Showing 54001 words to 57000 words out of 133773 words
Har ta nufi stair ta jiyo Muryar momy ta na amsa mata sallamar ta
Cak ta tsaya da tafiyar ta ta juyo ta kali momy kafin ta koma cikin parlourn ta zauna geffen momy
Ta zama momy ta ce mata " da ga ina ki ke haka "
" nowhere , na je wajen doctor Amar ne , tare da Snoopy ya tafi shi ne na je na kira shi "
" jiya ne su ka zo ko ni na ma manta , ya kamata na je na yi mishi barka da zuwa , rabo na da shi tun ya na da shekara hudu sai jiya da ya zo neman ki "
" what ? Momy ki na nufin kin san doctor Amar dama " Safa ta fada ta zaro idanu
Dawo da kallon ta momy ta yi kan Safa ta ce " ba d'an wajen kanwar mahaifiyar su Sami ba ne , ai tare su ka fara karatu shi da ......... " ba ta kai karshen maganar ta ba ta ga Safa ta tashi da gudu ta Haye stair
Da kallo momy ta raka ta har sai da ta Haye sannan ta meda kallon ta kan Tv din da ta ke kallo
Safa kuma ta na hawa kai tsaye bedroom din ta ta nufa , ta na shiga ta Haye bed din ta ta yi rub da ciki ta na kuka kassa kassa
Sai da ta dauki wajen ten minutes ta na kuka haka ba dalili kafin ta mike slowly ta nufi toilet ta shiga
Wanka ta yi sannan ta dauro da Alwalla dan lokacin sallat ya yi
Jim kadan ta fito daure da towel a kirjin ta , ta shiga dressing room , nan ma ba ta fi five minutes ba ta fito sanye da wata gown mara nauyi fara kal da wani hijab har kassa purple colour
Daddumar ta ta nufa ta hau ta tada sallar ta
Kamar dai kullum yau ma da ta Kamala sai da ta zauna karatun kur'ani har lokacin sallar isha ya zagayo ta tashi ta yi
Bayan ta gama duk sallolin ta , sai ta cire hijabin ta ta ajiye saman sofa sannan ta nufi bed din ta ta Haye ta konta ta kai hannu ta dauki remote ta kara gudun ac sannan ta kashe lamps din dakin ta janyo bargo ta rufe duk jikin ta har kai , ta karanto adu'ar barci ta lumshe idanun ta ba ta yi 30 minutes barci barawo ya yi gaba da ita
* WASHE GARI
Har wajen karfe 9 na safe , Safa ba ta farka da ga barcin ta ba , kuma momy ba ta tafi neman ta ba kawai ta sa kai ta fice ta tafi wajen aikin ta dan ta san kullum sai Safa ta riga ta fita shi ya sa ba ta tsaya neman ta ba
Ta na tsaka da barcin ta kawai sai ta ji wani mugun haske ya ziyarce ta
A hankali ta ware idanun ta kafin ta meda su da sauri da datse cikin wata yar siririyar murya ta ce " ke Balki rufe min Windows din nan "
" ba ita ba ce " ta jiyo Muryar shi ya na fada
A razane ta bude idanun ta ta fara bin dakin da kallo
Cen ta hango shi tsaye wajen Window ya nade hanayan shi a kirji ya na kallon ta , ashe shi ne ya janye curtain din ya bude Window din , ya shigo gidan nan ya janyo Snoopy su tafi wajen Rex sai ya ga har yanzu motar ta na cikin parking space , shi ne ya shigo ya wuce kai tsaye bedroom din ta nan ya gan ta konce
Bargon ta ta janyo ta rufe fuskar ta ta na fadin " please rufe haske ya yi min yawa "
Ba musu ya rufe Window din amma bai meda curtain din ba , sannan ya karaso bakin gadon ya tsaya ya na fadin " why har yanzu ba ki tashi ba , na zata kin tafi school. Ko ba ki da lectures yau "
Ba tare da ta fito da ga cikin bargon ta ba ta ce " ina da "
" kuma ki ke konce har yanzu , Oya wake up " ya fada ya na sa hannu ya janye duvet din ta
Da karfi ta sa hannayan ta duka biyu ta janyo duvet din ta na fadin " please let me , ba na jin jiki na "
