Showing 27001 words to 30000 words out of 133773 words
ki a ka fara wannan abun ba , mata dayawa su na yarda da kalaman da namiji har su mallaka musu abun da ya fi ko wane daraja a rayuwar su , sai su yi anfani da son da a ke musu su na sa yan mata su yi musu duk abun da su ke so , musaman idan da maganar aure tsakanin ku , za ki ga ya yi anfani da hakan ya na yi miki wasu abubuwa kamar mata da miji , idan kuma ki ka ki ba shi dama , ya ce miki ai da maganar aure tsakanin ku , nan gaba kadan za ki zama matar shi ko wani abu ya faru tsakanin ku ba matsala ba ce , bayan sun samu abun da su ke so har maganar auren janye wa su ke , Idan kuma a ka yi auren , ba zai taba yarda da ke ba , dan kullum tunanin shi kin konta da wasu mazan bayan shi , Djami kin yi ganganci gaskia , yanzu babyn da ke cikin cikinki ya za ki yi da shi , in yan gidan ku su ka san wannan maganar ya za ki yi da wane ido za ki kale su "
( 🤧🤧 gaskia Mansour bai kyauta miki ba , kema kin yi rashin hankali 🤧 ba sadakin ki ba ya kawo kawai tambaya ce ya yi amma za ki tashi ki bashi akalar rayuwar ki 🤧 gaskia mata ya kamata mu yi wa kan mu fada a kan yarda da saurayi lokaci guda har ya kai mu aika ta abun da za mu jima mu na nadamar shi 🤧 samarin yanzu duk Samarin shaho ne sai iya sa kaya da karya amma ba sisin kobo ba ilimi adini bare na boko 🤣🤣🤣 )
Ita dai Djamila ban da kuka ba abun da ta ke yi , ta rasa da wani ido za ta kali Safa da Haoua wannan abun kunya da me ya yi kama
Su na a haka Haoua ta ce " yanzu ya za muyi da wancen dan iskan mu kai karar shi police station "
Cikin nitsuwa Safa ta ce " no ko mun kai karar shi ba abun da zai faru , ai ita ta kai kan ta , ba abun da zai janyo mata sai kunya da kananan magaganu "
Da sauri Djamila ta katse ta da cewa " ni aborted din shi zan yi " ta fada cikin kukan nata
Hannu Safa ta kai ta dan buge ta a baya ta ce " ba ki da hankali ne , zunibi biyu ki ke son yi , ga na ciki , ga na zubar da shi , are you mad ? Yanzu ki fara fadawa dirty boy din nan ki na da ciki , da ga baya ma san abun yi " ta na gama fadar haka ta mike ta fara takawa ta bar wajen
Da sauri Haoua ta mike ita ma ta bar wajen
Su ka bar Djamila ita kadai zaune ta na faman kuka
Bangaran Safa kuma kai tsaye parking space ta nufa ta shiga motar ta ta tada ta bar school din
Bari dai in leko Noor yanzu gaskia
▪ABUJA ( GIDAN SU TWINKLE )
Zaune Noor ta ke cikin parlour ta na kallon Tv
Ta na sanye da wata gown mai bala'in kyau ta sha adon stone , light green colour ce , ta na da wani madauri da ga tsakiyar ta , ta na sanye da wani dan karamin hijab White colour
Ta daura wani Bowl dauke da popcorn saman cinyar ta , ta na ci ta na kallon Tv
Ta na a haka wata kyakyawar budurwa ta shigo parlour ta na sallama
Ta na sanye da wando jeans Navy blue , da riga dai'dai guyiwa white colour , ta na yafe da wani veil Baki , hannun ta rike da wata yar karamar bag
Yarinyar ta na da dan tsayi , da jiki , skin din ta chocolate ne mai kyau ta so ta dan yi kama da Sami musaman wajen hancin su , a shekaru za ta kai 23 years haka
Ta na shigowa ta samu doguwar sofa ta Haye ta na fadin "ke Noor , tashi kawo min ruwa "
