Showing 51001 words to 54000 words out of 133773 words
Djamila ta yi ta na gyada ma Safa kai
Sakin hannun ta Safa ta yi ta na shirin magana kamar da ga sama ta jiyo Muryar Amar ya na fadin " ke ki na meda hankalin ki ne kan karatun ? "
Dum ta ji gaban ta ya fadi , a dubu dari ta mike tsaye ta juya ta na kallon shi
Ya na tsaye bayan ta , ya na sanye cikin trouser white colour , da t-shirt navy blue , ya saka wata face mask baki sai tashin kamshi yake yi
Cike da rudu Safa ta nufe shi ta na fadin " Amar what are you doing here ? " ta fada kamar mai rada dan kar sauran students su jiyo ta
Ita ba ta san tun shigowar Amar cikin library din ba su ka tsare shi da ido ko wane ya na kara yabawa kyawan qui duk da ya na sanye da face mask
A hankali ya dan sunkuyo da kan shi ya matso da face din shi saitin ta ta kassa kassa ya ce mata " kawai na zo ne na yi miki barka da safya , na je gida na ga baki nan "
Da sauri Safa ta yi baya , ta ce mishi " okay ! Okay ! Please ka bar wajen nan , mutane su na kallon mu "
Slowly ya dago kai ya gyara tsayuwar shi ya fara bin libraryn da kallo
Dan karamin murmushi ya saki kafin ya karaso wajen table din su Safa , ya zauna saman chair din da ta tashi ya kali su Haoua ya ce " Hi ! Sannun ku "
Murmushi mai dan sauti Haoua ta yi kafin ta ce " yawwa sannu ka kai ma "
Sai da ya bari ta karasa maganar ta sannan ya ce " sorry ba na jin haoussa "
A hankali ya juyo ya kali Safa da ke tsaye bayan shi ya ce mata " Miss Safa , ko za ki koya min ? "
Iska mai zafi ta furza da ga bakin ta ta ce " please Doctor , ka koma gida , wlh za ka janyo min kananan magaganu "
Daga mata gera guda ya yi kafin ya ce " okay , amma kin koya min ko "
Da sauri ta ce " ba haoussa ba har chinese in ka na so zan koya maka "
Gyada kan shi ya yi kafin ya mike ya fara takawa ya nufe ta , a hankali ya sunkuye da kan shi ya kai dan bakin shi saitin kunen ta ya ce " no haoussar ma kadai ta isa " ya fada mata cikin harshen chinese
Ya na gama fadar haka ko ya mike ya ci gaba da tafiyar shi
Da sauri Safa ta juya ta na kallon shi , ta na son ta yi mishi magana amma ba hali , har sai da ya fita sannan ta juya ta koma saman chair din ta ta zauna
Ta na zama , Haoua da Djamila su ka Bushe da dariya har da tapi
Hararrar su Safa ta yi ta na fadin " lafya ku ke dariya haka "
Girgiza kai su ka yi a tare sannan Haoua ta ce " Haba ba banza ki ka ki kula duk samarin makarantar nan , ashe Doctor ya na gida ajiye " ta kai karshen su na sake bushewa da dariya
Tsaki Safa ta yi sannan ta fara tatare books din ta ta meda cikin bag din ta , ta dauka ta mike ta bar musu wajen
" ki gaishe ma na shi in kin je " Haoua ta fada dan sama sama ta na yar dariya
Bangaran Safa kuma ta na barin library kai tsaye class ta koma dan ta ci gaba da karatun ta , ta na shiga Class din ta ga ba kowa
Sai ta nufi chair din ta ta zauna ta fido books din ta ta ci gaba da karatun ta , amma har ga Allah gangar jikin ta ne kawai ke a wajen , tunanin ta ya tafi wani waje kawai sai tsintar kan ta ta yi ta na sakin wani cool murmushi allamun tunanin da ta ke yi ya yi mata dadi har mai lectures din su ya shigo ba ta da labari
* AFTER SOME HOURS
Bayan sun Kamala lectures din su misalin karfe 1 na yamma , kai tsaye Safa gida ta wuce
Bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn su , ta nufi stair kai tsaye dan ta san a wannan lokacin momy ba ta dawo ba
