Showing 21001 words to 24000 words out of 138779 words

Chapter 8 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

1988

ko kadan bata da kyankyami akan masu aikinta, ta riqo banan sosai, tace uwani ta canxa kuma xakiyi mamaki kada kisa damuwa a tare dake, uwani kuma taimakonta xanyi dalilinsa ta kamu da ciwon xuciya.

Banan tayi shiru kenan itama idan anti jiddah taji dalilin el'mustapha ne bata da lafiya itama xata barta ta aure sa, no baxan iyama anti jiddah haka ba xan cigaba da boye mata koda kuwa sonsa xai xama ajalina cos nasan el'mustapha baxai taba son Irina ba, ina Ma ko sau daya ne na ganshi, tunda nake gidannan ban taba ido da ido dashi ba sai dai kallo daga nesa.

Tashi ki shirya yanxu xaa kaiki asibiti kinji banan.

Ba musu kuwa ta tashi ta soma shiryawa, jiddah na fitowa sashen kitchen din ta tanufa,

Har ta gama shirya masa breakfast wani abu na nan a qirjinta ya tokare mata,wai ita ce da kishiya a yau, anya tayi Saar xuwa duniya kuwa, ko da yake itace ta jawa kanta, amma ita da xuciya daya tayi taimakon kuma tasan baxata taba tabewa ba.

Dai dai lokacin da suke ganiyar soyayyar su da el'mustapha a lokacin wata xata shigo rayuwar su, su dinga sharing love, anya xata iya? Wata ta dinga yin abinda suke da mijinta, rumtse idonta tayi ta jingina da bangon kitchen din da yaji marbles, hawaye mala mala a fuskarta a hankali ta dinga furta Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un,

A hankali ta fara samun sa'ida a xuciyarta har ta sami relief, ta kwashi kayan ta soma hadawa a dining,

Ta qara shiga dakin nasa, yana kwance wannan karon kansa na kallon fankar dakin, ya riqe goshinsa da hannunsa daya,

Gefen gadon ta xauna hade da Jan yatsar qafarsa, el'mustapha lafia? Ta fada tana murmushin yaqe

Kura mata ido yayi, shi kansa yasan qarfin hali take wai barawo da sallama,

Your breakfast is ready ta fada cikin sanyin murya uwa tasa ihu take ji, baiyi niyar miqewa ba, hakan yasa ta qara magana, komai bai ce ba ya tashi suka fito tare.

Breakfast suke daga ita har shi bamai cewa qala kowa da abinda yake tunani har lokacin da suka kammala, kallonsa tayi da murmushi a fuskarta,

Oya get ready,

For what ya tambaya yana kallonta,

For bathing mana ango, shiru yayi baice komai ba har lokacin da tajasa toilet, suna wankan tana adduoi a xuciyarta na Allah ya kawo mata sauqin kishin da ke ranta.

El'mustapha kuwa kallonta kawai yake, sai yanda tayi dashi binta yake kamar raqumi da akalarsa.

Da kanta ta shiryasa, yau kam harda babbar riga, ta feshe shi da taurare mai sanyin qamshi, ta tsura masa ido,

Shikenan yau beautiful man din ta xai dawo nasu ita da yar'uwarta, wasu hawaye suka xo mata da sauri ta rungumesa sosai kyam a jikinta, ya saki ajiyar xuciya, rungumota yayi sosai yana shafar jikinta hade da dora kansa a kafadunta.

Jiddah ko a fasa auren ne please, nima bana so kinsani.

Ta girgixa kanta bayan ta dago tana kallonsa, auren shekara daya ne el'mustapha kayi min alqawari da lokacin ya cika xaka sauwaqe Ma uwani.

Nayi alqawari,

Kayi min alqawari baxaka taba son uwani ba amma xaka kare haqqinta na aure,

Nayi alqawari,

Kayi min alqawari baxaka juyamin baya saboda ita ba.

