Showing 81001 words to 84000 words out of 133773 words
da motar Allamun barin wajen zai yi
da sauri ta ce mishi " no no , shikenan mu je , amma one minute "
cak ya tseda motar ya na murmushi ya ce " gaishe shi ne kawai zan yi mu fito " ya kai karshen ya na kashe motar ya zame belt din shi ya bude kofar shi da sauri ya sauka ya rufe
ya zagayo geffen Safa ya bude mata kofar
godiya ta yi mishi sannan ta sauko da ga cikin motar ya rufe kofar ya riko hannun ta , su ka nufi cikin gidan
kai tsaye kofar parlour su ka nufa , su na isa ya saki hannun ta ya danna Bell
ko one minute ba a yi ba , Noor ta bude musu kofar
ta na ganin Doctor ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " laa Doctor , kai ne ? "
dan karamin murmushi Amar ya yi kafin ya ce " zan iya shiga madam ? "
yar karamar dariya Noor ta yi kafin ta ja baya ta kara bude mishi kofar
a hankali ya shigo parlourn ya na sallama
cikin sa'a ko duk mutanan gidan su na nan har Daddy da Sami
Daddy na ganin shi ya saki wani kyawatencen murmushi ya mike tsaye ya na fadin " Doctor Amar da kan shi ne yau cik...... " kut maganar ta yanke sakamakon sauke idanun shi da ya yi saman Safa da ke tsaye bayan Amar
ita da kan ta Safa ta na ganin Daddy duk ta ji zuciyar ta ta yi mata wata muguwar bugawa , nan take ta fara danasanin tsayar da Amar da ta yi
Da sauri Safa ta juya har za ta bar wajen sai dai ta jiyo an riko hannun ta
dum ta ji zuciyar ta ta buga , har wasu yawu ta hadiye , a dubu dari ta juya kai sai ta ga ashe Amar ne ya riko hannun ta
ba tare da ya saki hannun ta ba ya ce " Baby ina kuma za ki je ga uncle din nawa "
a hankali Sami ya mike tsaye ya na maimaita kalmar baby cikin zuciyar shi
shi ba ma babyn ba , ji ya ke kamar ya san fuskar nan ta Amar Amma ya kassa tunawa a ina ya san ta
a hankali ita ma Twinkle da ke zaune ta mike ta nufi Safa , ta riko hannun ta , su ka karaso cikin parlourn ta na fadin " kar ki ji tsoro ke ma nan gidan mahaifin ki ne ! "
da sauri Safa ta yi kokarin kwace hannun ta ta na fadin " momy sake ni na tafi don Allah "
" Dole ki ce haka , mara mutunci kawai " RaΓ―ssa ta fada cikin bacin rai dan fa ita ta na jin haushin Abun da ya faru tsakanin ta da Amar , har ta kamu da son shi ya ce ya fasa
cikin ko in kula Noor ta ce mata " ki daina ce mata mara mutunci "
RaΓ―ssa na shirin magana Daddy ya ce ma Noor " ke Noor koma bedroom din ki "
" amma Dad...... " ba kai karshen maganar ta ba ya daga mata hannu ya nuna mata stair allamun ta Haye
dan karamin gunguni Noor ta yi kafin ta nufi stair da gudu ta Haye
ta na barin wajen Daddy ya tako a hankali ya tsaya gaban Safa ya ce " me ya kawo ki gidan nan ? "
Muryar ta har kerma ta ke yi ta ce mishi " ba . ba komai "
da sauri Amar ya ce mishi " uncle , tare da ni ta ke "
Amar na kai karshen maganar Daddy ya daga mishi hannu allamun ya yi shiru
halin Amar a bai sani ba , duk da hakan bai yi shiru ba sai da ya ce " i'm sorry uncle ba zan iya yin shiru ba , wai me ya ke faruwa ne wajen nan , ku su waye a wajen Ta , baby , wannan matar nan ita ce momyn ki ? " ya fada ya na nuna Twinkle
( kar fa ku manta duk maganar da Amar ke yi da turanci ya ke yin ta )
dan karamin murmushi Twinkle ta yi da turanci ita ma ta ce mishi " eh , I'm her momy ..... "
