Showing 33001 words to 36000 words out of 133773 words

Chapter 12 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9704

Safa ta yi allamun a'a


Murmushi takaici momy ta yi kafin ta ce " wai so ya ke ya aura miki Sami "
Tsaki Safa ta yi kafin ta kauda kan ta gefe cikin ko in kula ta ce " and so what dan ya ce hakan , cika baki ne kawai "


" Safa kin san abun da ki ke fada wai , ce miki na yi aura miki Sami ya ke son yi , za ki ce min h..... "


Cikin nitsuwa Safa ta katse ta da cewa " momy wlh ke fa ki ka damu da maganar wannan mutun , ba shi da iko a kan rayuwa ta , shaidar shi guda ya ce ni ɗiyar yayan shi ce , idan na kai wannan gaban kotu cewa zai yi ni ɗiyar matar shi ce kawai ba shi da hakin aurar da ni , wlh momy babu wanda ya isa cikin duniyar nan ya saka ni abun da ban yi niya ba bayan Daddy da momy , ko ke kin ci darajar sunan momy da na ke kiran ki da shi " ta na gama fadar hakan ta tashi ta nufi stair da sauri ta Haye


Ta na hawa Snoopy ya tashi da gudu ya bi bayan ta
Ita dai momy da kallo ta raka ta har sai da ta Haye sannan ta juyo ta na sauke ajiyar zuciya dan ta san halin Safa duk in ta ce ba ta san abu ko sama da kassa za ta hade ba za ta so shi ba , shi ya sa ta ke bin ta ta lalama in ta ce da karfi za ta bin ta za a yi kayan kunya









▪WASHE GARI MISALIN KARFE 10 NA SAFE









▪ABUJA ( GIDAN SU TWINKLE )








Zaune duk mutanan gidan su ke cikin parlour har da Daddy
Kallon Sami Daddy ya yi kafin ya ce " kai Sami na yi magana da Aziza a kan auren ka da wannan yarinyar , ta ce ita ba ta yarda ba , dan haka ni ba zan matsa mata ba dama ba son auren na ke ba , dan haka ka nemi wata yarinyar daban "


Da sauri Sami ya katse shi da cewa " haba Daddy , kai fa ka ke da iko da ita ba aunty ba , why za ka hana ni auren ta , i really love her "


" yaya Sami, wai wace yarinya ce wannan ? " Raïssa ta tambaye shi
" Safa " ya fada a takaice ba tare da ya kale ta ba


" What ? Wannan sakarar yarinya za ka ce ka na so , ai ka fi karfin ta yaya Sami " ta fada da dan karfi


Hararrar ta Noor ta yi kafin ta ce " ta dai fi karfin shi " ta kai karshen ta na murguna mishi baki


" Daddyyyyy ? " Raïssa ta fada ta na marairaice murya ta kali Daddy wai ita ta ji haushin maganar Noor


Kallon Noor Daddy ya yi ya ce " baby na , ki daina saka bakin ki in manya na magana , Raïssa yayar ki ce , ki dinga girmama ta kin ji ko ? "


Shagwabe fuska ta yi cikin ladabi da biyaya ta ce " To shikenan Daddy , Sister Raïssa ki yi hakuri ba zan kara ba " ta kai karshen ta na kama kunnuwan ta kamar da gaske


Hararrar ta Raïssa ta yi , kafin ta ja tsaki ta kauda kai gefe
" Raïssa ba ta baki hakuri ba komai ya wuce , sannan ku ma ina jiran maganar ku har yanzu ban manta ba "


A tare Farida da Fadila su ka ce " Daddy I'm not ready for marriage please " su ka fada su na marairaice fuska


Dan karamin murmushi ya yi kafin ya " hmmm za ku ga aiki na , ke Raïssa idan ba ki da mijin aure , akwai yaron kanwar mahaifiyar ku da ke karatu a UK na ji cikin next week zai zowa , idan ya zo zan mishi magana ya zo ki gan shi in ya yi miki zan kira Aunty ta ki na fada ma ta sai a shirya auren ku "


