Showing 1 words to 3000 words out of 138779 words
Chapter 1 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
*EL-MUSTAPHA*
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of Experts and Perfect Writers)
Fertymerh Xarah💞
sɪsᴛᴇʀ ʙʏ ʜᴇᴀʀᴛ ʜᴀᴜᴡᴀᴜ ᴀʜᴍᴇᴅ ʀᴜғᴀ'ɪ, ʏᴏᴜ ᴀʀᴇ ᴛʜᴇ ʙᴇsᴛ❤
1_5
Motoci ne keta sharara gudu tsakanin titin kaduna xuwa Abuja,
A qalla motocin xasu kai shidda koma fiye da hakan,
Dare ne mai tsananin sanyi, cikin watan nuwamba, haxo ya lullube duhun daren ta yadda ya fidda launi mai haske kamar hadadden hadari, wanda ya takura da yawan al'ummar birnin tarayya.
Daya daga cikin motocin A.I.G (Assistant inspector General of police) El_mustapha Maneer ne tare da Matar sa.
Kallon ta yake cikin alhini da son sanin asalin damuwar ta, ta yanda har ta takure kanta nesa dashi tana kallon hanya ta glass batare da ta damu da ta kwanta a jikinsa ba kamar ko yaushe idan suna cikin mota xasuyi tafiya.
Yayi tunani ya kasa gano laifinsa gurin uwargidan sa tun bayan barowar su kaduna bikin wani taro da akayi.
Tana sanye da suwaita ta rungume hannayenta duka biyu a qirjinta, alamar tana jin sanyi sosai amma hakan bai hanata takurewa guri daya ba saboda tana fushi dashi.
Murmushi yayi marar fitar da sauti bayan ya dauke dubansa daga gareta, Jiddah rigima, kome xatayi a rayuwa tana burgeshi, yana sonta sosai, so bana wasa ba, komai nashi xai iya salwantar wa saboda ita, yana yi mata son da alqalamin Pherty baxai iya rubutawa a takarda ba, saboda yaransa dake cikin motar suna tsaron lafiyar sa ya hana yaje gareta ya rarrashe ta tare dajin laifinsa har ake wannan fushin dashi.
Jiddah kuwa qara takure jikinta tayi, xuciyarta nayi mata wani xafi ganin halin ko in kula da mijin ta yayi da ita a yau, tasa yatsun ta biyu batare da tabari ya gani ba ta dauke wasu siraran hawaye da suka xubo a idanuwanta tana cigaba da kallon titi xuciyarta a daqushe tare da tunani iri iri duk a kansa.
Wata sassanyar ajiyar xuciya ta saki lokacin da taji saukar hannunsa cikin tafin hannunta, ta juya tana kallonsa ta cikin hasken farin wata da ya haske motar, bata ganinsa sosai ta dai san ba ita yake kallo ba hakan yabata damar janye hannunta a hankali hade da qara matsawa nesa da shi cikin tunxuro baki idanunta taf da hawaye.
Jikinsa ya qara sanyi, meke damun Jiddah, meyasa ta canxa masa haka lokaci daya?
11:30pm
Suka shigo garin abuja, dirar motocin su ya sanya Uwani miqewa da sauri ta gyara powder fuskarta hade da qara feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi.
Ta mirror take kallon kanta tana qara jujjuya jikinta, ita kanta tasani ta ko ina tayi bata da makusa har take ji Ma tafi matar gidan komai amma meyasa El mustapha ke ganin Jiddah tafi mata dubu a duniya, meyasa yake ganin Jiddah ce tauraruwa acikin mata, meyasa ya kasa gane yanda xuciyarta ta mutu da qaunarsa, har take kishin yar'uwar ta duk saboda shi.
Ina son elmustapha da izinin Allah sai na aure shi, sai na sami matsayi a xuciyarsa fiye dana Jiddah.
Jiddah tana fitowa motar bata tsaya wata wata ba tayi shigewarta kai tsaye, a falo taci karo da uwani tana fitowa kallon mamaki ta bita dashi wanda ya sanya uwani daburcewa...
'Uwani duk wannan kwalliyar ta mecece, ina xakije da wannan daren haka?