ba ta gama rufe bakin ta ba Daddy ya daga murya ya na fadin " no , ba ki da hadi da yarinyar nan , ke fice min gida "
da sauri Safa ta kwace hannun ta da ga cikin na Twinkle ta juya , ta tsaya dab da Amar ta kale shi idanun ta cike da ruwa ta ce " Sai da na ce maka ba zan shigo ba " ta na gama fadar haka ta nufi kofar fita parlourn ta fice da sauri
da sauri Amar ya juya ya bi bayan ta ya na kiran sunan ta
[18/09 Γ 21:07] null:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
ππ( A heart touching love story & destiny ) ππ
STORY & WRITTEN BY : MEERAH
γTHE ROYALTY LOVE ππΈπγ
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ : FREE BOOK
β€β EXILED PRINCE ββ€ : PAID BOOK
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
πππππππ
https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
ππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
______________________ββββββββββ_____________________
LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN β€βEXILED PRINCE ββ€
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
ππππ
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πππππ
Zain (Airtel)
08081129487
sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753
___________________πππππππππ____________________
ο½ PAGE 25 π₯ β€ ο½
Shi dai Sami tun farko ya tsare Amar da idanu ya na son ya san a ina ya san fuskar nan har sai da Amar ya bar parlourn Sami bai daina kallon shi ba
su na barin wajen Daddy ya kalli twinkle ya ce " Ya kamata ki manta da kin taba haihuwar wata yarinyar mai sunan Safa a duniya , na dauka wannan maganar kin bar ta tsawan shekaru "
" Haba , Safa fa yarinya ta ce , ni na haife ta , ta ya zan manta da ita "
cikin tsawa ya ce mata " idan ki ka tarda mahaifin ta kin manta da ita , Idan ki na son ki ci gaba da ganin ta a raye dole ki manta da ita " ya na gama fadar haka ya nufi stair ya Haye cike da bacin rai
Dariya sosai RaΓ―ssa ta yi ta na fadin " yau dai asiri da a ka yi wa mutum ya kare , yar rainin sens kawai " ta kai karshen ta na wurga ma Twinkle harara
" ke RaΓ―ssa ba ni son shirme wa ki ke fada wa haka , ko dan kin ga ina kyale ki shi ne na zama tsararr ki , kar ki manta na haifi dai'dai da ke , ba dan ya na prison ba " Twinkle ta fada cikin bacin rai dan yau ta gaji da abun da RaΓ―ssa ke yi mata cikin gidan
ta na gama fadar hakan ta nufi stair ta haye ita ma
da hararra RaΓ―ssa ta raka ta har sai da ta Haye sannan ta ja tsaki ta kauda kai
har ta bude baki za ta yi magana idanun ta su ka sauka cikin na Sami
ba shiri ta shanye maganar ta , ta rufe bakin ta ta na sake saken ta cikin zuciyar ta
shi kuwa Sami a hankali ya taka ya nufi door ya fice parlourn
* SAFA π
bayan ta fito parlourn kai tsaye gidan ta bari , ko da ta je bakin motar Amar , ta bude wajen driver ta shiga ko jiran shi ba ta yi ba
ya na fitowa gidan ya gan ta ta na neman tada motar
da sauri ya shiga wajen Mai zaman banza ya na fadin " Miss Safa , ki tsaya babu kyau tuki cikin bacin rai "
ko kallon shi ba ta yi ba ta tada motar ta juya ta ta bar wajen da mugun gudu
har shi kan shi doctor sai da ya ji tsoro ya na cewa ta rage gudun nan kar su samu hatsari amma ina ko jin shi ba ta yi
ya na tsaka da yi mata magana ya ga ta yi wani mugun cin burki har sai da kan shi ya bugun da gaban motar
