Showing 12001 words to 15000 words out of 138779 words

Chapter 5 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

1981

kinsani, ibrahim nace fa,

She can't control her tears batasan dalili ba sai xafi xuciyarta ke mata ta riqo hannunsa tana kallonsa,

Bana son kishiya el'mustapha ko wace iri ce, dan Allah kada kamin, ni kadai ce matar ka, ina son ka sosai.

Ya rungumeta sosai yana shafar bayanta cikin shigar rarrashi, namiji na qara aure ne bisa wani dalili nashi, bani da wani dalili da xai sanyani qara aure, bani da wata kalma da xan kare kaina a gaban Allah na rashin adalci tsakanin su, jiddah kadai nake so a rayuwata, jiddah kadai ce matata ba kuma wadda xanso bayanta sai ya'yana, ki cire wannan tunanin a xuciyarki kin sani bana son damuwarki kisa a xuciyarki ke kadaice matar el'mustapha kamar yanda UMMY take *Matar sadiq* ita kadai.

Kalamansa suka sanyaya xuciyarta, ta qara yarda da mijinta kuma tasani uwani sai dai tayi haukanta ta gama amma el'mustapha baxai so ta ba, meyasa ma xata damar da kanta akan uwani, idan taga bata canxa xani ba xata turata gida tare da yi masu bayanin komai.

Dalilin wannan ya sanya jiddah cire damuwarta ta kula da mijinta sosai harta manta da wata uwani a gida.

Kwana biyu sosai uwani ta fuskanci canji daga jiddah, sakin fuskar da take mata ta daina babu walwala, hakan yasa jikin uwani yayi matuqar sanyi komai a gidan tanayinsa dar dar musamman masu aikin gidan ta daina takura masu ko yi masu fada akan komai.

Inda surry taje neman mafita bata samu ba kuwa illah fada da sukayi sosai domin bata goyon bayanta,

Jiddah kam ko aike ta daina saka uwani, a falo idan suka hadu sama sama take amsa gaisuwar uwani, sanda qawarta yasmeen taxo kai tsaye tace,

Ki tura ta gidan ubanta jiddah, ta xauna acan har ta sami miji tayi aure amma xamanta a gidan xai iya haifar maki da matsala tun el'mustapha bai fuskanci halin da take ciki ba har yaxo ya gane kinsan mace ballantana irin uwani da idanunsu a bude yake, University takeyi a yanxu ke kuma secondary kawai kike da baki cigaba ba, inajin xatafiki makirci da wayewa akan maxa.

Hakane yasmeen, amma ni saboda iyayenta nake riqe da ita, ki duba irin halaccin da suka mini suka riqeni amana da dukiyata babu ha'inci, tun bansan kaina sosai ba nake tare dasu har sanda suka aurad dani ga abinda nake matuqar so a rayuwata, tsakanina da uwani babu banbanci a gurin su, sun bani amanar uwani tayi karatu a hannuna yanxu idan na maida masu ita ya xasuyi da karatunta daga kaduna xuwa abuja, xasu iya tunanin baxan iya riqe masu uwani bane tun suna raye banyi ba inaga basu raye, kinsan halin mutanen mu akwai mis_understanding,

Hakane na fahimce ki jiddah kiyi masu bayanin komai boye masu ba shine mafita ba gwanda susan abinda yar su ke shirin aikatawa, idan kuma baxaki iya ba ki tattarata ki maidata xama a hostel faqat🙅🏻‍♀

Shiru jiddah tayi cikin tunani iri iri da neman mafita, ko kadan batason el'mustapha yasan da maganar shiyasa take boye masa.

Bayan kwana biyu babu wani canji daga jiddah tsakaninta da uwani hakan ya sanya uwani kiran Banan,

Kije ki sanarda anty kin shigo dakina kin sameni a sume, kije mata a rude yanda xata gasgasta ki, idan kuma kikace qaryane banan kece mace ta farko a gidannan da xan wulaqanta duk ranar da naxamo matar gidannan.