'Anty Jiddah.. Uhm.. dama Yusuf ne yaxo to bai jima da tafiya ba, yanxu dama nake so na cire kayan na kwanta sai naji dawowar ku shiyasa Ma na fito.... ta fada cikin murmushi
Jiddah bata bi ta kan xancen ba ta soma tafiya tana fadin,
'Naji gidan shiru, ina Arham da Aryan ne.
'Sun jima da yin barci bayan sun gama rigimar nemanki,
Jiddah ta juya tana fadin
'Alhamdulillah, domin a yanzu ba abinda taxi muradi,irin taga yaranta cikin koshin lafiya,ta haura steps, Uwani kallo ta bita dashi tana sauke numfashi a hankali ganin asirinta bai tonu ba, juyawa tayi ta fita harabar gidan inda ta tsinkayosa tsaye duk police sun xageya sa, da alama magana yake dasu yanda taga duk sun tattara hankalinsu da nastuwarsu ta reda sunkuyar da kansu suna saurarensa.
Wannan dalilin ya sanyata dawowa Falon xaman jiransa.
Kai tsaye ya shigo falon idanunsa na kan wayar sa da alama akwai abin da yake nema kamar mai son yin waya, ko wanda ze tura saqo,
Qamshin turarensa ya soma fisgarta, jikinta ya dauki rawa, nan da nan wata irin kasala ta rufeta, a yanda takeji kamar ko yatsanta ba zata iya motsawa ba,haka zuciyarta ke ingizata tamkar taje ta rungumeshi, bata san wane irin so take masa ba,
'Barka da dawo wa yaya, cikin dauriya tayi maganar,da kashe murya irinta mai jan hankali...
Ya dago rinannun idanunsa yana kallonta wadanda ke qara ruruta wutar qaunarsa a xuciyarta, cikin sakin fuska ya soma yi mata mgn,
'Mun same ku lafia Uwani, ashe bakiyi barci ba,
Murmushinsa kawai tamkar ya barar da Uwani a falon, don haka duk qarfin halinta sai ta kasa tankawa illah girgixa kanta da tayi domin idan ta tilastawa kanta mgn a wannan lokacin tabbas xata iya bayar da mata domin ba abinda xai hana mata fallasa masa sirrin xuciyarta, bugu da qari Ma bata ga fuska a tare dashi ba.
Batare da yabi ta kanta ba, ya nufi sashen sa, kallon sa take harya bacewa ganin ta, ta qara kallon jikinta, sama da qasa,tana girgiza kai tana mai tambayar kanta,
Ko bai lura da kwalliyar da tayi domin sa ba, baiyi mgn ba kamar yanda Jiddah tayi magana, sai ta tuna elmustapha yana da halin ko in kula akan kowa idan ba Jiddah bace, tana gani Jiddah kome xatayi sai ya yaba yayi godiya amma saboda ba itace gabansa ba ya kasa gano abubuwan da takeyi domin sa.
Jiki a sanyaye ta nufi dakin ta, kuka take na zuci har yafito fili,tayi kukan sosai, Wanda tana ganin yin hakan kadai xaisa ta sami sassauci daga xafin da xuciyarta keyi ma ta, kamin ta samu damar cikar burinta.
Jiddah kuwa sai da ta duba yaranta biyu, twins maxa masu shekaru shidda shidda, tayi masu addua, wadda acikin ranta, tana fatar ta rayu da su har izuwa girmansu,kafin ta numfasa, taja musu kofa, ta nufi sashen ta,
Tana cikin cire kayan jikinta ya shigo dakin,ko baa fada ba tasan waye sai tayi qoqarin shigewa toilet, yayi saurin riqota yana kallonta,
'Haba jiddatulmusty, wannan fushin duk na menene, na kasa gano laifina, ki gayamin.
Ta dauke kanta gefe tana tunxuro baki, bai yi fushi ba saboda kome Jiddah xatayi masa a rayuwa yana birgesa yana sonta da yawa,
'idan kuma baxan sami amsar tambayata bane shikenan, xan barki kiyi ta fushin amma nima xanyi fushi da kowa da komai a gidannan har lokacin da xaki daina fushi dani ciki kuwa har abinci xan daina ci, ya juya kamar da gaske xai bar dakin yasan ba abinda ta tsana kamar xamansa da yunwa, kamar daga sama yaji muryarta,
'to ba kai bane.... sai kuma tayi shiru ya juyo yana kallonta,
'dana yi me?
