Showing 111001 words to 114000 words out of 133773 words

Chapter 38 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9722

ba , na ji zafin haka , Ko da mu ke RUSSIA duk cikin mu Amar ya fi kyakyawar zuciya , ga shi yanzu ya mutu a kan fadan da ba nashi ba , gaskiya ban ji dadin haka ba " ya kai karshen cikin raunin murya


" ni ma ban ji dadin haka ba , na san irin son da Safa ke yi mishi yanzu a ka ce ba ya nan na san zuciyar ta za ta karaya , sun yi mishi kisan wulakancin da ko dabba ba za a a iya yi mata hakan ba , Aryan , Acid fa su ka watsa mishi a fuska , duk rabin fuskar shi sai da ya kone , amma kuma ba su kyale shi ba , ni kai na sai da zuciya ta ta karaya lokacin da na gan shi cikin wannan halin , amma wani abun mamaki sai da na kai su har likita , ya yi wa doctor magana a kan a sakawa Assad zuciyar shi , ya yi wa Uncle Musadeeq letter har biyu amma kuma bai mutu ba , kenan ba dan an cire mishi zuciyar shi ba , Assad ne yanzu zai mutu " Sami ya fada cikin sanyin murya da allamun abun da ya faru ya taba mishi zuciya


wani cool murmushi Marwan ya saki kafin ya ce " ba abun da Amar ba zai iya yi ba a kan Assad , haka zalika ba abun da Assad ba zai iya yi ba saboda Amar , haka su ka tasso , ina fatan ko a ina ya ke yanzu Allah ya sa ya huta , Zan yi kewar ka aboki na " ya fada kamar zai yi kuka


murmushi mai dan sauti Sami ya yi kafin ya ce " Batun fitar da ga nan kuma fa ? "


shi ma murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " tunda Puppy ba ta cikin hatsari a yanzu , kawai ka fitar da ni da ga nan "


wani kyawatencen murmushi Sami ya saki ya na fadin " are you sure ? you are ready ? ka shirya fada da Ali ? "


wani dan karamin murmushi geffen fuska Marwan ya saki kafin ya ce " na tambaye ka wani abu ? "


gyada mishi kai kawai Sami ya yi allamun eh
sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " me ya sa ka ke goyon baya na , Ali fa mahaifin ka ne amma ka ke taimaka min na dauki fansa a kan shi "


wani dan karamin murmushi Sami ya yi kafin ya ce " tabbas Ali shi ya haife ni , amma ba zan rufe ido ya cutar da mutane , ina goyon bayan ka saboda kai dan uwa na ne , kuma har ga Allah ban ji dadin abun da ya yi wa uncle Abdoul Karim ba , zan iya fada maka wani labari da ba ka san da shi ba ? "


cikin rudu Marwan ya ce mishi " wane labari kuma ? "


dan jinkirtawa Sami ya yi kafin ya ce " kafin mahaifiya ta ta rasu , ta fada min dalilin da ya sa Ali ya kashe Uncle Abdoul Karim , ba komai ba ne face Twinkle "


