Showing 6001 words to 9000 words out of 133773 words

Chapter 3 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9696

kadai ki ka shigo wajen nan "
" what ? " ta fada da dan karfi ta na zaro idanu
Da sauri ta juya ta na shirin barin wajen sai ga Snoopy ya taho da gudu ya fada jikin ta ya na haushi


Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta rungume shi ta na fadin " Ina kuma ka tafi haka , inda ka bace , ko wani abu ya same ka ya ka ke so na yi ? " ta kai karshen ta na sakin shi


Dan marairaice fuska ya yi ya na haushi kassa kassa
Hararrar shi ta yi ta na fadin " Snoopy ba na son Abun nan da ka ke yi min , in ruwa ka ke so ba za ka fada min ba inda ka bacce fa "


Kallon Nabil ta yi kafin ta ce " please za mu iya tafiya ? "
Jinjina mata kai ya yi kafin ya yi gaba ita kuma ta bi bayan shi ita da Snoopy su ka bar wajen


Su na barin wajen yarinyar nan da ta yi wa Safa magana da farko ta juya ta na kallon yan uwan ta ta ce " amma yarinyar nan ba ta da hankali ko , kun ga yadda ta ke ma karen ta magana kamar mutun "


Dariya daya da ga cikin matan wajen ta yi kafin ta ce " haba kema Mariam na mi ne ce mata ba ta da hankali , ba ki lura ba ba cikakiyar bahaussa ba ce , ta fi kama da yan china har idanun su , da haussar ta ma ba dai'dai ta ke ba , kin san fa su kare kamar mutun ya ke a wajen su wasu tun su na yara a ke ba su karnukan su girma tare , amma da ga ganin yanayin yar nan ba ta da matsala gaskia "


Tsaki budurwar da ta kira da Mariam ta yi kafin ta ce " kin ga Yasmina matsalar ki ce , wlh in ta shiga hanya ta sai na taka ta " ta na gama fadar haka ta juya ta bar wajen


Girgiza kan ta Yasmina ta yi ta na jinjina halin Mariam kamar ba ita ba ta fara yi ma Safa magana cikin fara'a


Bangaran Safa kuma a tare ita da Nabil su ka zagaye office din
Sannan ya nuna mata office din ta
Kun san halin yan tiktok , sai da ta ciro wayar ta , ta fara yi ma office din video ta na fadin " Hi my people barkan ku da wannan lokaci , yau dai Allah ya karbi adu'a ta , ga ni na shigo Tashar Tauraruwa as their new member , so ku kasance tare da ni ranar Friday a Tashar Tauraruwa dan ci gaban shirin mu na Abokiyar hira byeeee "


Shi dai Nabil ya yi tsaye ya na kallon ta , ya na murmushi , shi duk ba karamin burge shi ba ta yi , abun da ba ta sani ba Nabil ya jima ya na bibiyar ta saman Tiktok , instagram da sauran su


Sai da ta Kamala videos din ta sannan ta kali Nabil ta ce " Sorry ina son na yi introducing wajen aiki na ne "


Murmushi yayi kafin ya ce " na gane ba komai, in kin Kamala sai mu tafi ko ? "
Jinjina kai ta yi kafin su juya su bar office din su ka haura hawa na biyu inda su ke yin daukar shiryeΒ²n su sannan ta baro building din baki daya wajen 11 da rabi haka
[13/08 Γ  21:59] MEERAHπŸͺ·πŸ©·: https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY






πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«
( YAR JARIDA )




















( A heart touching love story & destiny )


















STORY & WRITTEN BY : MEERAH A.K.A ANISH πŸ”₯❀✌




Marubuciyar littafin




TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ




❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
πŸ‘‡πŸ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i












TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP FAN'S GROUP


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY














BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM


























PAGE 3 πŸ₯€ ❀
































β–ͺSafa πŸ’‹
































Zaune ta ke cikin motar ta , ta yi parking bakin titi , ta kurawa wani kyakyawan gida ido babu ko kiftawa


Ta na a haka Snoopy ya yi mata haushi
A razane ta dawo cikin hayacin ta juyo ta kaleshi ta ce " haba Snoopy ka ba ni tsoro "
Yanzu ma haushi ya sake yi mata


