Showing 24001 words to 27000 words out of 133773 words
, ya na sanye da kayan barci ash colour masu bala'in kyau da laushi
Takowa ya ke yi a hankali kamar an yi mishi dole , da ga gani ka san cikin magagin barci ya ke
Kitchen ya shiga, ya nufi fridge ya bude ya dauki gorar ruwa guda daya sannan ya fito kitchen
A parlour ya tsaya ya zauna saman lamusasun sofas din nan sannan ya bude gorar ruwan ya kai baki
Ya na tsaka da shan ruwan ya jiyo wayar shi na ringing
Sai da ya ida shan ruwan shi sannan ya sauko da gorar ruwan ya rufe ya ajiye kassa geffen shi sannan ya kai hannu cikin aljihun shi ya fido wayar
Bai tsaya dubawa ya dauki kiran ya kai a kunne ya na murmushi ya ce " hello "
Sai da a ka dauki lokaci kafin ya jiyo wata zazzakar murya a na fadin " Yanzu zan shiga jirgi zuwa korea , ka shirya nan da three days zan dawo , ran monday za mu tafi Nigeria "
Kara fadada murmushin shi Amar ya yi kafin ya ce " Da gaske ka ke Ass...... "
Bai karasa maganar shi ba ya ji kiran ya tsinke
Sauko da wayar ya yi ya na dan murmushi ya ce " kai dai ka sa ni ba , dai ka yarda mu je ba , za ka ga abun da zan yi maka "
Ya na gama fadar haka ya mike ya nufi stair ya Haye
βͺNIGERIA ( KADUNA )
Wednesday : 10Am
βͺSafa π
A hankali ta ke tako stair din gidan , kan ta a sunkuye ta na latsa wayar ta
Ta na sanye cikin wando palazzo Red colour da shirt mai dogayen hannu white colour , ta saka dan karamin hijab zuwa kirji shi ma red colour , ta saka wasu sneakers a kafafun ta farare kal kamar ba a taka kassa da su , ita dai duk kayan da za ta saka sai ta yi musu dress code ba ta iya sa kaya barkatai ba haka tai ta harhada colours
Sai da ta sauko stair din ta nufi table din tsakiyar parlour ta dauki yar jakar ta da ke sama
Ta bude ta saka Wayar ta a ciki , sannan ta rataya jakar , ta dauki key din motar ta sannan ta juya ta fice parlourn
Kai tsaye parking space ta nufa , ta shiga motar ta , ta kunna ta ta bar gidan da gudu
Cikin abun da bai fi five minutes ba ta iso university din su
Ko da ta shigo ba ta wani shiga class ba , kai tsaye library ta wuce , dan ita dama wajen Haoua ta zo ba yin lectures ba
Kamar ko ta sani ta na shigowa library din ta hango su zaune ita da Djamila ko wace ta na rike da book's din ta ta na karantawa
Su na a haka hawa ta ga an ajiye mata wasu box guda biyu a gaban ta duk farare amma ta sama ta fi dan girma
Murmushi kadan Haoua ta yi dan ta san duk duniya babu wanda ke yi mata irin wannan abun sai mutun guda
A hankali ta mike ta juyo ,
Sai dai ta na juyowa ta ga Safa har ta kai bakin kofar library din ta fice
Nan take murmushi da ke kan fuskar ta ya bace ta koma ta zauna
Ta kai hannu ta bude box ta sama
Nan ta ga wani kyakyawan cake , pink colour mai bala'in kyau , ko ni sai da na hadiye yawu , da ga sama an rubuta HAPPY BIRTHDAY MY HAOUA da chocolate
Haoua na ganin shi ta dago kai ta kali Djamila ta ce " Djamila don Allah ki je ki ba wa Safa hakuri , wlh ba laifin ta ba ne "
Da sauri Djamila ta katse ta da cewa " to laifin wanene , dama Mansour ya jima ya na fada min , in rabu da ita ba mutuniyar kirki ba ce amma na ki yarda da shi "
