Showing 36001 words to 39000 words out of 133773 words

Chapter 13 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9713

ajiye mata sabon gaban ta ya ce " ga shi nan, duk wani abu da za ki bukata ya na ciki "


Slowly ta sauko da kan ta , ta dauki file din ba tare da ta yi mishi godiya ba, ta mike ta juya za ta bar office din


Har ta rike handle din kofar ta jiyo Muryar Doctor ya na fadin " wannan dakiyar ta ki ba za ta anfane ki ba in har wanda ya yi mata wannan abun ya na sama da ku , amma ina yi muku fatan sa'a, Allah ya ba ki ikon karbar ma ta hakin ta , ki je ta na cikin room 4 "


Jinjina mishi kai kawai Safa ta yi ba tare da ta ce komai ta sa kai ta fice office din
Ta na fita doctor ya saki wani cool murmushi shi gaskia bai ta ba ganin yarinyar da ta burge shi kamar wannan ba , da wannan tunanin ya ci gaba da aikin shi
[28/08 Γ  18:50] MEERAHπŸͺ·πŸ©·:






πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«
( YAR JARIDA )



















( A heart touching love story & destiny )


















STORY & WRITTEN BY : MEERAH ❀














Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ

❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀

( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯












TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i









TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY














BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM



















P A G E 1 2 πŸ₯€ ❀
























Safa kuma ta na barin office din ta wuce kai tsaye room 4 in da doctor ya fada mata
Bakin ta dauke da wasu kassa kassa ta shigo dakin , Djamila na konce saman gado ta kauda kai gefe ta daura hannun ta da ke sanye da catheter saman ciki , a na yi mata Karin jini


Chair din da ke bakin gadon Safa ta nufa ta zauna ta daura kafa daya bisa daya , ta nade hanayan ta a kirji , ta na rike da wayar ta da hannu guda


Cikin nitsuwa ta ce " Djami , ya jikin na ki ? "
Ba tare da ta kale ta ba ta ce " Da sauki "
Jinjina kan ta Safa ta yi sannan ta ce " Djami , bayan rabuwar mu , kin hadu da Mansour ne ? "


Gyada ma ta Djamila ta yi allamun e
" zan so ki fada min abun da ya faru lokacin da ki ka gan shi "


Ajiyar zuciya Djamila ta sauke sai da ta dan dauki lokaci kafin ta ce " Na fada mishi ina ciki , da farko ya bata rai har ya ce na zubar da shi amma na nuna mishi ni ba zan iya ba ina son baby na , ban san yadda a ka yi kawai kawai lokaci guda ya shiga ba ni hakuri , wai wassa ya ke min shi ma ya na son babyn , ni na dauka da gaske ya ke , da ga haka ya ce min mu tafi shan ice cream , ba musu na bishi mu ka tafi dan a lokacin gaskia ina kwadayin ta , bayan mun je restaurant din mun zauna ya ce min na jira shi zai yi order , sannan ya tashi ya tafi reception , jim kadan ya dawo rike da bowl din ice cream guda biyu , ya ba ni guda ya rike guda , mu ka cikin konciyar hankali ya na yi min wassa , har da cewa in na haifi mace sunan mamar shi zai saka ma ta haka dai na biye mishi mu ka yi hirar mu har wajen magriba sannan ya raka ni har kofar gidan mu kafin ya juya ya yi tafiyar shi , cikin daren na fara jin ciki na ya fara yi min ciwo kadan kadan , ban kawo komai a raina ba na yi barci a haka , washe gari tun wajen karfe 8 na fara jiyo hayaniya cikin gida , ina bude idanu na ciki na ya yi wata irin muguwar murdewa har sai da na yi kara , a hankali na fara jan kafa na fito dan neman taimakon mama , ina fitowa ko sannu babu ta hau ni da fada wai na jamu su abun kunya , ashe hayaniya da na ji , mahaifin Mansour ne ya zo ya ce an fassa auren mu dama tambaya ce kawai to sun janye , wai Mansour ya fada mishi ina dauke da cikin shege su kuma ba za su karbi dan gaban fatiha ba cikin ahalin su bare kuma wanda ba jinin su ba , da haka duk mutanan gidan su ka hau ni da fada har na fadi a wajen ciwon ciki na ya ci gaba da tsananta amma ba su lura ba , a haka har su ka watse su ka bar ni ni kadai a wajen , sai da na dan samu sauki dai'dai NaΓ―ma ta fito da ga wanka na roke ta ta dauko min waya ta har na samu na kire ki " ta kai karshen wasu hawaye na zubo mata