Jin haka ya saka banan fita da sauri sai dai bata fahimci inda mgnr uwani ta dosa ba na xamanta matar gidan, tana shigowa falon jiddah taci karo da qaton foton el'mustapha sai da taji wani faduwar gaba, tsura masa ido tayi tana kallonsa cikin jin sanyi a xuciyarta ta kowace kusurwa.

Tunawa da kalaman uwani ya sanyata fadawa dakin jiddah.

Yanda jiddah taga banan na hawaye cikin rawar jiki tana fada mata halin da uwani take ciki ya sanya hankalin jiddah tashi,

'Na shiga uku kada yarinyar mutane taxo ta mutu a hannuna, koda suka je uwani na kwance tsakiyar dakin ta sandare kamar da gaske, banan kuwa mamakin ta take da son sanin dalilinta nayin hakan.

Neman gaggawa jiddah taje ta nema ga security gidan, cikin mota aka sanyata suka nufi asibiti da ita,

Xuciyar jiddah a cunkushe tare da tunani da fargaba iri iri, har lokacin da Likitan ya kirata xuwa office dinta, da alama shima uwani ta hada kai dashine.

Patient din da kika kawo akwai damuwa a tare da ita mai tsanani, akwai abinda take so bata samu ba menene shi?

Dam xuciyar jiddah na buga ta dago tana kallon likitan hawaye shar a idanuwanta,

Da kyar tace mijina take so.

Mijinki take so? Ya tambayeta cikin tsananin mamaki alamar baisan da wannan xancen ba, jiddah ta gyada masa kai tana sharar hawaye,

Yace ke ba yayarta bace, nan Ma ta girgixa kanta,

Ok tor, abata abinda take so cos gab take da kamuwa da ciwon xuciya, kuma dalilin wannan xaku iya rasata a kowane hali.

Jikin jiddah ya dauki rawa, ta fashe da wani irin kuka sosai mai tsuma xuciyar mai saurare.

*El'mustapha*

*Haske Writers Association*

Fertymerh Xarah💞

18

sosai likitan ya karaya, kukan jiddah na tsuma xuciyarsa, yanaji kamar ya gaya mata gaskiya patient din lafiyan ta qalau sakashi tayi.

Bata qara sauraren shi ba ta fito daga office din, inda aka kwantar da uwani ta nufa, tana kwance idanunta a lumshe kamar da gaske barci take.

'meyasa xaki min haka uwani? Meyasa kike son mijina, meyasa kike son rabani da farin cikina, why can't you stay alone with Yusuf and free my husband, el'mustapha baya cikin k'addarar rayuwar ki, kece kika ja kuma watarana xakiyi dana sani kasancewar ki mata a gurin sa.

Daga inda uwani take kwance kamar ta tashi ta fara rawa saboda tsananin farin ciki, xata auri el'mustapha? Dana sanin me xatayi, ai baxata taba dana sanin auren sa ba tunda mallakarsa take son yi ya xamto ba wata sauran mace a xuciyarsa sai ni Aisha Uwani koda kuwa ke jiddah ce ko ya'yansa,

Ana maganar maza irin su el'mustapha wake sanyo su Yusuf aciki, idan tana tunanin ni kadai xan xauna a gurin Yusuf haka ma watarana ni kadai ce a xuciyar el'mustapha, sannu sannu ai bata hana xuwa sai dai a dade baa kaiba, muje xuwa.

Xama jiddah tayi tana sharar kwallah, numfashin ta na sauka a hankali saboda yanda xuciyarta ke mata xafi, bata da xabi a rayuwarta na ganin ta ceto rayuwar uwani ba dan komai ba sai dan iyayenta da suka riqe ta amana, baxata so yaranta su salwanta saboda wani dalili na damuwa ba, amma taya xata iya xama da uwani a matsayin kishiya, taya xata jure ganin el'mustapha da wata mace a rayuwarta.

Ya Allah ka kawo sauqi, ka bani haquri da juriya naganin na cinye wannan jarabawa taka.

Bata jima asibitin ba ta fice bayan ta turo wacce xata xauna da uwani,

Su Aryan na dawowa makaranta ta tura su inda mama mahaifiyar el'mustapha, ko kadan bata son hayaniya da yawan surutu, she needs to stay alone har lokacin da el'mustapha ya dawo.

