Showing 84001 words to 87000 words out of 133773 words
dauke da wasu lamusasun Royal sofas Farare kal kamar yanzu a ka fido su da ga cikin ledodin su
Sofas din guda biyar ne , Guda Three seaters , biyu Two seaters biyu One seater
da ga tsakiyar su kuma akwai wani chinesse carpet Fari kal mai girma , da ga saman shi kuma wata Table ce , ta glass fara kal ita ma , amma table din a rabe ta ke , kamar kananan table ne guda hudu a ka hada a ka yi gudar
haka kuma a geffen Doguwar sofar akwai wasu kananan Table guda biyu su ma na glass
kuma sofar ta na fuskantar wata makekiyar Tv plasma makale a bango
ga wata yar karamar table a kassan ta , wadda a ka daura remote da sauran su
bayan sofar kuma da ga geffen dama , wata Dining room ce , mai girma babu komai a cikin ta sai dining table Fara kal kamar ta glass dan har kyali ta ke yi , ta na zagaye da wasu Chair guda Goma Farare kal su ma
ni wannan farin dukka ya fara takura min , da allamun mai gidan nan ya na son white color , kuma ya na da tsabta kun san yadda abu fari ya ke da saurin daukar datti da gura amma wannan a gyare a goge su ke kamar yanzu a ka ciro su da ga cikin leda su
cen da ga bayan dining table din akwai wani wall na glass wanda zai sada ka da Kitchen da ga cikin Dining room din ka ga iya ganin abunda ke cikin kitchen din dan mirror din ba smoking ba ne wanda ba ka iya ganin abunda ke bayan shi
kitchen din ma kadai ta isa abun kallo , an yi mata tsari irin na kitchen din kassashen waje , ta na a share a goge kamar ba girki a ke a ciki ba
bari dai mu dawo cikin parlourn
a geffen Hagu akwai wani Stair fari kal zagaye da wasu bar ina ga na karfe ne , amma farare ne kal an yi musu wani design kamar flowers , har da wani blue color a cikin su kamar flowers din gaske
kassan stair din na hango wani dan corridor
a hankali na shiga cikin corridor din , nan na ga wani parlourn daban , amma girman shi bai kai na farko ba , nan kuma fournitures din light pink ne , har ceiling din
ya kawatu da wasu Sofas ma su mugun kyau , da wata doguwar sofa guda irin wannan sofas ma su bin bango , sai kuma one seater guda biyu
da ga tsakiyar su kuma wata yar karamar table ce , kamar ta wood haka
gaban table din kadan akwai wata table ta wood ita ma an daura wasu Decoder da remote , da ga saman ta kuma wata Tv plasma
a cikin parlourn akwai wasu door guda hudu a jere da allamun bedrooms ne
( π€§π€§π€§kai gaskiya na gaji da description din nan , bari mu koma cikin labarin mu )
da gudu wata kyakyawar yarinya ta ke sauko stair din parlour
yarinyar fara ce kal kamar ka taba jini ya fito , da ga gani wannan shalelen baba ce
a shekaru ba za ta wuce 4 to 5 years ba
kallo daya za ka mata ka san ba yar Africa ba ce , dan ta na kama tak da mutanan China
ta na da kananan idanun su farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma baka kirin da ita , ta na da dan karamin baki lips din ta kuma pink color
ta na da gashi sosai blond kamar Gold har wani kyali ya ke da allamun ya na shan gyara , ta na gudu gashin na tashi sama
ta na sanye da wani dan karamin wando kamar pant haka , da wata yar riga duk pink color
ta na gudu ta na yar karamar dariya , a haka har ta karaso cikin parlourn ta gudu bayan doguwar sofa ta buya ta na yar karamar dariya
a haka na jiyo Muryar wata mata ta na fadin " Safa ! Safa ! don Allah ki zo ki shirya kar mu yi late " ta na gama fadar haka na ga ta fara tako stair din
kyakyawar mace ce yar china 100% gaba da baya , har wadanan kananan idanun na su ta na kama tak tak da yarinyar da ta ke kira Safa kamar an tsaga kara , a shekaru za ta kai 33 years haka ko fi dan yanayin jikin ta na nuna ta na samun hutu sosai da gyara , ta na sanye cikin wata Abaya red color mai mugun kyau ta yi Rowling veil din ta a kai
ta na ida sauko stair din wani dattijo ya turo kofar shigowa parlourn ya shigo ya na sallama
wani cool murmushi matar nan ta saki ta na amsa mishi sallamar shi sannan ta ce " sannu da dawowa Darling "
Dattijon gaskiya kyakyawa ne jinin hausa fulani skin din shi chocolate ce mai mugun kyau ta konta mishi , ya na kananan idanun farare kal amma kwayar cikin su Brown ce , ya na da dogon hanci kamar pencil , ya tara gemu kadan ba sosai ba ga wani kontancen saje a geffen fuskar shi ya kara kyawata fuskar ta shi , da ga gani ka san mutumin arziki ne a shekaru zai kai 45 years haka