Ajiyar zuciya Safa ta sauke kafin ta sauke hannayan ta , ta kali Djamila ta ce " to sai ki kontar da hankalin ki yanzu , abun da su ke magana a kai Allah ya karbi abun shi , cikin ya Zube kin huta "


A razane Djamila ta ke kallon Safa ta na son ta yi magana amma ta kassa fitowa
Mikewa tsaye Safa ta yi sannan ta ce " zan je wani waje , yanzu ina dawowa " ta kai karshen ta na juyawa za ta bar dakin


Da sauri Djamila ta ce " Safa don Allah kar ki tafi ki bar ni " ta fada kamar za ta yi kuka


Juyowa Safa ta yi ta kale ta , ta saki wani cool murmushi ta ce " kar ki damu , yanzu ina dawowa ba zan jima ba " ta na gama fadar haka ta sa kai ta bar dakin
Ta na fita Djamila ta fashe da matsanincin kuka ta na dafe da cikin ta


Bangaran Safa kuma kai tsaye parking space ta nufa ta shiga motar ta ta fice Hospital din da matsanincin gudu
Cikin kankanin lokaci ta isa Police station
Ta na shiga ta yi parking motar ta ta fito ta shiga police station din ta na sallama kassa kassa kamar an yi mata dole


Duk officer din wajen sai da su ka hade yawu su na kallon ta da ga sama har kassa kowa na saka abun shi cikin zuciya
Sarai Safa ta lura da hakan amma ba ta bi ta kan su


Cike da nitsuwa da sanyin murya ta ce " please ina son ganin D.P.O "
Daya da ga cikin su ne ya ce " in kara ce ki ka kawo mu za ki fadawa ba sai kin kai ga D.P.O ba "


A hankali ta juyo kai ta kaleshi sama da kassa kafin ta juya ta kali wanda ke gaban ta ta ce " it's personal , amma tun da kun matsa , ku kiri D.P.O in da kan shi ka tambaye shi mun yi magana da shi zan zo , kuma ya ce idan na zo na same shi kai tsaye office din shi , dan kar ku ce na yi muku ba dai'dai ba ya sa na tsaya muku magana da kai tsaye zan wuce wajen shi , idan na fadawa D.P.O kun bata min lokaci na san ba za ki ji dai'dai ba "


Tsayawa officer din ya yi ya na kare mata kallo da kyau , zuciyar shi na gaskata abun da ta ce dan ta yi kama da irin manyan nan da su ke zowa wajen D.P.O kai tsaye
" okay za ki iya wucewa " ya fada mata ya na nuna mata hanya


Dan karamin murmushi ta yi na fadin " Thanks " sannan ta wuce wajen office din da ya nuna mata
Da kallo duka su ka raka ta har sai da ta shiga office din sannan officer guda ya ce " why za ka barin ta ta wuce a ka je karya ta ke yi ma na ? "
" to ko karya ta yi ma na ai ba za ta yi wa D.P.O ba , in har bai san da zuwan ta ba yanzu tsal za ta fito da gudu " wanda ya yi wa Safa magana ya fada ya na yar dariya


Bangaran Safa kuma a hankali ta shiga office din D.P.O ta na sallama
A hankali D.P.O ya dago kai ya na amsa mata sallamar ,
Ba laifi ya na da dan jini a jika dan a shekaru ba zai wuce 43 years ba haka , ya na sanye da kaki din shi


