Showing 48001 words to 51000 words out of 133773 words
fannin da bai samun kula yadda ya dace , mutane dayawa sai in ba su da lafya su ke tunowa da Asibiti , manyan kuma ba su bada talatin da ya dace ga Asibiti , sun fi son su fitar da kudin dan wajen sayen weapon , abun da ba lalle ya anfane mu ba, asibitoci nawa ne cikin garin nan ba su da kayan aikin kula da majinyatan su , sai dai in abu ya fi karfin su , su ce afitar da shi kassar waje , mafi yawwancin likitocin Garin nan duk private , ba kowa ke da karfin halin biyan service din su ba , public din kuma ba su da kayan aiki why ba za su fidda kudi su saya musu kayan aiki ba , na ga ko shi shugaban kassa idan ba shi da lafya likita ya ke tafiya , why ba zai je public ba sai dai private , kenan kan shi kawai ya sani , su sauran talakawa da ba su arzikin zuwa private su yi yaya ? , shi ya sa na fi bada hankali a kan Fanin lafya , saboda shi kadai ne mutane su ka yi neglecting sosai , al'halin shi ya fi kowa ne mahimanci , ai sai da lafya a ke komai "
Yar karamar dariya Amar ya yi kafin ya ce " Gaskia ki ka fada , amma me ya ki ka zama yar JARIDA ba ki zama doctor ba , hakan zai fi wajen bayar da gudun mawar da ki ke so "
Wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta kauda kan ta da ga gare shi
Sai da ta dan dauki lokaci kafin ta ce " ko cen dama ni aikin JARIDA ke burge ni , musaman a yanzu da duniyar mu ta zama sai a hankali , tun ina karama na ke da kudurin bayanar da gaskia , akwai wani kuduri da na taso da shi cikin zuciya ta , kuma ta wannan hanyar ce kawai zan iya banyanar da gaskiyar da a ka bunne , ta haka ne kawai zan iya wanke sunnan wanda a ka bata "
Da sauri Amar ya katse ta da cewa " sorry ban gane abun da ki ke son fada ba "
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta mike tsaye ta kale shi ta ce " Snoopy let's go home "
Da sauri Snoopy ya sauko da ga jikin Amar ya nufi Safa
Mikewa tsaye Amar ya yi ya na fadin " i'm sorry , idan na bata miki ba ta tare da Sani na ba "
Girgiza mishi kai ta yi ta na murmushi ta ce " no ba haka ba ne kawai na ga magriba ta gabato so zan koma gida ne "
" please yaushe zan sake ganin ki , ni fa ba kamar dan uwa na na ke ba , ba ni son zama ni kadai " ya fada cikin sanyi
Yar dariya Safa ta yi kafin ta ce " no wonder , duk lokacin da ka ji kadaici ka tardo ni gida , sai mu yi hira , kar ka manta ni fa Abokiyar hirar ku ce "
Yar karamar dariya su ka yi a tare kafin Amar ya ce " haka ne gaskia , to kema in kin samu dama zan so ki dinga zowa nan mu hira , kin ga ai duk gida guda mu ke " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda
Yar karamar dariya ta yi kafin ta fara takawa ta na fadin " see you next time "
Da sauri ya biyo ta ya bude mata kofar fita parlourn
Murmushi ta yi kafin ta ce " nagode " sannan ta sa kai ta fice
Ta na fita ya ce mata " beyyyy " da ga haka ya rufe kofar ya koma cikin parlourn ya Haye stair
Bangaran Safa kuma ta na fitowa ba ta tsaya ko ina ba sai gidan
Ko da ta shiga bedroom din ta ta wuce ita kadai, dan tun da su ka shigo gidan Snoopy ya tafi wassan shi
AMAR đ¤
Bayan ya like door din ya juya ya Haye stair din da sauri , ya shigo wani dogon corridor mai door wajen shidda
