Showing 87001 words to 90000 words out of 133773 words

Chapter 30 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9711

ta cere , har ciwon zuciya ya kamata ta shiga doguwar suma na sati biyu , ba za ta iya jure rayuwa babu ni ba , duk da ni ma ba zan iya rayuwa babu ita ba amma haka na danne zuciya ta na ce mata ta yi hakuri ba zan iya zama da ita ba , da ga haka na tashi zan bar mata office din saboda ba zan iya jure ganin hawayen ta ba , har na kai bakin kofar na jiyo Muryar ta ta na cewa ta yarda za ta karbi addini na , in har ta hakan ne kadai za mu iya kasancewa a tare na takaice miki labarin , momyn ki ta karbi kalmar shahada a ka daura mana aure , da farko familyn mu sun ki yarda saboda launin fatar mu , amma da mu ka nuna musu mu na son junan mu su ka yarda da auren mu , amma duk wannan abun familyn momyn ki ba su San cewa ita musulma ce a yanzu kuma na sauya mata suna na saka mata MRS MARWA ABDOUL KARIM , My Twinkle , My first lady , the love of My life " ya kai karshen ya juyawa ya kali Twinkle


da sauri ta fada jikin shi ta rungume shi tsam ta na fadin " Ina mutuwar son ka ka sani ko ? " ta fada kamar za ta yi kuka


a hankali ya zagayo da dayan hannun shi a bayan ta ya kai lips din shi saman forehead din ta ya manna mata kiss sannan ya ce " Ina mutuwar son ki ni ma baby "


kamar da ga sama su ka jiyo Muryar wani saurayi bakin kofar shigowa parlourn ya na fadin " and me ? Who loves me ? "


wata yar karamar kara Safa ta saki kafin ta diro da ga saman cinyar his excellency ta nufi saurayin nan da gudu ta na fadin " Aryan , Aryan ! "


ta na karasowa wajen shi ya sa hannayan shi biyu ya daga ta sama ya juya da ita cikin parlourn kafin ya ce " My Puppy , Na yi kewar ki over "


saurayin kyakyawan gaske ne , Fari kal da shi kamanin shi daya tak da Safa ya na kama da yan china , sai dai ya so ya yi jinin Hausawa , a shekaru ba zai wuce 15 years , kunsan yadda yaran turawa ke da saurin tassowa , Idan ka gan shi sai ka ce ya kai shekara 20 , ga shi kuma ya da tsayi da murdaden jiki , gashin kan shi golden ne kamar na Safa shi ma , mai mugun laushi ya daure shi a baya
ya na sanye da wani Jeans White color da T-shirt Navy blue , kafafun shi cikin wasu sneakers farare kal su ma ya hadu over


Sai da ya gama juyawar shi sannan ya tsaya , ya ce ma Safa " Na yi kewar ki sosai da sosai "


wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Aryan amma tare za mu koma Moscow ? "
" Yeah tare za mu koma " ya fada ya na fara takawa ya nufi sofa ya zauna


tsuke fuska Twinkle ta yi ta na cewa " Yanzu Marwan ba za ka gaishe ni ba "


wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya sauke Safa ya tashi ya nufi Twinkle ya rungume ta ya na fadin " na yi kewar ki over My momy "


rungume shi ta yi ita ma ta yi ta na fadin " ni ma na yi kewar ka sosai my boy "


a hankali ya raba jikin shi da nata ya na shirin magana His excellency ya kai hannu ya murde mishi kunne ya na cewa " Yanzu tsakani da Allah Marwan me na fada maka ? ba cewa na yi ba ka jira zan je na dauko ka ? "


" ashhhhh Daddy please let me da zafi wlh , kuma na yi wajen one hour da jirgin mu ya sauka na yi ta jiran ku amma ba ku zo ba , shi ya sa na taho na yi muku surprise "


sakin kunnen shi His excellency ya yi ya na cewa " ba za ka kira ni ba ? shikenan yanzu tafi ka yi wanka ka zo ka ci abinci "


" Okay dad " ya fada a takaice kafin ya juya ya mikawa Safa hannu
da gudu ta karaso wajen shi ya sa hannu ya daga sama ya daura saman kafadar shi ya nufi stair ya na fadin " Daddy ka sa a kawo min kayana bedroom di na "


ya kai karshen ya na fara taka stair , a nan ma wani dan karamin parlour ne , komai na cikin Pink color ne , ga wasu Door guda hudu a jere


kai tsaye Door ta biyu ya nufa , ya tura kofar ya shiga ya na sallama kassa kassa
wani kyawatencen parlour ne , ya kawatu da kayan more rayuwa har da fridge komai na cikin Milk color ne , da ga gani wajen kullum cikin Shara da guga ya ke


kai tsaye Door din da ke fuskantar kofar shigowa parlourn ya nufa , ya tura ta
nan kuma wani kyawatencen bedroom ne , komai na ciki Milk color ne , da wani Royal bed Fari kal shinfide da wata bedsheet Milk color mai mugun kyau , gadon ya na fuskantar wasu door guda biyu a tsakanin su kuma akwai wani dressing room dauke da kwallaban Perfume da lautions


