Showing 12001 words to 15000 words out of 133773 words
wa momy maganar ta
Kallon mai sanye da atamfa Safa ta yi kafin ta ce " Djami ko za ki biyo mu mu tafi tare , da ga nan sai mu je ko da sayan ice cream ne "
Murmushi Djamila ta yi kafin ta ce " yes of course ina zuwa mana "
Ta na gama fadar haka wani saurayi ya yi musu sallama
Safa na ganin shi ta dauki books din ta ta ci gaba da karantawa ba tare da ta amsa mishi sallamar shi ba
Haoua da Djamila ne su ka amsa mishi sallamar shi kafin Haoua ta ce " Mansour ya ka ke kwana biyu na bar ganin ka cikin school din nan "
Dan murmushi saurayin da ta kira da Mansour yayi kafin ya ce " Wlh wani aiki ne , na tafi Lagos , jiya na dawo "
Hannun shi ya daura saman kafadar Djamila ya na fadin " Baby ko zan iya ganin ki minti daya "
Murmushi ta yi ta na jinjina mishi kai kafin ta kali Haoua ta ce " ina zuwa "
Da to ta amsa mata , sannan Djamila ta mike ta riko hannun Mansour su ka fice libraryn ba ki daya
Su na fita Safa ta sauko da book din ta ta ja dan siririn tsaki ta na kallon Haoua ta ce " why wannan yaron ke zowa inda muke , in magana ya ke son yi mata ba zai iya bari su hadu cen gidan su ba "
Yar karamar dariya Haoua ta yi kafin ta ce " haba ke ma pretty , Boyfriend din ta ne fa , kuma kin san ya kai kudin tambayar auren ta , so ki daina takura wa kan ki a kan su please , Idan Djamila ta ji wannan maganar ba za ta ji dadi ba "
Tsaki Safa ta yi kafin ta ce " boy din nan bai konta min a rai ba , ban san ko dan mi ba , kuma gaskia Djami ta fi karfin wannan dan yaro dube shi fa dikaΒ² bai kai 27 years ba "
Dariya Haoua ta yi har da bubuga table din tsakiyar su
Sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce " amma Allah pretty kin iya shirman banza , yanzu wannan za ki kala ki kira da dan yaro , hmmm na rantse ko yanzu a ka barki da shi cikin dakin guda , wlh ba zai kyale ki da sauki ba "
Matse gera Safa ta yi kafin ta ce " what do you mean ? "
" ina nufin wannan da ki ke kira yaro , ya isa ya yi miki ciki kuma ki haife mishi babyn shi lafya " Haoua ta fada cikin tsokana
" Allah ya kiyaye , wa ni , oun oun wlh ko maza sun kare a duniya ba zan kula wannan dirty boy " ta kai karshen ta na yamutse fuska
Dariya sosai Haoua ta sake yi kafin ta ce " ke dai Pretty, ba ki san abun da duniya ta tanadar miki ba , na ga allamun ki na yawwan kaskantar da maza "
" no Haoua ba kaskantar da su na ke ba , kamar akwai mazan da ya ke da kin gan su kin san ajin ku bai zo daya ba , yanzu dubi Djami da wannan yaron kin san ba su dace ba "
" yo ai Safa ba dacewar ce ba a ke kallo , in har su na son junan su minene matsalar , yanzu dubi Tarihin Annabi Mouhammad ( S.A.W ) da matar shi ta Farko Khadija , ta fa bashi shekaru , kuma ta fi shi arziki , akasi ma aiki ya ke a karkashin ta , amma ba ta duba hakan ba ta ce ta na son shi , su ka yi auren su cikin abincin Allah "
Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " kin yi Gaskia , dan kin san Tarihin soyayyar su na burge ni shi ya sa ki ke yawwan fada min haka " ta kai karshen ta na yi mata hararrar wassa
Yar dariya Haoua ta yi kafin su ci gaba da hirar su har Djamila ta dawo ta same su sai lokacin komawa class sannan su ka tashi su ka tafi a tare
