Showing 42001 words to 45000 words out of 133773 words

Chapter 15 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9705

a cikin gidan ya yi ta , ita ba ta da labari
Tun da ta fara hauro stair ya ke bin ta da ido har sai da ta karaso ta zauna sannan ya kira sunan ta


Dan karamin tsaki ta yi kafin ta ce " me ya kawo ka gidan mu a wannan lokacin ? "


Cikin nitsuwa ya ce mata " please Safa listen to me , why za ki ce ba za ki aure ni ba , ni fa tsakani da Allah na yi wannan maganar, ba da wassa na ke ba , ko da niyar cutar wa "


Nade hanayan ta a kirji ta yi ya koma jikin sofar ta jinjina bayan ta , ta daura kafa daya bisa daya ta na kallon shi cikin ido ta ce " ni ban shirya aure ba musaman in da kai ne gwara ka ban lafya , wlh ba abun da zai sa na aure ka "


Da sauri ya katse ta da cewa " but i love you , i want to marry you , why za ki yi min ha........"


Bai karasa maganar shi ba Safa ta bushe da wata shegiyar dariya har da tapi
Shi dai kallon ta kawai ya ke ya na tunanin me ya fada da ya bata dariya haka


Sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta mike ta koma geffen shi ta zauna ta na kallon shi ta ce " Sami , ni fa ban iya boye boye ba , zan fada maka gaskia , i don't love you , ba dan wani abu ba da sai in ce na tsane ka baki daya , amma ba zan iya canja matsayin ka a waje na , na cewa kai sibling di na ne , ba na tunanin aure na iya shiga tsakanin mu , ko ya na shiga ni ba zan yarda ba saboda ba ni son ka , familyn ka sun kuntata min tun ina karama kuma har yanzu su na kan yi , ba zan iya shiga ahalin da ba su so na , na san watarana za su iya kashe ni , dan haka gwara ka cire wannan shirmen da ka ke kira da so da ga cikin zuciyar ka dan ni ban san shi ba , ko na fara jin shi ba na fatan na fara a kan ka " ta kai karshen ta na yar karamar dariya


Wani cool murmushi ya yi kafin ya ce " Safa you know you're extraordinary , na san abun da mu ka yi miki bai dace ba , kuma har yanzu ina bakin cikin hakan, amma ba yadda zan yi dole na saka ido na kalla , ko ba komai na gode da har yanzu ki na kallo na a matsayin dan uwan ki , na so allakar mu ta wuce haka , amma ba zan matsa miki ba a kan abun da ba ki so , ba zan so na kara miki wani bakin cikin ba , ki ji kin tsane ni baki daya , zan yi kokari wajen ganin na gyara abun da ke tsakanin ki da family na , saboda ke ma ki na ciki , amma zan so na yi miki tambaya guda in kin yarda "


A hankali ta gyada mishi kai allamun e


Mika mata hannun shi ya yi ya saki wani cool murmushi cikin sanyin murya ya ce " can i be your friend's ? "


Kallon hannun shi Safa ta yi kafin ta dago kai slowly ta kali cikin idanun shi , ba karya wannan karan shi ne na farko da ta ga sincerity din shi a ciki
Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta riko hannun shi ta na fadin " no you can not be my friend "


Dan zaro idanu ya yi ya na kallon ya ce " why ? "
Hararrar wassa ta yi mishi kafin ta janye hannun ta da ga cikin na shi ta ce " saboda yau na samo abun da na rasa da jimawa "
Cike da rudu ya ce mata " wane abu kuma ? "


Bai gama rufe bakin shi ba ta fada jikin shi ta rungume shi ta ce " my brother "


Wani kyawatencen murmushi ya saki nan take idanun shi su ka kawo ruwa
Da sauri ya datse su ya sa hannayan shi biyu ya rungume ta tsam ya na fadin " i have really missed you my sister "


Yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " me too "
Da ga haka ta raba jikin su ta na kallon shi
Matse gera ta yi ta na nuna shi ta ce " bari ganin mun shirya , wlh in ka yi min ba dai'dai ba sai na koya maka hankali " ta kai karshen ta na dunkule hannun ta ta yi kamar za ta kai mishi bugu


Yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " ni na isa , ai ina son rai na , ban shirya mutuwa ba "
Wannan karan a tare su ka yi dariya har da ita


Su na tsaka da dariyar su Momy ta shigo parlourn ta na sallama , a tare su ka kai kallon su gare ta su na amsa sallamar ta a tare


Yanayin da ta tardo su ba karamin tada mata hankali ya yi ba ba ta san lokacin da ta ce " Sami me ka ke yi a nan cikin daren nan "


Safa ce ta amsa mata da cewa " momy ba wani dare sosai ne ba fa , duka duka karfe 8 da yan mintina " ta kai karshen dai'dai momy ta zauna saman sofar da ke fuskantar ta su


Ta na zama Sami ya mike ya na fadin " ni kin tuno min ma , Aunty zan koma gida ni "


