Showing 120001 words to 123000 words out of 133773 words
Sami ya yi mishi ya na cewa " wa ka ke kira da momy ? "
wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya juya ya nufi Toilet ya shiga
da kallo Sami ya raka shi har sai da ya shiga toilet sannan ya saki wani cool murmushi ya juya ya baro bedroom din ya koma tashi
▪MISALIN KARFE 10 NA DARE
zaune duk mutanan gidan su ke a parlourn ban da Marwan , kowa ya na rike da wayar shi ya na faman latsawa , Sami da Khalifa kuma su na kallon football a Tv , Twinkle kuma ta na rike da wani Book ta na karantawa hankali konce
bangaran Noor kuwa musaman earpieces ta ke sanyeda ta tafi duniyar tunanin ta
su na a haka Ali ya turo kofar parlourn ya shigo ya na sallama
a tare duk su ka amsa mishi sallamar shi ban da Noor da ba ta jiya ba
wani kyawatencen murmushi ya saki ganin ahalin nashi baki daya zaune cikin parlourn
a hankali ya karaso cikin parlourn geffen Twinkle ya zauna ya na fadin " what happened today ? na ga duk ku na zaune a parlourn haka , wata ta samu ? "
wani dan karamin murmushi Sami ya yi ba tare da ya kalle shi ba ya ce " Nothing Dad "
ya na gama rufe bakin shi Raïssa ta ce " yaron uncle Abdoul Karim ya na cikin gidan nan "
cikin rudu Ali ya ce mata " wane yaron kuma ? "
" Aryan , yayan Safa wanda ya ke prison , dazu da safe ya zo " Fadila ta fada ba tare da ta dago kan ta ba
har ya bude baki zai yi magana ya ji an fara tako stair
slowly ya daga kai ya na kallon Stair din , wata irin muguwar bugawa zuciyar shi ta yi har sai da ya shiga karanto kalmar shahada kassa kassa
a hankali Marwan ya ke sauko Stair din ya na sanye da wando jeans Baki da t-shirt purple ya na taku kai a sunkuye ya na latsa wayarshi
a haka ya karaso cikin parlourn kamar ya san inda Sami ya ke kawai ya nufi sofar ya mika mishi hannu ya na fadin " na ga key din motar ka "
kallon shi da kyau Sami ya yi kafin ya ce " ina kuma za ka je cikin daren nan ? "
" nightclub " ya fada a takaice
hararrar shi Sami ya yi ya na fadin " kar ka raina min hankali "
wani dan karamin tsaki Marwan ya ja ya na cewa " ka ga don Allah ka ba ni , akwai abun da na ke son na sayo , sannan ka ban wani abu dan babu komai a waje na yanzu "
" bari mu tafi " ya fada ya na kokarin tashi
da sauri Marwan ya ce mishi " please ni fa ba karamin ya........ " kut maganar ta yanke sakamakon dago kan shi da ya yi idanun shi su ka sauka kan Ali da ya tsare shi da idanu babu ko kiftawa
wani cool murmushi Marwan ya saki ya na cewa " Uncle , are you okay ka na min irin wannan kallon ? ko ba ka gane ni ba ? "
a hankali Ali ya mike ya na fadin " me ya kawo ka gida na ? , ta ya ma a ka yi ka fito da ga wajen nan ? "
" kamar ya me ya kawo ni gidanka , ku ji min wata sakarar tambaya , Uncle da allamun ba ka ji dadin gani na ba ? " Marwan ya fada cikin sanyin murya
cikin bacin rai Ali ya ce mishi " get out ! fice min da ga gida mara kunya kawai , ban san ya a ka yi ka fito da ga wajen cen ba , amma ka tabbatar sai na mayar da kai , yanzu fice min da ga gida , Khalifa , Sami , ku fitar min da shi "
ko kallon shi ma Khalifa da Sami ba su yi ba , shi dama Khalifa ba sauraron maganar Ali ya ke ba sai abun da ya ga dama ya ke yi , bare shi uwa uba Sami da ya tsane shi baki daya
