Showing 18001 words to 21000 words out of 133773 words
ta ba
Mikewa tsaye momy ta yi ta nufi stair ta na fadin " ni na tafi , in ki na nema na ina bedroom "
Ko dago kai Safa ba ta yi ba , har sai da momy ta Haye war ta
Ajiye wayar ta gefe ta yi kafin ta mike ta nufi dining room ta shiga kitchen
Jim kadan ta fito rike da tray da plate din jollof rice da soyayyar kaza , sai glass biyu guda na ruwa guda na juice
Table din tsakiyar falon ta nufa ta ajiye shi sama sannan ta tura table din gaban sofar ta , ta mike ta juya ta nufi Tv ta dauki remote ta kunna ta sannan ta dawo rike remote din
Ta zauna saman sofa sannan ta dauki spoon ta fara cin abincin , ta na danna remove din ta na son ta saka Film ta kala
Ta na tsaka da hakan ta jiyo wayar ta ta fara ruri allamun shigowar sako
Da farko ta so ta kyale amma sai ta kai hannu ta duba screen din ta ga an turo mata γ Hi γ
Da wata bakuwar number , ga shi kuma number din ba ta Nigeria ba ce
Cike da shakku ta dauki wayar ta meda da γ Hi γita ma
Sannan ta ajiye wayar ta ci gaba da cin abincin ta ta na kallon Tv din ta
Ta dauki wajen good five minutes kafin a yi mata reply
Hannu ta kai ta dauki wayar ta karanto sakon kamar haka * How are you , and your day ? *
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta yi reply da * Fine , what about you ? *
Wannan karan ta na turawa a ka yi mata reply da * Fine Thanks For asking π *
* Okay , ko zan iya sannin da wa na ke magana * ta na gama rubuta hakan ta ajiye wayar ta geffen ta ta ci gaba da cin abincin ta
Wajen two minutes a dauka kafin a yi reply amma ba ta duba ba , ta ci gaba da cin abincin ta
Sai da ta Kamala , ta dauki ruwa ta sha , sannan ta dauki glass din juice ta ajiye saman table ta dauki tray din , ta mike ta nufi dining room ta wuce kitchen ta ajiye sannan ta fito
Ta na dawo ta zauna saman sofa ta mike kafafun ta saman table , ta kai hannu ta dauki glass din juice ta kai bakin ta ta na sha ta na kallon Tv
Cen ta jiyo wayar ta na ruri allamun shigowar sako
Ba tare da ta kali wayar ba ta kai hannu ta dauke ta , ta kawo saitin fuskar ta sannan ta karanto sakon kamar haka * Ba zan iya fada miki suna na yanzu ba , but ni dai babban masoyin ki ne , ina yawwan kallon shirin ki a tiktok , Instagram shi ya sa na yi kokarin samo number din ki kawai dan na fada miki abun da ke zuciya ta *
Sannan ta karanto na biyun shi ma * please ki amsa min mana , kar ki ji tsoro wlh mutun ne ni ba aljani ba π₯Ίπ₯Ί *
Yar karamar dariya ta yi dan fa maganar shi ta karshe ta ba ta dariya wai mutum ne ba aljani ba
* ba karamin abu zai ba ni tsoro , nagode da irin kwarin guyiwar da ku ke ba ni , ina jin dadin hakan sosai * ta tura mishi ta na murmushi
* okay nagode sosai , shin ko zan iya sannin sunnan ki , pleaseeeee π₯Ίπ₯Ί *
* My name is Safa π *
* just Safa ? *
* yes, just Safa , what is your name too ? *
* sorry , i can't tell you ππ *
* why ? , are you a criminal , a spy , or a celebrity ? *
* All π
*
* All ? π³π³π³ *
* yes All ππ kyawo na ne ya sa na zama Criminal , Dan leken asirin lafiyar ku ne ni , sannan kuma celebrity saboda kowa ya san ni , ko ke na san kin san ni π *
