Showing 39001 words to 42000 words out of 133773 words

Chapter 14 - HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) BY MEERAH.txt

Meerah   

28 Nov 2024

9701

wannan golden hair din na ta ya zubo ma ta har tsakar baya ta dukar da kai sai faman latsa wayar ta ta ke yi


Tun da ta fara tako stair din Djamila ke bi ta da ido ta na kallon ta
Har ta karaso cikin parlourn ta zauna geffen Snoopy sannan ta dago kai ta kali Djamila
Nan ta ga tray din da Balki ta kawo mata empty ba komai a ciki duk ta ciye
Yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Da kin fada min yunwa ki ke ji na sa a kawo miki abincin kirki "


Da sauri Djamila ta ce " a'a wannan ma na koshi "
Dan tabe baki Safa ta yi kafin ta ce " okay , tashi ki je ki yi wanka ki sauya kayan jikin ki , zuwa an jima sai na mayar da ke gidan ku "


Mikewa Djamila ta yi ta na kallon Safa ta ce " a ina bandakin ya ke ne ? "
Kallon Snoopy Safa ta yi kafin ta ce " tashi ka gwada mata guest room "
Dan karamin haushi ya yi kafin ya mike ya diro da ga saman sofar ji ka ke dib kamar wani babban abu
Takawa ya fara yi , ya yi gaba , a hankali ita ma Djamila ta bi bayan shi amma da ga nesa
Har sun yi dan gaba ta jiyo Muryar Safa ta na fadin " ki duba cikin closet ba a rasa kayan da za ki saka "
Da to Djamila ta amsa mata dai'dai lokacin da su ka shiga wani corridor kassan stair din
Door uku ne ke cikin corridor din , cen ta hango Snoopy tsaye bakin door ta farko
A hankali ta karaso wajen ta na kerma ta kai hannu ta kama handle din kofar ta na kallon Snoopy cikin ido
Ta na tura kofar ta shige ciki da gudu ta medo kofar , ta na yin haka ko Snoopy ya bar wajen da gudu shi ma ya koma wajen mamar shi


Bangaran Safa kuma ci gaba da latsa wayar ta ta yi kamar babu ita a wajen
Ta na a haka ta ga wani text ya bayana a saman screen
A hankali ta saki wani cool murmushi kafin ta karanto sakon kamar haka
* Hi Miss Safa ! Just to tell i will be in Nigeria very soon , i hope , i have the chance to see you
Sign : Musadeeq 😎 *


Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta mishi reply ta na cewa * I'm very happy to hear that , dama na jima ina burin na gan ka 😊 *


Ta na gama tura mishi Djamila ta fito da ga cikin corridor ta cikin parlourn ta na sanye da wata Abaya green colour mai kyau
Inda ta taso ta koma ta zauna ta na fadin " Safa wai ke kadai ki ke zaune cikin gidan nan ne , har yanzu ban ga mutanan gidan ba "


Dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " ni da momy da yar aikin mu sai.......... " ba ta karasa maganar ta ba sakamakon wayar ta da ta yi ringing
A hankali ta kai duban ta kan screen din * MD Mutalab * shi ne abun da ya bayana a kai
Daukan kiran ta yi kafin ta kai wayar a kunne ta na sallama
Amsa mata sallamar ta ya yi kafin ya daura da cewa " yawwa , Miss Safa ya ki ke , da fatan ban katse miki wani aikin ki ba "


Cike da fara'a ta ce " no ba wani aikin na ke ba , Hope na bar ku lafya ? "
" lafya lau alhamdoulilah , dama na kira ki ne dan na fada miki na ji labarin Doctor Amar Musadeeq na nan tafe Nigeria , Zan so ki samu dama ki tatauna da shi , kin san har yanzu babu gidan tashar da ta taba yin hira da shi , asali ma ba kowa ne ya san fuskar shi ba , so idan gidan tashar mu ta zama ta farko da ta yi hira da shi hakan ba karamin daukaka shirin ki zai yi ba , na barki lafya "ya na gama fadar haka ya katse kiran