Juyawa ta yi ta kali kofar gidan cikin murya mai sanyi ta ce " na sani , na cewa momy ba zan zo gidan nan ba amma zuciya ta , ba za ta iya jurewa ba "


A hankali ya marairaice murya ya na yi mata haushi kadan kadan
Hada kan ta ta yi da steering din motar sannan ta ce " Snoopy , don Allah kar ka fadawa momy , wlh ina son na je , zuciya ta na bukatar ta gan ta , amma ina jin tsoro "


Ta na gama fadar haka ya mike ya na haushi mai karfi
Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " na sani Snoopy ba za ka bari wani abu ya same ni ba , amma ai ita , za su iya yi mata ila idan mu ka tafi "


Daura hannun shi ya yi saman hannun ta
Daura hannun ta ta yi saman na shi sannan ta ce " Snoopy wlh tsoro na ke ji "


Janye hannun shi ya yi sannan ya juya ya daura su saman glass din kofar geffen shi , ya na haushi kwarai
Murmushi mai sauti ta yi kafin ta ce " kai ko "
Ta na gama fadar haka ta dago kan ta ta kashe motar , sannan ta bude kofar ta, ta fito

Ta zagayo ta budewa Snoopy kofa ya fito sannan ta like kofar ta ce mishi " mu tafi to , ban da jan fada don Allah "
Dan haushi ya yi mata kafin ya juya ya kali titi hagu da dama sannan ya tsalaka da gudu
Murmushi ta yi kafin ita ma ta bi bayan shi su ka iso bakin kofar gidan


Ta na isa bakin karamar kofar ta yi knocking
Bugu daya ta yi wani gateman ya bude mata kofar ya na tambayar wanene
Gaishe shi ta yi kafin ta ce " don Allah matar gidan ta na nan "


Gare mata kallo da kyau ya yi , sai ya ga ta na kama da yan gidan
Bai tsaya wani batta lokaci ba ya bude mata kofar ya na fadin " e ta na nan bismillah "
Murmushi ta yi kafin ta ce da Snoopy su ta fi ta na yin gaba , shi kuma ya bi bayan ta


Gidan gaskia ya na da girma ga kuma kyau ya tsaru iya tsaruwa
Geffen dama wani makeken parking space cike da motoci tsadadu kalla kalla , colour daban daban , white navy blue black sky blue pink duka akwai a kila motocin su kai wajen goma sha biyu


Geffen hagu kuma wani katon filin buga basketball da kuma na ball
Da ga bayan su kuma wasu runfuna ne guda biyu dauke da lilo wajen na zagaye da ciyayi sa flowers kamar garden


Wani balcony ta nufa mai dauke da wasu chair inrin na karfe haka guda uku , dayar ta fi girma sai yar karamar table da ke tsakiyar su


Ba ta tsaya wani kale kale ba ta nufi kofar da za ta sada ka da Parlour din gidan
Doorbell ta danna sannan ta ja baya kadan ta na jiran a bude mata
Shiru ba a bude mata ba har sai da ta danna sau uku , kafin wata House maid sanye da wasu kaya navy blue kamar uniform ta bude mata kofar ta na mata bismillah ta shigo


Ba musu ta daga kafa ta shiga parlourn zuciyar ta na duka uku uku , kamar ta juya ta bar wajen da gudu


Ta na shiga parlour din wani sanyi mai dadi ya dake mata fuska
Gaskia falon nan ya hadu kamar da glass a ka yi shi


Ka na shigowa ka na fuskantar wasu Stairs guda biyu zagaye da glass , da ga saman su ka na iya hango balcony din dauke da wasu sofas masu kyau da kyali navy blue