Ba ta san lokacin da ta bushe da dariya jin abun da ya ce
Sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta mishi reply da * wow sannu ko , duka kai kadai , seriously tell me your name now *
* okay my name is Musadeeq πΉ*
* okay Mister Musadeeq , Good night , lokacin barci na ya yi *
* okay Good night miss Safa β€ please can we keep contact π₯Ίπ*
* no problem π*
* Thanks π *
* Never mind *
* bye *
* bye *
Ta na rubuta mishi text na karshe ta ajiye wayar ta gefe ta ci gaba da kallon film din ta ta na shan juice din ta
Sai da ta kai wajen karfe 12 na dare ta na kallon film kafin ta kashe tv din ta dauki wayar ta ta koma bedroom din ta
Ko da ta koma ba ta konta kai tsaye ba , sai ta shiga ta yi wanka ta fito ta shirya cikin kayan barcin ta pink colour , ta shafa wasu lotion din ta , sannan ta Haye gadon ta ta konta ba tare da ta kashe wutar dakin ba, ba jimawa barci ya dauke ta
* ABUJA ( KUJE PRISON )
" Marwan Abdoul Karim , ka yi bako " wani soja ne tsaye bakin wata cell ya na kwallawa saurayin da ke cikin cell din kira , ba ka iya ganin komai da ga cikin cell saboda dare ne ga shi kuma wajen ba wasu lamps ba a dakwai
A hankali saurayin ya sauko da kafafun shi , ya na dan lumshe idanun shi allamun barci ma ya ke
Slowly ya bude bakin shi ya ce " wanene kuma ke nema na cikin wannan uban daren ? " ya fada kassa kassa yadda shi kadai ya ji abin da ya ce
Mikewa tsaye ya yi kafin ya tako a hankali ya fito cell din ya yi gaba, sojan na biye da bayan shi
Dakin da a ke kawo ziyara ya kai shi , sannan ya zaunar da shi saman chair , ya koma bayan shi ya tsaya ya na nade hanayan shi a kirji
Duk da wajen ba wani haske a dakwai sosai ba amma na samu damar ganin saurayin
Fari ne kal kamar ka taba jini ya fito , ya na da kyau kamar shi ya yi kan shi , ya na da yan kananan idanu irin na yan china farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma ash colour ce mai bala'in kyau , ya na da dan karamin baki , lips din shi pink colour duk da a bushe su ke , ya na da kwantacen saje a gefe da gefen fuskar shi , ga wani lalawsan black curly hair ya zubo mishi har tsakiyar baya , sai wasu yan sirarren da su ka zubo mishi a fuska , ya na da murdaden jiki gaskia , ga fafadan kirji Masha Allah , a shekaru zai kai 29 to 30 years wannan ga Dukan allamu chinesse ne , dan sam bai yi kama da Nigerian ba
Ya na sanye da wasu kaya Orange irin na yan prison , amma a wanke su ke fess fess , yanayin jikin shi ma ya nuna ko cikin prison din wannan ya na shan dadin shi dan babu datti ko kadan a jikin shi , sai bala'in kyau
A hankali ya juya kai ya kali sojan da ke tsaye bayan shi ya ce " ni fa barci na ke ji kun kawo ni nan kun tseda ni "
Dan karamin murmushi sojan ya yi kafin ya ce " sorry sir , ka jira ya na nan zuwa "
Dan karamin tsaki Marwan ya ja kafin ya kauda kan shi gefe , dai'dai lokacin da wani mutun sanye da wata jallabiya fara ya shigo ya na sallama
Karasowa ya yi ya zauna saman chair din da ta ke fuskantar ta Marwan
Ba ka iya ganin komai na face din shi sai idanun shi dan ya na sanye da face mask baki ga wajen kuma ba wani haske gare shi ba