ya na sanye cikin wasu manyan kaya na shadda fara kal da ita , sai tashin wani dadaden qamshi ya ke , Fuskar shi dauke da wani kyawatencen murmushi
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
πΈπ ( A heart touching love story & destiny ) ππΈ
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ππΈ
γTHE ROYALTY LOVE ππΈπγ
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ :FREE BOOK
β€β EXILED PRINCE ββ€ : PAID BOOK
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
πππππππ
https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
ππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
___________________________________________
LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN β€βEXILED PRINCE ββ€
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
ππππ
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
πππππ
Zain (Airtel)
08081129487
sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753
___________________πππππππππ____________________
ο½ PAGE 26 π₯ β€ ο½
a hankali Dattijon nan ya fara takawa cikin sanda ya nufi sofar da Safa ta buya a bayan ta
da sauri ya sa hannayan shi biyu ya daga Safa sama ya na cewa " wai ke ba za ki daina gajiyar min da baby na ba ? "
dariya sosai Safa ta yi har sai da kananan hakwaren ta su ka fito
a hankali dattijon nan ya zagayo ya zauna saman sofa sannan ya zaunar da Safa saman cinyar shi ya na ci gaba da kallon ta
sai da ta gama dariyar ta sannan ta ce " Daddy ka daina ce ma momy baby , dubi fa ta tsufa "
a hankali Dattijon nan ya kai hannu ya ja mata hanci ya na cewa " ki daina ce wa momyn ki ta tsufa , kar ki bata mata kin san fa ba ta son a na cewa ta tsufa " ya kai karshen ya dawo da kallon shi kan matar nan
wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta karaso cikin parlourn ta zauna geffen shi ba tare da ta ce komai ba
ta na zama Dattijon nan ya rage sautin Muryar shi kamar mai rada ya ce ma Safa " Gaskiya momyn ki ta na da kananan idanu , yanzu ga shi duk kun dauko kananan idanun ta na dan China "
wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " momy wlh Daddy cewa ya yi ki na da kananan idanu irin na yan china "
a tare matar nan da dattijon su ka zaro idanu sannan ya ce " kash , Wai ke ba ki iya rike sirri ba ? "
tsuke fuska matar nan ta yi ta na cewa " yanzu His excellency me idanu su ka yi maka " ta kai karshen cikin shagwaba kamar karamar yarinya
cikin sigar rarrashi His excellency ya ce mata " Haba My Twinkle ba abun da su ka yi min wassa ne fa na ke mata , kamar dai ba ki san halin yarinyar ki ba da son karawa miya gishiri , ai a haka na gani kuma na ce ina so , My first lady "
" His excellency na ce maka ka daina kira na da Twinkle , kai fa ka sauya min sunan nan kuma yanzu shi ne za ka ci gaba da kira na da hakan ni gaskia ba na so " ta na gama fadar haka ta mike ta fara takawa ta nufi stair ta Haye
da kallo ya rakata har sai da ta Haye sannan ya juyo ya kali Safa ya ce " momyn ki rigima gare ta wlh , ni ban ma san ya a ka yi na fada soyayyar ta ba da wasu kananan idanun ta kamar na yan china "
wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Daddy , momy fa ta fi ka kyau "
" oun na sani , ai kyawon ta ya na daya da ga cikin dalili na na auren ta "
" Da gaske Daddy ? Fadamin yadda a ka yi ku ka hadu da momy "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " shikenan bari na ba ki labari , a lokacin ina da shekara 28 haka ina a aiki a matsayin doctor , to sai mu ka tafi china wajen wani karin karatu , duk cikin Nigeria mu hudu ne kawai mu ka samu wannan damar , bayan mu je China , mun dan yi kwana biyu haka mun huta sai a ka dauke mu a ka kai mu wani babban Hospital wanda za mu fara aiki a cen , a ranar kuma momyn ta shigo Hospital din sun kawo mahaifin su ba shi da lafiya , Ta na sauke idanu sama na ta ji babu wanda ta ke so sama da ni "
ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Twinkle ta katse shi da cewa " I know , I have a good memory , but i don't think haka abun ya faru kamar yadda ka ke fada "
a hankali His excellency ya dago kai ya kale ta ta na sauko stair a hankali har ta karaso cikin parlourn ta dawo geffen shi ta zauna
murmushi mai dan sauti His excellency ya yi kafin ya ce " ki bari na gama ba ta nawa labarin sai ki ba ta naki "
" okay ci gaba " ta fada ta na daura kafa daya bisa daya ta zuba mishi ido