Sai da ya kai door ta karshe sannan ya yi knocking ya tura ya shiga
Wani kyakyawan parlourn ne , komai na cikin shi milk colour ne , ga wasu lamutsatsun sofas guda uku masu mugun kyau farare kal kamar yanzu a ka ciro su da ga cikin leda , ga wata makekiyar Tv plasma makale a bango
Komai na cikin parlourn ya hadu kuma ya tsaru komai na wajen a goge ya ke sai tashin kamshi wajen ke yi , da allamun wanda ke cikin part din nan ya na da tsabta sosai
Kai wajen wata door ya nufa , ya na isa ya daura hannun shi saman wani finger print
Nan take kofar ta bude da kan ta , bai bari ta karasa bude kan ta ba ya tura ya shiga ya na sallama a hankali
Ya na shigowa sai saman Assad da ke zaune saman wani katafaren Royal bed navy blue mai mugun kyau , ya na fuskantar kofar shigowa , hannun shi rike da wayar shi ya na latsa wa
Amar bai bi ta kan shi ba ya nufi wata Sofa da ke geffen damar door din shigo , ya zauna sannan ya ciro wayar shi ya fara latsawa shi ma
Ya yi nisa cikin duniyar shi ya tsinci Muryar Assad ya na fadin " Who is she ? " ya fada cen kassan makoshi kamar an yi mishi dole
Slowly Amar ya dago kai ya kale shi , har yanzu ya na ci gaba da latsa wayar shi ko dago kai bai yi ba
Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " She is my friend "
Cikin nitsuwa Assad ya katse shi da cewa " Friend ? Cikin abun da bai fi 5 hours ba , duka ko ten hours ba mu yi ba cikin garin nan har ka yi wata friend's "
Murmushi mai dan sauti Amar ya yi kafin ya daga kan shi saman ya ce " General ba za ka gane ba ne , tun kafin mu iso nan na san ta "
A hankali Assad ya kai hannu ya ajiye wayar shi saman bedside drawer sannan ya kali Amar ya ce " kenan ita ce dalilin da ka matsa mu taho Nigeria "
Sauko da kan shi Amar ya yi ya kali Assad ya ce " ka ma sani ka ke tambaya ta "
" why ? " ya fada a takaice
" fada min kai me ya kawo ka Nigeria sai ni ma na fada maka " ya kai karshen ya na daga mishi gera
Kauda kai gefe Assad ya yi kafin ya ce " wani aiki ne ya kawo ni "
" ni ma wani aiki ne ya kawo ni "
Mikewa tsaye Assad ya yi ya nufi wata door da ke kallon bed din ya na fadin " ka yi dai a hankali , kar ka je ka fada ramun bera "
Da sauri Amar ya katse shi da cewa " na Riga da na fada ma "
Cak Assad ya tsaya da tafiyar shi ya juyo ya kali Amar irin kallon nan na karun bayani
Wani cool murmushi Amar ya yi kafin ya ce " Bro ko na fada maka ba za ka gane ba , saboda zuciyar ka ta jima da ta bushe , wannan sensation ba ka san ta ba "
Shiru Assad ya yi na dan mintina kafin ya juya ya ci gaba da tafiyar shi ya shigo toilet
* SAFA đ
Bayan ta koma gida kai tsaye part din ta ta wuce , ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta dauro da alwalla , sannan ta fito ta shiga dressing room
Jim kadan ta fito sanye da wata Abaya Fara kal , ta yi Rowling veil din ta sai tashin kamshi ta ke yi
Kai tsaye wajen daddumar ta ta nufa ta hau sannan ta tada sallar ta cikin nitsuwa
Bayan ta gama ta zauna yin karatun kur'ani har sai da lokacin sallar isha ya zagayo ta tashi ta yi ita ma
Nan take ta ji duk ta tsargu kamar a na kallon ta , ga shi ta na sallat ba ta da ikon juyawa