cikin sanyin murya Fadila ta ce " why Daddy ? brother din mu ne , na ga shi ma ya na wa yancin zama a cikin gidan nan "
ta na gama fadar haka Farida ta daura da cewa " yeah Dad "
cikin bacin rai Ali ya ce musu " idan na sake jin muryoyin ku a wajen nan sai na fasa muku baki , ku tashi ku bar wajen nan " ya fada ya na nuna musu hanyar stair
wani dan karamin tsaki Farida ta ja kafin ta mike cike da bacin rai ta nufi stair , Fadila na biye da bayan ta su ka Haye
su na hawa Twinkle ta mike ita ma , idanunta na kan books din hannun ta , ta nufi stair ba tare da ta cewa kowa komai ba ta haye
su na barin wajen Ali ya tako ya riko hannun Marwan ya nufi hanyar fita parlourn ya na fadin " wuce ka fice min gida "
da karfi Marwan ya kwace hannun shi ya juya ya wanke Ali ya wani gigitacen mari
duk sai da su ka zaro idanu su na kallon Marwan , Sami har da sakin wani boyayen murmushi
gyara tsayuwar shi Marwan ya yi ya na nuna shi da yatsa ya ce " ka bar ganin ka na yayan mahaifina , wlh ba abun da zai hana ni yi maka dukan mutuwa , ba ruwa na da shekarun ka da girman ka "
hannu saman kunci Ali ya ke fadin " yanzu Marwan ni ka mara ? "
" na mare ka me za ka yi ? ko sake tura ni prison za ka yi ? , okay " ya kai karshen ya na rabawa ta geffen Ali ya nufi doguwar sofa ya zauna ya daura kafa daya bisa daya sannan ya ce " meda ni prison din , ina jira , don Allah cikin daren nan ka mayar da ni prison idan ka isa Ali " ya fada mishi cike da kasaita
a hankali Ali ya tako ya karaso gaban Marwan ya tsaya ya na fadin " Tabbas , ka cika cikaken dan iska "
bai kai karshen maganar shi ba ya ji Marwan ya bushe da wata shegiyar dariya har da daga kai sama
sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya sauko kan shi ya na kallon Ali ya ce " wai dama sai yanzu ka sani , ka je prison din ka tambaya wanene the boss , za fu maka iya iskancin nawa , Wanda ka sani da ma wanda ba ka sani ba "
ya na gama fadar haka ya sauko da kafar shi ya mike tsaye ya tsaya dab gaban Ali har su na iya jiyo nunfashi juna murya kassa kassa ya ce mishi " bari mu yi cikin ruwan sanyi kafin mutane su jiyo mu , na ba ka nan da sati guda , duk wata company , duk wani gida kai har ma kudin da a ka samu tsawan shekarun nan , duk wani abun Daddy da ke hannun ka ina son ya dawo hannu na nan da one week tun ina maka cikin ruwan sanyi , Idan kuma ka bari one week din nan ta wuce ba ka yi abun da na ce ba , za ka ga wanene ainahin Marwan Abdoul Karim "
" sai dai ka yi duk wani abun da za ka yi amma ba ka isa ba " Ali ya fada ya na kallon Marwan cikin ido
wata yar karamar dariya Marwan ya yi ya na juyawa
sai da ya gama dariyar shi sannan ya juyo ya kai wa Ali wani mugun bugu a face har sai da ya fadi kassa
a hankali Marwan ya tsuguna ya kai hannu ya shako wuyan Ali da karfi ya na fadin " ba shawara na ke ba ka ba , umarni ne ! ina ga Daddy was so nice with you , to ni ba Daddy ba ne , ba na tsoron ka , ba na kuma jin kunyar sa hannu na dake ka idan ba ka yi abun da na ke so ba , ba zan kashe ka ba a yanzu , sai na yi maka irin azabar da ka yi mana a prison za ka ji irin radadin da na ji , da ga yau ba za ka sake fita da ga cikin gidan nan " ya na gama fadar haka ya saki wuyan Ali ya na tura shi
nan take Ali ya fadi ya na rike da wuyan shi ya na tari