dawo da kallon shi ya yi kan Safa ya ce " ki na ji ko , Ta na sauke idanu sama na ta ji babu wanda ta ke so a duniya sama da ni , ni kuma a lokacin ban lura da ita ba ina kan aiki na , kuma cikin wani ikon Allah duk doctors din da ke cikin Hospital din , ni ne a ka bawa damar kula da mahaifin ta , sannu sannu na fara duba shi har mu ka share wajen one week ina tare da su amma ko so guda gaisuwa ba ta taba shiga tsakani na da ita , a haka har a la sallame su , kwana biyu bayan an sallama me su , na je wani Mall yin shopping , a nan na sake haduwa da ita , ita ta fara yi min magana ta gaishe ni ta ce min ita ce yarinyar majinyacin nan da na yi wa,magani , na ce mata eh na gane ta , da ga nan ta shiga yi min godiya na ran mahaifin ta da na ceto , na nuna mata ba komai duk cikin aiki na ne , a haka mu ka ci gaba da yin shopping din a tare mu na tafe ta na yi min hira a kan ta , bayan mun Kamala mu ka je reception na ce ta bari zan biya amma fir ta ki ta ce ita za ta biya saboda irin al'herin da na yi mata ba za ta iya bari na biya ba , haka mu ka shiga jayaya da ita har dai na hakura na bari ta biya , da ga haka mu ka baro Mall din amma kafin nan sai da ta karbi number ta , ta ce min za ta dinga kira na mu gaisa , da ga haka mu ka yi sallama , sannu sannu mu ka fara sanin juna ta na sake min , mu na wassa da dariya , mu na haduwa bayan na sauka da ga aiki , mu tafi shan coffee ko shan ice cream , wani lokaci ma mu tafi kallon film har soyayya ta shiga tsakanin mu , soyayya mai karfi yadda ko kwana ba ma iya yi ba mu ga juna ba , a haka har na Kamala aiki na a China , na komo Nigeria ko bankwana ban yi mata ba , amma tun bayan dawowa ta ba abun da na ke tunani sai ita na kassa barci , na kassa cin abincin har jinya na yi a Asibiti , family na ba rokon da ba su yi min ba na fada musu abun da ke damu na amma fir na ki yarda , a haka har na share wajen two months , a cikin na ukun na yanke shawarar komawa China dan na gan ta , sai dai ko da na koma china na neme ta na rasa , ashe bayan komawa ta Nigeria ita da familyn ta sun koma UK da zama , babu yadda na iya na kama hanya na dawo Nigeria inda na sake kontawa sabon ciwon , na rashin ta a kusa da ni , dan duk duniya ita kadai ce macen da na taba fadawa kalmar so yanzu kuma ga shi mun rabu , sannu sannu har sai da na share one year a haka , a cikin shekarar ba yin da ahali na ba su yi da ni ba a kan na yi aure ko zan samu saukin abun da na ke ji duk da ba su san abun da ke damu na ba , amma na ce ba na so saboda mace guda na ajiye wa gurbin mata a waje na kuma bayan ita babu wadda zan bawa , kawai watarana na je Hospital sai secretary di ta ta ce min na yi bakuwa , amma ta ce ta tafi an jima ta dawo , kawai na ce mata okay , after some hours ta dawo ta ce min guest di ta ta dawo kuma ta na son gani na yanzu , da ya ke a lokacin saura 30 minutes na sauka sai na ce mata kawai ta shigo , ba musu ta je ta ce ma bakuwar na ce za ta iya shiga , Jim kadan na ga an turo kofar office di na a shigo , lokacin da ta shigo kai na ya na sunkuye na ce mata ta zauna , ba musu ta karaso ta zauna ta na kallo na da murmushi a fuskar ta , sai na tambaye ta abun da ya kawo ta waje na sannan na dago kai , ina ganin ta na ji zuciya ta ta buga da karfi tamkar a mafarki haka na ke ganin ta wani kyawatencen murmushi ta sakin min ta daga min hannu ta ce HI , mamaki ne ya hana ni magana kawai na tsaya ina kallon ta babu ko kiftawa , ganin yadda na tsare ta da idanu ya sa ta cewa DEAR BA KA GANE NI BA ? ban san lokacin da wasu hawaye su ka zubo min ba , da gudu na tashi na je na rungume ta cikin fitar hayaci kamar wani ya ce zai kwace min ita , kin san abun da ya faru , ashe lokacin da na dawo da ga China bayan na je neman ta a lokacin ita ma ta je nema na kawai dai mun yi crossing ne ,
inin ranar a tare mu ka share shi , amma na fada mata ba zan iya ci gaba da soyayya da ita saboda ita ba musulma ba ce , ni duk na manta da wannan tun farkon soyayyar mu sai a lokacin , ta yi kuka kamar za ta hadiye ran ta , amma haka na danne mu ka rabu da juna , a tunani na ta koma UK a ranar ashe ba ta koma ba , washe gari early ina shigowa office ita ce guest na farko da ta zo waje na , na roke ta ta tafi saboda ba za mu iya kasance wa a tare ba tun farko laifi na ne da na manta ita ba musulma ba ce , haka ta dinga yi min magayi ta na kuka a kan kar na rabu da ita , har ta ba ni labarin auren da a ka yi kokarin yi mata bayan komawar su UK amma