'Na ganka da wata kuna magana, kuma qasaqasa kukeyi, har kuna dariya, kana so ka batamin rai ne kuma kayi Nasara and what else? Sai ga hawaye sharrr suna bin kuncinta, ba abinda ta tsana a duniya kamar ta bude idanu taga mijinta da wata mace, tana da mugun kishi, kishi mai tsanani kuwa shi kansa ya san da haka.
'ya salam.... Ya furta a hankali bayan ya dafe goshinsa da hannunsa na dama, ya dago yana kallonta,
'kin san wacece kuwa? Me xanyi da wannan matar jiddah?
'idan hakane meyasa kaja ta can gefe inda ba kowa kuna magana, kuma naga harda hannunka ta taba baka hana ta ba.
'saboda ke ne Jiddah, nasan kishi irin naki bana son bacin ranki ko kadan ya sanya na jata nesa da mutane muyi mgn amma meyasa idan kishinki ya rufe maki ido kina manta ko waye mijinki?,pls Jidda don't ever doubt ur trust in me, I give you my heart so honestly!,
Tayi shiru bata tanka ba, sai dai ta sami nutsuwa a xuciyarta domin ta yarda da mijinta baxai taba mata qarya ba,
'Wannan matar is a Christian, matar Captain Johnson ce, tana min mgn akan abubuwan da yake mata ne bayan ya rabota da qasarta yaxo da ita inda bata san kowa ba yana cutar da ita, tana ganin ba wanda xai masa mgn yaji kamar ni wannan dalilin ne yasanya har kika ganni da ita, maganar riqe min hannu da tayi kinsan su a gurin su ba wani abu bane halin da take cikine ya sanya na kyaleta.
Ta saki ajiyar xuciyata tareda wani zazzafan iska, wanda batasan tariqe shi ba se fitowarshi ta ji, hade da langabe kanta gefe tana kallonsa, se cemata yayi breath my dear....and don't repeate to act like dat I can take it anymore my dear, I am madly in love wit yhu, habawa da sauri Jidda ta dago kanta suna had'a 2eyes ya ce yes my Jiddah I love u.......pls say something I want to hear ur sweet voice,
'Cikin tsanaki ta bude bakin tace am sorry.... My dear Ka yafe min, yaja dogon hancinta yana murmushi,kurawa juna idanu sukayi 4 sometimes at d end Elmustapha ya janye Na shi tare da bata peck a forehead da kumatunta,
'I love you jiddana... ta fada jikinsa tana dariya, ya dauke ta cak suka nufi toilet.
My Wattpad Phertymerh1
*El_Mustapha*
Haske writers Association
Fertymerh Xarah💞
6_10
'Uwani.... Uwani, take kiranta cikin muryarta mai sanyin gaske,
Shiru Uwani bata amsa ba kuma bataji motsinta ba hakan ya bata damar isa dakin nata tana kiranta,
Babu alamar ta a dakin amma ta jiyo motsinta a toilet, ta fita daga dakin, harabar gidan ta nufa sashen masu aiki,
Bata jima ba ta dawo tare da wata yar budurwa a bayanta,
'kinga yanda su Arham suka bata falonnan, kuna cikin gidan amma ba wanda yayi tunanin gyarawa, idan wani baqo yaxo ya same ni a haka fa, ko shi maigidan?
'Dan Allah kiyi haquri hajiya, ba wanda ya gani acikin mu.... tayi saurin katse ta,
'Wannan ba magana bace, aikin kune na gyaran cikin gidannan, akai akai nake gayamaku kuriqa dubawa idan sun bata ku gyara ko dole ne ni xan riqa tashi kullum ina xaryar kiranku akan kuxo an bata ku gyara, idan aikin ne kun gaji dashi kuyi magana akawo wasu abarku ku tafi mana?
'insha Allah daga wannan baxaa sake ba, kiyi haquri hajiya.