ta na danna burkin ta juyo ta kale shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " mun iso "
a hankali ya dago kai ya kale ta , kafin ya juya ya kali gaban shi sam wajen bai konta mishi a rai ba
har ya juyo zai mata magana ya ga ta sauka da ga cikin motar , ta bude gidan baya ta na fadin " doctor sauko mu tafi don Allah " ta kai karshen ta na daukar box din ta ajiye a bayan ta rufe kofar ta fara takawa
da sauri ya sauko da ga cikin motar ya bi bayan ta kar a je wani abu ya same ta
Wajen cike ya ke da sojoji , allamun headquater ne ko kuma prison
ta na shiga ta nufi wani sojan tsaye bayan wani desk ta yi mishi sallama sannan ta ce " please ina son gan..... "
ba ta kai karshen maganar ta ba ya katse ta da cewa " Miss Safa ? "
a hankali ta gyada mishi kai allamun eh
" okay , ya fada mana zuwan ki , officer kai ta dakin ziyara yanzu ya na zuwa "
godiya ta yi mishi kafin ta kamo hannun Amar ta ja shi , su ka bi bayan officer din ya yi musu iso dakin ziyara shi kuma ya juya
ya na barin wajen Amar ya ce ma Safa " wai me mu ke yi a wajen nan ne ? "
a hankali Safa ta nufi table din da ta gani a wajen ta daura box din a sama ta bude ta
cake ne a ciki mai mugun kyau mai launin Sky blue , an rubuta happy birthday a sama
sai da ta ajiye sannan ta juyo ta kali Amar ta na murmushi ta ce " don Allah ka zauna minti daya ba za mu jima ba "
gyada mata kai ya yi kafin ya nufi chair din da ke bakin table din ya zauna , zuciyar shi na duka uku uku ya rasa dalili
Safa kuma tsaye ta yi ta kurawa kofar shigowa waje ido fuska dauke da kyawatencen murmushi
a hankali ta fara jiyo takun mutun
kamar ko ta san dakin a ka nufo nan take ta fara tapi ta na fadin " Happy birthday to you ! Happy birthday to you ! Happy birthday ! Happy birthday ! Happy birthday to youuuuu ! " ta kai karshen idanun ta na cikowa sa ruwa
dai'dai lokacin da Marwan ya shigo wajen Bachir na biye da bayan shi
ta na ganin shi ta nufe shi da gudu ta fada jikin shi ta na sakin kuka
a hankali Marwan ya sa hannayan shi biyu ya rungume ta tsam a jikin shi , ya lumshe idanun shi ji ya ke kamar ya yi kuka ya ce " na yi kewar ki my Puppy "
su na a haka su ka jiyo Muryar Amar a bayan su ya na fadin " A....Ar......Aryan !!!!!! " ya kai karshen ya na mikewa tsaye
slowly Marwan ya dago da ga Jikin Safa ya na murmushi ya ce mishi " No , Marwan Abdoul Karim "
Girgiza mishi kai Amar ya shiga yi kafin ya fara takowa a hankali ya nufi Marwan ya na fadin " No , No , No , Aryan Abdoul Karim , Aryan ba ka gane ni ba .... "
cikin nitsuwa Marwan ya katse shi da cewa " Doctor Amar Musadeeq ! "
a dubu dari Safa ta dago da ga jikin Marwan ta na fadin " Aryan , ka san shi daman "
yar karamar dariya Marwan ya yi ya na shirin magana idanun shi su ka sauka kan cake din da Safa ta ajiye saman table
da sauri ya raba jikin shi da na Safa ya nufi table din ya na fadin " um um um , wa ya yi batan cake a wajen nan ? " ya kai karshen ya na sa dan yatsa ya shafi Cream din saman ya kai a baki ya kai karshen ya na janyo chair din da Amar ya tashi ya zauna saman ta
yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta karaso wajen ita ma ta janyo chair ta zauna ta na fadin " Aryan ka bari na fara ba ka mana "
" ni zan fara baki , kash matsalar ban wanke hannu ba ! "