A hankali ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta kafin ya tambayeta me ya ke tafe da ita
A hankali ta janyo chair ta zauna sannan ta ajiye file din hannun ta saman table din
Cikin nitsuwa ta ce mishi " Good morning , my name is Safa , kara na zo ajiyewa ganin tsaya wa magana da wadancen bata min lokaci zai yi shi ya sa na wuto kai tsaye , wani ne ya yi wa friend di ta ciki sannan ya ba ta maganin zubar da ciki ba tare da sanin ta ba , wannan rapport din ta ne da ke nuna ta sha maganin zubar da ciki , yanzu haka ta na Asibiti a na kula da ita "


A hankali ta kai hannu ta ciro wayar ta da ga cikin jakar ta ta daura saman file din ta ce " cikin wannan wayar kuma akwai video na confession din ta yadda a ka yi ya ba ta maganin ba tare da sanin ta ba "


D.P.O na kallon ta cikin ido ya kai hannu ya dauki wayar ta , ya na kunnawa sai saman video din da ta yi wa Djamila ta na ba ta labarin abun da ya faru


Ashe rike wayar ta da ta yi video ne ta ke yi mata ba tare da ta sani
Duk abun da su ka tatauna sai da D.P.O ya ji ya kuma gani


Bayan ya gama kallon video din ya ajiye wayar gaban shi ya kai hannu ya dauki file din ya shiga dubawa


Ya na tsaka da dubawa Safa ta ce " cikin ice cream din ya saka mata maganin "


Slowly ya dago kai ya kale ta , ya ce " ta ya a ka yi ki ka san cikin ice cream din ya saka mata shi "


Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " hankali na ne ya ba ni "


Murmushi mai dan sauti D.P.O ya yi kafin ya ajiye file din geffen shi ya ce da ita " okay ba laifi , ki turo min video din da kuma pic din saurayin , idan mun kamo shi za mu mika karar kotu tare da hujojin da ki ka kawo " ya kai karshen ya na fido wayar shi ya mika ma ta tare da wayar ta


Karba ta yi ta tura mishi videon da wani pic na Mansour da ta taba dauka saboda bacin rana , to yau ranar ta baci


Ajiye wayar ta yi saman table ta tura wa D.P.O gaban shi sannan ta meda wayar ta cikin bag din ta ta ce " sunan yaron Mansour , gaskia ban san inda gidan su ya ke ba "


" ba damuwa wannan duk aikin mu ne , idan mun kamo shi za mu mika shi kai tsaye wajen kotu ba sai an yi shari'a ba ta yanke mishi hukuncin da ya dace "


Murmushi Safa ta yi kafin ta ce " Thanks a lot sir " ta kai karshen ta na ajiye mishi bandir din kudi yan dari biyar biyar a kila za su kai dubu dari daya


Mike wa tsaye D.P.O ya yi ya na fadin " no , ba sai kin ba da komai ba , ai hakin mu ne kula da al'umar da a ka ba mu , so rike kudin ki za su miki anfani wajen kula da friend's din ki "


Murmushi Safa ta yi kafin ta ce " nagode sosai , ni zan koma likita " ta kai karshen ta na mike wa tsaye za ta fice


Da sauri D.P.O ya ce mata " kin manta kudin ki "
A hankali ta juyo ta na fadin " ba komai tun da ba sai an bada komai ba , a rabawa yan wajen sadaka ce " to kai karshen ta na ficewa office din


Murmushi D.P.O ya yi kafin ya kai hannu ya dauki kudin sannan ya fito office din shi ma , a lokacin har Safa ta bar police station din baki daya


D.P.O na fitowa ya bi duk officer din da ke wajen ya ba su dubu biyu dubu biyu sannan ya ce musu zai turo musu hoton wani saurayi , ya na bukatar su tafi neman shi yanzu da ga haka kuma ya juya ya koma office din shi


Bangaran Safa kuma kai tsaye Hospital ta koma
Ta shiga Hospital din ta yi parking ta fito ta nufi kai tsaye dakin da Djamila ke konce


