Showing 78001 words to 81000 words out of 133773 words

Chapter 27 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9719

su taba ganin shi ba , yau dai na je da kaina na kawo muku shi , alma bara dai mu ji ta bakin shi "
ta na gama fadar haka ta juya ta kali Amar ta ce " Doctor barka da zuwa hilin Abokiyar hira "




[17/09 Γ  18:33] MEERAH πŸͺ·πŸ©·:




πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«
( YAR JARIDA )
















πŸ₯€β€( A heart touching love story & destiny ) ❀πŸ₯€














STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸ•Š


【THE ROYALTY LOVE πŸ•Šβ€βš˜γ€‘








Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ : FREE BOOK


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀ : PAID BOOK









TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054










DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i






DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite














BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM












LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN


GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❀⚘EXILED PRINCE ⚘❀
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank


IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
Zain (Airtel)
08081129487


sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753














___________________πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š____________________
















ο½› PAGE 24 πŸ₯€ ❀ }
















shiru Amar ya yi bai ce komai ba , Asali ma ya sunkuyar da kai ya daura hannun shi saman Forehead din shi


Duk mutanan wajen shiru su ka yi su na kallon shi , su na jiran Amsar shi
ganin yadda ya yi shiru ya sa Safa cewa " Doctor are you okay ? " ta fada dan hankalin ta ya fara tashi


ta na gama fadar haka ta ga ya mike tsaye ya na kallon ta ya ce " I'm sorry Miss Safa but ba zan iya ba , saboda ke na shigo Nigeria , amma ba zo nan ba da niyar daukar shirin ki ba , no , i'm here just to tell you how much i love you , Na san za ki dauka da wassa na ke yi , amma gaskiyar da ke cikin zuciya ta ce na fada miki , I love you Miss Safa , I love you " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen ya fice dakin daukar baki daya


da kallo duk mutanan wajen su ka raka shi har sai da ya fice sannan mai kula da camera ya ce a yanke
haka kowa ya tsaya cirko cirko ya na kallon Safa da ta yi sumar zaune
da sauri Yasmina ta Haye plateau din ta daura hannun ta saman shoulder din Safa ta na tambayar lafia


a hankali Safa ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta juyo ta kali Yasmina ta saki wani cool murmushi ta gyada mata kai


su na a haka kawai Safa ta jiyo Muryar mai kula da camera ya na fadin " Miss Safa yanzu ya za mu yi , Guest din ya tafi , ko akwai wani a kusa ? "
a hankali Safa ta girgiza mishi kai allamun a'a
mikewa tsaye ya yi ya na shirin magana Yasmina ta ce " Ni zan iya zama guest din "


karasowa wajen mai kula da Camera ya yi ya na fadin " Yasmina , shirin nan fa abun da ya shafi lafiya mu ke dubawa , a sani na dai ke ba doctor ba ce , yanzu ya za mu yi , duk wasu shirye shirye da za a yi mun riga da mun yi , na san kuma Md ba zai ji dadin haka ba , ya kamata mu san abun yi "


" Mohamed , ni ba doctor ba ce amma ina da masaniya a kan wasu abubuwa da su ka shafi lafiya , Specially abun da ya shafi contraception "


a tare Safa da Mohamed su ka hada baki su na maimaita abun da Yasmina ta ce , sannan Mohamed ya daura da cewa " Yasmina contraception bai shafi lafiya ba , kuma ba na tunanin zai ...... "


bai kai karshen maganar shi Safa ta katse shi da cewa " Contraception ya na cikin fanin lafiya mana , ina ganin za mu iya yin hira a kai , akwai cutoci dayawa da a ke iya kamuwa da su ta hanyar Sex , akwai kuma hanyoyi dayawa na contraception da su ke hana kamuwa da wadanan cututuka , kamar Cutar HIV ni a gani hakan ma zai yi , mu fara daukar kawai , ya fi da babu , ko ya ku ka gani ? "