'ki kira su jamila kuxo ku hada hannu yanxu ku gyara, kun sani a kowane lokaci baqi xasu iya xuwa gidannan, gidane da baa rabashi da mutane, idan kun gyara nan din ku duba dakin su Arham din kugani ko sun bata, ta juya ta fice,
Banan ta bita da kallo tana sauke ajiyar xuciya, ko kadan jidda bata iya fada ba kome xatayi da sanyi take masu, babu takura ko tsangwama kamar sauran mata masu muqami irin nata, ta xauna a hankali kwayar idanunta na kan makeken qaton photon elmustapha dake falon, ba qaramin kyawu yayi ba, a duk sanda xata shigo falon sai ta kalli photon yafi a qirga ba dan komai ba saboda kwarjini da yake mata, ta tsinci xuciyarta acikin begensa wanda tasan ko a mafarki baxata taba samun saba, ba kalar ta bane, ba ajin ta bane, yayi mata nisan da har abada baxai taba waiwayen ta ba, tana tsoron wani yasan da xancen koda acikin yan uwantane masu aikin gidan tasan asirinta xai tonu yanda jidda keda kishi tsab xata iya korata xuwa qauyensu.
Uwani ce ta fito da sauri daga dakinta, da kallabi a hannunta, kallon Banan take cike da wulaqanci,
'ke idan kin gama da falon nan kije ki wanke min toilet, kwana biyu rabon da ki wanke sa, harda dakin Ma xaki gyaramin kafin na fito, ta fice fuuu da sauri xuwa sashen jidda.
Kallonta Banan keyi harta bacewa ganinta, yatsina fuska tayi hade da tabe baki bayan ta juya tana kallon jamila dake shigowa.
'Yauwa kamar kinsan ke xanje nema, hajiya tayi fada yanxu a gyara falon nan ina indo,
'tun daxu ku nake nema, indo ce kawai ban gani ba, ban san inda ta shiga ba, suka soma gyaran falon.
Da sallama ta shiga dakin, idanunta akan na jidda,
'Anty naji kina nemana, ina toilet ne, kallonta jidda keyi,
'kaya xaki kaiwa Hajiya Ruhayma ta duba idan akwai wadanda xata siya aciki, tun kafin kayan su iso tayi min mgnr su, ki kula da kyau uwani nasan ki da rikicin kudi.
Murmushi Uwani tayi tana harhada kayan, insha Allah anti wannan karon baxaa sami matsala ba, xanje dasu har gidan qawayena na tallata maki nasan xasu siye.
Murmushi jidda tayi batare da ta qara magana ba harta gama harhada kayan, kallonta tayi,
'Anty jidda waye xai kaini, ibrahim ya tafi ya dauko su Arham makaranta, jidda ta tashi ta qarasa bakin window dakinta tana leqa harabar gidan,
'kuma motata ba isashen mai aciki amma bari na baki kudi sai kisa ko a hanya ne kafin ki qarasa.
Uwani ta washe baki, ba sosai taji dadin mgnr ba, a rayuwarta tana son taga tana hawa manyan motoci, ta ganta da manyan qawaye masu ji da kudi, ta ganta acikin qaton gida na alfarma, ta ganta da santalelen miji wanda ya morewa ilimi sosai kuma yake da kudi, shiyasa take son el_mustapha domin shine irin mijin da take son samu.
Jidda ta xuge zip din jakarta ta ciro kudi dubu biyar ta bata,
'ki lallaba dasu uwani nasan xasu isheki, karki jima sosai pls kinsan bana son yawon nan,
shikenan anti, ta karbi kudin ta qarasa bakin mirror tana gyara daurin kallabin ta,
Jidda bata damu ba idan da sabo ta saba da halin uwani na kuri da nuna ita watace, ta rasa wannan hali irin nata Sam bai dace da tarbiyar da aka basu a gida ba.