Wayoyin sa ya ajiye yana kallonta,

'ya jikin Uwani, inaji duk damuwar tane kika xauna anan shiru?

Ta sauke numfashi tana kallonsa batayi mamakin jin ya san uwani bata lfy ba cos duk abinda suke ciki idan dai har sun fita sai an buga an sanar dashi, akwai tsaro sosai tsakanin gidan da yan'sanda.

'Barka da bawowa,

Ya xauna kusa da ita,

Gobe xanje xamfara, akwai mutanen mu da yawa da aka kashe attack din da aka kai masu acan, am not happy idan kinje harda ASP Mukhtar Takai an kashe,

Subhanallah, Allah ya gafarta masu, ya tsare mana kai a duk inda kake.

Amin jiddana, kibani abinci inci inajin yunwa sosai, sai a lokacin ta tuna duk yinin ranar bata ci komai ba,

Ta tashi ta soma hada masa kayan abincin a inda yake xaune yana latsar wayarsa, duk wani movement din ta akan idonsa tana yin komai ne a sanyaye babu kwarin jiki, haka babu walwala a tare da ita kamar ko yaushe idan ya dawo daga office, ya dauki hakan a matsayin qila saboda yar uwarta bata lafia ne,

Tare suka ci abinci suna fira jefi jefi duk bai wuce al'ummar da ake kashewa bane da kuma mutanen sa yan sanda da aka kashe.

'Washe gari sai ga uwani ta dawo wai anyi discharging nata, yanda ta shigo gidan sukuku sai ka dauka kamar da gaske bata lfyr ne.

A raunane ta qarasa inda jiddah ta tsugunna da gwiwowinta duka biyu idanunta taf da hawaye,

'Anty dan Allah kiyi haquri, wlhy bada son raina bane kuma na haqura xanyi qoqarin ganin na manta dashi har qarshen rayuwata, ki tayani da addua anty ni nasan yaya baya sona ko kadan bai taba xuwa ya duba halin dana ke ciki har sanda nayi kwanci asibiti, ko ya jiki bai taba kira yayi min ba saboda bani ce a xuciyarsa ba, xanyi qoqarin ganin na fitar dashi koda kuwa son nasa xai salwantar da tawa rayuwar...... Ta soma numfashi sama sama hade da dafe qirjinta kamar da gaske,

Halin da take ciki yasanya jiddah rudewa, ta riqa ta da sauri tana kiran banan, uwani ta lafe jikin jiddah tana sauke numfashi da sauri sauri kamar wacce rayuwarta xata bar jikinta.

Kada ki mutu uwani, indai el'mustapha ne xaki aure shi kiyi rayuwa dashi kamar yanda kike buri, ni kaina nasan mutuwa xanyi xuciyata xafi take min.

Ta fashe da kuka sosai, jikin uwani yayi sanyi ta daina abinda take sai dai idanunta a lumshe suke, hawaye ke fitowa a idanuwanta jiddah tayi matuqar bata tausayi tana son farin cikin jiddah amma baxata iya haqura da el'mustapha ba, kuma ta yarda 100% jiddah na qaunarta da xuciya daya dalilin haka take ganin jiddah baxata cutar da ita ba, anty jiddah kiyi haquri baxan iya haqura da el'mustapha ba,

Banan ta shigo falon da sauri tana amsa kiran jiddah, halin da ta same su ciki yayi matuqar rudata, kuka sukeyi musamman jiddah, shekara uku tana xaune a gidan bata taba ganin hawayen jiddah ba sai ranar, bata bi ta kan uwani ba tayi inda uwar dakin ta,

'Anty jiddah meya faru, wani ya mutu ne.

Jiddah ta bude idanuwanta tana kallon banan, kafin ta dubi inda uwani take kwance tana hawaye sai ta tashi batare da tayi magana ba tabar falon.

Banan kallon uwani tayi kafin ta maida dubanta ga wani photon el'mustapha wanda yake tare da jiddah.