Nayi alqawari, sai me jiddah, tayi shiru tana sharar kwallah, talk jiddatulmusty el'mustapha naki ne, yana matuqar sonki baxai taba iya hada soyayyar ki da wata ba, trust me jiddah, idan na karya daya daga cikin alqawarin ki kibarni har abada, ta kallesa cikin son gasgasta maganar kuma hakanne.

Yau 25th ne ranar da ta amshi daurin auren El'mustapha Maneer da Aisha Adam (Uwani) miji ga Hauwa Ahmed (Jiddah ).

Auren da akayi sa acikin masallaci bayan sallah.

Jiddah ta dawo daga duba jikin banan sosai ta warware har Ma taci abinci ta saka ta tayi wanka, tana qoqarin shiga sashen ta sukayi kicibis da uwani na qoqarin fitowa, cikin wani uban lace Blue, baqaramin kyau tayi ba tasha make up wanda ya fito da sirrin kyawunta, idanu jiddah ta xuba mata cikin tsoron irin kyau da uwani tayi.

Murmushi uwani tayi tasan ko jiddah bata fada ba yanayin ta kawai ya nuna kwalliyar ta ta qawatar, ina ma el'mustapha xai shigo ya ganta shima, russunawa tayi cikin girmamawa,

'Anty jiddah tun daxu nake neman ki, yau bamu gaisa ba, kuma gashi yau rananr farin cikina ce burina ya cika na mallakar abinda nake so, qirjina ma 'ga daina min ciwo a yanxu xuwa shekara daya inaji komai xai dai dai ta na bar miki shi.

Da kyar jiddah ta iya hadiye wasu yawu da qarfi, ta tattaro nutsuwarta tana kallon uwani.

Nagani kam kwalliya kika xo ki nuna min kuma kinyi kyau, amma wanda akayi domin sa ba gani xaiyi ba ballantana ya yaba.

Nikam anty jiddah banxo dan kiji haushi ba idan Ma kika ce inje incire yanxu xanje na cire, idan kuma magana ta ce tabaki haushi kiyi haquri, xama nake so muyi dake na amana ba cutar wa.

Da xanfi farin cikin haka, ni ban iya cutar da mutum ba ballantana nayi qoqarin cin amanarsa, duk wanda nake xaune dashi da xuciya daya ne,

Ni xan iya baiwa duniya labarin wannan, kina da hali mai kyau ki godewa Allah.

Jiddah bata qara mgn ba tana qoqarin ficewa ta tsaidata,

'Anty jiddah nace kada ki gaji dani, kima yaya mgn ko ba komai ina da haqqi amin kayan aure, idan suma baida kudin ne ni xan iya rantawa na aramasa kudin yayi min,

Murmushi jiddah tayi,

Ai yanxu uwani kin fini kusa dashi, kece yar gaban goshi, ko kin manta yau kece amaryarsa sai yanda kikayi dashi,

Hakane kinyi gaskiya anti uwani daga nan ma xan masa mgnr honey moon din mu.

Kallon ta kawai jiddah tayi batace komai ba ta fice xuciyarta na mata xafi, ina Ma bata yarda da auren ba da waye uwani da xata tsaya gayamata magana haka,

Da dare uwani ta uban gayu ta gyara dakinta sai qamshin turaren wuta yakeyi, ta shirya kanta cikin wata hadaddiyar rigar barci, sai kai da kawowa take a dakin ta tana jiran xuwan el'mustapha.

Acan daki kuwa jiddah roqon el'mustapha take yaje ga uwani, qarfin haline kawai take amma kamar ta fashe da kuka takeji,

Kayi haquri mijina, ina sonka bana son Allah ya kama ka da laifin rashin adalci a tsakanin mu, ka yafemin tirsasawar danayi Ma akan auren uwani dan Allah ka yafemin, ya rungumota sosai hade da sumbatar ta a goshi,

Bana son wannan damuwar da kukan, I want my jiddah back as before, wannan ba jiddah na bace, jiddah na bata cikin damuwa, she is always happy, bata da lokacin kowa sai na mijinta ya fada yana qoqarin cusa hannuwansa cikin rigarta.