Ko kallon ta Noor ba ta yi ba ta ci gaba da kallon TV din ta
Kai hannu yarinyar ta yi ta dauki remote ta kashe Tv kafin ta kali Noor ta ce " za ki tashi ko sai na dake ki "
Slowly Noor ta jiyo ta kali yarinyar nan sama da kassa kafin ta ja dan siririn tsaki ta kauda kai gefe ta ce " in ni zan kawo miki ruwan kar ki sha "
Zaro idanu yarinyar ta yi ta na mikewa tsaye ta ce " Gaskia ne , wuyan ni ya isa yanka Noor , har ni za ki kalla ki fadawa wannan maganar "
Noor na shirin magana ta ga an turo kofar parlourn a na sallama
Ta na jiyo Muryar shi ta saki wata yar karamar kara ta fashe da kukan karya ta daura hannun ta guda saman kumatun ta
Wani dattijo ne ya shigo cikin parlourn ya na sallama , ya na sanye da manyan kaya na shadda Fara , kamanin shi Daya da Sami har yanayin Skin din su wato Chocolate , ya dan lattijantaka a shekaru zai kai 50 zuwa 55
Ya na shigowa ya jiyo kukan Noor
Da sauri ya nufe ta ya na fadin " Chalele na me ya faru ki ke kuka "
Cikin kukan karyan na ta ta ce " Daddy , ba Raïssa ba ce , wai cewa ta yi na dauko mata ruwa , shi ne na ce mata Film na ke kallo ta kira Maid ta kawo mata , shi ne ta dauki remote ta kashe min Tv har da mari na " ta kai karshen ta na saukowa da ga saman Sofar har sai da bowl din popcorn ya zube a kassa ta nufi stair da gudu ta Haye
Ta na hawa Daddy ya kali Raïssa ya ce " na lura ku na son takurawa yarinyar nan cikin gidan nan , to bari ki ji , na gaji da ganin ku cikin gidan nan , na ba ku nan da one month ko wace ta fito da mijin aure ko kuma na aura muku duk wanda na samu "
" What ? Daddy aure fa , ni gaskia ban shirya ma aure ba , kuma Daddy ni fa ban mare ta ba karya ce kawai ta ke yi min " Raïssa ta fada da dan karfi
Tsawa Daddy ya daka mata da cewa " Shut up , ba shawara na ke ba ki ba umarni ne , duk wanda ya sake yi wa yarinyar nan ko da kallon banza wlh ba mai raba ni da shi cikin gidan nan " ya na gama fadar haka ya nufi stair ya Haye shi ma
Da kallo Raïssa ta raka shi har sai da ya Haye stair sannan ta koma saman sofa ta zauna ta na gunguni ita kadai
Ta na a haka Fadila da Farida su ka shigo parlourn su na sallama
Su na sanye da Skert pink colour da kadan ya wuce guyiwa , da shirt fara mai dogayen hannu da dan karamin hijab zuwa kirji shima fari , su na rike da school bag
A tare su ka karaso cikin parlourn su ka ajiye bag din saman table kafin su zauna saman sofa two seaters
Kallon Raïssa su ka yi da kyau , har su na hada baki wajen tambayar ta lafya dan da ga gani yanayin face din ta , ta na cikin bacin rai
" wai ni wacen sakarar yarinya za ta yi wa sharri wajen Daddy, shi kuma ya yarda da maganar ta , har da cewa ya gaji da ganin mu cikin gidan nan " ta fada ta huci
Dariya Farida da Fadila su ka yi a tare kafin Fadila ta ce " ni dama sai da na fada miki , mu daina ragawa yarinyar nan , Daddy fa ya fi son ta fiye da mu "
Tsaki Raïssa ta ja kafin ta hararri Fadila ta ce " gwara tun wuri ku fido da mazajen aure dan Daddy ya ce one month ya bawa kowa in ba haka ba ya aura muku duk wanda ya ke so "