Sakin duvet din ya yi ya na fadin " faduwa ta zo dai'dai da zama , ke da ki ke da doctor guda a gida , fada min me ya ke damun ki " ya kai karshen ya na zama bakin gadon
Juya mishi baya ta yi ta na fadin " i don't need your help , please let me "
" Baby , please wake up , tell me what's wrong with you ? "
Slowly ta juyo , ta janye duvet din ta ta dago kai ta kaleshi ta ce " minene ka ce ? "
" what's wrong with you ? " ya maimaita mata
Girgiza mishi kai tayi kafin ta ce " no ba shi kafin wannan "
Shiru ya yi na dan mintina ya na kallon ta slowly ya ce " baby ? "
Tsuke fuska ta yi kafin ta ce " kar ka sake kira na da wannan sunnan ko na fassa maka baki "
" okay ! Okay ! Na gane abun da ke damun ki , yanzu tashi ki shirya mu tafi shan ice cream tun da ba ki son zuwa school din "
Bai gama rufe bakin shi ba ta sauko da ga saman bed din da gudu ta shiga toilet
Da kallo ya raka ta ya na dan karamin murmushin
Sai da ya ga ta shiga toilet ta rufe kofar sannan ya tashi ya fice dakin , amma ba parlourn kassa ya sauka ba , a na sama ya tsaya ya zauna saman sofa ya daura kafa daya bisa daya ya ciro wayar shi ya fara latsawa
Ya dauki wajen good 50 minutes a haka , har sai da ya fara gajiya da jiran ta , kar a je te koma barci ta share shi
Dan karamin tsaki Amar ya yi kafin ya mike tsaye ya fara takawa ya nufi bedroom din ta
Bai kai ga yin taku hudu ba ya tsaya cak ya na kare mata kallo
A hankali ta ke fitowa da ga cikin bedroom din ta na sanye cikin wata shegiyar Gown mai mugun kyau pink colour mai zannen flowers red & green colour da ga sama ta na da sirarren hannu da wata belt fara kal da ga tsakiya gown din ta zauna mata sosai kamar a jikin ta a ka yi ta
Ta na dan yafo wani veil fari kal da ga sama, wannan karan ba ta yi Rowling din shi ba , ta gyara gashin ta , ta meda shi baya ta daure ta sako wasu dan siraren guda biyu sun zubo mata a geffen fuska
Kafafun ta kuma na sanye cikin wasu sneakers White colour su ma da wata yar bag fara , sai tashin fitinannan kamshi ta ke , gaskia ta yi kyau over
( kamar na sace ta na gudu ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ )
Tun da ta fito ya tsare ta da idanu babu ko kiftawa ya na saki wani cool murmushi , ji ya ke duk ta tafi da imanin shi
Sai da ta karaso gaban shi ta na ce mishi su tafi amma sam bai ji ta ba sai da ta kai mishi bugu a ciki
Wata yar siririyar kara ya saki ya na daura hannun shi saman ciki ya ce " why ? "
Hararrar shi ta yi kafin ba tare da ta ce mishi komai ba ta fara takawa a hankali ta yi gaba
Murmushi mai dan sauti ya yi kafin shi ma ya juya ya bi bayan ta su ka sauko stair din a tare
Kai tsaye harabar gidan su ka fito
Su na fitowa ko ta ga wata dankareriar mota fara kal an yi parking din ta dai'dai kofar fita gidan abun ya ba ta mamaki
Ta tsaya ta na karewa motar kallo ta jiyo Muryar Amar da ga bayan ta , ya na fadin " mu je ko ? "
Ba musu ta bi bayan shi su ka nufi wannan motar ,
Da kan shi ya bude mata kofar motar ya na ce mata bismillah
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta shiga cikin motar , ta na shiga ya rufe kofar ya zagayo da sauri geffen driver ya bude kofar ya shiga
Ya na shiga gateman da ke zaune saman chair ya na kallon su ya yi sauri ya bude musu gate din
Kunna motar Amar ya yi , sannan ya danna hancin motar saman titi ya bar gidan da mugun gudu
