya fadamin ba "
" Amar in har wannan matar momyn ta ce , why ba za ta zauna tare da ita ba , sai ta zauna tare da kanwar mahaifin ta ? "
" Assad , ni ma ban sani ba , labarin yarinyar nan a boye ya ke , kuma an boye mata wasu abubuwa dayawa a ciki , Ita da kan ta cikin duhu ta ke "
gyada mishi kai Assad ya yi a hankali ba tare da ya ce mishi komai ba
a hankali Amar ya mike ya fara takawa zai fice dakin
a hankali Assad ya kira sunan shi , cak ya tsaya ya juyo ya na daga mishi gera guda
" Lokacin da na ke binciken prison din Nigeria , akwai wani prisoner me Sunan Marwan , duk shekara sai sun sauya mishi prison , yanzu haka ya na a Abuja , A binciken da na yi yanzu haka ya kusa cika shekara 15 a prison , kamar dai Aryan "
" ka na nufin Marwan zai iya kasance wa Aryan "
" may be , Abun da ya kara daukar hankali na a kan shi , Gobe ne birthday din shi shi ma "
DON'T FORGET TO SHARE PLEASE 🙏🙏🙏
[16/09 à 20:04] MEERAH 🪷🩷:
💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )
🥀💔( A heart touching love story & destiny ) 🥀💔
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🕊💦
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 : Free book
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ : paid book
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite
a duk me bukatar yin magana da ni kai tsaye zai iya samu na ta wannan number +22798999753 , WhatsApp ONLY
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
( 🤣🤣🤣✌✌ yau dai Amar zai fadawa Safa abun da ke cikin zuciyar shi a gaban Televison , zan sha kallo ni dai 🤣🤣✌✌ )
{ PAGE 23 🥀 ❤ }
dawowa Amar ya yi ya koma ya zauna geffen Assad ya ce mishi " yanzu me ka ke Tunani a kai "
" nothing ! " Assad ya fada a takaice kafin ya tashi ya nufi bedroom din shi ya shige ya bar Amar nan zaune
da kallo Amar ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya tashi shi ma ya fice part din
* SAFA 💋
bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn gidan su , har ta wuce stair ta jiyo Muryar Momy ta na kiran sunan ta
a hankali Safa