Showing 63001 words to 66000 words out of 133773 words
ya kalli kofar kassa kassa ya ce " I'm really afraid that you feel the same way as me right now , na san ba za ka iya jure irin wannan radadin ba " ya kai ya na juyawa ya meda hankalin shi kan laptop din shi
* SAFA π
Bayan ta shiga gidan su kai tsaye bedroom din ta ta wuce , ta shiga toilet ta yi wanka ta dauro ta Alwalla sannan ta fito ta shiga dressing room
Nan ma ba ta jima ba ta fito sanye da wata Abaya red colour ta yi Rowling veil din ta a kai
Kai tsaye wajen daddumar ta ta nufa ta hau ta tada sallar sa , sai da ta hada da ta azahar sa ta rasa duk ta yi , sannan ta zauna karatun kur'ani da kuma aduo'i sannan ta tashi ta Haye bed din ta ta konta ta na kallon ceiling
Ta dauki wajen good 30 minutes a haka kafin ta fara jiyo Muryar Amar a hankali ya na karatun kur'ani
Dan lumshe idanun ta ta yi a hankali kafin ta sake bude su , Slowly ta juyo ta kali saitin inda ta juyo muryar ta shi
Nan ta gan shi zaune saman sofa ya na rike da Alkur'anin ta ya na karantawa
Shiru ta yi ta na sauraron shi yadda ya ke karatun cike da nitsuwa da zazzakar muryar shi , nan take ta ji duk zuciyar ta ta fara yi mata sanyi
Sai da ya Kamala karatun shi sannan ya ajiye kur'anin saman table din gaban shi ya tasso slowly ya karaso bakin bed din ya zauna ya na kallon ta ba tare da ya ce komai ba
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " me kuma ka ke yi nan "
Gyara zaman shi da kyau ya yi ya jingina a jikin forehead din bed din , ya ce " no zo duba patient dita "
hararrar shi ta yi ta na fadin " wacece patient din ? "
" gaki nan konce " ya fada ya na kashe mata ido guda
Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " i'm fine so you can go now "
Noke kafada ya yi ya na fadin " no , ba inda zan je , sai dai ki tashi mu tafi tare "
Ba ta ce mishi komai ta yi dan karamin murmushi ta juya ta meda kallon ta kan ceiling
[13/09 Γ 00:30] MEERAH πͺ·π©·:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH π
γTHE ROYALTY LOVE πππΊγ
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ : FREE BOOK
β€β EXILED PRINCE ββ€ : PAID BOOK
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
ππππππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
πππππππ
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
ZA KU IYA SAMUN WANNAN PAGE A WATTPAD TA HANYAR WANNAN LINK
πππππ
https://www.wattpad.com/1476262651?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=bennybite
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
P A G E 20 π₯ β€
Sun dauki wajen good ten minutes a haka kafin Safa ta ce mishi " minene hadin ka da gidan da mu ka je da safe "
Kallon ta ya yi ya na fadin " ke ya kamata na fara tambayar me ye hadin ki da su dan tun da mu ka je gidan yanayin ki ya sauya "
Sai da ta dan dauki lokaci kafin ta ce " ni na fara tambaya "
Murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " labarin ya na da tsawo gaskia ban san ta ina zan fara ba "
" fara da ga farko mana "
Yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " okay zan fara da ga Farko , ni da Assad dai twins ne kamar yadda ki ka sani , Parents din mu duk haifafun Nigeria ne cikakun haoussawa ne , Mahaifin mu sunan shi Musadeeq Abdoul Qadir , mahaifiyar mu kuma Hassna , lokacin da su ka yi aure ina ga mahaifin mu ya na da shekara 25 , Mom kuma 18 , bayan sun yi aure sai da su ka dauki wajen one years ba su samu haihuwa ba , su na cikin ta biyu Mom ta samu cikin ta na farko , amma ba kai three months ba ya zube , ba su wani kawo komai a ran su ba su ka kai kukan su ga Allah cikin rahamar shi ko ba su kai ga yin two months ba ta samu wani cikin , a wannan karan ma ya sake zubewa , a yanzu ma ba su wani damu ba , asali ma bayan zubewar cikin , su ka bar Nigeria baki daya su ka koma UK da zama , bayan wani lokaci haka su ka sake wani cikin , yanzu ma ya sake zubewa , wannan karan ba su hakura ba sai da su ka je likita dan jin abun da ke damun su , nan doctor ya fada musu cewa , Mahaifar Mom ba za iya daukar baby ba , nan Doctor ya ba su shawarar su biya wata matar a dasa mata kon haihuwar su a mahaifiyar ta , sai ta haife musu babyn su in ya so da ga baya ko da biyan ta ne sai su yi , ashe lokacin da doctor din ya yi musu maganar akwai wata nurse me sunan Fatma da ta jiyo su , bayan sun baro hospital din nurse din ta biyo su har gida , nan ta fada musu cewar ta yarda a dasa mata kon haihuwar su , amma ta na bukatar kudin dan ta ci gaba da rayuwar ta a UK salary din ta ba ya isar ta kuma ta na da yan uwa da ta ke kula da su a Nigeria , ba musu su ka amince dan dama abun da su ke bukata kenan , a haka su ka fara zuwa Hospital a na Duba Mom har lokacin da ta samu ciki , a ka cire shi da ga jikin ta a ka dasa wa nurse din nan , a tare Mom da Dad su ka dinga kula da nurse din nan , har gida ta dawo da zama tare da su , a haka har lokacin haihuwar ta ya zo , ta haifi Twins maza kamanin su daya sai dai kwayar idanun su ta banbanta , nan kuma a ka samu matsala dan nurse din nan tsaye ta yi ta ce ta fasa ba ta son kudin a bar mata babyn ta , abun ba karamin tadawa Mom & Dad hankali ya yi ba , babyn nan ba na ta ba ne ita kawai ta yi sanadiyar shigowar su duniya ne amma babu daya me jinin ta , amma nurse din nan ta ki ta ce ba za ta iya rabuwa da su ba , sai da babyn nan su ka yi two weeks a hannun nurse din nan kafin a samu sulhu tsakanin su , nan Mom da Dad su ka hakura su ka ce za su iya bar mata baby guda , ta ba su gudan tun da su biyu ne , kuma za su ba ta makudan kudade yadda za ta kula da kan ta , ta kuma kula da babyn , har karatun shi ma sun dauki nauyin shi , jin hakan ya sa nurse din nan ta yarda , ta ba su babyn na farko , su na karbar shi ko kwana ba su yi ba a garin UK su ka shiga jet su ka koma RUSSIA da zama , ita kuma nurse din nan ta dauki babyn ta ta koma cikin ahalin ta da shi , nan kuma ta shiga sabuwar cakwakiya dan ahalin ta sun ce ba su yarda da yaron nan ba , dama ba karatu ta je yi ba yawwan banza ta tafi , duk yadda ta so ta kwatanta mu su yadda ta samun babyn sun ki yarda , haka ta dauki babyn ta , ta koma UK da shi , bayan na cika shekara hudu ta sake dawowa da ni Nigeria wajen Sister din ta wadda ita ce Matar uncle di na danmu ka je gani dazu da safe , da ga Nigeria kuma mu ka tafi RUSSIA wajen Mom & Dad di na , wani abun mamaki da mu je ka a ranar Mom ta haifi babys din ta da kan ta Twins kuma , ashe bayan tahowar su RUSSIA magani su ka fara nema har