Sai da ta Kamala sallar ta , ta zauna karatun adu'a , wajen 20 minutes amma har yanzu ba ta daina jin a na kallon ta ba
Bayan ta Kamala aduo'in ta , ta juyo slowly ta kali kofar shigowa dakin ta
Sai da ta ji gaban ta ya fadi , ganin Amar tsaye bakin kofar ya nade hanayan shi a kirji ya na kallon ta fuska dauke da wani kyawatencen murmushi
Da sauri ta mike tsaye ta nufe shi cike da rudu ta na fadin " Doctor me kuma ka ye yi nan cikin daren nan haka , idan momy ta gan ka wlh zan samu matsala "
" kar ki damu ai ita ta kwada min bedroom din ki "
" what ? " ta fada da dan karfi
Murmushi kadan yayi kafin ya ce " kayan nan su na yi miki kyau sosai , me ya sa ba ki yawwan saka su "
Kallon kan ta ta yi kafin ta ce " cikin gida na ke , na mine zan sa wasu manyan kaya , kuma ni har yanzu ban saba da temperature din Nigeria ba gaskia " ta kai karshen ta na warware veil din ta
" okay ! Yanzu kuma me za mu yi , dan ni fa gaskia nan zan zauna , ba ni iya zama da wacen kurman "
Yar karamar dariya ta yi ta na sa hannu ta zuge zip din Abayar ta
Da sauri Amar ya juya a razane ya na fadin " ke ba ki shiga dressing room ki sauya kayan na ki , da mutun fa a dakin "
Dariya sosai Safa ta yi kafin ta karaso geffen shi ta ce " na ji , yanzu ba ni hanya na wuce "
Slowly ya juyo ya kale ta , ta na sanye cikin wasu tracksuit sky blue masu mugun kyau
Shi bai ma san ya tsargu da kallon ta ba sai jin Muryar ta ya yi ta na fadin ya ba ta hanya
Da sauri ya kai kan shi ya matsa baya kadan ya ba ta hanya ta wuce
" Thanks " ta fada kassa kassa ta na wucewar ta , ta nufi Gym fin ta
Bayan ta ya bi shi ba a hankali su ka shiga gym din a tare
Su na shiga ta juyo ta kaleshi ta ce " ka iya martial art ? "
Jinjina mata kai ya yi bai ce komai ba
" good ! Dama na gaji da yi ni kadai "
Murmushi kadan yayi ya karaso gaban ta su na fuskantar juna ya tsaya ya dai'dai kamar za su fara fada ya ce " na yi a hankali dan kar na ji miki ciwo "
Bai gama rufe bakin shi ba ta kai mishi wani wawan bugu a ciki har sai da ya dan zaro idanu
Da sauri ya dago kai ya kale ta , kafin ya ce wani abu ta riga shi cewa " ya ? Ko na bari ka huta ? "
" shikenan , tun da haka ki ke so " ya kai karshen ya na kai mata bugu
Da sauri ta sa hannu ta tare shi
A haka su ka ci gaba , duk bugun da ya kai mata sai ta kare , duk shi ya fi shan bugu har sai da ya dinga ce mata ta yi hakuri ta kyale shi
Sai misalin karfe 10 na dare sannan su ka baro Gym din su ka koma parlourn su ka zauna
Su na a haka Balki ta kawo musu tray shake da Fruits ta ajiye musu saman table sannan ta juya ta koma kitchen
Ta na barin wajen Amar ya ce ma Safa " Gaskia nan gaba ke da Big bro za ki dinga training gaskia ni ba zan iya ba wannan sai ki kashe ni "
Yar dariya Safa ta yi kafin ta ce " kai fa ka ce min ka iya "
" ni na dauka yar koyo ce shi ya sa na ce e , amma gaskia ba zan kuma ba "
" okay na ji shikenan , yanzu dai ni zan je na konta , gobe ina da zuwa university " ta fada ta na mikewa tsaye
Shi ma mikewa tsaye ya yi ya na fadin " okay , ni ma ya kamata na je na konta ina bukatar at least 8 hours na barci , so good night "
Murmushi mai dan sauti Safa ta yi kafin ta fara takawa ta nufi stair ta na fadin " good night " ta kai karshen ta na Hayewa stair