Kamar da ga sama ta ji an amsa mata sallamar ta
Cak ta tsaya da sauri ta kai kallon ta cikin parlourn
Nan ta ga Amar konce saman sofa, ga Snoopy konce kassa shi ma
Da lumshe idanun ta ta yi ta daga kai sama , ba ta ce mishi komai ba ta wuce ta Haye stair
Ta na hawa Amar ya kali Snoopy ya ce " Aboki na , ina ga yau ran mamar ka ya baci "
Dan karamin haushi Snoopy ya yi ba tare da ya dago kan shi ba
Juya kan shi Amar ya yi ya kali ceiling sannan ya ce " ni ma haka na gani "
Sai da ya dauki wajen five minutes kafin ya sake cewa " za ka iya tafiya wajen Rex in ka gaji da zama kai kadai "
Kamar jira ya ke yi ko ya tashi da sauri ya fice parlourn
Ya na fita Amar shi ma ya tashi ya fice parlourn cikin nitsuwa ya bi bayan Snoopy su ka tafi gidan su
Bangaran Safa kuma ko da ta shiga bedroom din ta , kai tsaye toilet ta wuce ta yi wanka
Jim kadan ta fito sanye da bathrobe , ba ta tsaya bata lokaci ta Haye saman bed din ta , ta yi rub da ciki ba jimawa barci ya yi gaba da ita dama a gajiye ta ke
Ba ta farka da ga barcin ta ba sai da wayar ta ta fara karar kiran Sallat
A hankali ta kokarin bude idanun ta , ta na karanto adu'ar tashi da ga barci
Ko da ta bude idanun ta ma sai da ta dauki wajen good ten minutes a haka kafin ta mike a hankali zaune ta na karewa dakin kallo kamar bakon ta
Saukowa da ga saman bed din ta yi ta nufi toilet ta yi wani wankan , ta dauro da Alwalla sannan ta fito ta shiga dressing room
Jim kadan ta fito sanye da wani skert pink colour har kassa , da wata Shirt fara , da wani veil white colour ta yi Rowling din shi a kai sai tashin kamshi ta ke yi
Ko da ta fito ta nufi daddumar ta , ta Haye sannan ta tada sallar ta , cikin nitsuwa ta yi kayan ta , ta zauna karatun adu'a sannan ta tashi ta dauki wayar ta , ta fito dakin a haka
Kai tsaye parlourn kassa ta sauko , ta yi zaton za ta tardo Amar sai ta ga ba kowa a cikin parlourn
Ba ta kawo komai a ran ta ba ta nufi sofa ta zauna , ta na faman latsa wayar ta
Bai fi five minutes da zaman ta ba , ta ga an turo mata pic ta WhatsApp da wata number ta Nigeria
Babu tsoro ta shiga discution din ta fara download din pic din
Wani kyawatencen murmushi ta saki lokacin da idanun ta su ka yi mata arba da pic din
Amar ne konce saman bed din shi ga Snoopy da Rex konce saman kirjin shi abun ba karamin burge ta ya yi ba
A hankali ta mike tsaye ta nufi door din fita parlourn ta fito harabar gidan
Tun da gate man ya gan ta ya yi sauri ya tashi da ga saman chair din shi ya bude mata kofar fita
Godiya ta yi mishi ta na dan murmushi kafin ta sa kafa ta fice gidan baki daya
Kai tsaye gidan su Amar ta nufa , har yanzu dai wadanan jibga jibgan sojoji su na nan tsatsaye kamar ba su gajiya
Ba ta bi ta kan su ba ta nufi door din shi gidan , tun kafin ta karaso sojan da ke kula da gate din ya bude mata , dan murmushi ta yi ta na yi mishi godiya kafin ta shiga gidan ta na sallama kassa kassa
A hankali ta ke tafiyar ta har ta karaso wajen dan balconyn da zai sada ka da parlour
Hannu ta kai ta dan bubuga door din kafin ta tura ta a hankali ta shiga ta na sallama
* ASSAD 🔥
Zaune ya ke cikin parlourn shi kadai ya na faman latsa laptop din shi , da ga shi sai short da singlet duka farare kal kamar sabi , ya saka wasu glass bakake
Slowly ya dago kan shi ya kale ta ya na amsa mata sallamar ta , amsawar da shi kadai ya ji abun shi