" Ni dai ban da matsala da hakan " Yasmina ta fada ta na kallon Mohamed
shiru ya yi na dan lokaci kafin ya ce " okay , amma kin tabbatar ki na da kwarewa a kai "
wani kyawatencen murmushi Yasmina ta saki kafin ta ce " kar ka samu damuwa "
" ni ma na san wasu abubuwa a kai , so kawai mu fara " Safa ta fada ta na kallon Mohamed
gyada musu kai kawai ya yi kafin ya juya ya koma saman kujerar shi
Safa da Yasmina su ma su ka nufi Chair din su ko wace ta zauna


su na zama Mohamed ya ba da umarni a fara daukar
ya na fadin haka Safa ta kali camera ta saki wani cool murmushi ta ce " Assalam alaikum , barkan mu da wannan lokacin , kamar dai kullum ku na tare da Safa , a cikin zauren mu na Abokiyar hira , na tashar Tauraruwa , a yau kuma ina tare da Abokiyar aiki na Miss Yasmina "


ta na gama fadar haka ta juya ta kali Yasmina ta ce " Yasmina barka da zuwa zauren Abokiyar hira , sai a yi wa ma su kallon mu sallama "


dan karamin murmushi Yasmina ta yi kafin ta ce " Assalam alaikum ma su kallon mu , na san ba sai na gabatar da kai na ba "


yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Gaskia ne ba sai kin gabatar da kan ki ba , yau ma su kallon mu ni da Abokiyar aiki na za mu tatauna ne a ka abun da ya shafi contraception , na san dayawa za su yi mamakin abun da na ce , ko kuma ku ce me ye anfanin shi , eh ba kunnuwan ku ba , contraception na fada , ku biyo mu dan jin Abun da za mu tatauna a kai , Miss Yasmina kamar dai yadda na fada yau a kan contraception za mu yi magana , dan so ni da ma su kallon mu ki yi mana karin bayani a kai , da kuma mahimancin shi "


dan jinkirtawa Yasmina ta yi kafin ta ce " Contraception dai hanyoyin da a ke anfani da su ne dan guje wa samun ciki ba tare da son ma'auren ta , yana taimakawa mace da namiji wajen gujewa daukar ciki a lokacin jima'i. Akwai hanyoyi daban-daban na hana haihuwa ga mata da maza. Yana da mahimmanci a yi la'akari da mafi kyawun hanyar hana haihuwa , wadda ba ta da hatsari ga lafiyar ku , mai sauki , without imposing too much stress on the couple , mai tasiri dan gujewa samun akasi , sannan kuma Reversible as soon as it stops "


a hankali Safa ta gyada kan ta kafin ta ce " Ko za ki iya fada mana wasu hanyoyin contraception "


" hanyoyin contraception gaskia su na da yawa , ba mamaki bayan wanda na sani akwai kuma wasun , akwai kuma wanda su ke shirin shigowa , akwai naturel method , local , chemical , oral , emergency contraception , gaskia abun da yawa "


" To ko za ki iya fada mana , wanda ki ka sani , kamar wanda anfani da shi ya yi dai'dai da ka'idodin da ki ka fada yanzu "


" yeah , akwai su dayawa kamar pill Haka , na san dayawan matan mu na Nigeria da shi su ke anfani , ba Nigeria kadai ba , ita ce wadda a ka fi anfani da ita a yau , sannan akwai condom , duk cikin contraception method shi ne ma fi sauki , a ko wace pharmacy za a yi samun shi , kuma ba shi da wata tsada ba zai wuce naira dari ba , bayan haka kuma ya na hana kamuwa da cututukan da a ke iya kamuwa da su lokacin sex , kamar dai cutar HIV , amma sai ki ga mutane dayawa wai su na jin kunyar su tafi pharmacy su ce condom za a ba su "


yar karamar dariya Safa da Yasmina su ka yi a tare sannan Safa ta ce " ko shi wanda ke sayar wa bai ji kunya ba , sai wanda ya je saye ? "