Jin shiru ya saka uwani bude idanuwanta, wayam babu jiddah a falon ta dubi banan cikin mamaki abinda taga tana kallo, ba zato ba tsammani banan taji saukar Mari a kuncinta wanda ya saka ta xabura hade da dafe kuncinta tana xaton ko jiddah ce.

Ganin uwani ce ya sakata xare idanuwanta,

'meyasa kike kallonsa, ki gayamin ko na illataki a yanxu,

'bashi ne nake kallo ba anty jiddah nake kallo, ina tausayinta ne na ganta tana kuka.

Mtsewwwww good for you, fice daga falon nan munafuka, sum sum ta fice da sauri bako waiwaye.

*El'mustapha*

*Haske Writers Association*

Fertymerh Xarah💞

19

Sum sum uwani tabar falon ta nufi dakin ta.

Daren ranar suna kwance da el'mustapha,

'ina so naje birnin kebbi gobe tunda xakaje xamfara, dama ina so na duba hajiya kwana biyu banje ba.

'meyasa baxaki bari idan nadawo muje tare ba, nima ina so naje na gaidata.

'A'ah, ina son naganta ne baxan iya jiran ka ba, please let me go,

'akwai abinda kike boyemin jiddah, my eyes are on you, kina ganin kamar hankalina ba guri daya yake ba, kina cikin damuwa kike boyemin, meyasa kika canxa min jiddah, ashe dama akwai lokacin da damuwar ki baxata xamo tawa ba, why did you change, kigayamin damuwar ki, ina so nasani a yanxu.

Tayi qoqarin saita numfashinta, jikinta ya dauki rawa, hawayen da take boyewa suka soma xarya,

'amma kasan ina son ka ko?

damuwar ki nake son ji, ba son da kike min ba, idan har ban cancanta nasan damuwar ki babu mgnr wata soyayya da kike min, you are deceiving yourself jiddah.

Ba yanxu take son sanar dashi ba har sai taji raayin iyayen su tukunna, tasan halin el'mustapha sarai xai iya hanata tafiyar idan batayi da gaske ba, hannunsa ta riqo tana kallonsa.

Uwani ce damuwa ta you know, ban gayama dalilin kwanciyarta asibiti ba, likitoci sunce tana cikin damuwa kuma ta kamu da ciwon xuciya a kowanne lokaci xata iya rasa rayuwarta, nayi juyin duniyar nan ta gayamin damuwar taqi shine nake so naje na sanar da hajiya kada wani abin yaxo ya sameta batare da sanin su ba.

Yaja numfashi yana kallonta, you are right jiddah na fahimce ki, amma tare da uwani xakije ne?

Aa bana son tasan da tafiyar Ma,

Allah ya tsare ya kaiki lafia, amma ni bana son kina damar da xuciyarki saboda uwani, kinsan dalili? Ta girgixa kanta tana kallonsa,

Saboda uwani bata taba damuwa dake hakan ba, akwai wani abu dana ke boye maki game da uwani wanda ke baki sani ba, tun daga lokacin nadaina ganin mutuncin ta.

Xuciyar jiddah ta tsananta bugawa to kodai el'mustapha ya san uwani na sonsa ne?

Sanda akace xaa yi maki c.s ga haihuwar twins wlhy uwani is happy, ina kallonta babu damuwa a tare da ita kamar iyayenku, hajiyarku harda kuka tayi, did you know that, jiddah ta girgixa kanta.

Duk wani movement din ta a hospital ina lura dashi, har sanda akace kin haihu da kanki, ol what uwani is asking a lokacin likita tana da rai ko ta mutu, kallon da nayi mata ya sanya mahaifinta bige mata baki yana salallami, bansan meyasa ba from that day nasaka idona akanta musamman saboda ke, amma ke saboda rashin lafiyarta kin rude kin shiga damuwa, kin tura ya'yanki inda mama saboda damuwar uwani ba lafiya, kin daina kulawa dani sai Ma nida ke qoqarin kulawa dake saboda uwani, You have to put eyes on her, kidaina yarda da ita cos ni ban yarda da ita ba again kuma bana qaunarta ko kadan, sorry to say idan kinji xafin kalamaina but am telling you the fact, kuma ban gaya maki mgnr saboda xumuncin ku ya lalace ba, rayuwar nan wanda ka yarda dashi shike cutar da kai sai a hada kai dashi a cutar da kai, ko ya xame ma sanadiyar rasa farin cikin ka, idan Ma bai xama makashin ka ba.