Karasowa ta yi cikin parlourn ta na gaishe da shi , amma ina sam ba ya jin ta , ya yi nisa cikin duniyar shi duk sai ya ji ya kassa janye idanun shi da ga saman ta dan fa ba karya kayan nan sun yi mata mugun kyau ,
A hankali ta karaso gaban shi ta dan sunkuyo da kan ta, ta na lekon face din shi ta ce " Hello ! here the earth is there anyone ? "
Cikin zafin nama ya kai hannu zai damko wuyan ta , da sauri ta kauce ta taro hannun shi ta murde shi baya ta na fadin " Haba malam da ga gaisuwa ka na neman ka kashe ni "
Kallon cikin idanun ta ya yi na dan lokaci , cikin sanyin murya ya ce mata " okay, sake min hannu " ya fada da turanci
Ita ma kallon cikin idanun shi ta ke yi babu ko kiftawa , ta fara sakin hannun shi a hankali ba tare da ta sanye idanun ta ba
Ta na sakin shi ya kauda kan shi ya ci gaba da latsa wayar shi
A hankali ta koma geffen shi ta zauna ta na lekon abun da ya ke cikin laptop din
" fice min da ga nan " ya fada mata cen kassan makoshi kamar an yi mishi dole
Kare mishi kallo da kyau ta yi , ta na shirin magana Rex da Snoopy su sauko stair da gudu su ka shigo parlourn su na haushi
Ko wane ya nufi mai gidan shi ya fada jikin shi
Rungume Snoopy Safa ta yi ta na fadin " Baby na , shi ne za ka tserewa ka bar ni ko " dan karamin haushi ya yi ya na girgiza bindin shi ya fido tongue din shi ya lashe mata kumatu
Yar karamar dariya ta yi ta na fadin " shikenan shikenan ya isa haka ni ban yi fushi ba "
A hankali ya sauko da ga jikin ta ya koma gefen Rex ya zauna
Shi dai Rex bai da wannan hayaniyar kamar Snoopy , dan ya san halin uban gidan na shi , ba ya son hayaniya shi ya sa bai cika yin haushi ba in har ba tabo shi a ka yi ba
* AMAR 🤙
A hankali ya ke sauko stair , ya na tafe ya na latsa wayar shi , ya na sanye cikin wando three cuter baby blue da singlet
A haka har ya karaso cikin parlourn ya zauna dayan geffen Assad ba tare da ya san da Safa na wajen ba ma
Sai da ya zauna sannan ta yi mishi gyaran murya
Da sauri ya dago kan shi , ya kali geffen ta , daga mishi gera guda ta yi ta na murmushi
Murmushi shi ma ya yi mata Kafin ya ce " Miss Safa , sannu da zuwa "
Ta na shirin magana Assad ya riga ta cewa " please in hirar ku za ku yi ku ban waje "
Cikin ko in kula Safa ta ce mishi " ba mu hana ka ba barin wajen kai ma "
A dubu dari ya dago kan shi ya kale ta ya na zaro idanu ta cikin glass din shi , har Amar sai da ya zaro idanu ya na kallon ta baki sake ,
Ita ba ma damu da kallon da su ke yi mata ba sai ma kauda kan ta gefe da ta yi ta na dan girgiza kan ta kamar ba ita ta yi maganar nan ba
Gyada kan shi Assad ya yi kafin ya mike ya na rike da laptop din shi ya bar parlourn ya nufi stair ya Haye
Ya na barin wajen Amar ya matso kusan Safa ya ce " Na tambaye ki , kin san wata Army ta Russia da a ke kira da Russian bear "
Dan jinkirtawa ta yi kafin ta gyada mishi kai allamun eh
Gyara zaman shi ya yi kafin ya ce mata " to kin san General of the Russian Bear Army Sasha Zurvan ? "
Yanzu ma gyada mishi kai ta yi kafin ta ce " eh na san shi , na dai san sunan shi , amma ban taba ganin shi ba , saboda ina yawwan karanta news a kan shi "
Yar karamar dariya Amar ya yi kafin ya ce " kennan ki na karanta news ? "
Hararrar wassa ta yi mishi kafin ta ce " ni ba Yar JARIDA ba ce , ina karanta wa mana , musaman wanda a ke posting a social media "
" kin dai ga abun da a ke rubutawa kan shi k......"