a hankali ya dago kai ya kali Bashir ya ce " Bash , kawo mana ruwa please da spoon "
da to bashir ya amsa mishi kafin ya juya ya bar wajen
ya na barin wajen Amar ya karaso ya na fadin " Aryan da gaske kai ne ? ba mafarki na ke ba "
a hankali Marwan ya dago kai ya na murmushi ya gyada mishi kai allamun eh sannan ya daura da cewa " ni daman na san za ka zo , amma na dauka kai da Sasha za ka zo ina ka baro shi "
Amar na shirin magana su ka jiyo Muryar Assad bakin kofar dakin ya na fadin " I'm here "
a tare duk su ka juya su ka kali kofar dakin ,
wani kyawatencen murmushi Marwan ya saki ya na fadin " Bismillah , ku zo na yanka birthday cake din da sister na ta yo min "
ba musu Assad ya karaso cikin wajen ya nufi wasu Chair cen karshen room din ya janyo guda ya dawo geffen Marwan ya ajiye ta ya zauna ya na kallon Marwan ya ce " How ? Tsawan shekara nawa ? ka san irin neman da na yi maka kuwa ? "
wani kyawatencen murmushi Marwan ya saki ya na shirin magana bashir ya shigo dakin ya na rike da Spoon uku , da Gorar ruwan Faro guda uku ya nufi table ya ajiye su gaban Marwan sannan ya koma bayan shi ya tsaya
godiya Marwan ya yi mishi kafin ya kai hannu ya dauki Spoon din , bai tsaya bata lokaci ba ya kai ta tsakiyar cake din nan ya gunto ya kai bakin shi
yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Aryan yi a hankali mana "
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " Sister , wai kin san yaushe rabo na da na ci cake , kullum sai dai su ba ni wata sakarar shinkafa ko taste ba ta da "
marairaice fuska Safa ta yi kafin ta ce " kullum ina son zuwa wajen ka amma momy ta ke hanawa "
cikin rudu ya ce mata " Wace momy kuma ? "
" Aunty Aziza kanwar Daddy "
wani siririn Tsaki Marwan ya ja ya ajiye spoon din hannun shi ya ce " wlh wannan matar makira ce , munafuka , annabi a Fuska fir'auna a zuci "
cikin rudu Safa ta ce mishi " Aryan momy ce fa "
Marwan na shirin magana su ka jiyo Muryar Amar na fadin " Aryan please ku yi magana yadda za mu gane "
" yeah , sai wani yare ku ke cen daban , Aryan ya kamata ka fada min yadda a ka yi ka zo nan yadda zan iya fitar da kai " Assad ya fada dan da Hausa ya ke yi wa Safa magana
wani cool murmushi Marwan ya saki kafin ya jingina bayan shi a jikin chair din shi ya na kallon Safa
π€£π€£ YAU DAI ZA MU LEKO TARIHIN RAYUWAR MASOYINA
βͺSOME YEARS BEFORE
βͺABUJA
wani makeken gidan , mai mugun girma kamar unguwa guda , duk harabar gidan ciyayi ne da flowers , ta ko ina akwai Sojoji su na kai kawo ko wane rike da gun da ga ganin fuskokin su babu wassa a ciki
akwai wata hanya ta tiles zagaye da flowers wadda za ta sadaka kai tsaye da ginin
ginin ya tsaru gaskiya kamar da glass a ka yi shi , duk wasu Windows na glass ne
kai tsaye kofar da za ta sada ni da parlourn gidan na nufa ,
a hankali na kama handle din kofar na tura
wani dadaden qamshi ne ya fara kai min karo , ga wani gumi mai sanyi da ke tashi cikin parlourn
ina shiga parlourn na san da wannan ba gidan kananan mutane ba ne
komai na cikin parlourn White color ne , har walls din
haka zalika Tiles din farare ne kal sun sha mopping , ka na ma iya ganin kan ka a ciki , kamar mirror , kamar ba taka su a ke yi ba
parlourn ya na da girma ya kawatu iya kawatuwa , dan funitures din ma kadai sun isa abun kallo
Parlour ya na