[16/08 Γ 22:47] MEERAHπͺ·π©·:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH πββ€
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
πππππ
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
πππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE 5 π₯ β€
* UNITED KINGDOM ( LONDON )
Wani tanpasheshen office ne na glass , mai bala'in kyau da girma
Komai na cikin office din sai kyali ya ke kamar , yanzu a ka ciro kayan da ga cikin ledodin su
Tiles din wajen sai kyali ya ke kamar ka zuba ruwa ka sha , ya sha mopping ba kadan ba , kai a takaice kun san yadda manyaΒ²n office din kassashen waje su ke to wannan ma haka ya ke ba sai na fada muku ba
A hankali a ka turo kofar glass din
Wani kyakyawan matashi ne ya shigo office din , kan shi a sunkuye ya na duba wayar shi ya na sanye da wasu kaya blue da ga saman su wata blouse Fara irin ta doctor , ya na sanye da face mask Fari
Kai tsaye wajen Desk din shi ya nufa ya zauna saman lalawsan chair din wajen , ya na ci gaba da latsa wayar shi
Ya na a haka wata baturiya sanye da kaya irin na shi ta shigo amma ita ba ta sanye da blouse
Ta na shigowa ta nufi bakin desk din da sauri ta na fadin " Doctor akwai matsala , mara lafiyan da a ka ma theater jiya har yanzu bai farfado ba " ta fada da turanci
Slowly ya dago da kan shi ya sa hannu ya zame face mask din shi
Allahuma Barik , Gaskia matashin nan ya hadu , skin din shi fara da ita , amma ba fari sosai ba ta so ta dan yi chocolate , ya na da dara daren idanun farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma ash colour ce , ya na da dogon hanci mai kyau da dan karamin baki lips din shi pink colour ma su laushi kamar audiga , ya na da kontancen saje baki kirin , eyebrow din shi masu kyau a konce kamar shi ya zana su , ya na dogayen eyelashes sai su ka karawa dara daren idanun shi kyau , ya na da yar suma kadan amma ba sosai ba , dan a bayan keya kawai ya tsaya , gashin kan shi darck black ne har wani kyali ya ke da ga gani ka san ba kananan kudade a ke kashe mishi ba
Ya na da dan tsayi , ga kuma murdaden jiki kamar wanda ya samu horon kwararen soja , dan da ga gani bugu guda zai yi maka mai kyau lahira ta yi bako a shekaru zai yi 33 years haka
Dan guntun tsaki ya ja kafin ya ajiye wayar shi saman table din ya kali nurse din cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ya ce " kun duba bugun zuciyar shi " ya fada da turanci shi ma
" eh ta na bugawa amma alurar da a ka yi mishi , ya kamata a ce ta sake shi yanzu " ta fada cike da shaku
" LΓ©a , ki kontar da hankalin ba abun da zai same shi , ku dai ku tabatar da zuciyar shi ta na bugawa , zai farfado , ai dama alurar ta na kaiwa 24 hours so don't worry " ya fada cike da nitsuwa kafin ya sunkuyar da kan shi ya dauki wayar shi
" but doctor "
Daga mata hannu ya yi kafin ya ce " LΓ©a , please let me , wani aikin na ke yi a yanzu "
" okay sir " ta fada ta na sunkuyar da kai kafin ta juya ta fice ta ja mishi kofa
Ta na fita ya kai wayar shi a kunne a ce " sorry bro wlh wata nurse duk ta bi ta takura min "
A daya bangaran kuma sai da a ka dauki wajen good five minutes kafin na jiyo wata irin zazzakar sexy voice a na fadin " okay ! " a takaice cikin sanyin murya