Allah ya sa su ka samu , mun yi One week a cen Momy ta ce za mu koma UK amma na ce ni ba zan je ba , zan zauna tare da yan uwa na , abun nan ya yi matukar kona mata rai har zubewa ta yi saman guyiwowin ta , ta na roko na kar na bar ta na yi hakuri mu koma , Nan ne Dad ya kawo shawarar ta bar ni a nan RUSSIA na yi karatu na , bayan na Kamala sai na koma cen UK wajen ta har na samu aiki , cike da zumudi na yarda saboda a lokacin da na ga Assad ji na yi kamar ba zan iya rabuwa da shi ba , shi ma haka ya ji cikin zuciyar shi amma sai ya danne ya na yi min fuska , ba dan Momy ta so ba ta hakura ta bar ni a RUSSIA ta koma UK amma duk bayan three months ta na zuwa gani na , sannu sannu na fara karatu a RUSSIA ni da Assad da kuma wani friend's din mu da ya zo da ga Nigeria shi ma , a haka har Wassiq da Wassif little brothers din mu su ka taso mu ka ci gaba da karatun mu a tare , Bayan wasu shekarun mu ka samu little sister kuma mai sunan Rahaf , amma mu na kiran ta da Puppy , lokacin da ta cika shekara 10 Mom ta rasu , a lokacin saura one years na Kamala karatu na na doctor , lokacin da momy ta dawo dan gani na ta ji labarin Mom ta rasu abun ya yi ma ta matukar Zafi , a lokacin har ta zauna a nan RUSSIA ta ci gaba da kula da Puppy saboda yanayin shekaru ga ta kuma ya mace kar ta taso ba uwa a kusa da ita , bayan na Kamala karatu na , sai momy ta ce za mu koma UK , ba yin da ba mu yi da ita ba a kan ta hakura mu zauna a RUSSIA mu zama family guda , Dad har rokon ta ya yi ta yarda ta aure shi dan su ci gaba da kula da yaran su tunda ai ita ma na ta ne , amma fir ta ki , ba yadda na iya dole na hakura mu ka koma UK , amma duk holiday din mu a RUSSIA mu ke yin shi ni da ita , kuma har izuwa yanzu ba ta taba yin aure ba , ni kadai ne yaron ta kuma ni kadai na rage mata dan duk ahalin ta sun rasu har sister din ta da ke nan Nigeria duk sun rasu shi ya sa ba ta son ina yin nesa da ita ko tafiyar nan da zan yi sai da Assad ya kire ta kan shi ya fada mata sannan ta hakura , wannan shi ne labari na , kin ji dalilin da ya sa na ce miki uncle di na bai san da zaman Assad ba "
Mikewa zaune Safa ta yi ita ma ta jingina bayan a jikin forehead din gadon ta kale shi ta saki wani cool murmushi ta na shirin magana ta ga ya sauka da ga saman bed din ya na fadin " tashi ki je ki yi sallat lokaci ya yi , an jima zan dawo " ya kai karshen ya na fice wa dakin
Da kallo ta raka shi har sai da ya fita ya ja mata kofar sannan ta tashi ta shiga toilet
Shi kuma kai tsaye gidan ya bari baki daya ya nufi gidan su da sauri sauri
Babu ko sallama ya shigo parlourn gidan ya na kwallawa Assad kira da karfi
Da gudu ya Haye stair har ya na neman ya fadi
Kai tsaye part din su ya shiga ya na ci gaba da kiran Assad
Ya na shigowa ya ga ba ya cikin parlourn sai ya wuce bedroom din
Turo kofar ya yi ya na fadin " Assad where are you ? "
Ya kai karshen dai'dai lokacin da Assad ya fito da ga cikin toilet ya na daure da towel a kugunshi , hannun shi kuma ya na rike da wani dan karamin ya na tsane jikin shi wani abun mamaki kuma ya na sanye da bakaken glass din nan na shi kamar kullum
Kare mishi kallo da kyau Assad ya yi kafin ya ce " lafya ka na yi min irin wannan kiran " ya fada ya na karasowa ya zauna bakin gadon su