Taku biyu ta yi a hagun ta , nan na ga wani tanpasheshen Parlour ya kyawatu da fournitures tsadadu masu bala'in kyau
Tsaya wa zanya na muku kyau wannan parlour sai kun ce karya na ke
Sofas din wajen guda shida kuma duka navy blue ne , biyu Three seater , biyu two seaters , biyu one seater
Da ga tsakiyar su kuma wata makekiyar table ce ta glass fara kal , kassan ta kuma wani lalawsan carpet ne white colour mai ratsin blue , abun ba karamin kyau ya karawa wajen ba
Su na fuskantar wata makekiyar Tv plasma , kassan ta kuma wata drawer ce , dauke da wasu vase guda biyu na glass dauke da Roses ciki abun ba karamin kyau ya yi ba
Cen bayan sofas din wata dining room ce dauke da dining table white colour ta glass zagaye da chais wajen 12 , six navy blue , six white colour
A geffen damar dining room din wata door ce ta glass wadda za ta sada ka da kitchen din gidan
Gaskia gidan ya hadu tsayawa fada muku yadda ya ke zai daukin mana duka book din na , so kowa ya ci gaba da kwakwolwar shi




Ta na shigowa cikin falon ta yi arba da wasu yan mata guda biyu su na zaune saman sofa three seaters sun daura kafa daya bisa daya
Su na sanye da wando jeans Baki , da T-shirt mai kananan hannu , guda pink colour gudar kuma Orange , kan su Na sunkuye su na latsa wayar su kira Iphone 13 pro max pink colour duka biyun


Kamanin su daya dan da ga gani ka san twins ne , a shekaru za su kai 19 to 20 kennan sun bawa Safa shekara guda
Launin skin din su Chocolate ne mai matukar kyau , da ga gani ka san renon madara da ice cream ne , sun yi luwai luwai abin su


Safa na ganin su ta saki dan karamin murmushi ta ce " Fadila , Farida sannun ku "


Slowly su ka dago kan su a tare su na yi mata wani banzan kallo
Amma ita Safa ko a jikin ta , sai ma kara fadada murmushi ta da ta yi


Mai sanye da t-shirt orange ce ta fara magana ta ce " ke me ki ke yi a nan , Get out "
" Fadila ba wajen ki ba ta zo , wajen wacen basamudiyar kamar ta ta zo " wadda ke sanye da t-shirt pink ta fada


Dawo da kallon ta ta yi kan yarinyar ta na hararrar ta ta ce " mu ba mu da samudawa cikin gidan , sai dai y'ay'an Fir'auna "
A tare su ka Bushe da dariya har da tapi


Safa dai da kallo ta ke bin su ba ta da abun da za ta ce musu
Sai da su ka ida dariyar su sannan ta ce " Farida momy ta na nan wajen ta na zo "


Wani mugun kallo Farida ta yi mata kafin ta ce " wacece momy a nan , ai ba ki da wata momy a cikin gidan nan "
Da sauri Fadila ta katse ta da cewa " ke Fifi Twinkle ta ke nufi "
" o ki na nufin wannan mai kananan idanu kamar ke " Farida ta fada ta na nuna ta da yatsa


Murmushi Safa ta yi ta na jinjina musu kai allamun e
Dariya su ka sake yi a tare dai'dai lokacin da wata kyakyawar yarinya ta ke sauko stair din
Ta na sanye da mini skert zuwa guyiwa , da T-shirt white colour , ta na tafe kai a sunkuye ta na latsa wayar ta


Kamanin ta sak da na Safa babu inda ta baro ta , saidai wannan ba ta da shape kamar Safa kuma karama ce dan a shekaru ba za ta wuce 12 years ba


A hankali ta ke sauko stair din har sai da ta karaso ta wuce Safa ta zauna saman sofa one seater ta na ci gaba da latsa wayar ta


Ta na zama Fadila ta harare ta ta ce " ke malama tashi ki je ki kira uwar ki "
Slowly yarinyar ta dago kai ta kali Fadila da ga sama har kassa kafin ta ja tsaki ta ce " tun da ta ki uwar ta bace ko " ta kai karshen ta na kauda kai gefe


Nan idanun ta su ka sauka kan Safa tsaye tun dazu ta saki dan karamin murmushi
Ta na ganin Safa ta saki wani cool murmushi sannan ta mike ta nufi Safa ta rungume ta , ta na fadin " Safa , i'm really happy to see you , how is your way "


Rungume ta Safa ita ma ta yi ta na fadin " fine sister ! Na same ki lafya " ta kai karshen su na raba jikin su