A hankali Safa ta mike tsaye ta na fadin " doctor Amar Musadeeq ? Musadeeq ! No kar a je abun da na ke tunani shi ne , kuma yanzu ya ce min ya na nan tafe Nigeria ! ko dai da Doctor Amar na Chating ban sani ba , My idol ? " wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta sake cewa " Tabbbb akwai ta ko "
[29/08 Γ  11:52] MEERAHπŸͺ·πŸ©·:






πŸ’«πŸ₯€ HASKE BIYU πŸ₯€πŸ’«

( YAR JARIDA )















( A heart touching love story & destiny )


















STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🩷












Marubuciyar littafin


TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ

❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀

( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i












BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM













PAGE 13 πŸ₯€ ❀

















β–ͺ UNITED KINGDOM















β–ͺAMAR πŸ€™


















Zaune ya ke cikin katafaren parlourn su ya na zaune ya na faman latsa wayar shi ya saki wani cool murmushi
Ya na a haka wata kyakyawar mata ta fara tako stair din ta shigo parlourn ta na sanye da Abaya red colour mai bala'in kyau ta yi Rowling veil din a kan ta
Sam ba ta yi kama da Amar ba , asali ma ita skin din chocolate ne ya dan ciza , kuma ka na ganin ta ka ga cikakiyar Bafulatana , a shekaru za ta kai 50 years haka


A hankali ta karaso cikin parlourn ta zauna saman sofar da ke fuskantar ta Amar ta na murmushi ta yi magana da turanci ta ce " Doctor wannan murmushi haka kai kadai , Allah ya sa da sirikar tawa ka ke chating "


Ba tare da ya kale ta ba ya ce " eh da ita ce " ya kai karshen ya na kara fadada murmushin shi


Dan zaro idanu ta yi ta na kallon shi baki sake
Ta na shirin magana ya riga ta cewa " monday za mu tafi Nigeria ni da Assad "
" Masha Allah , gaskia na ji dadi haka , Allah ya sa da ga cen ku dawo da sirikai na , dan na gaji da wannan tuzurancin na ku , musaman Assad , mutun sai ka ce machine ba shi da lokacin hutu ko kadan "


Murmushi mai dan sauti Amar ya yi kafin ya ce " momy yi a hankali fa kin san ya na iya jiyo mu da ga inda ya ke , kin ga , ga shi nan ma ya na kira na "
Ya na gama fadar haka ya kai wayar shi a kunne ya na fadin " Hi Bro ! you're back ? "


A daya bangaran kuma sai da ya dan dauki lokaci kafin a amsa mishi da cewa " ba za ka fara tambayar lafya ta ba sai in na dawo , in ban dawo lafya ba "


Yar karamar dariya Amar ya yi kafin ya ce " ai dan na san ba abun da zai same ka ne ya sa ban tambayi lafyar ka ba "


Sai da a ka dauki wajen good five minutes kafin a ce " ka shirya gobe ina nan zuwa " ya na gama fadar hakan ya katse kiran


Sauko wayar Amar ya yi ya na murmushi ya kali matar nan ya ce " ki shirya gobe yaron ki na nan zuwa "
Ya na gama fadar hakan ya mike ya Haye stair ya bar matar nan ita kadai a parlourn


( GASKIYA YA KAMATA MU LEKO WANNA WANDA AMAR KE WAYA DA SHI πŸ€”πŸ€”πŸ€” )















β–ͺRUSSIA ( MOSCOW )


















