Showing 108001 words to 111000 words out of 133773 words

Chapter 37 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9715

face din shi


wata irin razananiyar kara ce ta saki ta juya da sauri sai jikin Musadeeq dama ya na tsaye a bayan ta , ya na cin karo da face din Amar ya lumshe idanun shi da sauri ya karanto kalmar shahada cikin zuciyar shi


Fatma kuma wani matsanincin kuka ta saki a jikin ta na fadin " yanzu wa ya yi wa Amar di na wannan Aikin , me ya yi musu da za su raba ni da shi haka ? wane mara imani ne ya mishi wannan kisan , ko tausayi ba bu , inallillahi wa'ina illaihi raji'un "


shi dai Musadeeq ya kassa cewa komai sai hawaye ke zubo mishi bibiyu
A hankali Sami ya karaso wajen su , cikin Sanyin murya ya ce musu " ni na san wanda ya yi mishi hakan , kuma na San dalilin shi na yin hakan "


a tare Musadeeq da Fatma su ka juyo su ka kale shi
murya na kerma Musadeeq ya ce mishi " ka sani ? su wanene su ka yi mishi haka ? ka fada min don Allah ka fada min , me Amar di na ya yi musu da za su yi mishi irin wannan kisan gillan ? "


dan sunkuyar da kai Sami ya yi kafin ya ce " Ba shi su ka so kashewa ba , Safa su ka yi kokarin kashewa , kawai Amar da Assad sun yi kokarin kare ta ne , su ka yi musu wannan abun "


" Safa ! " Musadeeq da Fatma su ka fada a tare cikin rudu


gyada musu kai Sami ya yi ya na cewa " Eh , Safa , Wadda ku ka zo nemawa Amar auren ta , ita ce a ka kai wa hari , kalma ta karshe da ya furta shi ne ku nemawa Assad auren ta a madadin shi , ba ya so a raba zuciyar shi da abun da ta ke so , Saboda zuciyar shi ce a jikin Assad "


" Ina ta ke ita Safar , ba abun da ya same ta ? " Musadeeq ya tambaye shi


" ta shiga doguwar suma , kuma ta yi amnesia saboda bugun da ta samu a kai , tun ta na karama iyayen ta su ka rasu , a tare mu ka tasso ni da ita kuma duk duniya ba ta da wani dan uwa da ya wuce ni , na ba ku auren ta har gaban Allah bayan ni babu wanda zai iya ba ku auren ta sai mahaifin ta , kuma Allah ya yi mishi cikawa , zan so lokacin da za a yi jana'izar Amar , a aura auren ta da Assad don Allah wannan shi ne kadai abun da na ke nema a wajen ku "


a hankali Fatma ta juya ta kali Amar , ta na kuka ta ce " ko de kuwa ba ka ba mu auren ta ba ni da kai na zan nemawa Assad auren ta , ko dan burin yaro na ya cika , tun da har ita ce muradin zuciyar shi , dole ta shigo cikin ahalin mu "


ta na gama rufe bakin ta Musadeeq ya daura da cewa " mu je na gan ta don Allah , ina son na ga wacece "


gyada mishi kai Sami ya yi kafin ya juya ya fara takawa zai fice dakin
a hankali Musadeeq ya saki Fatma ya na ce mata " Ki jira ni ina zuwa " da ga haka ya juya ya bi bayan Sami ya fice dakin


ya na fita ya ga Sami tsaye bakin kofar dakin da ke fuskantar na su Amar
a hankali ya karaso dakin su ka shiga a tare shi da Sami ya na sallama kassa kassa
ya na shigowa idanun shi su ka sauka kan Safa da ke konce Saman gadon jinya
ta na sanye da wata gown blue zuwa guyiwa , an yi mata wani dress a kai , a na yi mata karin jini


a hankali Musadeeq ya karaso gaban gadon ya na bin Safa da Kallo , irin kallon nan kamar na sani