Kamar da ga sama su ka jiyo Muryar TWINKLE ta na fadin " in ya yi mata ? Ka ce in ta yi mishi dan in ba ya son ta ba za a iya mishi dole ba "


Hararrar ta Raïssa ta yi kafin ta ce " to ke zakakiya wa ya sawo bakin ki "


A tare Daddy da Sami su ka daka mata tsawa sannan Daddy ya daura da cewa " wannan matsayin mahaifiyar ki ta ke , ban son iskanci , ya za ki kale ta ki fada mata irin wannan maganar , maza ba ta hakuri "


Kauda kai gefe Raïssa ta yi
" Dad dalilin mi za ta ba ta hakuri , da ba ta shigo maganar da ba ta shafe ta ba ai da ba za a ba ta amsa ba " Khalifa ya fada ya na tabe fuska kamar da shi a ke


A hankali TWINKLE ta mike tsaye ta fara takawa ta Haye stair
Da kallo Raïssa ta bi ta har sai da ta Haye sannan ta ja dan tsaki ta ce " ki fi ruwa gudu , in in tashi ki je bangon duniya ma "


Cike da bacin rai Sami ya ce " ke Raïssa wai me ya sa ba ki da kunya ne , ko dan shekarun ta ba za ki girmama ta ba "


Tsaki ta ja ta na kauda kai gefe , hakan ko ba karamin batawa Sami rai ya yi ba
Cikin zafin nama ya taso da ga saman sofar shi ji ka ke Tasss ya wanke ta da wani gigitacen mari ya na nuna ta da dan yatsa cike da bacin rai ya ce " ba tsaren wassan ki ba ne ni , in shi khalifa ya kyale ki , ni zan kashe ki cikin gidan nan , ba karfi na ki ka ci ba dan haka nan gaba ki san irin abun da za ki fada min , idan ba haka ba gidan nan zai ma na kadan sakara kawai "
Ya na gama fadar haka ya juya ya fice parlourn da sauri


Ya na fita Daddy ya mike shi ma ya Haye stair ya bi bayan matar shi ba tare da ya ce komai ba
Ya na barin wajen Noor ta bushe da wata irin shegiyar dariya har da tappi ta tashi da gudu ta Haye stair ta na fadin " Allah calama Allah gwandama Allah kara " ta fada cikin jan fada


Da hararra Raïssa ta bi , ji ta ke kamar ta tashi ta shako ta ta tilo ta ta stair din ta mutu kowa ya huta dama ga bacin ran marin da Sami ya yi mata ita ta zo ta kara mata wani bacin ran


Tsaki Khalifa ya yi ya na tashi shi ma ya fice gidan
Ya na barin wajen Fadila ta mike ta zo geffen Raïssa ta zauna ta dafa kafadar ta ta ce " Sis tsaya ki ji , kin ga wadanan matan uku , duk sai sun malake zuciyoyin mazan gidan mu , ko shi khalifa da aure na iya shiga tsakanin shi da Noor da ya ce ya na son ta , gwara ki ba kan ki lafya ki rungumi sorry " ta kai karshen ta na yar dariya


" Fice min da ga nan " Raïssa ta fada cike da bacin rai


Daga kafadun ta Fadila ta yi kafin ta tashi ta koma gefe Farida ta zauna ta ci gaba da latsa wayar ta
Ita dai Farida ba ta cewa komai , sai faman latsa waya ta ke ta na sakin wani dan karamin murmushi













▪KADUNA (G.R.A )












▪Safa 💋












Zaune ta ke cikin parlourn su na sama , ta na faman latsa wayar ta cikin konciyar hankali , Snoopy na konce geffen ta saman sofa


Su na a haka wata waya da ke saman table din gaban ta ta fara ringing
A hankali ta kai hannun ta ta dauki wayar ba tare da ta janye idanun ta da ga kan wayar hannun ta ba