TO FA YANZU WASSAN ZAI FARA
NA TAFI YIN BARCI GASKIA π₯±π₯±π₯±π₯±π₯±π₯±
[19/08 Γ 20:17] null:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE 7 π₯ β€
Marwan na ganin ya saki wani makirin murmushi ya koma ya konta a jikin chair din ya na kai hannu ya nade gashin kan shi a baya
Kallon dattijon nan cikin ido ya yi ya na murmushi ya ce " Gaskia yau da kafar dama na tashi , Ali Abdourahman ne da kan shi ya zo ga ni na cikin wannan daren "
" kai Marwan , dan ba ka da kunya sunan nawa kai tsaye za ka kira shi kar ka manta ko ni wanene " Dattijon da ya kira da Ali ya fada
Matsowa Marwan ya yi ya daura hanayan shi biyu saman table din tsakiyar su ya na kallon shi cikin ido ya ce " na fada Ali Abdourahman , me za ka yi , na san sarai ko kai wanene , maciya amana kawai , inda na san kai da ba zan fito ba " ya kai karshen ya jan tsaki
" kar ka manta inda ka ke Marwan , ka San abun da za ka fada min , ka San wanda ya turo ka nan "
Dariya Marwan ya yi kafin ya koma ya jingina a bayan chair din
Sai da ya ida dariyar shi sannan ya ce " oh na san inda na ke , kai ma kar ka manta inda ka ke , kar manta arzikin wanene ka ke ci , kar ka manta gidan wanene ka ke ciki , kar ka manta ba ni kadai ne ba Abdoul Karim a duniyar nan , dayan ya na waje , kamar ka kashe maciji ne ba ka sare kan shi ba , gaskiyar da ka ke boyewa tabass za ta fito wata rana "
Cikin tsawa Ali ya katse shi da cewa " kai Marwan ka San abun da za ka fada min , kar ka manta ni ne silar shigowar ka wannan wajen , dayan Abdoul Karim da ka ke cewa ya na waje , me ya isa ya yi , ba abun da ya isa ya yi , kuma shi ma sai na kawo karshen shi kamar yadda na kawo karshen ka "
Mikewa tsaye Marwan ya yi kafin ya ce " ka ga malam idan ka ida cika bakin na ka za ka iya tafiya please , barci na ke ji wlh , ka zo ka cika min kunnuwa da surutun banza , no sens kawai "
A dubu dari Ali ya mike cikin tsawa ya kali Marwan ya ce " kai Marwan ni ka ke ce ma no sens , wlh sai na ga bayan ka yadda na ga na mahaifin ku , wlh ba za ka bar prison din nan da rai , sai dai gawar ka ta fita "
Kallon sama da kassa Marwan ya yi mishi kafin ya ce " mu da Allah mu ka dogara ba da mutun ba , Ali idan ka isa kamar yadda ka ce ka sa gawa ta ta bar prison din nan gobe , ni kuma na yi maka alkawari duk ranar da ka bari na fita prison din nan a raye , ka tabbata to kai za ka shiga cikin kassa , dan prison ta yi maka kadan , shari'ar ubangiji kadai ta kamace ka " ya na gama fadar haka ya yi sojan nan na biye da bayan shi
Cikin zafin zuciya Ali ya shiga daga murya ya na fadin " idan ka isa ka dawo nan ka kashe ni , wlh sai na ga bayan ahalin ka ba ki daya , sai na ga bayan ahalin Abdoul Karim "
Sai surutan shi ya ke yi shi kadai
Marwan ya jin shi amma ya ki kula mishi ya ci gaba da tafiyar shi , sai da ya ga ba abun bauta sai Allah , ya sa kafa ya bar dakin ya na huci kamar zaki
Bangaran Marwan kuma sai da su ka je bakin cell din shi ya shiga sannan sojan nan ya ce " Sir , me ya sa ba za ka meda karar nan kotu ba, tun da kassan ba ka da laifi " ya kai karshen ya na jan bar ya rufe dakin da key
