Showing 123001 words to 126000 words out of 133773 words
ka manta ba shi kadai ya ke aikin nan ba "
wani dan karamin murmushi Marwan ya saki kafin ya nunawa Sami screen din wayar shi
cikin rudu Sami ke kallon screen din kafin ya ce " su wanene wannan ? "
a hankali Marwan ya mike ya saka wayar shi cikin aljihu ya na fuskantar Sami ya ce " iyalin barister Habib ne , zan sa a dauko su a boye min su , da su zan yi anfani dan ganin dukiyar mahaifina ta dawo gare ni , batun Ali kuma ba zai iya barin gidan nan ba " ya kai karshen dai'dai lokacin da ya karaso bakin Window
a rude Sami ya ce mishi " ba fa dan ka ce mishi ba zai sake fita , hakan na nufin zai zauna cikin gidan kamar yadda ka ce , sannan kuma zai iya yi musu waya "
cikin nitsuwa Marwan ya katse shi da cewa " Sami , wai yaushe rabon ka da ka fita harabar gidan nan ? "
" ina ga wajen sallar Magriba , me ya faru ne ? " Sami ya fada cikin rudun wannan tambayar Da Marwan ya yi mishi
wani dan karamin murmushi Marwan ya saki kafin ya ce " ya kamata ka zo ka ga abun da ke faruwa " ya kai karshen ya na nade hanayan shi a kirji
ba musu Sami ya tasso ya karaso bakin Window din , sai da ya karewa Marwan kallon kafin ya juya ya kalli cikin gidan
[03/10 Γ 07:45] MEERAH πͺ·π©·:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
ππ( A heart touching love story & destiny ) ππ
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ππΈ
γTHE ROYALTY LOVE ππΈπγ
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ :FREE BOOK
β€β EXILED PRINCE ββ€ : PAID BOOK
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
ππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP POSTING ROOM
πππππππ
https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054
DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
______________________________________
LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN , COMPLETE KUMA 400
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN β€βEXILED PRINCE ββ€
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
ππππ
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πππππ
Zain (Airtel)
08081129487
sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753
_____________________________________
ο½ PAGE 36 π₯ β€ ο½
ba musu Sami ya tasso ya karaso bakin Window din , sai da ya karewa Marwan kallon kafin ya juya ya kalli cikin gidan
nan ya ga wasu jibga jibgan sojoji cikin fararen kaya cike da harabar gidan sai kai kawo su ke yi kowane rike da hannayan shi a baya
a razane Sami ya juyo ya kalli Marwan da ke ta faman sakin murmushi ya ce " Aryan su waye wadanan ? "
kai tsaye Marwan ya ce mishi " Sojojin Assad ne , bayan Sallar Magriba su ka shigo gidan nan , da ga yanzu babu wanda zai iya barin gidan nan ba tare da izini na ba , duk wasu motocin gidan nan sai a ka saka musu tracker , duba wayar ka ka gani babu service ko ? "
da sauri Sami ya kai hannu cikin aljihun shi ya fido wayar shi ya na kallon screen din , ban ya tabbatar da Eh babu Service
wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya " barka da shigowa Prison din Marwan Abdoul Karim "
wasu yawu Sami ya hadiye ya na kallon Marwan , a hankali ya bude baki ya ce " ni fa ban gane ba , please explain me "
murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya ce " ni na saka Assad ya cire phone signal din gidan nan baki daya , ba za ku iya kira ba , haka zalika ba wanda zai iya kiran ku , wadanan sojojin da ka ke gani umarni na kadai su ke bi , kuma na ce musu kar su bar kowa ya shigo gidan nan , haka kar su bar kowa ya fita gidan nan ba tare da izini na ba , sai na bawa Ali azabar da ta fi ta prison , ba zai sake saka kafa a waje ba , ko da harabar gidan nan ce " ya kai karshen ya na bushewa da dariya
shi dai Sami kallon Shi kawai ya ke , lalle Marwan ya cika tantiri , duk yau din nan ya fito prison amma har ya shirya wannan tubbun , gaskiya nan Ali ba ka da hanyar tsira , ga Marwan da Sami sun hade maka kai , ga kuma uwa uba ogan namu a gefe lokaci kawai ya ke jira ya diro maka
sai da Marwan ya Kamala dariyar shi sannan ya ja wani dogon nunfashi ya na cewa " wuce mu tafi ice cream na ke so " ya fada ya na juyawa ya fara takawa ya nufi kofar fita
da sauri shi ma Sami ya juya ya bi bayan shi su ka fito tare
kai tsaye gidan su ka baro , cikin motar Sami
βͺRUSSIA ( MASCOW )
a hankali ta ke Sauko stair din gidan , ta na sanye da wata gown pink color mai mugun kyau har , ta yafa veil din ta shi ma pink color
ta sauko stair din Fatma ta fito da ga cikin kitchen ta na rike da tray , dauke da wani farin Mug a sama sai tiriri ya ke da allamun coffee ne a ciki
Fatma na ganin ta ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " yawwa Safa , don Allah ko za ki kai wa mai gidan naki coffee din shi "
da murmushi a face din ta , ta karaso wajen Fatma , ta sa hannu ta karbi tray din murya kassa kassa ta ce " a ina ya ke momy ? "
" Pool " Fatma ta fada a takaice ta na juyawa ta koma kitchen
a hankali Safa ta daga kafa ta nufi kofar fita parlourn ta fito
harabar gidan ta na mugun girma , a takaice dai unguwa guda ce gidan , cike ta ke da wasu jibga jibgan sojojin cikin kaki din su ko wane rike da jibgegiyar gun , fuskokinsu a daure tamau kamar hadari , sai kai kawo su ke yi a cikin habar gidan
cen na hango wasu building guda hudu biyu na fuskantar juna biyu na fuskantar juna , an yi musu wata yar karamar kariya da ga gaba da flowers kamar irin gidajen nan na haya , building din duk two floors ne ma su girma , sai dai part din da Safa ta fito a ciki ya fi su dukka girma
a hankali ta ke tafiyar ta hannun ta rike da tray
geffen dama ta bi ta fara tafiya kafin ta yi kwana
nan na ga wani katon garden , cike da ciyayi har da bishiyoyi gwanin burgewa
cen nesa kadan da garden din na hango wata Swimming pool mai girma zagaye da wasu chair ta ko'ina , kowace chair akwai wata yar umbrella a saman ta sai yar table da ga gefe , chair din sun kai wajen su goma
cen na hango Assad cikin ruwan nan , babu ko riga a jikin shi , wannan kakarfar surar jikin shi ta fito , ya daure gashin shi a baya , dan ya juyawa hanyar baya
Safa na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta ci gaba da tafiyar ta cikin nitsuwa
sai da ta dauki wajen one minute kafin ta karaso bakin pool din nan ta tsaya ta na sallama
ba tare da ya juyo ba ya amsa mata sallamar ta cen kassan makoshi
" na kawo maka coffee " ta fada ta zubewa saman guyiwowin ta bakin pool din ta ajiye tray din gaban ta sannan ta ida a zama a wajen
a hankali Assad ya yi baya kafin ya juyo , wani abun mamaki kwayar idanun shi duk green ce , sai ka kare mishi kallo da kyau za ka lura kamar ba sa kama da allamun contact lens ne ya saka
a hankali ya karaso wajen Safa ya kai hannu ya dauki Mug din ba tare da ya ce mata komai ba ya juya zai bar wajenta