Cikin bacin rai Haoua ta ce " ke Djamila kin san abun da ki ke fada kuwa , shekara uku yanzu mu na tare da Safa dai'dai da rana guda ba ta taba fada mana wata bakar magana ba , saboda wani sakaran banza cen za ki watsa mata kassa a ido , me Safa a ba ta yi ma na ba , kar ki manta har shopping ta ke daukar mu ta kai mu mu zabi kayan da mu ke so sannan ta biya da kudin ta , duk wasu bukatun mu ita ke biya ma na su , har kudin karatun mu ita fa ke biyan su "
" ya isa don Allah Haoua , cewa fa ta yi ta na son saurayin da zan auren , bayan kuma ta san mu na tare ni da shi "
" ke dai wlh an yi sakara ma in ce , duba ki gani har Abbas , saurayin da ya fi ko wane kyau da kudi a cikin university din nan , ya ce ya na son Safa amma ta share shi , samari nawa cikin university din nan su ka ce su na son ta amma ta ki kula su , sai wani sakare banza cen "
Da sauri Djamila ta katse ta da cewa " Haoua ki daina ce mishi sakare "
Mikewa tsaye Haoua ta yi ta bugi table din tsakiyar su da hannu ta har sai da hankalin sauran daliban ya dawo kan su , ta ce " na fada sakare mara mutunci , kin san dalilin da yi wa Safa wannan kazafin , Ganin shi ta yi restaurant din da mu ka je shan ice cream ranar nan ya na tare da wata yar iskar yarinya su ka shigo restaurant din ya na rike da kugun ta , lokacin da su ka yi ido hudu da Safa sai su ka juya da sauri ya bar wajen dan kar ki gan shi , ko jiya abun da ya sa Safa ta dake shi , cewa ya yi ya na son ta har ya yi kokarin ya taba ta shi ne ta dake shi , amma da ya ke ke idon ki ya rufe ba ki ganin komai sai shi ba ki tsaya ki iya tantance mai fadar gaskia da karya , wlh kin ba ni kunya Djamila , wlh idan ba ki je kin ba wa Safa hakuri ba , ki cire ni da ga cikin layin aminan ki "
Ta na gama fadar hakan ta dauki bag din ta ta saka , ta dauki box din nan da Safa ta ajiye mata , ta bar wajen , ta fice libraryn baki daya
Ta bar Djamila nan zaune sai faman muzurai ta ke yi da ido
Sai da ta dauki wajen good 30 minutes a haka , har sai da ta rage ita kadai cikin library din sannan ta tashi ta dauki jakar ta jiki ba kwari ta fito library din
Sai tunanin kalaman Haoua ta ke cikin zuciyar ta , ta rasa wa za ta kamawa , ba karya ta san Safa ba ta taba yi magana da wani saurayi cikin school din nan ba , ko gaishe ta su ka yi sai dai ta daga musu hannu , ta ya za a yi ta ce ta na son Mansour mutumin da sai ta saye shi , shi da ahalin na shi baki daya , ita sai yanzu ta fara tantama a kan abun da Mansour ya fada mata
Cikin harabar school din ta fito , ta samu wani bancin karkashin wata bishiya ta zauna ta dafe kan ta da duk hannayan ta biyu
Ta na a haka ta jiyo Muryar Mansour ya na fadin " kin ji tsoro ne ? "
A razane ta dago kai a tunanin ta shi ne
Sai ta ga Safa tsaye gaban ta , ta na rike da wayar
Ta na shirin magana Safa ta daga mata hannu alamun ta tsaya
Ba musu ta yi shiru ta na sauraron recording din maganar da ta yi da Mansour ba tare da ya sani ba
Duk abun da ya fada ma Safa sai da Djamila ta ji , nan take ta ji zuciyar ta ta yi mata nauyi , idanun ta su ka kawo ruwa
Lips din ta na kerma ta bude baki ta na shirin magana , Safa ta juya ta bar mata wajen