Wani kyawatencen bedroom ne mai mugun girma , komai na cikin white colour ne
Cen na hango wani matashin Saurayi zaune saman wani katafaren bed na alfarma fari kal da shi har bedsheet din saman shi fara ce kal
Matashin ya na sanye da wandon jeans Black colour da T-shirt Navy blue
Ya na da yalwatacen gashi baki kirin curly ya zubo mishi ya rufe mishi fuska ta gefe da gefe
Ya sunkuyar da kai ya na faman latsa waya , hanayan shi farare kal amma ba fari cen ba , ya na da dogayen yatsu ma su kyau
Duk jikin shi a murde ya ke dan har ka na iya gano shatin jiyojin shi duk saman hanayan shi , ya na da fafadar kirji , t-shirt din baki daya kamar ta yi mishi kadan dan duk surar jikin shi a na iya ganin ta


Ya na a haka ya jiyo a na yi mishi knocking a kofa
Shiru ya yi bai amsa ba , kuma ya ji bugun kofar
A hankali a ka turo kofar , wata kyakyawar budurwa ta shigo wajen ta na sallama
Ta yi jinin haoussawa sosai , skin din ta chocolate ne mai mugun kyau ya konta har wani shining ya ke , da ga gani wannan renon ice cream ce dan yanayin jikin ta ya nuna ta na samun hutu sosai
Ta na da yan dara daren idanun farare kal kamar madara amma kwayar cikin su ash colour ce
Ga wani dan karamin bakin ta , lips din ta pink colour ma su laushi da ga gani
Ta na sanye da wata gown red colour mai kyau har kassa ta na sanye da wani dan karamin hijab zuwa kirji
Ta na da dan shape amma ba sosai ba a shekaru ba za ta wuce 18 to 19 years ba haka


Cikin wata yar siririyar murya cike da nitsuwa ta yi magana da turanci ta ce " Big bro , Daddy na son magana da kai "
Ta na gama fadar haka ta juya ta bar dakin , a hankali kofar ta fara yin gaba ta like kan ta


Sai da ya dauki wajen good 20 minutes da fitar yarinyar nan , sannan ya mike slowly kai a sunkuye ya fara takawa ya nufi kofar , ya bude ya fito dakin
Nan ya shigo wani parlourn komai na cikin shi da ga peach sai white colours


Bai tsaya parlourn ba ya fito part din baki daya ya na tafiya kai a sunkuye
A haka ya ci gaba da tafiyar shi har sai da ya wuce wajen door hudu da wani parlourn na sama wajen kamar yar balcony ce ya nufi wani stair zagaye da glass
A hankali ya fara sauko stair din ya na saukowa , har yanzu dai wannan kan na shi a sunkuye ya ke , ya na latsa wayar shi


A haka ya sauko ya karaso cikin wani parlourn na ji da gani kai kace ba da kudi a ka saye kayan parlourn ba
Duk abun da ke wajen peach da white colour ne
A hankali ya nufi wata doguwar sofa three seaters white colour ya zauna ba tare da ya kali mutanan da ke cikin parlourn ba


Ya na a haka ya jiyo Muryar wani lattijo da ke zaune saman sofar da ke fuskantar ta shi ya na fadin " Assad ina son yin magana da kai "


Ya na gama rufe bakin shi wani katon kare ya shigo parlourn da matsanincin gudu ya nufi saurayin da lattijon nan ya kira da Assad
Karen ya na da girma sosai , ya na da kuma jelar gashi kwarai brown colour mai mugun kyau , da ga gani wannan karen ya na samun kula ta musaman
Ya na isowa gare shi ya fada mi shi a jiki ya na haushi har sai da wayar hannun shi ta fadi


A dubu dari Assad ya dago kai ya kali karen nan ya ce mishi " Rex ! Sit down " ya fada da dan karfi


Da sauri karan ya sauko da ga jikin shi ya zauna a kassa geffen kafar shi ya na sunkuyar da kai


A hankali saurayin nan ya sa hannu ya janye jelar gashin kan shi ya meda ta baya ya daure sannan ya kai hannu ya dauki wayar shi , kafin ya jingina bayan shi a jikin sofar ya daura kafa daya bisa daya ya na kallon dattijon nan