Sai da su ka bar unguwar sannan ya kale ta ya ce " ina mu ka yi dan ni ban san Garin nan ba "
" ba damuwa mu je zan gwada maka "
Da to ya amsa mata kai ya meda hankalin shi kan tukin shi
Kwatancen ta shiga yi mishi har su karaso restaurant din da ta ke yawwan zuwa ita da su Haoua
Bayan ya yi parking din motar a parking space ya yi sauri ya sauko ya zagayo ya bude mata kofar yanzu ma
Hararrar wassa ta yi mishi kassa kassa ta ce mishi " sai ka sa mutanan wajen nan sun lura da mu "
Mika matta hannun shi ya yi ya na fadin " i don't care "
Murmushi kadan ta yi kafin ta daura hannun ta saman na shi , sannan ta sauko da ga cikin motar ya meda kofar ya rufe , su ka nufi cikin restaurant din su na rike da hannun juna
Sun yi sa'a babu mutane dayawa a yanzu dan bai fi mutun 8 da su ka tardo cikin restaurant din ba
Wata table mai chair biyu su ka nufa a tare
Sai da su ka karaso sannan ya saki hannun ta ya janyo mata kujera , ba musu ta zauna saman chair din , shi kuma ya ja dayar chair ya zauna su na fuskantar juna
Su na zama wani server ya karaso table din su ya na tambayar su abun da za a kawo musu
Safa na shirin magana Amar ya riga ta ba da order din bowl din ice cream biyu daya ta chocolate daya kuma vanila , da to server ya amsa mishi kafin ya juya ya bar wajen
Ya na barin wajen ko wayar Amar ta fara ringing
Hannu ya sa cikin aljihu ya ciro wayar ta shi ya kali screen din wayar
Wani kyakyawan murmushi ya saki kafin ya sa hannu ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na fadin " Sai yau ka tuno da ni ko ? "
A daya bangaran kuma yar dariya Fares ya yi kafin ya ce " Sorry Doctor ka tafi ka bar ni da aiki ba dole ka ji ni shiru ba , anya ni ba zan biyo ka na dan huta ba "
Yar karamar dariya shi ma Amar ya yi kafin ya ce " no yi hakuri ka zauna ka kula ma na da Hospital ni ma ba zan jima ba "
" okay na ji na ba ka two weeks ka dawo ko ni na taho "
Da sauri Amar ya ce " haba guy ai ko one month Albarka , kar ka manta ni da Sasha mu ke tare ko yanzu ya gama aikin shi sai mu juyo "
" haba don Allah ? Yanzu da gaske Sasha ya na Nigeria , kam ! Kuma bai mutu ba har yanzu "
Katse shi Amar ya yi da cewa " ban son shirme ya mutu kamar ya , ko kai za ka zo ka kashe shi "
Yar karamar dariya Fares ya yi kafin ya ce " kar fa ka manta Nigeria ta na daya da ga cikin colony din US kuma US da RUSSIA babu jituwa a tsakanin su , ka san in a ka san wanene Assad ba karamar cakwakiya za a sha ba , ga shi kuma Nigeria temperature din su ta kai wajen 30 to 40 degree Celsius al'halin a RUSSIA temperature din su ba ta wuce 10 degree ba wani lokaci har negatif ce , ka na tunanin zai iya supporting ? "
" ni na ke supporting ? , inda ba zai iya ba , ba zai zo ba " Amar ya fada dai'dai lokacin da server ya dawo rike da tray dauke da bowl biyu na ice cream Ya ajiye daya gaban Safa dayan kuma gaban Amar kafin ya juya ya bar musu wajen
" okay haka dai ka ce ! Yanzu fada min ka samo abun da ka je nema " Fares ya tambaye shi ya na daga gera guda kamar ya na gaban shi
Satar kallon Safa Amar ya yi , ya ga hankalin ta na kan wayar ta sannan ya ce " eh na samo "
Cike da zumudi Fares ya ce " da gaske don Allah ta na ina , ya take , kun yi magana da ita "