" ya aura mana duk wanda ya ke so har da ke malama , ke Fifi tashi mu tafiyar mu " Fadila ta fada ta na mike ta nufi stair ita da Farida
Da kallo Raïssa ta raka su har sai da su ka Haye sannan ita ma Raïssa ta mike ta Haye stair din ta na faman bata rai
▪ Misalin karfe 4 na yamma
▪Safa 💋
Zaune ta ke cikin parlour ta na kallon chanel din MTV hits ta na kallon wakoki
Ta na sanye cikin mini skert white colour , da yar karamar t-shirt zuwa cibi pink colour ta saki wannan golden hair din na ta
Ta na a haka Snoopy ya figo Parlourn ya na dan Haushi ya karaso wajen sofar da ta ke zaune ya konta ya na shafa cinyar ta
Murmushi ta yi kafin ta ce " lafya wa ya koro ka " ta fada ta san halin shi in sun yi bako
Dan karamin haushi ya yi ya na ida kontawa a wajen dai'dai lokacin da Sami ya shigo parlourn ya na sallama
Ta na ganin shi yanayin face din ta ya sauya , kamar ba ta ji dadin ganin shi ba
Cen kassan makoshi ta amsa mishi sallamar shi kafin ta meda kallon ta kan Tv
Shi kuma ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofa da ke geffen ta ta ya na kallon ta ya ce " Me ki ke yi a gida , ba ki je school ba yau ko me ? "
Ba tare da ta kale shi ba ta ce " ba mu da lectures yau "
Kallon Snoopy ta yi kafin ta ce " Snoopy je ka kira min Balki "
Dan karamin haushi ya yi wai shi ba ya zuwa
Matse fuska Safa ta yi kafin ta ce " Snoopy ba na son wannan abun da ka ke yi , maza tashi ka je ko kuma na yi maka fushi "
Ba dan ya so ya mike ya nufi dining room ya shiga kitchen
Ya na shiga Sami ya ce mata " wai ba za ki daina magana da wannan karan ba , ke fa ba yarinya ba "
Ta na shirin magana wayar ta da ke saman table ta yi ringing
A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta na kallon screen din
Ta ga number din ta Nigeria ce , ita dai ta san bayan momy , Haoua da Djamila sai Musadeeq da Mutalab ba wanda ke da number din ta
Cike da shakku ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na sallama
A daya bangaran kuma amsa mata sallamar ta Nabil ya yi kafin ya daura da cewa " Abokiyar hira, ya ki ke , shikenan tun da ki ka tafi ko waiwayo mu ba za a yi ba "
Dago kai ta yi a hankali dai'dai lokacin da Balki da Snoopy ke fitowa da ga cikin dining room su ka karaso cikin parlourn
Snoopy ya Haye saman sofa ya konta geffen Safa ya na kallon ta
Balki kuma ta na ganin Sami ta koma dining room dan ta gane kiran me a ka yi mata
Safa kuma daura hannun ta ta yi saman kan Snoopy ta na shafawa a hankali kafin ta ce " Sorry ban gane da wa na ke magana ba "
Yar karamar dariya Nabil ya yi kafin ya ce " Dama na san haka za ki ce , wajen boss na karbi number din ki , Nabil ne abokin aikin ki "
Daga kai sama ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta medo ta saki wani cool murmushi ta ce " Ah okay na gane ya ka ke ya aiki kuma "
" Lafya klau wlh , ya yi ke kwana biyu "
Murmushi ta yi ta na kallon Snoopy ta ce " alhamdoulilah thanks God "
" okay ya yi kyau , na zo miki da wani albishir mai dadi "
Dan washe baki ta yi kafin ta ce " Toooo ! Minene wannan albishir ? "
Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Mariam mai gabatar da shirin Jarida , to sun koma Katsina da zama , ba za ta ci gaba da gabatar da shirin ba , boss ya ce duk wanda ya ga zai iya gabatar da shirin a madadin ta , sai ya yi mishi magana , shi ya sa na kira ki dan na fada miki ko ki na son shiga wajen ta "
" hmmm nagode sosai , na yi shawara na gani , in mun gamu Friday zan fada maka "
" okay no wonder , zan bar ki na san ki na aiki sai an jima "
Murmushi ta yi kafin ta ce " okay bye " ta na gama fadar hakan kiran ya katse
Sauko da wayar ta yi ta ajiye saman table kafin ta kali Snoopy ta daura lips din ta saman forehead din shi ta sumbata
Shi dai Sami da kallo ya ke bin ta , ya rasa abun da zai ce mata
Sai da ta gama wassan ta da Snoopy sannan ta juyo ta kali Sami lokacin har Balki ta kawo mishi Drinks da snacks amma bai taba su ba
Matse gera ta yi ta na fadin " why are you look at me like this ? "
Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi ya na girgiza mata kai kafin ya ce " nothing , kawai dai ina kallon yadda ki ke wasu abubuwa kamar karamar yarinya "
Daga mishi gera guda ta yi kafin ta ce " me kuma na yi irin na yara ? "
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE⚘❤
GA ACCOUNT ADRESS 👇👇👇👇
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
KO KUMA TA CREADIT DA TA WADANAN NUMBER 👇👇👇
Zain (Airtel)
08081129487.
Mtn
07067953066.
NAIRA 200 NE ONLY
SANNAN KU TURA SHAIDAR TURA KUDIN A WANNAN NUMBER ( +22795577612 )
🩷✨✌️
[25/08 à 15:25] MEERAH🪷🩷:
💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🔥💦
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
P A G E 10 🥀 ❤
Dan karamin murmushi Sami ya yi kafin ya ce " sister wai me ya sa har yanzu ba ki sakin jiki da ni ? "
Daga kafadun ta ta yi allamun ban sani ba , kafin ta juya ta kali Snoopy ta ce " baby tashi ka je "
Ba musu ya diro da ga saman sofar ya girgije sannan ya fice parlourn da gudu
Ya na barin wajen ita ma ta mike ta na shirin barin wajen
Da sauri Sami ya riko hannun ta ya janyo ta ta fado a jikin shi
" ki ba ni amsa mana kafin ki tafi , why ki ka tsane ni a yanzu , lokacin da ki ke baby saman cinya ta ki ke wassa ko kin manta , why ki ka daina yanzu " ya fada ya na kallon face din ta
" i'm not a baby , so let me , kai da kan ka ka fada ni ba yarinya ba ce " ta fada ta na kokarin kwatar hannun ta
Sakin ta ya yi , dama jira ta ke , ta tashi da sauri ta yi baya ta na hararrar shi ta matse gera ta ce " tashi ka fice mana gida "
Komawa ya yi ya jingina a bayan sofar ya daura kafa daya saman daya cike da isa ya ce " in kin gaji da gani na sai ki bar gidan ga kofa nan "
Tsaki Safa ta yi kafin ta juya ta nufi hanyar stair
Da sauri ya ce mata " idan kin je ki sauya wadanan kayan kin ji ko "
Yar karamar kara Safa ta yi ta na bubuga kafafun ta ga kassa kafin ta juyo ta ce " ka san Allah in ka kara yi min magana cikin gidan nan sai na kakarya , ka bari in na je gidan ku sai ka yi min rashin mutuncin da ka saba " ta fada da dan karfi kafin ta juya ta Haye stair da gudu
Shi dai Sami da kallo ya rakata har sai da ta Haye sannan ya yi yar karamar dariya ya ce " you'll be mine very soon " ya kai karshen ya na dan murmushi
▪After two days
FRIDAY : 7pm
▪Safa 💋
Zaune ta