komawa Marwan ya yi ya zauna saman sofar bayan shi ya kali Raïssa ya ce mata " ke tashi kawo mishi ruwa "
ai bai gama rufe bakin shi ba ta tashi da gudu ta nufi dining room
ko one minute ba ta yi ba ta dawo rike da glass din ruwa , ta nufi Ali ta Zube saman guyiwowin ta ta sa hannu ta talabo kan shi ta kai glass din saitin bakin shi
da sauri Ali ya fara shan ruwan nan har zubewa su ke yi
sai da ya shanye su sannan ya mike zaune ya na nunfashi sama sama
wata yar iskar dariya Marwan ya yi ya na fadin " ka ji tsoro ? kadan ma ka gani , sai na kashe ka cikin gidan nan , Sami ina son ka je office din shi gobe , duk wasu file da laptop din shi ka tataro ka kawo min da ga yau ni zan ci gaba da kula da business din mahaifina , kai kuma malam Ali ko harabar gidan nan ba za ka sake saka kafa ba , a nan za ka zauna duk wani aikin gidan da ga shara wanke wanke zuwa guga duk kai za ka yin su "
da sauri Raïssa ta katse shi da cewa " kai ba ka da hankali ne , mahaifin nawa ? wlh ba ka isa ba , ka bar ganin ka je prison za ka zo ka yi mana iskanci cikin gidanmu ka na fada mana abun da ka ga dama "
wani cool murmushi Marwan ya sakin mata kafin ya mike a hankali ya karaso gaban ta ya tsaya
shiru ya yi ya na kallon ta ya na murmushi ba tare da ya ce komai ba , ita ko sai hararrar shi ta ke yi
ba zato ba tsanmani kawai ta ji ya wanka mata mari har sai da ta fadi kassa ta na sakin kara
a hankali ya tsugunna gabanta ya na fadin " O'O lafiya ki ka fadi ke daya , akwai zafi ne ? " ya kai karshen ya na kokarin taba face din ta
cikin hannu guda ya matse face din ta ya dago kan ta ya ware mata idanu da kyau ya ce mata " ba a fada miki cewa babu kyau sa baki cikin maganar manya ba ? da uban ki na ke magana ki bari in na tabo ki sai ki saka min baki , sakara kawai " ya kai karshen ya na sakin face din ta ya mike tsaye ya koma saman sofar da ya taso ya zauna
" tunda ki na da bakin kare uban ki , za ki taimaka mishi cikin aikin shi , da ga yau ke za ki dinga yin girki a cikin gidan nan , ina son breakfast di na ya Kamala karfe 7 dai'dai , lunch kuma karfe 1 na yamma diner kuma karfe 9 , idan ki ka haura ko da one minute ne sai jikin ki ya fada miki , tun bana sunana kawai ku ke ji yanzu za ku tabbatar ko ni wanene "
dawo da kallon shi ya yi kan Ali da ya ke zaune ya zuba mishi ido babu ko kiftawa
a hankali ya matso bakin sofar ya na nuna shi da yatsa ya ce " duk abun da na zama laifin ka ne , yanzu kuma ka shirya girbar abun da ka shuka , you've signed your death sentence by yourself Mister Ali " ya na gama fadar haka ya tashi ya nufi stair ya haye abun shi
ya na barin wajen Raïssa ta saki kuka ta na fadin " Daddy ka na gani fa ya mare ni ? "
ba tare da ya juyo ba Khalifa ya ce mata " ko shi kan shi Daddy ba ki ga irin marin da ya sha ba , me ki ke so ya yi miki , ai aikin gama ya riga da ya gama "
kara sautin kukan ta Raïssa ta yi ta na fadin " ni gaskiya ba zan yarda ba wlh sai na rama , shi har ya isa ya sa hannu ya mare ni "
" yo ke wacece , har Daddy gashi nan zaune ya sa hannu ya mara bai rama ba ke me ki ke tunani za ki yi a kan shi " Sami ya fada ya na kokarin danne dariyar shi
" amma........ " ba ta kai karshen maganar ta ba Ali ya katse ta da cewa " ke don Allah malama yi wa mutane shiru sakara kawai "