Da sauri Amar ya nufi bed din shi ma ya zauna ya na fadin " Sasha ka na tune da wannan friend's din mu wanda mu ka fara karatu da shi a RUSSIA "
Shiru Assad ya yi na dan second kafin ya daga mishi gera guda ya ce mishi " ai friend's din su na da yawa "
Da sauri Amar ya katse shi da cewa " Nooooo ! our best friend , Wanda ya sakawa Rahaf sunan Puppy , Wanda ku ka siya Rex tare da shi , what's his name ? "
" Aryan Abdoul Karim ? "
Da sauri Amar ya ce " yes ! Shi , Sasha ya na ina , yanzu wajen 15 years tun bayan dawowar shi Nigeria bai koma RUSSIA ba babu kuma labarin shi "
" Amar , don't forget Aryan ba na Nigeria ba ne ....... "
Da sauri Amar ya katse shi da cewa " Sasha please use your brain , Aryan , Daddyn shi na Nigeria ne , kuma ya tabatar mana da ga Nigeria ya taho RUSSIA shi da wata friend's din momy ka na tune da ita "
Gyada mishi kai Assad ya yi allamun e
Ci gaba da magana Amar ya yi ya na fadin " she is our neighbor , ita da Miss Safa su ke zaune a cikin gidan nan , lokacin farko da na je gidan ina tambayar Miss Safa , nan na yi karo da ita , ta tsaya mu ga gaissa ta na tambaya ta mutanan gida , da farko ban gane ta ba amma yanzu ina da tambacin ita ce , ita ce Sasha "
" to ko ita ce me ka ke son na ce mata ? " Assad ya fada ya na mikewa zai bar wajen
Da sauri Amar ya sha gaban shi ya na fadin " Sasha ba ka son ka san abun da ya samu Aryan ne , he was your best friend ! Ta ya zai dauke lokaci guda babu shi babu alamun shi just like this , in ya na nan Nigeria ya kamata mu san halin da ya ke ciki , ya na raye ko ya mutu "
Shiru Assad ya yi na dan mintina bai ce komai ba ya na dai kallon Amar , sai da ya gaji da kallon Amar din sannan ya raba ta geffen shi ya wuce ba tare da ya ce mishi komai ba
Dan daga kan shi sama Amar ya yi ya lumshe idanun shi kafin ya sauko da kan shi slowly
" na fi ka damuwa a kan shi , ba ka yi mamakin yadda mu ka sauka cikin gidan da ya ke fuskantar gidan matar da ta rike shi a RUSSIA ba , bayan komawar ka UK sai da na zo Nigeria har sau biyu dan neman shi , amma ban yi nassara ba , wannan zuwan ma da na yi na zo ne dan na samo inda ya ke , kar ka manta Aryan kamar family na ya ke , wannan bacewar ta shi lokaci guda ta jima ta na damu na, amma wannan karan ba zan bar Nigeria sai tare da shi " Assad ya fada da ga haka kuma ya sa kai ya shige dressing room
Dan karamin murmushi Amar ya yi ya na jinjina kan shi kafin ya fara takawa ya fice dakin
* WASHE GARI
Yau tun karfe 7 na safe Safa ta farka da ga barcin ta ta shiga kitchen , musaman yau ta ce ita za ta shirya wa Amar da Assad breakfast ,
Wajen karfe 8 ta Kamala ta koma bedroom din ta yi wanka ta shirya cikin wando palazzo da T-shirt duk pink colour ta saka wata yar hula a kan ta sai baza kamshi ta ke
Da ga haka ta fito ta koma kitchen ta dauki basket din ta nufi gidan Su Amar
Bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn gidan
Amar ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi , ya na sanye da wanda three cuter da t-shirt
Ya na ganin ta ya saki wani cool murmushi , ya na amsa mata sallamar ta
Karasowa ta yi cikin parlourn ta ajiye basket din hannun ta saman table ta ce mishi " our breakfast ! "
Kallon basket din ya yi