Showing 45001 words to 48000 words out of 133773 words

Chapter 16 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9702

sauri ya zo ya bude mata kofar
Da gudu ta danna hancin motar cikin gidan kai tsaye parking space ta nufa ta yi parking ta kashe motar sannan ta sauko
Ta na sanye da wata gown Fara an yi mata zanen flower da pink , yellow & green , ta yi mata kyau over
Ta na fitowa motar ta , ta sa hannu ta warware veil din ta , ta riko shi a hannu tare da bag din ta , ta saki wannan golden hair din na ta duk ya bazun mata a baya


A hankali ta shigo parlourn su ta na sallama kassa kassa kai a sunkuye


Kamar da ga sama ta ji an amsa mata sallamar ta
Cak ta tsaya ta dago kai ta na kallon wani saurayi da ke zaune saman sofa ya ba ta baya ba ta iya ganin face din shi


A hankali ta karaso cikin parlourn har ta kawo wajen sofar da ya ke zaune ta ga ya mike tsaye ya juyo slowly ya na kallon ta


Cak ta tsaya ta na kallon shi cikin ido ita ma ta kassa wani kwakwaran motsi
Ta na a haka sai ganin ta yi ya saki wani cool murmushi ya ce " Miss Safa ? " ya fada ya na nuna ta da dan yatsa


Jinjina mishi kai tayi kafin ta ci gaba da takawa ta nufi wata sofar ta zauna sannan ta ce " wanene kai ? "


Komawa shi ma ya yi ya zauna ya na " please yi magana da turanci ko French ba na jin haoussa sosai " ya fada da turanci


" who are you ? And what are you doing here ? Are you waiting for someone ? " ta dinga jero mishi tambayoyin


Shiru ya yi ya na kallon ta , sai sakin murmushi ya ke yi
Ta na shirin magana Snoopy ya shigo da gudu cikin parlourn ya na haushi, ya nufi Safa ya Haye jikin ta


Yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " ni ma na yi kewar ka baby na " ta kai karshen ta na sumbatar forehead din shi
Shi kuma ya Haye saman sofar geffen ta ya zauna
Da sauri ta ce mishi " tashi ka kirawo min Balki "
Wani dan marayen haushi ya yi kafin ya ida kontawar shi allamun ba zan je ba
" please baby , ba ka ga mun yi bako ba " ta fada mishi a hankali kamar mai rada
A hankali ya mike ya diro da ga saman sofar ya girgije jikin shi sannan ya nufi dining room da gudu


Da kallo su ka raka shi a tare kafin saurayin nan ya juyo ya kali Safa ya ce " wannan karan kin jima ki na tare da shi ? "


Cikin ko in kula ta ce mishi " ba ka ba ni amsar da na yi maka "
Ba ta gama rufe bakin ta ba ya ce " oh i'm sorry , Amar Musadeeq nice to meet you "
Dum Safa ta ji zuciyar ta ta buga, har da zaro idanu ta na kallon shi baki sake ta ma rasa abun da za ta ce mishi
Su na a haka Snoopy ya fito da ga cikin dining room ya na tafiyar shi a hankali
Har ya zo zai wuce ta gaban Amar
Ya yi sauri ya riko shi ya na fadin " ina kuma za ka je ba mu gaisa ba "
Ya na gama rufe bakin shi Safa ta ce " sake shi , ba ya son wanda bai sani ba ya na taba shi , mugun rigimame ne "
Ai ko ba ta gama rufe bakin ta ba ta ga yadda Snoopy ke yi wa Amar wassa har da rungume shi
Shi kuma Amar ya na biye mishi su na wassa har sun manta da Safa


Ita dai kallon su kawai ta ke yi , abun ya so ya ba ta mamaki yadda Snoopy ke wassa da Amar , wanda ko momy da kan ta ba ya kula ta yau an samu wani ya na yi mishi wassa haka