Kaman nin shi sak irin na Amar kamar an tsaga kara , sai dai wannan ya so ya dan fi Amar haske , sannan ya fi murdewar jiki kuma lips din shi sun fi na Amar cizawa na shi sun so su yi red ma haka , ga shi kuma ya na sanye da bakaken glass ba ka iya ganin cikin idanun shi


Cikin nitsuwa dattijon nan ya fara magana ya na fadin " Assad , please idan ka je Nigeria kar ka dawo ba tare da matar ka ba , dubi don Allah yadda shekaru su ka ja ka amma har yanzu ko budurwa ba ka da , so ka ke ka kare rayuwar ka kai kadai "


Cikin nitsuwa Assad ya katse shi da cewa " yes , dama ni kadai na shigowa duniya haka zan bar ta kuma , babu wani gurbi na mace a rayuwa ta , saboda ba na bukatar ta , ba na bukatar wadanan halitun a kusa da ni , in har ka sa rai a maganar aure na , to zuciyar ka za ta buga ka mutu na dauki gawar ka na je na bunne na dawo na yi zama kai ta shafa ba ni ba "
Ya na gama fadar haka ya mike ya nufi hanyar fita parlourn , da sauri Rex ya mike ya bi bayan shi


Da kallo wannan lattijon ya raka shi har sai da ya fita sannan ya saki wani cool murmushi ya girgiza kan shi ya na fadin " duk ranar da soyayya ta kama ka wlh ba za ta yi maka da sauki ba " ya kai karshen ya na yar karamar dariya












β–ͺ NIGERIA ( KADUNA )












β–ͺSAFA πŸ’‹
















Kallon ta Djamila ta yi ta na fadin " Safa lafya kin mike ki na ta sambatu ke kadai ? "
Dawo da kallon ta kan Djamila ta yi kafin ta ce " no ba komai " ta kai karshen ta na sakin dan murmushi ta koma ta zauna


A takaice haka su ka share inin ranar a tare su na zaune waje babu me ce ma wani ufan , Safa na faman latsa wayar ta , ita kuma Djamila ta na zaune ta na kallon , a haka har lokacin sallat ya yi su ka tashi su ka yi sallar su
Sai wajen karfe 5 na yamma sannan Safa ta shirya za ta meda Djamila gidan su
Cikin sa'a ko duk mutanan gidan su na nan , nan ta samu ta yi musu bayanai a kan abun da ya faru , sannan ta ba su hakuri , da ga nan ta ja wa Djamila kunne a kan abun da ta aikata , da kuma saurin yarda da Mansour da ta yi , ba ta baro gidan ba sai da ta tabbatar hankalin kowa ya konta sun rungumo Djamila sannan ta sa kai ta fice musu gidan su


Sai misalin karfe 6 ta koma gida , ko da ta koma ba ta tsaya ko ina ba sai bedroom din ta , ta yi wanka ta shirya cikin wasu kananan kaya blue colour , sannan ta daura wata Abaya da ga saman su ta saka hijab din ta sannan ta gabatar da sallar ta dan lokacin sallar magriba ya yi
Bayan ta Kamala sallar ta , nan ma sai da ta zauna ta yi karatun kur'ani , ta karanta aduo'i , har sai da a ka yi kiran sallar isha sannan ta tashi ta gabatar da sallar
Da ta ida ta cire abayar da ta saka a saman kayan ta , ta koma dressing room da ita sannan ta fito bedroom din gaba daya


Kai tsaye parlourn kassa ta sauko , ta na tafe ta na latsa wayar ta ko kallon gaban ta ba ta yi
Sai da ta karaso cikin parlourn ta zauna saman sofa ta na ci gaba da latsa wayar ta ko kai ba ta dago ba bare ta san da mutun a parlourn ko babu


Ta na a haka kawai sai ji ta yi an kira sunan ta
A hankali ta dago kan ta , ba ta sauke idanun ta ko ina ba sai cikin na Sami
Ashe ko sallar isha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login