Yanzu ma sai da ya kara satar kallon Safa , cikin Russian language ya ce mishi " Duk yadda ka ke tunani ta wuce haka nan , She is so beautiful and very cute , wani ikon Allah gidan da mu ka sauka ya na fuskantar na su , yanzu haka mu na tare , mun fito shan ice cream " ya na gama fadar haka ya ga Safa ta saki wani cool murmushi na dan second ta na ci gaba da latsa wayar ta
" Doctor ka ce min har ta shigo hannu , ka yi kokari ka dawo UK da ita tun wani bai kwace maka ita ba , tsaya ma , ka fada mata ka na son ta ? "
Shiru Amar ya yi na dan lokaci kafin ya ce " no ban fada mata ba "
Dan tsaki Fares ya yi kafin ya ce " Matsala ta da kai kenan , you are very Shy , I love you din ne ka kassa fada ma ta "
" i don't like that ka sani ko , ko a tunanin fadin hakan is so easy ? So ka ke na ce ma ta ina son ki , kuma tun ba yau ba na kamu da son ki , tun lokacin da ki ka fara posting videos din ki saman social media , accidently na fara kallon su har na ji na kamu da son ki , ko zuwa Nigeria kawai dan na gan ki ne , kai a tunanin ka za ta yarda "
" Allah ya sa ta na jin Russian , ta ji duk abun da ka fada min yanzu na ga yadda za ka yi " ya kai karshen ya na bushe wa da dariya
Dan tsaki Amar ya yi kafin ya ce " sai an jima ka fara damu na " ya na gama fadar haka ya sauko wayar shi ya katse kiran ba tare da ya jira amsar Fares ba
Ajiyar wayar saman table din ya yi kafin ya kali Safa ya ce " i'm sorry na kyale ki , wlh wani aboki na ne ya kira ya ji ko mun sauka lafya "
" Uhmmm " kawai ta fada mishi ba tare da ta janye idanun ta da ga saman wayar ta ba
Shiru shi ma ya yi ya tsaya ya na kallon ta , bai taba ice cream din shi ba har sai da ta gama sannan ya tura mata ta shi gaban ta ya na fadin " kara da wannan "
Kallon shi ta yi kafin ta ce " ba za ka sha ba ne "
Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no ba na sha sugar sosai "
" okay ! " ta fada a takaice ta na kara janyo bowl din gaban ta , ta fara sha ta ci gaba da latsa wayar ta
Shi kuma Amar ya koma ya jingina a bayan chair din ya nade hanayan shi a kirji ya zuba mata wadanan Ash eyes din na shi babu ko kiftawa
Ta na tsaka da shan ice cream din ta debo spoon za ta kai wa a baki , wannan dan siririn gashin da ta zubo a geffen fuskar ta , ya fito da ga baya kunnen ta ya nemi fadawa cikin ice cream din
Da ido ta kali gashin , ta na shirin ajiye wayar ta , ta ji hannun Amar ya janye ya meda mata shi bayan kunne
A dubu dari ta dago kai za ta kale shi , ai idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi dan shi ma ita ya ke kallo , sai su ka yi ido hudu
Nan take ta ji ta tsargu da kallon cikin idanun shi , duk sai ta ji ta kassa janye na ta idanun
Wani cool murmushi ya sakin mata , cikin wata zazzakar murya mai mugun dadi da ba ta taba jin yayi magana da ita ba ya ce " ya dai lafya ki na yi min irin wannan kallon kar ki cinye ni " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda
Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta yi sauri ta sunkuyar da kan ta , ta meda idanun ta kan wayar ta
Babu shiri ta ji saukar lalawsan lips din shi saman forehead din ta ya yi mata kiss
Nan take ta dauke lokaci guda ta kassa motsi
Sai da ya koma saman chair din shi ya zauna sannan slowly ta dan dago da kan ta ta kale shi
[09/09 à 19:59] MEERAH 🪷🩷:
💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