Sai da ya ida biye mishi sannan ya ce mishi ya je waje ya jira shi
Ba musu Snoopy ya sauko da ga jikin shi ya fice parlourn da gudu
Sai da ya fita sannan Amar ya kali Safa ya ce " amma kin jima ki na da karen nan ko , na ga ya na jin magana ba kamar Rex ba "
" wanene kuma Rex ? " ta tambaye shi ta na daga mishi gera guda
" Abokin big bro di na , shi ma, na shi karen ya na kama da wannan tak , sai dai na shi ya samu horon soja , ko za mu je ki gan shi " ya fada ya na dan murmushi
Girgiza mishi kai kawai ta yi dan ta rasa abun da za ta ce da shi


Sarai ya gane abun da ta ke tunani , sai ya ce mata " i'm sorry, na zo muku gida ba tare da sanin ka , just na kassa hakura ne , ina son na gan ki , kuma jiya kafin mu tafo sai da na duba localization din ki na ga gidan da ki ke ciki ya na fuskantar wanda za mu sauka a ciki , shi ya sa na taho nan kai tsaye ko gidan ban shiga ba "


Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " no ba haka ba ne kawai zuciya ta ta kassa yarda ne da abun da na ke gani "


" why ? Ba aljani ba ne ni , ki yarda da ni ba da niyar cuta na zo gare ki ba " ya fada mata cikin sanyi


" no ba haka ba ne , ni ma na kassa tantance abun da zuciya ta ke rada min "


Dan karamin murmushi ya yi kafin ya mike tsaye ya na kallon ta ya ce " ba komai , ni zan koma gida , please idan kin samu dama zan so ki dan leko mu , ni da brother di na ne mu ke tare "


Mikewa tsaye ita ma ta yi kafin ta ce mishi " okay , Allah ya kai mu "


Juya wa ya yi ya fara takawa ya fice parlourn ya bar ta nan tsaye
Ya na fita ta saki wani kyawatencen murmushi cikin zuciyar ta kuma ta na fadin " ko ba komai ya hadu gaskia , amma muryar shi da na ji a waya da kuma ta yanzu ta so ta dan banbanta "
Da wannan tunanin ta bar parlourn ita ma ta Haye stair da sauri
Ta na barin wajen ko Balki ta fito da ga kitchen rike da tray
Har ta karaso cikin parlourn kawai sai ta ga ba kowa
Dan karamin tsaki ta ja kafin ta juya ta koma kitchen din ta ci gaba da aikin ta


Bangaran Safa kuma ta na hawa ta wuce kai tsaye bedroom din ta ta shiga wanka
Jim kadan ta fito daure da towel a kirjin ta , ta wuce dressing room
After some minutes ta fito sanye da wata gown navy blue mara nauyi ta na sanye da wani hijab shi ma navy blue
Kai tsaye wajen daddumar ta ta nufa ta fara gabatar da sallar la'asar dan lokacin ta ya yi

Bayan ta Kamala sallar ta , ta cire hijabin ta , da gown din ta ajiye saman sofa ashe ta na sanye da wasu kananan kayan da ga kassa , Mini skert ne zuwa guyiwa da wata yar t-shirt duka pink colour , ta saki wannan golden hair din na , yau har wani curly ya yi , wayar ta ta dauka saman bedside drawer , da wani dan karamin book kamar diary haka sannan ta fito dakin


Kai tsaye parlourn kassa ta sauko , ta na tafe ta na latsa wayar ta , har ta karaso wajen sofa sannan ta zauna ta ajiye diary din geffen ta , ta ci gaba da latsa wayar ta