" momy ? " Marwan ya katse shi , ya na dan zaro idanu


gyada mishi kai Sami ya yi kafin ya ce " Eh , momy , Tun lokacin da ya gan ta ya kamu da son ta , sun sha samun sabani da momyna saboda Twinkle , har ya kai ya fara sa hannu ya na dukan ta , amma ba ta taba fadawa kowa abun da ke faruwa tsakanin su ba , kuma ko so guda ba ta taba nunawa Twinkle wani canjin saboda da ta san ba laifin ta ba ne , laifin Ali ne da ya kamu da soyayyar matar kannen shi , bayan Farida da Fadila sun cika shekara hudu , a lokacin ne ya fara shirye shiryen yadda zai yi ya kashe uncle Abdoul Karim dan ya mallake dukiyar shi ya kuma auri Twinkle , ashe a lokacin momy ta ji , kawai sai ta je ta fadawa Aziza ita ko ba ta san kansu guda da Ali , kawai Aziza ta zagayo ta fadawa Ali abun da momy ta fada mata , da kuma recording din da ke hannun momy na maganar da ya yi da abokan shi a kan shirin su wanda ta shirya gwadawa uncle Abdoul Karim , Aryan gaban ido na Ali ya sa hannu ya kashe momy da ciki a jikin ta , ko tausayin abun da ke cikin ta bai ji ba ya sa hannu da kan shi ya kashe ta , kuma babu wanda ya san wannan labarin da ga ni sai Allah sai shi Ali , sai kuma kai yanzu , ban so fada maka wannan labarin ba , amma dole yanzu ka sani , ina son ya biya abun da ya yi wa momyna , ka yi hakuri na so na yi anfani da kai ne dan daukar fansar momyna a kan Ali , saboda ni ba zan iya yin komai a kan shi ba , ba ni da wata huja da zan nuna a kama shi da kisan momy , shi ya sa na ke son ka fito , idan na gan shi a prison saboda kisan uncle Abdoul Karim zan iya rage radadin momyna da ya kashe min , har yanzu ina bakin cikin wannan ranar , kuma har yanzu ta kassa fita da ga cikin kwakwolwa ta " ya na gama fadar haka wasu hawaye ma su zafi su ka zubo mishi


da sauri ya kauda kai gefe ya na sa hannu ya goge hawayen shi
ya na a haka kawai ya ji hannun Marwan saman face din shi ya na goge mishi hawaye
a hankali Sami ya sauke ajiyar zuciya ba tare da ya juyo ba ya ce " ka yi hakuri , kawai dai na so yin anfani da wannan damar ce dan ganin an bawa Ali hukuncin abubuwan da aikata , hakan kuma ya na nufin yin anfani da kai , ka yi hakuri , i know , i was'nt be honest with you "


cikin nitsuwa Marwan ya katse shi da cewa " Sami , ni ka daina ba ni hakuri , na yi maka alkawari sai Ali ya biya a kan mutuwar Daddy , Amar da kuma ta momy , za mu ba shi hukuncin da ya dace da mutane irin su , marasa tsoron Allah , ma su son zuciya "


a hankali Sami ya juyo ya kali Marwan ya ce mishi " that's why na ke alfaharin kasancewa ta dan uwan ka "


wani murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya ce " ashe dama haka ka iya kuka ? ai ko Safa ba za ta yi irin wannan kukan ba , dubi don Allah sai ka ce wani karamin yaro "


wata yar karamar dariya Sami ya yi kafin ya ce " za ka fara maganar tsagar ka ko ? "


dariya shi ma Marwan ya yi kafin ya ce " ban rike ka ba tashi ka tafi "


mikewa Sami ya yi ya na fadin " shikenan zan tafi , dama dare ya yi ya kamata na koma gida , ka kula min da kan ka "


a hankali Marwan ya mike , su ka rungume juna kafin su yi sallama Sami ya fita
Marwan kuma ya koma cikin cell din shi zuciyar shi cike da farin cikin ba abun da ya samu Safa , wani bangaran kuma ya na jimamin mutuwar Amar






▪TWINKLE






a hankali ta ke sauko Stair , da ga gani kassan akwai abun da ke damun ta dan ga shi nan konce a saman face din ta


karasowa ta yi cikin parlourn , nan ta tardo Noor , Raïssa , Farida da Fadila su na zaune kowace rike da wayar ta ta na latsawa


sofar da Noor ke zaune ta nufa ta zauna geffen ta , ta na fadin " Noor , na ga wayar ki don Allah "


" okay momy " Ta fada cikin nitsuwa kafin ta mika mata wayar
a hankali Twinkle ta kai hannu ta karba ta fara latsawa
ta dan dauki lokaci a haka kafin ta kai wayar a kunne da allamun wani ta kira , amma sai a ka ce mata wanda ta kira wayar shi na kashe


sauko wayar ta yi ta sake saka numbar ta danna kira nan ma a ka ce mata wayar na kashe
sai da ta yi wajen kira har hudu amma wayar ta na a kashe


cikin sanyin murya Noor ta ce mata " momy wai wa ki ke ta kira haka ? ki na ji wayar a kashe ta ke "