da sauri ta sa hannu cikin ruwan ta riko hannun shi ta na fadin " ina kuma za ka je , ba za ka tsaya tare da ni ? "
" sake min hannu " ya fada ya na matse gera
nan take yanayin face din ta ya sauya , ba musu ta sake mishi sannu ta na fadin " me ya sa ka ke gudu na ? idan wani laifi na yi maka ka fada min mana don Allah , wlh ba na jin dadin abun da ka ke min General , ni fa matar ka ce amma ba a daki daya mu ke kwana ba , Daddy ya ce min accident na yi satin da ya wuce , kuma ba zan iya tuna rayuwar mu ta baya , amma ni ina jin son da na ke yi maka cikin zuciyata , why za ka sauya min lokaci guda ? shi ne auren soyayyar da mu ka yi kenan ? " ta fada cike da bacin rai
shi dai shiru kawai ya yi ya na kallon ta da allamun ranta a bace ya ke
har ya bude baki zai yi magana ta daga mishi hannu ta na fadin " ba na son jin abun da za ka fada min , ka sani ba na da cikakiyar lafiya , amma hakan bai sa ka zauna ka na kula da ni yadda ya dace , asali ma ko kallon kirki ba ka tsaya ka min , idan ka daina so na ka fada min ko zan rage radadin da zuciya ta ke yi........ "
ba ta kai karshen maganar ta ba sakamakon sarawar da kan ta ya yi mata har sai da ta kai hannu ta dafe shi ta na lumshe idanun ta
da sauri Assad ya dawo bakin pool din , ya ajiye Mug din hannun shi gefe sannan ya riko hannun ta ya na fadin " are you okay ? "
da sauri ta kwace hannun ta ta na fadin " ni kyale ni "
" kin sha maganin ki ? " ya tambayeta cikin sanyin murya
a hankali ta sakin mishi wani marayen kuka ta na fadin " ban sani ba , ka daina nuna damuwa a kai na , na san ba ka damu da ni ba , ka kyale ni ko mutuwa ce ma na mutu ka huta " ta kai karshen ta na mikewa tsaye
amma ko taku biyu ba ta yi ba wani jiri ya debe ta kawai ta fadi a kassa ta na kuka
ta na faduwa ya ji zuciyar shi ta yi mugun bugawa har sai da ya dafe saitin zuciyar shi da hannu ya na karanto kalmar shahada kafin ya ja wani dogon nunfashi ya na sanye ajiyar zuciya
a hankali ya juya ya nufi wajen fita pool din ya fito da ga shi sai short
kai tsaye wajen chair din nan ya nufa ya kai hannu ya dauki wata bathrobe da ke ajiye a sama ya saka ta
sannan ya juya ya nufi Safa da ke ta faman kuka kamar wata baby , ya dauke ta
maimakon ya nufi hanyar komawa gidan kawai sai na ga ya zagayo ta bayan ginin ya nufi wata yar door ta glass , ya na isa kofar ta bude kan ta , ya daga kafa ya shiga sannan ya juyo
nan take kofar ta rufe , kamar lift ta yi sama da su
ko ten second ba a yi ba lift din ya tsaya kofar ta bude , sai ga su cikin dressing room mai mugun girma wannan sai ya yi wa wata amaryar parlour
bai tsaya a dressing room din ba ya sa kafa ya fito bedroom din shi
kai tsaye bed din shi ya nufa ya zauna da ita a saman , sannan ya zauna bakin gadon ya kai hannu wajen bedside drawer ya bude box na farko ya fido A box ya bude ya fiddo wasu drug guda uku sannan ya rufe A box din ya mayar da ita cikin bedside drawer ya rufe
a hankali ya mike ya nufi yar table din da ke gaban sofar dakin ya kai hannu ya dauki jug din da ke saman ta , ya zuba ruwa a cikin glass , sannan ya dauki glass din ya dawo bakin gadon ya zauna ya na mika mata drugs din da glass din ruwan
ba musu ta kai hannu ta karba , ta kai drug din a baki ta hadiye sannan ta kora da ruwa
sai da ta sha wajen rabin ruwan sannan ta sauko glass din ta ajiye saman bedside drawer