" na san ta yi maka kama da tsohon Abokin Assad Aryan Abdoul Karim ko ? " Sami da ke bayan shi ya fada


ba shiri Musadeeq ya juya ya kalli Sami ya ce " ta ya a ka yi ka sani ? "


wani cool murmushi Sami ya saki kafin ya ce " Saboda kanwar shi ce , na san ba za ka manta Aryan ba saboda har auren yarinyar ka ka ba shi , First time da na ga Amar , na ji a jiki na kamar na san shi , ko na taba ganin face din shi amma na kassa tuna a ina ne , sai yau , lokacin da Aryan ke RUSSIA ya na yawan turo min hotunan sa tare da Amar "


" Do you mean kai dan uwan Aryan ne ? Tsawan shekaru sama da goma ni da Assad mu ke neman shi amma mun kassa Samo shi , kenan Safa kanwar shi ce ? "


gyada mishi kai Sami ya yi ya na cewa " kanwar shi ce , amma batun Aryan Assad ne kadai zai iya ba ku amsa ba ni ba , shawara guda zan ba ku , Tun kafin Safa ta dawo cikin hayacin ta ku dauke ta da Assad ku koma RUSSIA saboda akwai ma su bibiyar rayuwar ta ba daya ba biyu ba , kuma in har ba ganin gawar ta su ka yi ba , ba za su hakura ba , don Allah ku ceci rayuwar kanwa ta na roke ku " ya kai karshen kamar zai yi kuka ya na hade hannayan shi ya na rokon shi


girgiza mishi kai Musadeeq ya yi ya na cewa " no , Safa yanzu kamar diya ta ke a wajen mu , saboda Matar Assad ce , in dai ina raye ba abun da zai same ta , cikin daren nan za mu bar garin nan " ya na gama fadar haka ya juya da sauri ya fice dakin


ya na fita Sami ya tako a hankali ya tsaya gaban gadon Safa ya saki wani cool murmushi ya ce " Shikenan ? yanzu ma za su sake raba ni da ke ? ki yi hakuri duk abun da ya faru , ki yi hakuri abun da mu ka yi miki , na yi miki alkawari wannan karan da hannu na zan karbar miki hakinki , ba zan kyale shi ba wannan karan , ina yi miki fatan Alhairi a nan gaba , in sha Allah zan zo wajen ki bayan komai ya kare , ki kula min da kan ki kin ji ko ? I love you my sister " ya na gama fadar haka hawaye su ka zubo mishi , ya matso da lips din shi saman forehead din ta ya manna mata kiss


da ga haka ya dago kai ya juya ya fice dakin a hankali


ya na fita Dakin da a ka kontar da su Assad ya koma
bakin shi da Sallama ya shigo dakin , nan ya tardo Musadeeq da Fatma tsatsaye bakin gadon Amar su na kallon shi su na faman Hawaye a tare har shi kan shi Musadeeq


cikin nitsuwa Sami ya ce mishi " zan je gida amma ba zan jima ba zan dawo "
gyada mishi kai kawai Musadeeq ya yi ba tare da ya ce komai ba
a hankali Sami ya juya ya fice dakin kai tsaye likitar ya baro
[26/09 Γ  10:59] MEERAH πŸͺ·πŸ©·:






πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«


( YAR JARIDA )











πŸ•ŠπŸ’”( A heart touching love story & destiny ) πŸ’”πŸ•Š










STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸŒΈ




【THE ROYALTY LOVE πŸ•ŠπŸŒΈπŸ’•γ€‘










Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ :FREE BOOK


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀ : PAID BOOK












TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/BBWVomizhgVKzcxJo4XRpG






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP POSTING ROOM


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054






DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i


DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite










BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM










___________________________________________


LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN , COMPLETE KUMA 400


GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❀⚘EXILED PRINCE ⚘❀
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank


IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
Zain (Airtel)
08081129487


sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753




___________________πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š____________________













BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM














ο½› PAGE 32 πŸ₯€ ❀ }












β–ͺG.R.A ( GIDAN SU SAFA )










bakin shi da sallama Sami ya shigo parlourn gidan , nan ya tardo Aziza zaune saman sofa ta yi zugum waje guda , da ga ganin yanayin ta kassan ta na cikin tashin hankali


bai bi ta kan ta ba ya nufi stair ya Haye kamar gidan shi , ta na ganin shi amma ba ta ce mishi komai ba dan a halin yanzu ba ta da karfin yin wani jaye-jayen da shi


jim kadan Sami ya sauko stair din ya na sanye da jeans black color da t-shirt red color , da allamun wanka ya yi a part din Safa
ya na saukowa ya shiga kwallawa Snoopy kira


wannan karan Aziza ba ta yi shiru ba sai da ta ce mishi " me kuma za ka yi mishi ? ina Safa ta ke tun safe da ta fita ba ta dawo ba , kuma na san kai ka san inda ta ke "


ko sannu Sami bai ce mata ba ya ci gaba da kwallawa Snoopy kira
ya na gama rufe bakin shi Snoopy ya shigo parlourn da gudu ya nufi stair a tunanin shi Safa ce


Sami bai ce mishi komai ba , sai da ya haye stair ya shiga bedroom din ta ya ga babu kowa sannan ya sauko ya nufi Sami ya na haushi da karfi allamun Safa ya ke tambaya


a hankali Sami ya zube saman guyiwowin shi ta kai hannu ya fara shafa jikin shi ya na fadin " ka yi hakuri Aboki na , amma momyn ka ba za ta iya dawowa ba , ka yi hakuri ka ji ko ? amma mu je zan kai ka wajen Aryan , na san za ka ji dadin zama da shi fiye da wannan matar "


ya na gama fadar haka Snoopy ya yi mishi wani marairaicin haushi , da ga haka Sami ya mike
har ya yi taku biyu ya jiyo Muryar Aziza ta na fadin " Ina kuma za ka tafi da shi ? ina tambayar ka ina Safa ta ke ? Sami ba dai wani abu ku ka yi mata ba ? "


cikin bacin rai Sami ya juyo ya ce mata " yi min Shiru ! , wace Safa kuma ? Safar da wancen matsiyacin dan uwan ki ya kashe ? shikenan kun huta kun ji dadi ta mutu ko ? "


a razane Aziza ta karaso gaban shi ta na fadin " Sami ban ban gane abun da ka ke cewa ba , where is Safa ina Safa ta ke ? "


wani dan karamin murmushin takaici Sami ya yi ya na cewa " congratulations , She is die , kun kashe ta kun huta ko ? why ? me ta yi muku ? kin fi kowa sani bayan uncle Abdoul Karim da momyn ta da Marwan ke kadai ce wadda ta ke iya kallo ta ce ta na da Family a duniyar nan , amma saboda son zuciya irin naki da na dan uwan ki , ta rasa komai nata , yanzu gashi ta rasa rayuwar ta , you're HAPPY now ? " ya kai karshen hawaye na zubo mishi


a hankali ya kai hannu ya goge hawayen shi ya na cewa " wannan shi ne son da ki ke yi mata ? na san ke ce ki ka kira Ali ki ka ce mishi kar ya bar Safa ta tafi ganin Aryan , burin ki ya cika , ba ta je ganin shi ba , yanzu haka maganar da na ke miki ta na cikin kassa tare da uncle Abdoul Karim , za ki iya cin moriyar dukiyar ta ta bar miki , kuma ki saurare ni , wlh sai Allah ya fidda mata hakin ta abun da ku ka yi mata , na bar ki lafiya , Snoopy let's go ! "
ya na gama fadar haka ya juya ya fice parlourn ya bar ta nan tsaye ta yi sumar tsaye


a hankali hawaye su ka fara zubo mata ta na girgiza kai ta na fadin " no , no , no , Safata ba ta mutu ba , ba ta mutu ba , Ali why za ka min haka ? na shiga uku yau ni Aziza ? " ta na gama fadar haka ta saki kuka kamar wata karamar yarinya ta daura hannayan ta biyu a kai