Shiru tayi tana saurarensa, maganar sa gaskiya ce, uwani tana son rusa farin cikinta saboda son el'mustapha, no it can be possible, uwani baxata mata haka ba tasan uwani tana son ta kuma tana nuna mata soyayya, gashi sanadiyar el'mustapha tana neman rasa rayuwarta, idan har mgnr el'mustapha gaskiya ce uwani ta cutar da ita Allah baxai barta ba kuma xai saka mata, duk wanda yayi niyar aikata alheri baxai taba tabewa a rayuwa ba, taimakon uwani xatayi saboda iyayenta kada ta rasa rayuwarta dalilinsa.

'Wannan tunanin yayi yawa jiddana kixo ki kwanta, el'mustapha need you today komai ina so daga jiddatulmusty,

Murmushi tayi tana kallonsa cikin so da qaunarsa, tau baban biyu bani minti biyar kacal na shirya,

Janyota yayi, ya kwantar da ita, a hakan nake son jiddana, bana son wani abu da xatayimin saboda ta birgeni, kome jiddah xatayi ina son ta, tana birgeni, kuma duk wanda baya son jiddah nima bana son shi.

Hannu tasa ta rungumosa sosai, yayin da ya hada fuskarsa da tata yana shaqar qamshin jikinta.

*

'Washe gari el'mustapha ya nufi xamfara, jiddah Ma ta shirya sai da xata tafi ne ta sanar da uwani xataje birnin kebbi kan maganar taji raayin iyayen idan sun amince.

Abu biyu ne ya hadewa uwani farin ciki jiddah ta amince xata bari ta auri el'mustapha da kuma yanda xata shige mata gaba a auren, sai fargabar abbanta wanda take ganin da kyar ne xai iya amincewa da auren da kuwa ta shiga uku.

Sai dai abinda jiddah ta jiyo uwani na fada a waya yayi matuqar bata tsoro da tada hankalinta matuqa wanda ya xama dole ta amince da auren el'mustapha da uwani idan ba so take ta ruguza mata farin cikinta ba.

'Walllahi baxan haqura da el'mustapha ba surry kidaina min mgnr bana so, da kinsan yanda numfashina ke bugawa tare da qaunarsa da baki nemi in barshi ba, ke idan fa ta kama ko nijar xan iya xuwa inda boka domin farin cikina.

Hankalin jiddah ba qaramin tashi yayi ba jin uwani ta ambaci boka, abin ya kai har haka, meyasa uwani keson ganin bayanta, bata nunawa uwani taji komai ba sai dai kallon da takewa uwani a yau daban ne da irin wanda ta saba yi mata a matsayinta na yar'uwa.

Babu kunya ta soma yiwa jiddah godiya ta rakata har harabar gida, inda mota ke jiranta, police biyu ne tare da ita wadanda xasuyi tafiyar, ta bude motar ta shiga tana adduar tsari a xuciyarta.

Tun da jiddah taje masu da mgnr da abinda ya sami uwani a asibiti iyayen suka soma kumfan baki, basu yarda da maganar ba kuma basu yarda uwani ta auri el'mustapha ba, domin ya xama cin amana garesu,

Duk iya qoqarin jiddah ta kasa shawo kansu sai Ma sabani da suka samu da hajiya wanda ta dauki fushi da ita mai tsanani,

Dalilin hakan yasa jiddah ta fasa komawa a ranar dole sai tayi convincing iyayen har su amince da auren bata son abinda xai taba mijinta da lafiyarta dan baxata iya  gayamasu abinda taji uwani ta fada a daxu ba.

My wattpad phertymerh1

*El'mustapha*

*Haske Writers Association*

Fertymerh Xarah💞

Mom of

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login