ya na ganin haka ya mike zai bar wajen
da sauri ta riko hannun shi kamar za ta yi kuka ta ce " kar ka tafi ka bar ni please , wai me na yi maka ne da ke gudu na haka ? "
cikin nitsuwar nan tashi ya ce " please ki daina kukan nan , ba ki san kukan ki na yi wa zuciyata illa ba ? I'm sorry zan gyara in sha Allah "
shagwabe mishi fuska ta yi ta na fadin " da gaske ka ke ? "
a hankali ya gyada mata kai allamun Eh
wani cool murmushi ta saki kafin ta nufe shi da sauri ta fada jikin shi ta rungume shi
tsit ya yi daukewar wucen gadi dan duk zaman nan da su ka yi da ita a Mascow a matsayin matarshi wannan shi ne karon farko da ta taba jikin shi , wani bakon yanayi ya tsinci kan shi a ciki
wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sa hannayan shi ya na neman ya raba ta da jikinshi ya na fadin " okay , sakani na tafi "
a hankali ta dago kan ta ta shagwabe fuska ta ce " ba za ka yi min kiss ba ? "
dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta cikin zuciyar shi ya na fadin " wane irin kiss kuma "
ya na yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya ji saukar lips din ta saman nashi
wata irin muguwar faduwa ce gaban shi ya yi har sai da ya ga wani dan dishi dishi
ba shiri Safa ta dauke lips din ta da ga saman nashi ta datse idanun ta da karfi ta na fadin " Washhhh Allah " ta fada ta na dafe kai da hannu guda
a razane Assad ya riko hannun ta ya na fadin " what happened again ? "
kamar za ta yi kuka ta ce mishi " ban sani ba , ji na yi kamar arrow ta ratsa kai na , wai me ya ke damu na ne haka ? "
ya na shirin yi mata magana ya ga ta yi baya ta konta ta daina motsi da allamun suma ta yi
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya mike ya nufi toilet ya shige
ya dauki wajen 30 minutes kafin ya fito daure da towel , sai wani dan karamin a hannun shi ya na tsane gashin kan shi
kai tsaye dressing room ya nufa
jim kadan ya fito sanye da Trouser na Army da wata T-shirt fara , ya daure wanan curly hair din nashi a baya , ya saka wasu glass bakake a idanun shi
kai tsaye bedside drawer ya nufa ya dauki wayoyin shi sannan ya baro dakin
kai tsaye part din ya baro , ya na fara sauko stair ya ga ya ga Musadeeq da Fatma zaune saman sofa guda da Allamun hira su ke yi gwanin burgewa
ko sannu Assad bai ce musu ba ya sauko stair din ya nufi hanyar fita
da sauri Fatma ta ce mishi " Assad , yaushe ka dawo kuma ? ina ka baro Safa ? "
ko kallon ta bai yi ba ya na tafiyar shi kai a sunkuye ya na latsa wayar shi
" Assad dawo ina son magana da kai " Musadeeq ya fada cike da isa
a hankali Assad ya juya ya nufi sofar da ke fuskantar su ya zauna kai a sunkuye ya ce " yi maganar ka , sauri na ke "
cikin sanyin murya Musadeeq ya ce mishi " Assad , ina ka baro yarinyar nan ? "
a takaice ya ce mishi " ta na barci "
" Assad , ka fi kowa sanin yarinyar nan ba ta da lafiya , why ba za ka tsaya ka kula da ita ba , she is your wife " Musadeeq ya fada cikin raunin murya
wani dogon nunfashi Assad ya ja kafin ya dago kai ya kalli Musadeeq ya ce " Daddy , me ya sa za ku aura min yarinyar nan ? ni na ce ina son ta ne ? ba na son ta kuma ba zan taba son ta ba , dan haka ku daina ce min na kula da ita , i'll never do that "
" kai ba ka son ta , amma zuciyar da ke jikinka ta na son ta , kar ka manta zuciyar Amar ce a jikin ka , kuma ka fi kowa sanin yadda Amar ke son yarinyar nan ,