Ita dai Djamila ta kassa motsawa jin abun da kunnuwan ta su ka jiyo mata sam ta kassa yarda
Safa kuma ta na barin wajen kai tsaye parking space ta koma , ta shiga motar ta
Ta na shiga Haoua ta ce " ya kin saka mata ta ji "
Kallon ta Safa ta yi kafin ta ce " e ta ji ya , kin san kin ka shawara me kyau , ko ni da farko na yi tunanin na yi recording maganar da zai yi , dan na san dole zai zuwa ya yi min maganar ganin shi da na yi a restaurant "
Jinjina kan ta Haoua ta yi kafin ta ce " gaskia kan ki na ja " ta kai karshen ta na yar dariya
Hararrar ta Safa ta yi kafin ta ce " ba ni son wannan maganar ta ku ta haoussawa "
" na ji shikenan , yanzu minene shirin da za mu yi mishi " Haoua ta fada
Kallon gaban ta Safa ta yi kamar mai tunanin wani abu ta ce " Haoua ina ji a jiki na akwai wani abu a kassa tsakanin Djami da wannan sakaran, wanda ba ta fada mana ba , ko kuma ta fada mana amma ba ta fadi gaskia Dukan ta ba "
Cike da shakku Haoua ta ce " wane abu ki ke magana a kai "
" ban sani ba , amma ya kamata mu tambaye ta , kin san fa kafin mu dawo Nigeria da zama karatun JARIDA na fara yi , da ga kalaman mutun ina iya ganewa in karya ya ke ko gaskia "
" no really ? " Haoua ta fada ta na zaro idanu
Jinjina mata kai Safa ta yi kafin ta ce " really , ke ni fa akwai magaganun da ku ka sha yi min , cikin raina na san da karya ce amma na kyale ku " ta kai karshen ta na juyowa ta kali Haoua
Yar karamar dariya Haoua ta yi kafin ta ce " To sannun ki , kin sani kuma sai ki yi shiru , ya yi kyau , nan gaba sai na daina yin magana gaban ki "
Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " hmmm , na san ba za ki iya ba , amma kin san wani abu a duk lokacin da ki ka ce min tsakanin ki da Allah ku ke tare da ni , ko so daya ban taba jin karya ba ce "
Murmushi ita ma Haoua ta yi kafin ta ce " an yi sa'a, na dauko ita ma karyar ce za ki cewa "
Girgiza mata kai Safa ta yi kafin ta ce " no , wannan ita ka dai ce kalmar da ke sa zuciya ta ta yi sanyi a kowa ne lokaci , har na rage rashin yardar da na ke yi wa mutane , shi ya sa ba zan so abun da ya same ku ba ke da Djami , saboda ku kadai abokai na, na gaskiya "
Riko hannun ta Haoua ta yi cikin sanyin murya ta ce " mun gode da irin wannan soyayyar da ki ke nuna mana , don Allah abun da Djamila ta yi miki kar ki rike shi a rai "
Katse ta Safa ta yi da cewa " ni dama ban rike ta a rai ba , inda na rike ta da ba zan dawo school din nan , amma kin ga gani , yanzu tashi mu je wajen ta akwai tambayar da ke son yi mata "
Da sauri Haoua ta rungume ta ta na fadin " Allah ya bar mana ke har abada "
Dan karamin murmushi Safa ta yi ta rungume Haoua ita ma , sa ga nan su ka raba jikin su
Su ka fito motar a tare su ka nufi inda Safa ta baro Djamila
Ta na nan inda ta ke ko motsi ba ta yi ba , sai faman zaro idanu ta ke hawaye na zubar mata
GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN β€βEXILED PRINCEββ€
GA ACCOUNT ADRESS ππππ
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
KO KUMA TA CREADIT DA TA WADANAN NUMBER πππ
Zain (Airtel)
08081129487.
Mtn
07067953066.