Kamar wadda ta tuno wani abu ta mike a dubu dari ta nufi stair da gudu
Har ta daga kafa za ta taka stair na farko ta tsaya , dan karamin tsaki ta ja kafin ta juya ta nufi kofar fita parlourn
Bayan ta fito parlourn cikin harabar gidan , kai tsaye wajen gate ta nufa
Da sauri gateman ya taso ya na tambayar in ta na bukatar wani abu
Ba ta bi ta kan shi ba sa kafa ta fice gidan , ta na fita ko Snoopy ya taso da gudu da ga inda ya ke zaune ya bi bayan ta a hankali ba tare da ta sani ba
Gidan da ke fuskantar na su ta nufa da farko har ta fara da na sanin tahowar ta saboda jibga jibgan sojojin da ke tsatsaye bakin gate din gidan
Sai dai wani abu da ba ta sani ba , Amar ya fada musu cewa yanzu sun yi bakuwa in ta zo su bar ta ta wuce
Haka ko a ka yi , tun kafin Safa ta yi musu magana mai kula da gate din ya bude mata kofar da kan shi
Sai da ta kare mishi kallo da kyau sannan ta sa kafa a hankali ta shiga gidan
Nan ta ga abun da ya fi karfin ta , duk gidan cike ya ke da manya manyan sojoji kowane rike da gun sai zagaye harabar gidan su ke yi , ga wasu manya manyan motoci cike da parking space , motoci ma su nunfashi kallo guda za ka yi musu ka san ba na kananan kudi ba ne , har sai da ta fara tambayar kan ta anya Amar doctor ne kamar yadda ta fada


Wajen wani dan balconyn da zai sada ka da cikin gidan ta nufa
A hankali ta kai hannun ta ta yi knocking kofar , shiru har ta dauki wajen ten minutes
Sake kai hannu ta yi ta yi knocking a karo na biyu nan ba shiru ba a bude mata ba
Dan karamin tsaki ta ja kafin sa hannu ta tura kofar a hankali sannan ta shiga ta na sallama
Gaskia parlourn ya hadu ga shi kuma da girma , komai na cikin Milk colour ne abun ba karamar kayatarwa ya yi ba
Cen ta hango Amar Zaune saman wata doguwar sofa bayan ta dakwai wani stair mai kyau zagaye da glass


Ya na sanye da trouser black colour da wata T-shirt navy blue , ya daure gashin kan shi baya ya saka wasu glass bakake a ido , ya na faman latsa laptop din da ke gaban shi saman table , ga wani kare sak Snoopy konce geffen kafar shi


Safa na ganin karen ta yi sauri ta karaso cikin parlourn ta na fadin " Snoopy me kuma ka ke yi nan ? "
Ba ta gama rufe bakin ta ba Snoopy da ke tsaye bayan ta ya yi mata dan haushi


A razane ta juya ta na kallon shi , a rude ta juya ta kali karen da ke konce geffen kafar wanda ta ke tunanin Amar ne
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " please Amar ina son mu yi wata magana "
Ko dago kai bai yi ba bare ya ba ta amsa , ba kuma bai ji ta ba , sarai ya ji ta tun shigowar ta parlourn
[03/09 Γ  21:46] MEERAHπŸͺ·πŸ©·:




πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«
( YAR JARIDA )





















( A heart touching love story & destiny )






















STORY & WRITTEN BY : MEERAH







Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯








DOMIN SAMUN WANNAN LITTAFIN DA GA FARKO ZA KU IYA JOING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i







TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION




πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡




https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY












BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM



















PAGE 15 πŸ₯€ ❀
















A hankali ta yi taku biyu ta karaso kusa da shi kadan ta ce " please Doctor ! "
Da sauri Karen nan ya dago kan shi ya daka mata wani wawan haushi , ba dan da ya ke ta saba da kare da yanzu ta saki fistari


Ya na shirin tashi ya biyo ta , saurayin nan ya ce " Rex , koma ka konta " ya fada da turanci kamar an yi mishi dole


Cak Safa ta tsaya ta zuba mishi ido babu ko kiftawa kamar wadda ta ga wani abun tsoro
Ta na a haka ta ji an fara tako stair a hankali
Daka kan ta ta yi ta kali stair din , Dum ta ji zuciyar ta ta buga har sai da ta zaro idanu ta na kallon Amar da ke sauko stair din a hankali ya na latsa wayar shi kai a sunkuye
Ya na sanye da wando three cuter black colour da t-shirt white colour