Kiran ta dauka ta kai wayar kunne ta yi sallama a hankali , da allamun hankalin ta na tare dayar waya


Ba tare da an amsa sallamar ta ba ta fara jiyo kuka kassa kassa
Da sauri ta ciro wayar da ga kunnen ta ta kali screen din
A rude ta meda wayar a kunne ta na fadin " Djami lafya me ke faruwa ne ki na kuka haka "


Cikin kukan na ta ta ke fadin " pretty don Allah ki zo ina son ganin ki "
" calm down , fada min me ke faruwa ne ? " Safa ta fada cikin nitsuwa
Ba tare da ta ba ta amsa ba ta katse kiran


Saukowa wayar Safa ta yi ta na bin screen din da kallo
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kali Snoopy ta ce " Baby zan fita ka ji , kar ka yi barna, in ka na son wani abu ka fadawa Balki " ta kai karshen ta na daura hannun ta saman kan shi ta shafa kadan kafin ta janye ta dauki wayoyin ta , ta mike ta nufi bedroom din ta


After some minutes ta fito sanye da wata gown pink colour mai zanen flower , ta na da shilalen hannu , gown din ta yi mata kyau over
Ta yi Rowling veil din ta pink colour shi ma a kai , ta na rataye da wata bag fara yar madaidaiciya sai tashin qamshi ta ke


Kai tsaye gidan ta fice cikin motar ta , ta na tafiyar ta kamar ba jiran ta a ke yi ba


Sai da ta dauki wajen good 15 minutes kafin ta iso gidan su Djamila
Bakin kofar gidan ta yi parking sannan ta sauko ta shiga gidan ta na taku kamar wanda kwai ya fashe mata a ciki


Ta na shigowa harabar gidan ta ja birki , ta na kallon Djamila da ke konce a kassa ta na zubar da jini


Da gudu Safa ta yi kan ta a rude ta na fadin " Djami lafya me ya same ki haka Djami ? "


Ba ta gama rufe bakin ta ba wata mata ta fito da cikin wani dakin ta na fadin " abun kunyar da ta je ta debo mana shi ne ta yi kokarin kashewa "


" what ? Djami aborting ki ka yi ? " ta fada da dan karfi
A hankali Djamila ta girgiza mata kai ta kassa cewa komai saboda azabar da ta ke ji


Tsaki matar nan ta yi kafin ta juya ta koma cikin dakin da ta fito
Ta na shiga Safa ta ce " Djami wai me ya ke damun ki ne ? "
" don Allah ki taimaka ki kai ni asibiti , mutuwa zan yi " Djamila ta fada murya kassa kassa


A hankali Safa ta mike tsaye ta taimaka mata ta mike tsaye , ta na dafe da cikin ta
Ta na jan kafa har su ka fito gidan , Safa ta bude mata gidan baya ta kontar da ita sannan ta shiga gidan driver ta tada motar da uban gudu ta bar layin


Cikin abun da bai fi 10 minutes ba su ka iso wani private Hospital
Da gudu Safa ta shiga parking space ta yi parking motar ta ta fito da gudu ta nufi hall din likitar ta na kwallawa nurse kira da karfi ta kai karshen ta na karasowa Reception


Da sauri wata nurse ta nufo ta ta na tambayar ta lafya
Cike da rudu ta ke cewa nurse din ta zo akwai wata mara lafya cikin motar ta
Da sauri nurse din ta koma ta turo gado ita da wata nurse su ka fito su ka nufi parking space Safa na biye da bayan su


Su na isowa wajen motar ta yi sauri ta shiga gaban su ta bude mu su gidan baya inda Djamila ke konce
A tare su ka kakama su ka fito da ita su ka kontar da ita saman gadon su ka koma cikin Hospital din
Su na shigowa su ka wuce kai tsaye A&E Room da ita dan sun lura da jinin da ta ke zubarwa ga shi kuma ba ta cikin hayacin ta
Ita dai Safa tun reception ta tsaya ta na cika register