Ta soma girgixa masa kanta, please el'mustapha kaje tana jiranka, your new bride... Cak ya tsaya yana kallonta,

Jiddah ta daina sonsa a yanxu, ta daina kishinsa, yau jiddah ita ke roqonsa yaje ga wata macen, shi kam me xai tsinta a jikin uwani, mexai sa ya hada shimfida da uwani, kada Allah ya nuna masa wannan ranar.

Ya cire hannuwansa daga cikin rigarta jiki a sanyaye ya sauko daga saman gadon, bai qara waiwayen ta ba ya fice, uwani najin alamun takun mutum xai fito daga dakin ta xura da gudu daga laben da takeyi ta nufi dakin ta tana addua Allah yasa yaxo kai gaskiya jiddah mace ce mai gaskiya bata da son xuciya ai na dauka baxata barshi ya xo ba da nayi Allah ya isa domin nike da shi ehe.

Sanin muhimmanci sallama ya saka shi yinta, yana sanye da kayan barcinsa masu kyau da taushi, qamshin turaren sa ya gauraye dakin uwani wadda tun shigowar sa jikin uwani ke rawa sai take neman abinda xata rufe jikinta dashi, ita kanta batasan tana kunya da tsoron el'mustapha ba sai yau ashe duk cika baki ne takeyi a bayan idonsa, a xahiri kuwa wane ita.

Wata xungureriyar farar takarda ya miqa mata kansa a sunkuye har lokacin bai kalle ta ba,

Jikinta ya dauki rawa, ta soma ganin dakin na juyawa da ita, takardar mecece yake bata kada dai el'mustapha ya sake ta ne, a daren ta na farko, daren da kowace mace take alfahari da farin ciki dashi.

Jikinta yayi sanyi ta kasa miqa hannu ta karbi takardar,  ba dan komai ba sai dan tsoron abinda xata tarar acikinta.

Ganin haka el'mustapha ya ajiye mata takardar a gefen gadon da take xaune, ya juya ba tare da yayi magana ba ya fice.

Pherty..... ✍🏻

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

25

Zuru tayi tana kallon farar takardar, har lokacin jikinta rawa yake, kafin ta fara kuka.

Shikenan ta faru ta qare dama tasan el'mustapha baxai so ta ba, ya karbi auren ne domin ya wulaqantata, ai kuwa kansa yayi mawa saboda takardar jiddah xata bawa ita acewar ta tace, dan wlhy bai isa ya sakeni a farkon daren aure na ba.

Ta dauki takardar da sauri ta sakata cikin wardrobe din ta, baxan nuna masa na karanta takardar ba dan Ma karnaga sakin, jiddah xan bamawa ko saki nawa ne ya xamto itace yayi Ma bani ba, sai inga yanda xaiyi Allah yasa saki uku ne aciki ta tafi ta barmin shi har abada inga qarshen soyayya, ingani idan baxasu iya rayuwa ba kamar yanda suke fada.

Da wannan tunanin uwani ta kwanta barci, mafarkinta a ranar duk cike yake da el'mustapha, gani kawai take suna ta xuba soyayya ita dashi.

Jiddah kuwa a ranar ta kasa barci, tayi kuka harta gode Allah, once in life el'mustapha din ta kwance da wata macen ba ita ba, tunani iri iri, ganin bata da mafita ya sakata shiga toilet ta dauro alwallah taxo ta fara sallah.

El'mustapha kuwa bashi da damuwa illah ta kewar jiddah sa, rigar barcinta ya sakawa pillow ya rungume, barcinsa yake hankalinsa a kwance batare da tunanin komai ba.

'Washe gari jiddah ce a kitchen tare da banan suna hada breakfast suna hira abinsu.

'Anty kinga har yanxu kaka bata xo dubiya ta ba, ta dade sosai wannan karon kuma ina so na ganta.

'kibari idan kukayi hutu bata xo ba sai kije, ai ba abin damuwa bane banan, meyiwuwa wasu hidimomi suka yi mata yawa.

'hakane anty, amma a makaranta an fara mana maganar kudin waec da neco.