Dan karamin murmushi doctor din ya yi kafin ya ce " Bro ya zancen tafiyar mu Nigeria , an yi wajen two months ina ma ka maganar an ma ka yi shiru "
Yanzu ma sai da a ka dauki dogon lokaci kafin a ce " next week ina da Tafiya Korea , so idan na dawo sai mu tafi " a na gama fadar haka a ka katse kiran
Duk maganar nan da su ke yi da turanci su ka yi ta
Doctor ko ya na jin an katse kiran ya sauko da wayar shi ya yi dan karamin murmushin geffen fuska kafin ya ce " hmm bro kenan , Allah ya sa idan mu ka je ka fada tarkon soyayya ko wannan miskilanci na ka zai rage "
Ya na gama fadar haka ya ajiye wayar shi saman table sannan ya mike ya nufi wata door ta glass cikin office din , ya na isa bakin kofar ta bude kan ta ya shiga ciki
Jim kadan ya fito sanye da Trouser black colour da T-shirt Cherry colour mai kyau
Ya na fitowa ko a ka turo kofar office din na shi , wani matashin shi ma ya shigo
Ya na sanye da jeans White colour da T-shirt navy blue ya na tafe ya na latsa wayar shi
Sai da ya ka tsakiyar office din sannan ya kashe wayar shi ya saka ta a aljihu ya dago kai dai'dai lokacin da doctor ya karaso wajen da ya ajiye wayar shi , shi ma ya dauka ya sa a aljihu
Sannan ya juyo ya kali matashin nan ya ce " Fares , kai ma tafiya za ka yi ? "
Gyada mishi kai Fares ya yi kafin ya ce " I'm really Tired to day , in samu dai wata babe ta yi min taussa "
Dariya doctor din ya yi kafin ya karaso ya dan buge shi a kafada sannan ya yi gaba zai fita office din ya na fadin " ai kan ka ne babe , ni don Allah wuce mu tafi "
Juyowa Fares ya yi ya bi bayan shi su ka fito office din sannan doctor din ya janyo kofar ya daura yatsar shi a finger print din , nan take kofar ta yi wata kara kamar an sa mata key sannan lamps din ciki su ka mutu
Doctor na ganin hakan ya juya su ka bar wajen shi da Fares
Su ka karaso kofar wani lift , su ka tsaya dan da allamun a kwaye mutane a ciki
Ba su dade da tsayuwar ba kofar ta budu wasu nurses biyu su ka fito
Su na ganin su tsaye su ka dan sunkuyar da kai su na fadin " good evening doctors "
Gyada musu kai kawai Fares da doctor su ka yi kafin su shiga cikin lift din
Su na shiga Kofar ta like su ka fara yin kassa
Kallon doctor Fares ya yi kafin ya ce " Amar , wai ya zancen yar Chinar nan ta ka , kwana biyu na ga ka bar min maganar ta " ya fada cikin zolaya
Dan karamin murmushi Amar ya yi kafin ya ce " ta na nan "
" wai har yanzu ba ka san sunan ta ba , yanzu in ka je ta ya za ka gano ta "
Murmushi geffen fuska Amar ya yi dai'dai lokacin da lift din ya tsaya kofar ta bude , ya sa kafa ya fice ya na fadin " na sani , kawai dai ba ni da niyar fada maka "
Dan zaro idanu Fares ya yi ya bi bayan shi da sauri ya na fadin " why , ko dan ba ka son in fadawa bro din ka ka fada soyayyar yarinyar da ba ka taba gani ba
" Tell him if you want, that is your probleme " ya fada mishi dai'dai lokacin da su ka fito ginin su ka nufi wani makeken parking space cike da tsadadun motoci