Bakin ta dauke da sallama kassa kassa ta shigo dakin
Yadda ta bar ta haka ta tardo ko motsi ba ta yi ba , sai dai jinin da a ka saka mata ya kare


Ta na shiga ta koma saman chair din da ta zauna da farko ta zauna ta na kallon ta ta ce " za ki iya tashi na Meda ki gida , dan ni fa ba na jin dadin zama a Hospital "


Jinjina mata kai Djamila ta yi ta na kokarin mikewa zaune , da sauri Safa ta mike ta riko hannun ta , ta janye mata catheter din a hankali sannan ta taimaka mata ta mike zaune kafin ta sauko da kafafun ta a hankali kassa


A hankali ta tsaye ta na cije lips din ta ba karya har yanzu ta na dan jin zafi , amma a hakan ta mike su ka fito Hospital din ita da Safa
Har nurse sai da su ka tsayar da su a kan ba a ba su izinin tafiya amma Safa ta share su , ta nufi motar ta ta budewa Djamila ta shiga sannan ta tada ta bar wajen da mugun gudu dama gwana ce ai


Kai tsaye gidan su ta nufa da Djamila , ita dai Djamila da ido kawai ta ke bin ta kassa cewa komai
Har sai da Safa ta karaso gidan su , nan Djamila ta sha ruwan idon ta, yau dai ta ga irin Daular da Safa ke ciki
Ba ta ida shan ruwan mamakin ta ba sai da su ka shigo parlourn nan ta zama cikakiyar bakyauya


Su na shiga Safa ta nufi doguwar Sofa ta Haye ta konta ta na warware veil din ta
Ita dai Djamila ta na tsaye bakin kofar ta kassa karasowa


Ganin hakan ya sa Safa dan dago kai ta na kallon ta ta ce " me ki ke jira a nan, zo zauna mana za a kawo miki abun sha na san ki na jin yunwa "


Ba musu Djamila ta karaso cikin parlourn ta na jan kafa a hankali ta zauna saman sofar da ke geffen ta Safa


Ta na zama ko Snoopy ya shigo da wani matsanincin gudu
A razane Djamila ta mike ta na sakin kara ta rasa wajen guduwa dama mugun tsoron kare gare ta


Da sauri Safa ta mike zaune ta na fadin " ke kontar da hankalin ki ba abun da zai miki " ta kai karshen dai'dai Snoopy ya karaso wajen kafar ta ya zauna ya na fido halshe waje ya na kallon Safa


A hankali Djamila ta koma ta zauna ta na fadin " Safa wannan abun da ga ina kuma "


Dan murmushi Safa ta yi ta na daura hannun ta saman kan Snoopy ta na shafawa a hankali ta ce " he is my baby , ko " ta kai karshen ta na dawo da kallon ta kan Snoopy
Dan karamin haushi ya yi allamun e


Da ga haka ta janye hannun ta , ta mike tsaye ta na fadin " baby , je ka cewa Balki mun yi baki ta kawo musu abun tabawa , Djami ki saki jikin ki , ni zan shiga wanka ina zuwa "
Ta na gama fadar haka ta fara takawa ta nufi stair ta Haye da sauri, ta na barin wajen Snoopy ya mike ya nufi dining room da gudu ya shiga kitchen
Ita dai Djamila da kallo kawai ta ke bin su , ta rasa abun da za ta ce


Ta na a haka Snoopy ya fito da ga kitchen da gudu ya nufi Sofar da Safa ta tashi ya Haye ya zauna ya na kallon Djamila da duk ta matse waje guda kamar ya ce zai cinye ta ,
A haka Balki ta fito ta same ta
Cikin girmamawa ta gaishe ta sannan ta ajiye ma ta tray din snacks da fruits da juice , sannan ta juya ta koma kitchen
A hankali Djamila ta kai hannu ta dauki barin lemon guda ta fara sha dama yunwa ta ke ji tun jiya ba ta ci komai ba


After some minutes Safa ta fara sauko stair din a hankali ta na sanye da wani dan karamin wando zuwa cinya , da yar t-shirt duk pink colour , ta saki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login