Mikewa itama Safa ta yi ta na fadin " okay , amma sai ka yi sauri kar ka hadu da yan yankar kai " ta kai karshen ta na yar karamar dariya ta juya ta fara takawa ta nufi stair ta Haye da sauri


Da kallo momy ta raka ta har sai da ta Haye sannan ta kali Sami ta ce " ba na son na sake ganin ka a kusa da ita cutar nan ta ku ta isa haka , ka kyale ta , ta yi rayuwar ta , kun raba ta da iyayen ta hakan bai ishe ku, sai kun bulo da wata hanyar daban dan cutar da ita "


Dan karamin murmushi Sami ya yi kafin ya fara takowa ya zo gaban ta ya tsaya ya na kallon cikin idanun ta ya ce " a dai bar kaza cikin gashin ta , idan an a ka fige ta wlh sai kin rasa bakin magana , kar ki manta abun da ki ka aikata , Good night "


Ya na gama fadar haka ya ci gaba da takawar shi ya fice parlourn
Ita dai momy da kallo ta raka shi har sai da ya fice sannan ta mike ta Haye stair ita ma su ka bar parlourn ba kowa a ciki











▪ ABUJA ( GIDAN SU TWINKLE )














zaune duk mutanan gidan su ke cikin parlourn , Banda Sami , wasu na kallon Tv , wasu na faman latsa wayar su , musaman Farida da ke ta faman Sakin murmushi


Su na a haka Daddy ya kalli Raïssa ya ce " Raïssa , ki shirya Doctor Amar na nan zuwa ranar monday , amma matsalar a Kaduna zai sauka , sai dai bayan kwana biyu ya zo ki gan shi "


Dan tsaki Raïssa ta yi , ta na yamutse fuska ta ce " Daddy wanene Amar kuma ? "


Daddy na shirin magana Noor ta riga shi cewa " yanzu Raïssa ba ki san Doctor Amar ba , kam amma an baro ki a baya " ta kai karshen ta na yar dariya


Hararrar ta Raïssa ta yi kafin ta kali Daddy ta ce " Daddy ka ga ni ko , wlh duk kai ka sa ta raina ni "
[01/09 à 21:18] MEERAH🪷🩷:






💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )



















( A heart touching love story & destiny )
















STORY & WRITTEN BY : MEERAH 💞💋










Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥








GA DUK ME BUKATAR WANNAN BOOK DA GA FARKO ZAI IYA JOING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK


👇👇👇👇👇👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION


👇👇👇👇👇👇


https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY










GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY




















BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM


















PAGE 14 🥀 ❤






















Cikin nitsuwa Daddy ya katse ta da cewa " yo ai gaskia ta fada , mutumin nan dan uwan ki ne baki daya , amma ki ce baki san shi ba "


Da sauri Noor ta taso ta koma geffen Daddy ta na fadin " Daddy kyale ta , ka san fa ba a zamanin mu ba ta ke , ai ko ba dan uwan ta ya kamata ta san Doctor Amar , babban mutun ne fa , ba a UK kadai ba , har a nan Nigeria ba wanda bai san shi ba , sai dai a ka ce ba kowa ya san face din shi ba , asali ma ko patient din shi ba duka su ke ganin face din shi ba "


Murmushi mai dan sauti Daddy ya yi kafin ya ce " to sannu malama ! Ke ta ina ki ka san shi haka , anya ba ke ma zan wa shi ba ? "


Da sauri ta girgiza mishi kai ta na fadin " a'a Daddy ni gaskia ban ni so , ni fa har yanzu baby ce , ga su Raïssa, da Farida zaune , sai a ce ni za a ba shi , a ka je wani mumuna ne shi ya sa ba ya son a na ganin face din shi ni gaskia ba ni so " ta kai karshen cikin shagwaba


Yar karamar dariya Daddy da Twinkle su ka yi
Ita dai Raïssa sai faman hura hanci ta ke yi , ta rasa wani irin mugun abu ya kamata ta yi wa wannan yarinyar , dan ta san ko kashe ta ta yi ba za ta ji saukin abun da ke cikin zuciyar ta ba






















* WASHE GARI (MISALIN KARFE 10 NA SAFE)














* KUJE PRISON












Zaune Marwan ya ke saman wani banci , Bachir na zaune geffen shi ya na yi mishi hira , shi kuma Marwan ya na sauraron shi sai a kai a kai ya ke saka bakin shi


Su na a haka wani sojan ya iso wajen ya na sallama
A tare su ka amsa mishi sallamar sa , da ga nan ya sanar da Marwan cewar ya yi bako


Kallon sojan ya yi , sai da ya dauki dan lokaci kafin ya ce mishi " sai dai ya iso nan , dan gaskia ba zan iya tashi ba "
Ya na gama fadar haka ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi


Ba musu sojan nan ya juya
Ya na barin wajen Bachir ya yi murmushi mai dan sauti kafin ya mike tsaye ya koma bayan Marwan ya tsaya