" Noor , Safa ce na ke son kira , tun safe na ke jin gaba na na faduwa , shi ya sa na ke kiran ta na ji in ta na lafiya "


ba ta gama rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar Raïssa ta na cewa " Allah ya sa ma ta mutu "


a tare Farida da Fadila su ka bushe da dariya kafin Farida ta ce " ya wuce ta na tare da Amar , su na cen su na shan duniyar su "


cikin bacin rai Noor ta ce mata " ba dan ke ki na tafiya shan duniyar ki ba ya ke nufin kowa ma hakan ya ke , yan bakin ciki kawai to ba abun da ya same ta anniyar ku ta bi ku "


cikin bacin rai Farida ta mike ta nufi Noor ta daga hannu sama za ta mare ta
Cikin zafin nama Twinkle ta riko hannun ta , sannan ta tura ta baya har sai da ta nemi faduwa
a hankali ta mike ta na kallon ta ta ce " idan hannun ki ya taba ta , gidan sai ya yi mana kadan , mara kunya kawai , za ku tashi ku ba ni waje ko sai na saba muku ! "


a hankali Fadila ta mike ta karaso gaban ta ta tsaya ta na fadin " kin ga malama ba ki da ikon ba mu umarni a gidan nan yawwa , saboda ba gidan tsohon mij........"
ba ta kai karshen maganar ta ba kawai ta ji saukar mari Tas a kumatun ta


" idan ki ka bari na maimaita abun da na fada sai miki dukan mutuwa a cikin gidan nan " Twinkle ta fada cikin bada umarni , yau dai sun kai ta makura


da sauri Raïssa ta mike ta na fadin " kan uba , ke wa ya ba ki izinin marin ta ? lalle yau kin debo ruwan dafa kan ki cikin gidan nan , ke har kin isa , ko wanda ya haife mu ba kai ya sa hannu ya mare ta bare ke shara kawai "


wani dogon nunfashi Twinkle ta ja , ta na shirin magana Sami ya turo kofar parlourn ya shigo ya sallama
bin su da kallo ya fara yi ya na fadin " lafiya , ku ka yi tsatsaye ? " ya kai karshen ya na zama saman sofa one seater


kamar za ta yi kuka Fadila ta ce mishi " mari na wannan tsohuwar matar ta yi " ta fada ta na nuna Twinkle da ta koma ta zauna ta na ci gaba da latsa wayar Noor kamar ba a yi komai ba


" and so what dan ta mare ki ? ba momyn ki ba ce "


da sauri Farida ta katse shi da cewa " no wannan ba momyn mu ba ce , kawai matar Daddy ce , kuma ba ta da izinin sa hannu ta dake ta , kuma wlh sai na fadawa Daddy , Fadila wuce mu tafi " ta kai karshen ta na kama hannun Fadila su ka juya a tare su ka bar wajen






[27/09 à 17:55] MEERAH 🪷🩷:






💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫


( YAR JARIDA )













🕊💔( A heart touching love story & destiny ) 💔🕊












STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🌸








【THE ROYALTY LOVE 🕊🌸💕】








Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 :FREE BOOK


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ : PAID BOOK
















TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP POSTING ROOM


👇👇👇👇👇👇👇


https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054








DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK


👇👇👇👇👇👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i








DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite












BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM










___________________________________________


LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN , COMPLETE KUMA 400


GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE ⚘❤
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
👇👇👇👇
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank


IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
👇👇👇👇👇
Zain (Airtel)
08081129487


sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753


___________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊____________________













BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM















{ PAGE 33 🥀 ❤ }






















su na barin wajen Sami ya juyo ya kali Raïssa ya ce mata " me ki ke jira ke kuma ? , wuce ki tafi "


sai da ta juya ta harari Twinkle sama da kassa kafin ta ja wani siririn tsaki ta nufi stair ta Haye da sauri


da kallo Sami ya raka ta har sai da ta Haye sannan ya tasso da sauri ya dawo geffen Twinkle ya zauna murya kassa kassa ya ce mata " momy ki na ji ko ? ki kontar da hankalin ki ba abun da ya samu Safa , yanzu haka maganar da na ke miki sun tafi RUSSIA tare da familyn Amar "


cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " RUSSIA kuma ? me ta tafi yi a cen ? "


" momy ki kontar da hankalin ki zan fada miki abun da ya faru , amma ba yanzu , kawai zan so ki san ba abun da ya samu Safa , ta na nan cikin koshin lafya so don't worry "


wani dan karamin murmushi Twinkle ta sakin mishi kafin ta ce " shikenan , idan kun yi waya da ita ka ce ina gaishe ta "


dan karamin murmushi Sami ya yi mata kafin ya gyada mata kai kafin ya tashi ya nufi stair ya Haye
sai da ya Haye sannan Ta mikawa Noor wayar ta , ta tashi ta nufi stair ta Haye ta bar Noor nan zaune ta na faman latsa wayar ta









🥀🕊🥀🕊🥀🕊🥀🕊🥀🕊🥀🕊🥀🕊🥀🕊













▪AFTER ONE WEEK














▪KUJE PRISON












tsaye ya ke cikin cell din shi ya juyawa kofar baya , ya na sanye da Trouser White color da T-shirt navy blue , kafafun shi cikin wasu sneakers navy blue ma su mugun kyau


ya na a haka Bashir ya shigo ya na yi mishi Sallama
a hankali ya juyo ya na rike da kayan prison din shi , ya ninke su , da murmushi a face din shi ya karaso wajen Bashir ya mika mishi kayan ya na fadin " karbi kayan ku "


wani dan karamin murmushi Bashir ya saki kafin ya kai hannu ya karbi kayan ya na fadin " yanzu kenan tafiya za ka yi ka bar ni ? "


wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya raba ta geffen Bashir ya wuce ya na fadin " kar ka damu zan dinga kawo maka ziyara "


cike da zumudi Bashir ya ce " Da gaske Sir ? "
wata yar karamar dariya Marwan ya yi ya na kai hannu ya dafa shoulder din Bashir ya na cewa " wassa na ke , ai ni da dawowa prison sai a lahira idan akwai ta , wannan karan ma akasi ne a ka samu , amma duk lokacin da ka samu hutu ka dinga zuwa gida zan jira ka "


wani dan karamin murmushi Bashir ya yi kafin ya ce " na gode sosai Sir "
murmushi kawai Marwan ya yi mishi dai'dai lokacin da ya iso wajen fita prison din
nan wasu sojoji su ka tsayar da shi
su ka ce ya sa hannu cikin wasu takardu , sai da ya dauki takardun daya bayan daya ya karanta su sannan ya sa hannu


cikin zolaya daya da ga cikin su ya ce " Sir , mu na jiran dawowar ku "
hararrar wassa Marwan ya yi mishi kafin ya ce " dawowa ina ? , sai dai in da karfi za ku zuwa ku dauko ni "


a tare sojojin su ka yi dariya da ga nan su ka yi mishi sallama , su na yi mishi addu'a
da ga haka ya sa hannu cikin takardun ya yi musu sallama shi ma ya yi musu godiya da karamawar da su ka yi mishi da ga haka ya juya ya fito prison din


ya na fitowa ya daga kai sama ya lumshe idanun shi ya saki wani cool murmushi murya kassa kassa ya ce " Freedom " da ga haka ya ja wani dogon nunfashi ya na saukewa a hankali


kamar da ga sama ya ji Bashir ya rungume shi ta baya ya na fadin " zan yi kewar ku sosai sir "


a hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login