Da sauri ta katse shi da cewa " ni ko na gani , duk yawwan cin post din da na karanta a kan shi cewa su ke wai zuciyar shi ta bushe , kai ka ga training din da ya ke ba wa sojojin shi kamar ba mutane ne ba , wlh akwai wani post da na karanta sai da na yi one week ina tunanin shi , ni ba na ma fatan hanya ta hada ni da wannan mutun , saboda wannan muguntar ta shi ne ya sa ba ya bayana kan shi "
Dariya sosai Amar ya yi har da dafe ciki jin abun da ta fada
Hararrar shi ta yi ta na fadin " lafya ka na dariya haka "
Tsagaita dariyar shi ya yi kafin ya ce " ashe haka ki ka iya surutu "
Hararrar wassa ta yi mishi ta na dan murmushi kafin ta kauda kan ta gefe ta na ci gaba da murmushin ta
" shikenan , Brother di na fa zuciyar shi ba a bushe ta ke ba , kawai yanayin aikin shi ne , da kuma muguwar punishment da ya ke bawa criminel shi ya sa mutane dayawa su ke yi mishi kallon bashi da zuciya ko mara imani , amma ya na da ita mai kyau ma wadda ba a ko ina za ki same ta ba , ke a tunanin ki inda ba shi da zuciya wannan maganar da ki ka yi mishi , wlh sai dai gawar ki ta bar gidan nan "
Kare mishi kallo da kyau Safa ta yi " ni fa ban gane abun da ka ke fada ba " ta ce mishi dan ita ba ta gane inda ya dosa ba gaskia
Jinkirtawa ya yi kafin ya ce " Assad shi ne General of the Russian Bear Army Sasha Zurvan "
Dum Safa ta ji zuciyar ta ta buga da mugun karfi , sai zaro idanu ta ke yi ta na kallon Amar ta kassa yin magana
Shi ko ya na ganin haka ya sake bushewa da dariya har da dafe ciki
A hankali Safa ta kai hannu ta dauki wani pillow da ke saman sofar ta fara kai mishi bugu
Cikin dariyar ta shi ya ke fadin " shikenan shikenan ya isa ba zan sake ba "
Tila mishi pillown ta yi da karfi kafin ta mike tsaye ta na fadin " Snoopy let's go home "
Da sauri Amar ya mike ya na fadin " haba Miss Safa da ga wassa za ki ce kin tafi "
" no ba haka ba ne , akwai abun da na ke son yi ne , Snoopy let's go " ta kai karshen ta na fara takawa ta yi gaba Snoopy ya tashi ya bi bayan ta su ka fice da ga parlourn
Da kallo Amar ya raka ta har sai da ta fita bai yi kokarin tsayar da ita ba
Sai su ka fice sannan ya mike ya nufi stair ya Haye a hankali
Kai tsaye part din su ya koma , amma da ya je sai ya ga babu kowa a ciki part din, bai wani damu ba kawai ya wuce toilet
[08/09 à 11:51] MEERAH 🪷🩷:
💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
*( YAR JARIDA )
*
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🦋🕊
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE 17 🥀 ❤
Bangaran Safa kuma kai tsaye gidan su ta koma , bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn gidan