Tsaya wa ya yi ya kali Fares sannan ya ce " Fares ko na fada maka ba za ka gane ba , I don't how na fada soyayyar yarinyar da ban taba gani ba , dubi kuma irin tazarar da ke tsakanin mu da ita , amma ina ji cikin zuciya ta ita ce muradin rai na , kai ne shaida ban taba cewa ina son mace sai a kan ta , son da na ke yi mata ya wuce misali , kuma ni ma ban san yadda hakan ta faru ba , amma na ji a rai na she is my soulmate forever , ina me tabbatar maka sai na bawa zuciya ta abun da ta ke so ka jira ka gani "ya na gama fadar hakan ya yi gaba abun sa
Wajen wata dankareriar mota fara kal ya nufa ya bude kofar driver ya shiga ya bar wajen da gudu , Fares na nan tsaye ya na kallon shi har sai da ya hau titin , sannan shi ma nufi motar shi ya shiga ya bi bayan Amar da gudu
* Nigeria ( Kaduna )
* Safa π
Zaune su ke cikin office din Doctor Badariya Moussa , ita da Haoua da Djamila
Bayan sun Kamala gaissawa sai Safa ta ce " Dama na zo ne a kan wata alfarma da na ke nema wajen ku "
Doctor Badariya Moussa kwarariyar gynecologist a nan garin kaduna , mace ce mai farin jini dan ta na da kirki sosai , kowane wata sai ta bada kudi tallafi ga gidan marayu , mace ce mai dan jini a jika dan ba ta ida tsufa ba cen , a shekaru za ta kai 46 years haka , amma in ka gan ta kamar yar shekara 30 dan ta na kula da jikin ta sosai , ta na da kama jiki kamar yan mata ta ke
Dan murmushi Doctor ta yi kafin ta ce " in dai zubar da ciki ne ba ma yin sa a nan "
A tare Safa, Haoua da Djamila dariya ta kubce musu
Sannan Safa ta ce " no doctor mu ba wannan ya kawo mu ba "
Yar dariya doctor din ta yi ita ma kafin ta ce " wassa ne na ke yi muku , ina jin ki wata Alfarma ce ta kawo ki nan "
" yawwa , dama akwai wani shiri ne da na ke haskawa a kafafun yadda zumunta , so yanzu an dauke aiki a Tashar Tauraruwa , zan so ki ba ni dama mu tatauna a kan cututukan da su ka shafi mata a shirin da zan fara ranar Friday "
Jinjina kan ta Doctor ta yi kafin ta fara juya chair din ta kamar karamar yarinya ta ce " that's good , ina yi miki barka , babu damuwa , Allah ya kai mu , a ina ne za mu haska shirin "
Cike da zumudi Safa ta ce " a Abuja ne , karfe 10 na safe za mu yi daukar , sai misalin karfe 5 na yamma za a saki shirin "
" Abuja ! Abuja ! Abuja " Doctor ta fada a hankali ta na daga kan ta sama kamar mai tunani
Da sauri Safa ta marairaice fuska ta na fadin " please kar ku ce a'a , zan zo har gida na dauke ku , bayan mun Kamala kuma na medo ku , pleaseeeee "
Yar karamar dariya doctor ta yi kafin ta ce " ya isa haka ba sai kin yi min kuka ba , zan yi tunani a kai , duk shawarar da na yanke zan sanar da ke "
Da sauri Safa ta mike ta zagayo da gudu ta rungume doctor ta na fadin " Thank you , nagode nagode nagode sosai "
Da sauri Haoua ta ce " ke pretty kar ki karaya mata baya mana "
Da sauri Safa ta sake ta ja baya ta na murmushi ta ce " Sorry Doctor "
Murmushi doctor ita ma ta yi kafin ta ce " ji na ke kamar na san ki a wani wajen amma na kassa tunowa "
Da sauri Djamila ta ce " na san ku ma ku na kallon shirin ta na Abokiyar hira "
Girgiza kai doctor ta yi kafin ta ce " no , ba nan ba , na taba ganin ki a wani wajen , ko dai mai kama da ke ce na gani , tell me ba ki da Twins ne ? " ta tambaya cike da tantama
Girgiza mata kai Safa ta yi kafin ta ce " no ni kadai ce wajen momy na "
Daga kafadun ta doctor ta yi kafin ta ce " no wonder , amma gaskia ina ji a jiki na kamar na