'eyyeh ashe Banan an xama yan mata, na manta ai wannan shekarar kike gamawa,  kice su arham sun kai ga babbar anti.

Murmushi banan tayi tana kallonta,

'Anty ai xaki sakani University nima kamar anti uwani.

Me xai hana banan, inaso kiyi karatu, kinga ni banyi ba iyakar secondary ne kawai dani, kuma bayan nayi aure banyi qoqarin shiga ba kasancewar el'mustapha baya so, Uwani kuma kinga saboda bata da aure ne har kika ga ta cigaba kuma yanxu xata cigaba tunda kinga tana kai ya aure ta, dan haka kema ina so kiyi karatu koda kin sami mijin aure ki cigaba, ilimi yana da matuqar muhimmanci ga 'ya mace, ina so watarana kaka tayi alfahari da bokon ki.

Banan tayi dariya tana kallon jiddah cikin tsananin qaunarta,

'Anty jiddah rayuwarki daban ce, halinki mai kyau ne kuma kina da kirki, shiyasa nake matuqar sonki, mutanen gidannan Ma basu da magana sai ta alherin ki, baxan iya cutar dake ko cutar da jinin ki ba shiyasa kika ga ina matuqar qaunar yan biyu saboda mamansu bata kyamace ni ta soni da xuciya daya.

Jiddah ta wanke hannuwanta a sink, kafin ta juyo tana kallon Banan,

Nagode da kulawar ki sosai akan twins, Allah xai saka miki, taimaka ki kwashe kayan ki jera a dining, ni xanje wanka.

Cikin shirinsa na uniform ya fito, suna hada ido da jiddah ya sakar mata murmushi,

'Uwargidan el'mustapha, amaryar el'mustapha, mata kadai a xuciyar el'mustapha da fatar kin tashi cikin qoshin lafiya,

Murmushi tayi tana kallonsa,

'Good morning my cwt, angon uwani.

Bai wara mgn ba ya qarasa dining yana duba abubuwan da ta hada masa,

Xama yayi yana fadin, all dis for me jiddana, gashi kuma am late ina sauri.

Ta qaraso tana fadin, all for you an your bride, ka jirata ta fito mana.

Hannu yasa ya mintsineta, ya jawota kacokan ya dorata akan qafafunsa,

Bari na duba ki matata nagani wai akwai sona kuwa a xuciyarki, jiya kin barni cikin kewa da kyar na sami barci, kafin tayi magana ya hada bakinsa da nata.

Suna haka uwani ta fito cikin shirinta, ganin su a haka ba qaramin tada hankalinta yayi ba, haka taji falon na juya mata, ga wani uban kishi daya danne mata qirji.

Ai wallahi sai dai na katse maku abinda kuke amma baxan koma ciki ba, ta qarasa dining da sauri.

El'mustapha sarai ya ganta amma jiddah bata ganta ba kasancewar bayanta ke fuskantar uwani,

Tana isa dining ta daga murya sosai yanda xasu ji ta,

'Anty jiddah sannu da aiki,

Sosai jiddah ta jiyo ta sai dai batayi yunqurin barin jikin el'mustapha ba kasancewar bai bata wannan damar ba ya riqeta sosai a jikinsa,

Uwani ta xauna ji take kamar ta fashe masu kai a yanda suke, da kyar jiddah ta tashi, ta xauna gefensa tana qoqarin hada masa tea,

'is ok jiddah, sauri nake kuma tuni na qoshi tunda na sami abinda nake so daga jikinki, taji nauyin maganar sa saboda uwani amma bata nuna ba,

Tace amma kasan xan shiga damuwa idan har bakaci abinci ba, tukunna Ma idan kaje me xakaci haka xaka xauna a office da yunwa.

Bani farfesun naje dashi ya isheni, da kanta ta hada masa ta bashi, xata raka sa ya dakatar da ita.

'Na hutar dake xauna kiyi breakfast dinki, kafin tayi magana ya juya da sauri ya fice.