Da kallo ya raka ta har sai da ta Haye stair din sannan ya fara takawa ya nufi hanyar fita parlourn ya fice gidan baki daya
Ko da ya koma gidan su kai tsaye part din su ya wuce , duk part din da ke cikin gidan ya fi son ya zauna tare da dan uwan shi
Ko da ya shiga ya ci karo da Assad tsaye bakin kofar bedroom din su ya na sanye da short da singlet , ya nade hanayan shi a kirji
Ci gaba da takowa Amar ya yi ya karaso gaban shi ya tsaya ya na shirin magana Assad ya riga shi cewa " da ga ina ka ke ? "
Kallon sama da kassa Amar ya yi mishi sannan ya ce " O'O ni ma sa min idon ka ke yi " ya kai karshen zai raba ta geffen Assad ya wuce
Da sauri Assad ya taro shi cikin tsare gida ya ce " Amar , tambayar ka na yi da ga ina ka ke "
đĢđĨ HASKE BIYU đĨđĢ
*( ~YAR JARIDA )*~
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH đĒģđŠĩ
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA đđđē
â¤â EXILED PRINCE ââ¤
( LOVE MEETS POWER ) đđĨ
~*TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL*~
đđđđđđđđ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
~*TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION~
*
đđđđđđđđ
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
~PAGE~ 16 đĨ â¤
Dan karamin tsaki Amar ya yi ya na kauda kai gefe ya ce " bro ni fa ba karamin yaro ba ne da za ka tsaya ka na tambaya ta ina na je "
" Okay , duk abun da ya faru da kai kar ka ce ban fada maka ba " ya na gama fadar haka ya juya ya koma cikin bedroom din
Da kallo Amar ya raka shi har sai da ya Haye saman bed sannan shi ma ya shigo cikin dakin , ya wuce toilet
After some minutes ya fito sanye da bathrobe ya shiga dressing room , jim kadan ya fito da ga shi sai short ya nufi bed geffen Assad ya konta
* WASHE GARI ( misalin karfe 11 na safe )
* SAFA đ
Zaune su ke cikin library din university , ita da Haoua da Djamila , Alhamdoulilah Djamila yanzu jiki an samu sauki , kuma duk yan gidan su sun sake mata fuska kamar ba a yi komai ba , sai dai yanzu ta zama shiru , maganar kirki ma ba ta yi , Sai dai ta yi zaune waje guda , ta yi zugum kamar gunki ta kurewa waje guda ido , da ta zauna ba abun da ta ke tunani sai babyn ta , har ga Allah ta so cikin nan kamar rayuwar ta , yanzu kuma ta rasa shi , ba ma shi kadai ba , ta rasa kimar ta , da darajar ta , saboda mutumin da ba tsakanin shi da Allah ya ke tare da ita ba , yanzu ya na ina ? Ya gudu ya bar ta , da cikin bai Zube ba , yanzu ita da babyn zai gudu ya bar su , ga shi ba wani halin kirki gare su ba , ya za ta yi da shi , ci da sha suturar shi, karatun shi duk wa zai kula mata da su , ga shi har yanzu ba ta Kamala karatun ta ba , kenan sai dai ta hakura da karatun ta kula da babyn ?
( Allah ne kawai ya cece ki da ga wannan tubbun đ´đ´ )
Ta yi nisa cikin tunanin ta ya jiyo Muryar Safa ta na fadin " Djami tunanin mi ki ke yi haka tun dazu ina yi miki magana "
A razane ta dawo cikin hayacin ta na fadin " no ! no ! ba komai "
Kare mata kallo da kyau Safa ta yi
Cikin sanyi ta riko hannun Djamila ta saki wani cool murmushi ta ce " okay , ki rage yawwan tunani kin ji , ga exams nan sun gaba to ya kamata ki maida hankali kan karatun ki "
Dan karamin murmushi