Rike bar din Marwan ya yi ya na murmushi ya ce " Bachir , kar ka damu , wanda zai fitar da ni da ga wajen nan ya na nan zuwa "
Murmushi Bachir ya yi shi ma kafin ya ce " Sir wajen shekaru sama da goma ka na cikin wannan gidan kuma kullum maganar ka daya ce , amma har yanzu wanda zai fitar da kai bai zo ba , shin wanene ma wannan ? "
" hmmm za ka san shi nan gaba , ina ji a jiki na zai zo gani na cikin wannan satin in sha Allah , kuma na San ba zai bari na ci gaba da zama a nan ba , you know why ? "
Girgiza mishi kai Bachir ya yi allamun a'a
Murmushi Marwan ya yi ya na kai hannun shi ya dan bubuga kafadar Bachir kafin ya janye hannun shi ya juya ya na fadin " good night barci na ke ji " ya kai karshen ya Hayewa saman gadon shi ya konta
Murmushi shi ma Bachir ya yi sannan ya ce " good night sir "
Har ya yi gaba , ya dawo ya tsaya bakin kofar cell din shi ya na gadi , dan duk cikin jail don nan babu wanda Bachir ke so da girmamawa kamar Marwan , ko boss din su ba ya girmama shi kamar yadda ya ke ganin girman Marwan duk da shekara daya kawai ya ba shi , amma ya na bala'in son shi har cikin zuciyar shi , shi ya sa ya tsaya ya na gadin shi , dan bayan magaganun da Ali ya fada ya na tsoron ya turo wani dan ya kashe shi
Bangaran Ali kuma ya na fitowa dakin ya nufi hanyar barin prison din
Nan bakin kofar ya tsaya ya na magana da wani sojan
Cikin girmamawa sojan ya ce " sorry sir , ba zan iya abun da ka ke so ba , Sir Marwan ya na karkashin kulawar shugaban kassa da kansa dan ko ciwon kai ya yi , manya doctor ke baro Hospital din su dan su zo su duba shi , na san duk wanda ya yi kokarin taba shi ba zai kwana da rai ba , dan ko sir Marwan bai kashe shi ba wajen ceton ran shi ba , to zai fuskanci hukun shi da ga wajen shugaban kassa "
" One hundred millions na ce za ni ba ka , kawai kashe min shi na ke son ka yi , ka ce attacking din ka ya yi shi ne ka karre kan ka "
Murmushi sojan ya yi kafin ya ce " sorry sir , na kashe mutane dayawa a filin yaki amma ban taba kashe mutun ba saboda kudi , kuma ba zan fara ba yau " ya na kai karshen maganar shi ya raba ta geffen Ali ya wucewar shi ya koma bakin aikin shi
Dan takaici da bacin rai Ali ji ya yi kamar ya koma ya shake Marwan da wannan sojan baki daya ma
Amma babu yanda ya iya haka ya hakura ya shiga motar shi ya tada ta ya bar wajen rai cike da bakin ciki
KADUNA
Safa π
Zaune su ke cikin library ita da Haoua da Djamila , dan sun fi zama a cen lokacin da ba su da lectures , su na hirar su , su na karatu
Su na a haka Safa ta mike ta na fadin " Zan je cafeteria , kishi na ke ji wlh "
Da sauri Haoua ta ce mata " zauna bara na kawo mana drinks " ta kai karshen ta na mikewa
Mikewa Djamila ta yi ita ma ta na fadin " tsaya min mu tafi na taya ki daukowa " ta kai karshen ta na bin bayan Haoua su ka bar Safa ita kadai ta na ci gaba da karanta book din ta
Ta dan jima a haka kafin ta ji a zabce mata book din ta ta sama
A dubu dari ta dago kai ta na kallon shi
Wani makirin murmushi ya sakin mata kafin ya ce " kin ji tsoro ne ? "
Hararrar