▪AFTER ONE HOUR














Safa ta na zaune saman waiting chair ta na faman latsa wayar ta cikin konciyar hankali
A haka wani doctor ya karaso wajen ya na yi ma ta sallama ya na tambayar ahalin yarinyar da a ka kawo yanzun nan


Cikin ko in kula Safa ta ce " mariniya ce , ni ka dai ce yar uwarta "
" okay , biyo ni office di na " ya fada ya na juyawa ya fara takawa ya yi gaba
Cikin konciyar hankali ta mike ta bi bayan shi ta na ci gaba da latsa wayar ta


A tare su ka shiga office din doctor su na yin sallama a tare
Shi ya nufi chair din shi ya zauna sannan ya ce mata bismillah ta zauna
Ba musu ta zauna saman chair din da ke fuskantar shi ta na kallon shi ba tare da ta ce komai ba


Cikin nitsuwa ya ce mata " shin kin san ta na da ciki ? "
Jinjina mishi kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba


Shi ma jinjina kan shi ya yi kafin ya ce " kin san da hakan , amma ba za ki iya tsaya ki kula da ita ba yadda ya dace "


Cikin nitsuwa Safa ta katse shi da ce " Doctor , ka fada min abun da ke damun ta kai tsaye ba sai ka shiga yi min kwana ba "


Dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " shikenan , maganin zubar da ciki ta sha , yanzu haka cikin da ke jikin ta ya zube , an yi sa'a ya fice ba tare da ya yi ma ta illa ba "


A hankali Safa ta lumshe idanun ta , ta sake budewa , cikin nitsuwa Safa ta ce ma Doctor " please Doctor zan iya samun ko da photocopie na rapport din ta ? "


" me kuma za ki yi da shi , ai aikin gama ya riga ya gama , ba anfanin da zai miki " Doctor ya fada cikin ko in kula


Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta matso ta kale shi cikin ido ta ce " Doctor , ba ita ba ta sha wannan maganin , ba ta shi akayi ba tare da sanin ta ba , ina bukatar rapport din dan na kai wannan karar gaban kotu , ya fuskanci hukuncin da ya dace "


Kare mata kallo da kyau Doctor ya yi na dan mintina kafin ya ce " shawarar da zan ba ki , gwara ki ba wa kan ki lafya ki je ki kula da yar uwar ki , duk da ban yarda da cewa ita yar uwar ki ce ba , amma hakan zai fi mu ku , ko kin kai wannan karar kotu ba abun da za su iya yi miki "


Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta koma jikin chair ta jingina ta na kallon cikin ido
Cike da kasaita ta ce mishi " ku na daya da ga cikin dalilan da ya sa mata ba su da daraja a cikin society din ga , a matsayin ka na doctor kamata ya yi ka fara tambaya ta ya a ka yi ta shan wannan maganin , da tunanin ka , ya kamata ka yi nazari a kan abun da na ce , ba da sanin ta ta sha wannan maganin , wanda ya yi mata cikin shi ya ba ta wannan maganin ta sha , yanzu a ganin ka inda ta mutu da kisan kai za a kira wannan abun , tun da ba ta mutu ba , abun da ta rasa ya kama a kwacin mata hakin shi , ni ba wani abu na roke ka ka , kawai photocopie na rapport din ta na ke so , sauran zancen duk ba na ka ba ne , dan na san ba abun da za ka anfane ni da shi bayan rapport din , dan haka kawai ka ba ni ba sai mun shiga musayan yawu ba "




Gaskia ba karamin kwarjini ta yi wa doctor ba yanayin da yi maganar ji ya ke kamar ya na magana da wani babban mutun da ya san ciwon kan shi , ba da yarinyar da sai ya yi d'iya da ita


Dan karamin murmushi doctor ya yi kafin ya dauki wani file ya fice office din
Ta wutsiyar ido Safa ta raka shi da kallo har sai da ya fita sannan ta juyo ta na sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta sannan ta daga kai sama


Jim kadan Doctor ya dawo rike da file din da wani kuma daban
Ya na zuwa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login