Murmushi yarinyar ta yi kafin ta ce " fine sister , samu waje ki zauna bari in kawo miki ruwa na san kin debo rana "
Da sauri Safa ta ce " no momy kawai na zo gani wucewa zan yi "


Daga kafadun ta yarinyar ta yi ta na fadin " okay bara na je na kira miki ita " ta kai karshen ta na juyawa ta hau stair da gudu
Kamar da ga sama ta jiyo muryar namiji da ga bayan ta ya na fadin " wacece wannan kuma "
Dum Safa ta ji gaban ta ya fadi , dan ta gane kowane


A hankali ya karaso cikin parlourn ya tsaya gaban Safa ya zuba mata idanu
Kyakyawan saurayi ne sanye cikin wandon jeans brown da t-shirt red ya yi wani shegen aski da ga ganin shi ka san ba mutun kirki ba ne


A hankali Safa ta dago kai ta na kallon shi ta ce " good morning khalifa "
" ke sunan nawa za ki kira kai tsaye babu ko girmamawa " ya fada da dan karfi


Dariya Farida da Fadila su ka yi kafin Fadila ta mike ta karaso geffen Khalifa ta tsaya ta nade hanayan ta a kirji ta na fadin " yo dama ina ta ga tarbiyar da za ta girmama na sama da ita kar ka manta fa jinin kafurai ce "


Wani mugun kallo Safa ta yi ma Fadila kafin ta ce " gwara jinin kafuran da jinin azzalumai mara imani ko ba komai ba ma cin amanar yan uwan mu "
Zaro idanu Fadila ta yi ta na kallon ta ce " ke wa ki ke fadawa haka "
Tsaki Safa ta ja ta na kauda kai gefe ta ce " wanda ya bawa kan shi "


" ki yi hankali cikin gidan mu ki ke fa " khalifa ya fada ya na nuna ta da yatsa
Ba tare da ta kale shi ba ce " oh dama abun wani ya na zama na wani , kamata ya yi kace gidan satar ku "


Maganar ba karamin sosa wa khalifa zuciya ya yi , ya ma rasa abun da zai yi mata , kawai sai ya juya ya kama stair guda ya Haye dan ya san in ya ce zai sa ma Safa hannu sai dai a dauki gawar ta


Ya na Hayewa wannan yarinyar ta sauko ta na rike da hannun wata kyakyawar mace fara kal , da ga gani kassan cikakiyar yar china ce dan babu ta inda ta baro yan china , ta na kama sak da Safa da yarinyar da ke rike da hannun kawai dai ta dan lattijantaka , amma yanayin jikin ta ya na samun hutu , a shekaru za ta kai 50 years haka


Safa na ganin ta saki wani kyawatencen murmushi nan take idanun ta na kawo ruwa amma ba ta bari sun zubo ba


Haka itama wannan matar ta na ganin Safa ta saki wani cool murmushi ta ida sauko stair din
Da sauri ta nufi Safa ta rungume ta ta na fadin " Safa na , ya ki ke na yi kewar ki sosai my daughter "


" na yi kewar ki ni ma momy " Safa ta fada hawaye na zubar mata
Raba jikin su matar nan ta yi da na Safa kafin ta juya ta kali yarinyar nan ta ce " Noor kawo wa sister din ki ruwa mana "


Har Noor ta juya ta nufi dining room Farida ta taro ta da cewa " ke malama tsaya nan ba gidan ciyar da marayu ba ne "


Murmushi takaici Safa ta yi kafin ta ce " no momy ni ba na bukatar komi, na zo ne kawai don na gan ki , tun na gan ki yanzu zan koma "


Ba ta gama rufe bakin ta ba Fadila ta ce " haii barka to malama sai a fice mana da ga gida " ta kai karshen ta na shirin sa hannu ta tura Safa


Da sauri Snoopy ya shiga tsakiyar su ya na kallon Fadila ya yi mata wani irin haushi har sai da ta saki kara ta yi baya da gudu


Da sauri Safa ta ce " kai Snoopy ya isa haka "
Wani dan karamin haushi ya yi kafin ya girgije ya koma bayan Safa ya tsaya
" momy ni na tafi amma zan dawo " ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login