dariya kadan Yasmina ta yi kafin ta ce " ni maganar ni ta ma ban dariya , amma haka ne yadda ki ka ce , ko shi wanda ya ke sayar wa ya na anfani da shi , na minene kai da ke je saye za ka yi kunya , ni fa duk abun da ya shafi lafiya ta ba na jin kunyar yin shi gaskiya "
" Gaskiyar ki , ai lafiya ita ce komai , Dayawan mutane su na jin kunyar magana ta wannan fanin , amma ban ga abun jin kunya ba , na ga abun da ya shafi lafiyar mu ce , ya kamata mu yi magana a kai , ko ba komai za mu karu da abun da ba mu sani na , Specially contraception ta na da mahimanci a yanzu bisa yadda how the demographics increase "


cikin nitsuwa Yasmina ta katse ta da cewa " don haka ne ake gudanar da gangamin wayar da kan jama'a a cikin al'ummar yankin don gudanar da family planning da kuma tazarar haihuwa , sai ki ga mace da yara Ι—aya Ι—aya har goma sha biyu , kuma dukan su bai wuce shekara guda ke tsakanin su ba "


" Sha biyu fa ? " Safa ta fada ta na dan zaro idanu


" wlh Sha biyu ko fin haka ma , yanzu ke yaro bai taso ba , ba ki fida shi nono ba , amma har ya na da kanne , ya za ki yi da su "


" shi ya sa contraception ke da mahimanci , za ki samu damar hutawa , shi ma yaron da ki ka haifa za ki samu damar kula da shi yadda ya kamata , shekarun nan na farko su na da mahimanci sosai wajen baby , a lokacin su na bukatar kulawa yadda za su taso babu wata tangarda "


" haka ne amma dayawa ba su gane wa , specially wanda ke cikin kauyuka , da kuma wa an da su ka yi karatun kur'ani tsantsa , da an dauko zancen family planning da tazarar haihuwa , sai ki ji sun ce , Manzon Allah ( S.A.W ) ya ce mu yi aure dan mu hayayafa , ya samu al'umar da zai yi alfahari da ita ranar gobe kiyama "


da sauri Safa ta katse ta da cewa " sai hankalin ka na waje guda za ka samu damar ba wa yaron ka tarbiyar da ta dace , duba ki gani yara nawa su ke kan titi su na bara , yara nawa ne ke gidan yari , an like su saboda an kama su , su na sata , sun kwace wa wannan waya , sun haura gidan wannan sun yi mishi sata , wasu har da makamai , duk terorrist din nan ba yara ba ne , su na da uwa , su na da uba , kun taba tambayar su dalilin da ya sa su ke yin hakan , ba komai ba ne rashin samun kula ne , kai yanzu ka na da yaro har wajen goma sha biyu , kuma aikin da ka ke bai wuce ya kawo maka dubu goma ga wata , ya za ka yi da abincin su , tufafin su , illimin su , kawai sai ki ga uba ya dauki yara wai ya kai su makarantar kwana ta islamya da ga nan ne yaran ke samun dama su zama bata gari , da ga baya a zo a na tsine wa yaron "


" ba laifin shi ba ne , laifin iyayen ne , tun farko da kun tsaya kun tsara rayuwar shi da hakan ba ta faru ba "
" wannan daukar Al'haki ne kawai , yanzu wace shawara za ki iya ba wa ma su kallon mu "


dan jinkirtawa Yasmina ta yi kafin ta ce " ni dai shawarar da zan iya ba wa ma su kallon , gaskia ban da ita "
a tare Yasmina da Safa su ka yi yar karamar dariya sannan Safa ta ce " kamar ya ba ki shawara "
" ah tom , kowa dai ya San me gyara shi "
dan gyada kan ta Safa ta yi kafin ta ce " Gaskia kam kowa ya San mai gyara shi , to ma su kallon mu a nan za mu kawo karshen shirin mu , Miss Yasmina sai a yi wa ma su kallon mu sallama "