da sauri ta tashi ta nufi stair da gudu ta haye ta na kuka
wai ku tsaya duk abun nan fa da ya faru Noor ta na zaune saman sofa ta na faman latsa wayar ta kamar babu ita a wajen
a hankali Ali ya mike tsaye ya kalli Sami da Khalifa da kyau irin kallon nan na takaici kafin ya ce " ku dai wlh an yi asarar maza , ku na ji ku na gani wani ya shigo cikin gidanku ya sa hannu ya daki mahaifin ku , amma ku kasa daga ko dan yatsa , kun dai ji kunya wlh "
juyowa Khalifa ya yi ya kale shi cikin ko in kula ya ce " to mu minene namu a ciki ? mu mu ka hada ku da za mu raba ku ne , na ga ai kai ka fara jan shi , da ka rike girman ka da hakan ba ta faru ba " ya kai karshen ya na mikewa ya nufi stair ya Haye
har Sami ya bude baki zai yi magana Ali ya riga shi cewa " yi min shiru don Allah , kar ka bata min rai sakare kawai " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya nufi stair
da kallo Sami ya raka shi har sai da ya haye sannan ya mike ya na fadin " kanka a ke ji " ya kai karshen ya na fara takawa ya nufi stair ya Haye
ya bar Noor nan zaune ita kadai ta na faman latsa wayar ta da allamun ta tafi duniyar tunanin ta dan sai wani cool murmushi ta ke saki
bangaran Marwan kuma kai tsaye bedroom din shi ya wuce
ya na shiga ya Haye saman gadon shi ya yi rub da ciki da allamun bai ji dadin sa hannun da ya yi wa Raïssa ba , bai taba tunanin wata rana zai iya daga hannu ya taba mace da sunnan bugu , sai ga shi yau ya bugi macen da ta ke matsayin kanwar shi ma , gaskiya bai ji dadi ba , amma ba yadda ya iya dole ta sa hakan duk cikin tsarin plan din su ne
ya na konce a haka ya jiyo Muryar Sami ya na fadin " Aryan , are you okay ? "
a hankali Marwan ya juya a mike zaune bakin gadon shi ya saki wani dan karamin murmushi ya ce " yeah , am okay "
" are you sure ? na ga yanayinka ya sauya lokaci guda , ko dai yunwa ka ke ji ? " ya kai karshen ta na sakin wani dan karamin murmushi
hararrar wassa Marwan ya yi mishi ya na fadin " Eh , yunwa na ke ji , amma kai zan ci , dan rainin sens kawai , ni kyale ni barci zan yi " ya kai karshen ya na komawa ya yi rub da ciki
wata yar karamar dariya Sami ya yi kafin ya karaso bakin gadon ya zauna ya na fadin " ba Wata yunwa , fada min gaskiya "
wata yar karamar Ajiyar zuciya Marwan ya sauke kafin ya juya ya mike zaune geffen Sami ya ce " why lokacin da na fara yi wa Ali magana ba ka tashi ka bar wajen ba ? na san Khalifa dama ba ya jin maganar shi , lokacin da ka ga na fara yi mishi magana kamata ya yi ka tashi ka tafiyarka , yanzu na dake shi a gaban ka , kuma ba ka wani yi yunkurin tsayar da ni ba , zai fara tunanin wani abu , har ya gani bakin mu guda "
a hankali Sami ya gyada mishi kai ya na cewa " Eh fa ka yi gaskiya , amma kar ka damu ba zai gane komai ba "
" no Sami , dole sai mun yi takun mu cikin duhu , yadda ba zai ga komai ba " Fadin Marwan ya na kai hannu saman bedside drawer ya dauki wayar shi
dan jinkirtawa Sami ya yi kafin ya ce mishi " yanzu minene shirin mu na gaba ? "
fara latsa wayar shi Marwan ya yi ya na fadin " kamar yadda na ce maka , gobe ka je office din shi ka dauko min duk wani abu da ya shafi business din shi , files , laptop dukka "
cikin nitsuwa Sami ya katse shi da cewa " to ka na ganin shi Ali zai yarda ya bar maka business din ? kar fa