Dogon tsakin da uwani taja ne ya dawo da hankalin jiddah xuwa gare ta, batayi magana ba kuma bata qara kallon uwani ba,

'An shiga haqqina Allah ya gani, abinda ke xuciyata kuma na barwa kaina sani, na yafe ko ban yafe ba, ta murguda bakinta tana qoqarin ture kayan dake gabanta.

Kallonta jiddah tayi cikin son gasgasta abinda taji uwanin na fadi,

Me kike cewa uwani?

Cewa nayi an min shige, kwana bakwai ne girkina saboda kowa yasan ni budurwace, amma saboda me xaa xauna da mijina ranar girkina ana tsotsar bakinsa, nima sai na rama wlhy.

Murmushi jiddah tayi cikin mamakin uwani, wai mijinta, a yanda tasan halin uwani iyayenta Ma bata raga masu ba wurin maida masu magana ya saka ta ja bakinta tayi shiru, ta dauki kofin tea ta kai bakinta tana sha.

'Wannan halin ko in kula da jiddah tayi akan uwani yayi matuqar bata mata rai da fusatata,

Ni dama nasani ba saboda tausayina yasa aka aura min shi ba sai dan a qara cusa min baqin cikin da xai sa xuciyataa ta fashe na mutu a huta dani an yarda kwallon mangwaro, to yanxu na fara rayuwa, kuma ba wanda ya isa ya rabani da mijina, ta bigi table din ta tashi a fusacce ta bar gurin.

Binta da kallo jiddah tayi har ta bacewa ganin ta, batayi mamakin abinda uwani tayi mata ba a yau domin shine karo na biyu, sun taba irin wannan fadan kamar uwani xata dake ta saboda ta gayamata gaskiya akan iyayenta da take Ma rashin kunya, tun daga lokacin bata qara mata magana akan ta daina ba, sai yau da ta qara mata wannan, dama tasan halin uwani idan tana neman abu a gurinka xata riqa baka girma kamar xata hadiye ka amma da xarar buqatarta ta biya to ba shege a gurinta sai kai.

Allah ya shiryeki uwani shine abinda jiddah ta fada tana qoqarin cusa arish a bakinta.

A gurguje🙄

2 month

'Surry ke kallon uwani tana yatsina fuskarta,

Dube ki dallah malama, kin bata wayonki da qurciyarki, dubi yanda kika dawo, son maso wani qoshin wahala, kuma abinda aka gina da cin amana ai baya kyau.

Ko ma me xakice kice, ban kiraki kixo gidana ba ehe, wanda nake so tunda bake bace akansa ba ruwanki.

Hakane, ni uwar karambani da cusa kai,  maganar makaranta kindai na xuwa tunda kikayi aure, ko miye dalili.

'Na ajiye karatu, bautar aure nake yi.

'ni badan na ganki da casbi a hannu kina a ba da na soma xargin kin fara shaye shaye, yaushe Ma kika fara riqa carbi a hannunki ne, ko duk el'mustapha ne ya sauyaki.

Shiru uwani bata tanka ba,

Saboda auren kike cewa kin fasa karatu uwani, kima kanki fada uwani ynxu kike da damar karatun kafin ki fara haihuwa, shekarun da kikayi a baya kina nufin sun tafi a banxa?

Karatu dai nikeyi ba wani shege ke min ba, kigayamin tun da nake xama a ajin me nake fahimta ko kin manta irin kwakwalwata ne, dana bata lokacina ina shiga aji bana fahimtar komai gwanda na xauna nayi bautar aure tunda har nayi secondary, kin manta semester can da result ya fito duka c.o ne uku kawai nayi passing na kawo result gidannan matar nan harda dangwara ta tana cemin takkwala ko ban gayamiki haka ba?

Dole xataji haushi saboda kudin da take kashe maki na School uwani wlhy ko nice xan qara da ce maki mai kwakwalwar kifi saboda naki daqiqancin yayi yawa, abinda ke qara bani haushi akanki ayi maki dictation baki iya rubutawa copying Ma da kalma daya daya kikeyi shiyasa nake juya maki baya idan aka shiga jarabawa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login