Sai da ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofa geffen Assad ba tare da ya dago kan shi ba , ya jingina a jikin headboard din sofar ya daura kafa daya bisa daya sannan ya ce " da ga zuwan ka sai aiki, ko hutawa ba ka yi , kar ka manta Hutu fa mu ka zo nan "
Shi sam bai san da Safa da ke tsaye gaban su ta zuba musu ido


Bangaran Safa kuma tun lokacin da Amar ya karaso cikin parlourn ta yi sumar tsaye , ita sai yanzu ta lura wanda ta fara yi wa magana ya dan fi Amar haske , ya fi shi murdaden jiki , ya kuma tara gashi ba kamar Amar ba , bayan haka su na kama tak kamar an tsaga kara


A hankali Assad ya mike tsaye ya na rike da laptop din shi cikin wata sexy voice din shi ya ce " Rex let's go " ya fada ya na takawa , da sauri Rex ya mike ya bi bayan mai gidan shi , a tare su ka Haye stair su ka bar Safa da Amar cikin parlourn


Sai da su ka bar wajen sannan Amar ya ajiye wayar shi saman cinyar shi ya dako kai a hankali
Bai sauke idanun shi ba ko ina sai saman Safa da ta yi sumar tsaye ta na kallon shi


Dan karamin murmushi ya yi kafin ya mike tsaye ya nufo ta na fadin " Miss Safa what are you waiting for here ? Please come have a seat " ya fada ya na nuna mata Sofar da ke geffen ta


Wasu yawu ta hadiye murya na kerma ta ce " Doctor , wanene wannan wanda na tardo , wlh na zata kai ne har na yi mishi magana "


Murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " he is my twins , mu yan biyu ne "
A hankali ta gyada kan ta
Kallon Snoopy Amar ya yi kafin ya ce " Aboki na , tare ku ka zo kenan ? " ya kai karshen ya na mika mishi hannu , ba musu Snoopy ya nufe shi da gudu ya Haye jikin shi ya na haushi kadan kadan


" please mu je ki zauna tun dazu ki na tsaye "
Ba musu ta karaso wajen sofa ta zauna ta na kallon shi
Shi ma wajen sofar da ya taso ya koma ya zauna tare da Snoopy
Sai da ya zauna sannan ya ce mata " how are you , da fatan na baro ki lafya "
Sai yanzu ta saki wani cool murmushi kafin ta jinjina mishi kai allamun e


Murmushi shi ma ya yi mata sannan ya ci gaba da shafa jikin Snoopy
Cikin nitsuwa ta ce mishi " Doctor wata Alfarma ce na zo nema wajen ka "
Slowly ya dago kai ya kale ta ya daga mata gera guda allamun minene
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " Please idan ka samu dama ina son ......."


Ba ta karasa maganar ta ba ya daga mata hannu alamar ya isa haka sannan ya ce mata " ba damuwa sai dai Friday din ga ba zan samu damar tafiya ba sai dai Next week "
Dan zaro idanu Safa ta yi baki sake cike da mamaki ta ce " ta ya a ka yi ka san abun da ya kayo ni ? "


Dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " kin manta ina Following duk Chanel din ki , ai da haka ne na samo in da ki ke " ya kai karshen ya na daga mata gera guda
Wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " ohhh Musadeeq , ni na ma manta ! Thank you so muchhhhh , dama Boss di na ne ya kawo shawarar , amma gaskia zan ji dadin yin hira da kai "
" zan iya tambayar ki wani abu ? "
Gyada mishi kai ta yi allamun e


Dan matso wa ya yi bakin sofar ya rike hannayan shi ya ce " kin San na jima ina bibiyar chanel din ki , kuma duk yawwan cin hirar da ki ke yi a kan health ne , zan so in san tsakanin aikin JARIDA da na LIKITA wanene ya fi burge ki ? "


Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " aikin JARIDA mana shi na fi so "
" to me ya sa duk hirar da za ki yi a kan health , why ba za ki maganar wasu abubuwa daban kamar abun da ke faruwa cikin society din ku "


Dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce " Saboda shi kadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login