kallon camera Yasmina ta yi ta na yi musu sallama
ta na rufe bakin ta Safa ta daura da cewa " da ga haka zan ce mu hadu da ku a sati a gaba cikin zauren Abokiyar hira tare da ni Safa , na bar ou lafya "


ta na gama fadar haka Mohamed ya daga murya ya na fadin " Cut ! "
ya na gama fadar haka Yasmina da Safa su ka mike da ga saman chair din su su ka sauko da ga saman plateau din
a tare su ka karaso wajen su Mohamed , ya na shirin magana da Safa kawai ya ga ta wuce shi ko sannu babu ta fice wajen baki daya
da kallo duk su ka raka ta har sai da ta shige lift ta bar wajen babu wanda ya yi kokarin tseda ta , sai ma aikin su da su ka ci gaba da yi


bangaran Safa kuma , ta na baro wajen daukar , ta nufi hall din fita building din baki daya , kai tsaye parking space ta nufa , wajen motar su


da sallama a bakin ta ta shigo motar , Amar ya na zaune wajen driver ya gama kan shi da steering motar
ya na jin sallamar ta ya dago kai a hankali ya saki wani cool murmushi ya ce " har kun gama "
" uhm " ta fada mishi ba tare da ta kale shi ba ta na kai hannu za ta saka belt din ta


bai ce mata komai ba ya tada motar su ka bar wajen baki daya
tafiya su ke yi saman titin ba wanda ke ce ma wani ufan
har sai da Amar ya karaso gidan su twinkle ya yi parking din motar bakin kofar gidan sannan ya kashe ta , ya juyo ya kali Safa cikin sanyin murya ya ce mata " ki yi hakuri na san na bata miki , na kassa jurewa ne , dole na fada miki abun da ke cikin zuciya ta , Safa i really love you , ban san ta ya hakan ta faru ba , kawai na kamu da son ki lokaci guda , ki yarda da ni wlh ba da niyar cutar wa na ke fada miki haka ba , zan so ki ba ni dama na gwada miki irin son da na ke miki pleaseeeeee " ya kai karshen ya na marairaice murya


slowly ta juyo ta kali shi na dan lokaci kafin ta saki wani cool murmushi ta ce " sai yanzu ka samu kwarin guyiwar fadamin ka na so na ? "
wani dan karamin murmushi geffen fuska Amar ya yi kafin ya ce " A yi min afuwa "
" matso ka ji "
ba musu ya dan matso da face din shi kusa ta ta
ita ma matsowa kadan ta yi da face din ta har su na iya jiyo nunfashin juna sannan ta ce mishi " Na jima da na san da wannan zancen , kawai dai na kyale ka na gani in za ka iya fadamin hakan ko kuma ka na jin tsoro " ta fada mishi cikin harshen Rassian
hakan na nufin duk maganar da ya yi da harshen Rassian ta ji shi ?


a razane ya dago kai ya na kallon ta , hakan na nufin duk maganar da ya yi da Rassian ta ji shi , har maganar da ya yi da Fares ?


* ai lokacin ne ma ta san cewa ya na son ta , in ba ku manta ba lokacin da ya ke wayar tare da Fares ya tambaye shi ya ta ke , ya ke fada mishi ta na da kyau sosai , a lokacin ta saki wani dan karamin murmushi , abun da ya fada ne ya sa ta sakin murmushin , amma shi bai gane ba , ku dai ku biyo ni dan jin yadda a ka yi ta ke jin Rassian language *


ya yi nisa cikin tunanin shi kawai ya jiyo Muryar ta , ta na fadin " please yi sauri ka dawo akwai wajen da na ke son zuwa "


" ba za ki sauko ba ke ? " ya fada mata
a hankali ta girgiza mishi kai allamun a'a
bai ce mata komai ba ya yi baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login