bangaran Sami kuma ya na fitowa gidan su Assad ya shiga
bakin shi da sallama ya shigo parlourn gidan , nan ya tardo Sohan rungume da Rahaf da ke ta faman kuka


sun ji shigowar Sami , amma ba su ce mishi komai ba
shi ma bai kawo komai a ranshi ba , ya cewa Sohan " please ku shirya kayan ku , za ku koma RUSSIA cikin daren nan , sannan wannan sunnan shi Snoopy , abokin Safa ne tare da shi za ku tafi "
ya na gama fadar haka ya juya ya kali Snoopy da ke bayan shi ya ce " Snoopy , tare da su za ka tafi , kar ka damu ba abun da ya samu momyn ka , yanzu haka ta na cen ta na jiran ka "


wani haushi mai karfi Snoopy ya yi jin an ce Safa ta na jiran shi
da gudu ya nufi stair ya Haye , ya tafi wajen Rex
Sami na ganin Haka ya juya ya fice parlourn ya shiga motar shi ya bar gidan ya koma Hospital wajen su Musadeeq








β–ͺAFTER SOME HOURS






β–ͺKUJE PRISON ( ABUJA )








zaune Sami ya ke cikin dakin da a ke kawo ziyara ya na jiran Marwan
ya dauki wajen good ten minutes a haka kafin Marwan ya shigo dakin babu ko sallama , ya yi tsaye waje guda idanun shi sun koma jazir
a hankali ya bude baki Muryar shi har ta shake ya ce wa Sami " where is Safa ? "


wani dan karamin murmushi Sami ya sakin mishi kafin ya ce " don't worry , yanzu haka da ga airport na ke , sun koma RUSSIA tare da ahalin Assad "


wata irin nanauyar ajiyar zuciya Marwan ya sauke cikin zuciyar shi ya na godewa Allah da babu abun da ya samu kanwar shi


a hankali ya karaso cikin dakin ya janyo chair ya zauna ya na kallon Sami
cikin nitsuwa Sami ya shiga ba shi labarin abun da ya faru bayan fitar shi da ga nan sannan ya bashi labarin Jana'izar Amar da a ka yi da kuma auren Assad da Safa bisa umarni Amar , da komawar su RUSSIA sannan ya daura da cewa " yanzu haka maganar da na ke maka da Aziza da shi Ali duk sun dauka Safa ta mutu "


Sami na gama rufe bakin shi Marwan ya bushe da wata shegiyar dariya har da lumshe idanun ya na dafe ciki
a rude Sami ke kallon shi , ya fada mishi rasuwar abokin shi ya kuma zai yi irin wannan dariyar ko dai ya zauce ?


Marwan kuwa , sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya ce " Sami , tun farko Ali fushin damusa ya ke gani , yanzu kuma zai ga fushin Lion , sarkin dawa , Sami , mutuwa ce kadai za ta raba Assad da Ali , in har ya dawo cikin hayacin shi ya samu labarin cewa shi ne ya kashe Amar wlh ko da yakin duniya na uku za a yi a Nigeria sai Assad ya yi wa Ali kisan wulakancin da ya yi wa Amar dan duk duniya babu abun da Assad ya tsana fiye da a taba dan uwan shi Amar , in da farko da ni ya ke yakin , yanzu kuma zai san me a ke kira da yaki dan Assad ba zai kyale shi ba " ya kai karshen ya na wata yar karamar dariya


wani dan karamin tsaki Sami ya yi kafin ya ce " kai ina ce maka , Amar ya mutu , Safa ta yi amnesia , an kuma aura mata aure da Assad kai ka samu damar yin dariya "


" to me ka ke so na yi in ba dariya , Safa ta yi amnesia ba laifi za ta dawo cikin hayacin ta , batun auren ta da Assad kuma shi ma ba laifi dan ni dama tun kafin ta mallaki hankalin kan ta na bawa Assad auren ta saboda tun ta na karama ya ke son ta , kawai dai yanzu ne da ya ji labarin Amar ya na son ta ya sa ya hakura ya bar wa Amar , zancen Mutuwar Amar kuma ba zan maka karya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login