Jim kadan sojan nan ya dawo tare da Sami na biye da shi
A tare su ka karaso gaban Marwan su ka tsaya su na yi mishi sallama kafin sojan nan ya juya ya bar musu wajen
Ya na barin wajen Sami ya samu geffen Marwan ya zauna ya na ci gaba da kallon Marwan ba tare da ya ce komai ba


Dan karamin murmushi Marwan ya yi kafin ya ce " brother-in-low , me ya kawo ka tun da sasafen nan , ko ka zo ka ba ni katin gayatar auren ka ne ? "


Dan tsaki Sami ya yi kafin ya kauda kan shi gefe ya na fadin " sai na bar zowa wajen ka , wlh ka cika fadawa mutane bakar magana "


" a haba , nan ne bakar magana , ni na zata blue ce ma " ya kai hannu ya na yar karamar dariya


Hannu Sami ya kai ya dan bugi cinyar shi ya na yar dariya shi ma
Cikin sanyin murya ya ce " bro wai yaushe za ka fita da ga gidan nan , na gaji da ganin ka a nan , ga shi kuma ka hana ni na medo case din ka a kotu , ka hana ni na biya tarar fitar da kai why ? "


" ina jin dadin zama a nan ne , na san a nan ba wanda zai yi kokarin kashe ni , ko kwace min dukiya ta " ya fada mishi cikin ko in kula


Marairaice fuska Sami ya yi kafin ya ce " please, ka bari na fitar da kai, na yi maka alkawari ba wanda zai sani , barin kassar ma za mu yi baki daya , bro wlh ba na jin dadi duk lokacin da na tuno halin da ka ke ciki "


Wani cool murmushi Marwan ya yi kafin ya ce " kar ka damu Sami , wanda na ke jira ya kusa isowa "


Katse shi Sami ya yi da cewa " Bro , wai wanene wannan wanda ka ke jira , ya kai wajen shekara 10 yanzu , tun bayan rasuwar uncle kullum sai ka fada min wannan maganar da na tado maka zancen fitar da kai da ga nan , me ya sa har yanzu bai zo ba ya fitar da kai "


Shiru Marwan ya yi bai ce komai , har yanzu dai bai bude idanun shi ba
Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " dalilin zuwan shi ne bai yi ba , yanzu kuma ya yi "
Da sauri Sami ya sake katse shi da cewa " who ? Ka fada min ta yadda zan taimaka mishi , mu fitar da kai da ga wajen nan da sauri "


Wani cool murmushi Marwan ya yi kafin ya ce " ba sai ka taimaka mishi ba , tamkar robot haka ya ke aiki , mutun ne mai muguwar kwakwolwa , ko rufe ido ya yi zai iya fada maka abun da ke gaban shi , wanda na ke jira , ko da duk yan prison din nan ya yi niyar fitar da su , to tabas sai ya fitar da su kuma ba wanda ya isa ya dakatar da shi , ka roki Allah kar ya sa ku hada mumunar hanya da shi , har zuwa ranar da zai bar garin nan , in ba haka ba za ka riga shi barin duniya " ya kai karshen ya na yar karamar dariya


Dan siririn tsaki Sami ya ja kafin ya mike ya na fadin " ina ga gidan mahauka ta ya kamata a kai ka ba prison ba , ni na tafiya ta " ya kai karshen ya na juyawa ya fara takawa ya bar wajen


Ya na barin wajen Bachir ya dawo geffen Marwan ya zauna ya na fadin " Sir ko ni zan so in ji wanene wannan wanda ka ke jira tsawan shekaru haka "


" wacece ya kamata ka ce " Marwan ya fada a takaice


Dan zaro idanu Bachir ya yi cike da rudu ya maimaita abun da Marwan ya fada
Cikin ko in kula Marwan ya ce mishi " My sister " ya na gama fadar haka ya sauko da kan shi ya bude idanun shi ya mike ya fara takawa ya bar wajen
Da sauri Bachir ya mike ya bi bayan shi ya na son ya tambaye shi wacece wanan, shi dai a sanin shi kanwar Marwan guda kuma ta rasu , to wace sister ya ke nufi
Sai dai in ce Marwan kadai ya san amsar tambayoyin mu ba ki daya dan ko ni zan so na san wanene wannan ko in ce wacece wanan
















AFTER ONE DAY








* KADUNA ( G.R.A )









MISALIN KARFE BIYU NA YAMMA














SAFA 💋


















Tun da ta karayo kwanar gidan su ta fara ganin wasu irin jibga jibgan sojoji tsatsaye su na rike da manya manyan bindigu sai tsami su ke sha , su na zagaye da gidan da ke fuskantar na su , gidan da tun shigowar ta kaduna ba ta taba ganin an bude shi ba , yau kuma ga sojoji zagaye da gidan , sojojin ma ba na Nigeria ba dan wadanan farare ne kal da su ba su yi kama da na Nigeria ba
Ita ba ta kawo komai a ran ta ba ta ci gaba da tukin ta har ta karaso kofar gidan su ta shiga dannawa gateman horn
Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login