a geffen door ta farko akwai wata Sofa three seaters , sai wata one seater a geffen ta
ga wani Chinesse carpet Fari kal gaban ta , saman shi akwai wata yar karamar Table ta glass dauke da flowers irin na decoration haka


cen bayan gadon akwai wata yar table , dauke da books da wata yar karamar laps kamar bedside lamps , sai wata yar chair din ta kamar office haka
a geffen ta Table din akwai wani Wall na zalar glass , an rufe shi da wasu curtain white color su ma abun dai Masha Allah


kai tsaye saman gadon ya sauke Safa sannan ya kai hannu cikin aljihun shi ya fido wayoyin shi ya ajiye saman bedside drawer
ya na shirin magana wata Maid ta shigo janye da trolley biyu ta na sallama


dan runsunawa ta yi ta na cewa " barka da zuwa yallabai "
ba tare da ya juyo ba ya ce mata " yawwa kai mu su dressing room " ya fada ya na kokarin cire watch din hannun shi
da to ta amsa mishi kafin ta ja trolley din ta nufi door ta biyu ta shiga
ta na shiga , kuma ta fito sannan ta karaso geffen Marwan ta ce " Sir ku na bukatar wani abu ne ? "


" no za ki iya tafiya " ya fada ya na zama bakin gado ya kai hannu ya fara cire sneakers din shi


" Puppy , tashi mu tafi ko ? " ta fada ta na mikawa Safa hannu


noke mata kafada Safa ta yi kafin ta konta saman gadon ta juya mata baya
wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya ce mata " don't worry za ki iya tafiya kawai "


" okay sir " ta fada ta na dan runsunawa kafin ta juya ta fice abun ta


ta na fita Marwan ya mike tsaye ya ce ma Safa " Puppy , zan shiga wanka , kar ki yi min barna kin ji ko ? na san halin ki "


" Aryan , don't forget I'm an angel , babu abun da zan yi "


" hmmmm na ji madam , ke dai kawai na tardo kin taba min kaya , ba zan ba ki gift din ki ba " ta fada ya na fara takawa ya nufi door ta farko


da sauri Safa ta mike zaune ta na fadin " da gaske Aryan ka kawo min gift ? "


" bari na fito ki gani " ya fada ya na shiga toilet din ya janyo Door


sai da ya dauki wajen good one hour cikin Toilet din kafin ya fito sanye da bathrobe , bai bi ta kan Safa ba ya wuce dressing room


ya na shiga ko wayar shi ta fara ringing
da sauri Safa ta mike zaune ta kai hannu ta dauki wayar ta jingina bayan ta a jikin forehead din gadon ta dauki kiran sannan ta kai wayar a kunne ta na fadin " Hello "


Shiru ba a amsa mata ba , a hankali ta sauko wayar ta ga kalli screen din ta ga kiran bai katse ba
sai ta meda wayar a kunne ta sake cewa " Hello ! Here the earth , is There anyone ? "


sai da a ka dauki wajen Two minutes kafin ta jiyo wata Zazzakar sexy voice cike da nitsuwa a ka ce mata " where is Aryan ? "


wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " me za ka ba ni idan na fada maka ? "


ta na gama fadar haka ta ji an kwace mata wayar ,
da sauri ta juyo ta na kallon Marwan tsaye bakin gadon sanye da wasu pajama blue ma su mugun kyau
" me na ce miki ah ? "


" but Aryan , ba abun da na yi fa yanzu na dauki wayar , kuma tambaye shi ba abun da na ce mishi " ta fada cikin shagwaba


bai ce mata komai ba ya kai wayar a kunne ya ce " Hi guy , how are you ? "


a daya bangaran kuma a ka ce mishi " who is she ? "


murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya ce " ina ruwan ka uban tambaya , where is Doctor ? " ya fada da turanci


dan jinkirtawa ya yi kafin ya amsa mishi da cewa " Ya na barci " ya ba shi amsa da turanci shi ma


" Gaskiya Doctor ya ji dadin rayuwar shi , har ya samu damar yin barci "


" na ga kai har damar komawa gida ka samu "


" Hmmm na ji shikenan , tell me How are you , ya jikin naka ? "
" Fine , yaushe za ka dawo ? "


wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya ce " har ka fara kewa ta kennan ? "


wani dan karamin tsaki mutumin nan ya yi kafin ya katse kiran ba tare da ya ce komai ba
sauko wayar Aryan ya yi ya na yar karamar dariya kafin ya kai hannu ajiye ta saman bedside drawer , kar ku manta duk maganar nan da su ke da turanci su ka yi ta


πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«
( YAR JARIDA )













πŸŒΈπŸ’– ( A heart touching love story & destiny ) πŸ’–πŸŒΈ












STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸŒΈ




【THE ROYALTY LOVE πŸ•ŠπŸŒΈπŸ’•γ€‘














Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ :FREE BOOK


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀ : PAID BOOK
















TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054






DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i


DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite












BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM












___________________________________________








LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN


GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❀⚘EXILED PRINCE ⚘❀
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank


IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
Zain (Airtel)
08081129487


sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753












___________________πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š____________________














ο½› PAGE 26 πŸ₯€ ❀ }


















a hankali Dattijon nan ya fara takawa cikin sanda ya nufi sofar da Safa ta buya a bayan ta
da sauri ya sa hannayan shi biyu ya daga Safa sama ya na cewa " wai ke ba za ki daina gajiyar min da baby na ba ? "


dariya sosai Safa ta yi har sai da kananan hakwaren ta su ka fito
a hankali dattijon nan ya zagayo ya zauna saman sofa sannan ya zaunar da Safa saman cinyar shi ya na ci gaba da kallon ta


sai da ta gama dariyar ta sannan ta ce " Daddy ka daina ce ma momy baby , dubi fa ta tsufa "


a hankali Dattijon nan ya kai hannu ya ja mata hanci ya na cewa " ki daina ce wa momyn ki ta tsufa , kar ki bata mata kin san fa ba ta son a na cewa ta tsufa " ya kai karshen ya dawo da kallon shi kan matar nan


wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta karaso cikin parlourn ta zauna geffen shi ba tare da ta ce komai ba


ta na zama Dattijon nan ya rage sautin Muryar shi kamar mai rada ya ce ma Safa " Gaskiya momyn ki ta na da kananan idanu , yanzu ga shi duk kun dauko kananan idanun ta na dan China "


wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " momy wlh Daddy cewa ya yi ki na da kananan idanu irin na yan china "


a tare matar nan da dattijon su ka zaro idanu sannan ya ce " kash , Wai ke ba ki iya rike sirri ba ? "


tsuke fuska matar nan ta yi ta na cewa " yanzu His excellency me idanu su ka yi maka " ta kai karshen cikin shagwaba kamar karamar yarinya


cikin sigar rarrashi His excellency ya ce mata " Haba My Twinkle ba abun da su ka yi min wassa ne fa na ke mata , kamar dai ba ki san halin yarinyar ki ba da son karawa miya gishiri , ai a haka na gani kuma na ce ina so , My first lady "


" His excellency na ce maka ka daina kira na da Twinkle , kai fa ka sauya min sunan nan kuma yanzu shi ne za ka ci gaba da kira na da hakan ni gaskia ba na so " ta na gama fadar haka ta mike ta fara takawa ta nufi stair ta Haye


da kallo ya rakata har sai da ta Haye sannan ya juyo ya kali Safa ya ce " momyn ki rigima gare ta wlh , ni ban ma san ya a ka yi na fada soyayyar ta ba da wasu kananan idanun ta kamar na yan china "


wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Daddy , momy fa ta fi ka kyau "


" oun na sani , ai kyawon ta ya na daya da ga cikin dalili na na auren ta "


" Da gaske Daddy ? Fadamin yadda a ka yi ku ka hadu da momy "


wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " shikenan bari na ba ki labari , a lokacin ina da shekara 28 haka ina a aiki a matsayin doctor , to sai mu ka tafi china wajen wani karin karatu , duk cikin Nigeria mu hudu ne kawai mu ka samu wannan damar , bayan mu je China , mun dan yi kwana biyu haka mun huta sai a ka dauke mu a ka kai mu wani babban Hospital wanda za mu fara aiki a cen , a ranar kuma momyn ta shigo Hospital din sun kawo mahaifin su ba shi da lafiya , Ta na sauke idanu sama na ta ji babu wanda ta ke so sama da ni "


ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Twinkle ta katse shi da cewa " I know , I have a good memory , but i don't think haka abun ya faru kamar yadda ka ke fada "


a hankali His excellency ya dago kai ya kale ta ta na sauko stair a hankali har ta karaso cikin parlourn ta dawo geffen shi ta zauna


murmushi mai dan sauti His excellency ya yi kafin ya ce " ki bari na gama ba ta nawa labarin sai ki ba ta naki "


" okay ci gaba " ta fada ta na daura kafa daya bisa daya ta zuba mishi ido


dawo da kallon shi ya yi kan Safa ya ce " ki na ji ko , Ta na sauke idanu sama na ta ji babu wanda ta ke so a duniya sama da ni , ni kuma a lokacin ban lura da ita ba ina kan aiki na , kuma cikin wani ikon Allah duk doctors din da ke cikin Hospital din , ni ne a ka bawa damar kula da mahaifin ta , sannu sannu na fara duba shi har mu ka share wajen one week ina tare da su amma ko so guda gaisuwa ba ta taba shiga tsakani na da ita , a haka har a la sallame su , kwana biyu bayan an sallama me su , na je wani Mall yin shopping , a nan na sake haduwa da ita , ita ta fara yi min magana ta gaishe ni ta ce min ita ce yarinyar majinyacin nan da na yi wa,magani , na ce mata eh na gane ta , da ga nan ta shiga yi min godiya na ran mahaifin ta da na ceto , na nuna mata ba komai duk cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login