NAIRA 200 NE ONLY
SANNAN KU TURA SHAIDAR TURA KUDIN A WANNAN NUMBER ( +22795577612 )
π©·β¨βοΈ
[23/08 Γ 22:14] MEERAHπͺ·π©·
:
π«π₯ HASKE BIYU π₯π«
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH βπ
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA πππΊ
β€β EXILED PRINCE ββ€
( LOVE MEETS POWER ) ππ₯
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL πππ
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
π²π²DASHEN ALLAH WRITER'S ASSICIATION π²π²
( D.A.W.A ) π²π²
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE 9 π₯ β€
A hankali Safa da Haoua su ka karaso wajen su na yi mata sallama
Amma ko amsa musu ba ta yi ba
A tare Safa da Haoua su ka zazauna geffen ta , su ka saka ta a tsakiya
A hankali Haoua ta daura hannun ta saman shoulder din ta , ta ce " Djami kontar da hankalin ki please , ki godewa Allah da ki ka gano gaskiyar wanene Mansour tun kafin a yi auren ku "
Haoua na gama fadar haka Djamila ta fashe ta kuka kamar wata karamar yarinya , hawaye na zubo mata bibiyu
Haoua na shirin magana Safa ta riga ta cewa " Djami ki daina wannan kukan please "
Da sauri Djamila ta rungume Safa ta na fadin " ki yi hakuri don Allah , wlh na yi nadamar yarda Mansour a rayuwa ta " ta ke fada cikin kukan
Dan bubuga bayan ta Safa ta yi kafin ta ce " please ki daina wannan kukan ya isa haka " ta kai karshen ta na dago kan ta ta sa hannayan ta biyu ta shiga goge mata hawayen ta
A hankali Djamila ta fara rage sautin kukan ta ce " Allah ya isa tsakani na da shi wlh ba zan iya yahe mishi cin amana ta da ya yi , na yarda da shi fiye da rayuwa ta , ba abun da ban yi ba a kan shi amma shi ne zai yi min haka "
Ta kai karshen ta na raba jikin ta da na Safa ta koma ta daura hannayan ta biyu a kai
Dafa kafadar ta Haoua ta yi cikin sigar rarrashi ta ce " ki yi hakuri Djami , in sha Allah sai ya yi nadamar .. "
Ba ta karasa maganar ta sakamakon hannun ta Safa ta riko allamun ta yi shiru
" Djami fada min gaskia , Wannan Dirty boy din ya yi miki wani abu ? " Safa ta fada ta na daura hannun ta saman shoulder din ta
Kallon ta Haoua ta yi ta na zaro idanu ita ba ta gane inda tambayar Safa ta dosa ba
Ita kuma Safa da allamun magaganun Djamila sun sa ta fara yin wani tunanin daban
Su na a haka su ka jiyo Muryar Djamila ta na fadin " Safa, wlh na yi nadamar mallaka mishi kai na , ban San abun da ya shige ni ba a lokacin har na yarda "
Katse ta Haoua ta yi da cewa " ke Djamila maganar me ki ke yi haka yi magana yadda zan gane " ta fada cikin rudu
Safa ce ta amsa mata da cewa " ta na nufin ya yi dis virgin din ta , i think she is pregnant "
A dubu dari Haoua ta mike ta na fadin " What ? Pregnant fa ki ka ce Safa , ke Djamila da gaske ne abun da ta fada ? " ta kai karshen ta na dawo da kallon ta kan Djamila da ta sunkuyar da kai ta na kuka kassa kassa
Sai da ta dan dauki lokaci kafin ta jinjina mata kai ba tare da ta ce komai ba
Salati Haoua ta yi ta na daura hannayan ta saman kai
Ita dai Safa da ido kawai ta ke bin su dan dama ta hango hakan
Cike da takaici Haoua ke fadin " haba Djamila , haba Djamila ta ya za ki yi irin wannan abun , ina ilimin ki , sau biyu ki na saukar Alkur'ani ki na cikin ta ukun , amma za ki yarda ki aika ta zunibi irin wannan "
Da sauri Safa ta katse da cewa " Haoua ya isa haka don Allah " ta fada da dan karfi
Komawa Haoua ta yi ta zauna ta buga tagumi
Dafa kafadar Djamila Safa ta yi cikin sanyin murya ta ce " Djami ban ga laifin ki ba , na san ba a kan