Uwani ta jima da fita kafin tajiyo hayaniyar twins nata,
'Mami... Mami..., we are back,
Murmushi tayi bayan ta ware masu hannuwanta biyu sukaje da gudu suka rungumeta, daya bayan daya ta sumbace su a goshi tana kallonsu da murmushi a fuskarta,
'da fatan yau bakuyi fada a aji ba? Arham ya dubi Aryan shima kallonsa yake, (kallo daya xaka masu ka gane cewa identical twins ne),
Aryan ne yayi fada Mami, harda karyawa friend dina pencil dinshi yayi kuka, shine na dauki nawa na bashi.
Ka kyauta Arham, xan gayawa Abba ya siyama wasu masu kyau, kuma yaje da kai Magic land, shi kuma da bayajin magana kullum yake fada a class ba ruwana dashi, tashi daga saman jikina munyi fada.
Ba musu kuwa ya tashi, fuskar nan tasa ba yabo ba fallasa ya matsa gefe daga garesu, ta dauki Arham tana fadin, muje Banan tayi maka wanka yaron Mami da Abba, ya qanqameta har suka fita, a tunaninta Aryan din xai biyo sune, har ta kai arham wajen banan bai xo ba,
Uniform dinsa kawai tagani a qasa ajiye, tana jin motsin ruwa ta nufi da toilet da sauri, xindir ta samesa cikin jacuzzi yana qoqarin hada ruwan wanka, ta daure fuska tamau tana kallonsa,
Fito tun ban fara dukanka aciki ba, ba musu ya fito, haka ta riqo hannunsa suka fito, fada tayi masa sosai har sai da ya bata haquri kafin ta kaishi inda Banan.
Har suka xo cin abinci bai saki fuska ba, tunda anyi masa fada fushi yakeyi abincin Ma ya gagara ci tun daxu sai juya spoon yake yi, suna haka uwani ta shigo da fara'arta, bakinta dauke da sallama,
Jidda ta amsa mata tana kallonta,
'sai yanxu kike dawowa Uwani, tun daxu is after 10 fa yanxu, kin kyauta kenan?
'Dan Allah kiyi haquri anty jidda wlhy surry ta tsaidani wai sai nayi isha naci abinci, amma anty jidda kinga nayi maki ciniki sosai, biyu ne kawai aka dauka bashi, sai wadannan dana dawo dasu.
'bata kudin nake ba uwani, Allah ya gani bana son kina fita kina dadewa a waje dan Allah ki daina,
'xan kiyaye insha Allah, ta miqa mata kudin tanayi mata bayanin komai dalla dalla,
Kallon twins tayi tana murmushi, My twins are back, shine ba magana,
Arham yace anty Uwani nayi nemanki ban ganki ba ina kika je,
Dama nasan xaka nemeni ai, shi wannan meke damun sa ne,
Jidda ta kwashi kayan ta nufi dakin ta, Aryan yana ganin haka ya tashi shima cikin falon ya koma ya xauna jira yake abbansa yaxo ya gayamasa tunda Mami tayi masa fada, uwani Ma shigewarta tayi, arham kuwa kekensa ya hau ya soma xagaye da ita tsakiyar falon.
Jiniyar motocin da sukaji wanda ke nuni da dawowar mahaifinsu ya sanya arham sakin keken ya nufi harabar gidan da gudu, Aryan kuwa ko motsi bai yi ba a hakan jidda ta sauko ta same sa.
Uwani kuwa tunda taji alamar dawowarsa ta nufi toilet a gurguje ta watsa ruwa yau duk yanda xaa yi sai tayi hira da elmustapha ko xata sami nutsuwa a xuciyarta.
Da sallama ya shigo falon dauke da Arham, sannu da xuwa jidda tayi masa, da fara'a ya amsa yana kallonta kafin ya maida kallonsa ga Aryan, ajiye arham yayi ya nufe sa,
'nasan ba mai tabamin yaro haka sai Mami right? Ya gyada kai yana kallonsa idanunsa taf da hawaye, kafin yayi mgn arham yayi caraf yace,
'Abba fada yayi a class shine Mami tayi masa fada yake fushi.
Ya dauke sa yana fadin, Mami ta kyauta sosai Aryan, menene amfanin fada a class, idan ka qara dukan ka xanyi sannan babu kyau fushi da Mami, tell her sorry.
Sai ga hawaye sharrr na bin kumatunsa kamar wanda aka