Showing 54001 words to 57000 words out of 138779 words
Chapter 19 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
gajiya da kallon fuskarsa ko kadan.
Kowa yayi mamakin dajin da suka shigo, baxaka taba tunanin akwai wata halitta mai rai a gurin ba, sun tsorata da lamarin uwani dama qarfin xuciya irin nata da har take iya xuwa nan ita kadai batare da tsoro ba.
Nesa da gidan sukayi parking motocinsu duka suka fito, kafin kace me duk sun xagaye gidan yayin da wasu ke shiga cikin gidan suna buya a hankali.
Tun daga nesa goga da likitan da ya kira ya tsinkayo yan sanda xagaye da gidan, ya tsaya cak cikin mamaki ya akayi yan sanda suka san da gidan har suka xo,
Ya ciro wayarsa ya soma kiran kurma jikinsa na rawa, dai dai lokacin kurma na sheqe ayarsa da budurwarsa,
Har wayar ta tsinke baa dauka ba, goga ya sake kira, kurma yaja dogon tsaki cikin takaici bayan ya janye jikinsa daga nata kallon wayar yake yana ganin goga ya dauka da sauri hade da dura masa ashar.
Goga bai damu da xagin ba ya gayamasa abinda ya gani.
Police ya nanata a xuciyarsa, gabansa ya fadi ya sauka daga saman gadon bayan ya bigi duwawunta😂,
Bindigarsa ya soma dauka yana fitowa har lokacin kida ke tashi, police ya fada da qarfi wanda ya saka kowa tsayawa cak bayan sun kashe sautin.
Nan da nan kowa na soma neman makaminsa yayin da wasu suka soma buya.
Likita ya juya da sauri yabar gurin, goga kasa tafiya yayi jikinsa yayi sanyi ya sami wuri inda baxaa ganshi ba ya buya yana kallon yanda xaa fito dasu kurma.
Jin an kashe sautin gidan kuma kowa sai gudu ake mata da maxa ana buya hankalin jiddah ya dawo jikinta,
Meke faruwa, meyasa suke gudu suna buya kada dai wani abu ne yaxo ya cutar da ita.
Taya xata iya daukar arham ta gudu dashi, waye xai taimaketa ya daukar mata shi ita kuma tayi rarrafe, Sam baxata iya xuwa ko ina ta bar yaron taba koda kuwa gawar sace kawai dan ta tsira da tata rayuwar, duk abinda xai xo ya same shi tafiso harda ita dan ta huta da wannan axaba da take ji a tare da ita, ta qara rungume arham qamqam a jikinta kamar wani xai xo ya kwace mata shi, ta daga kanta sama,
Ya Allah save us, Allah ka kare min yaro na, Allah ka tserar damu daga wahala, sai ga wasu hawaye sharrr na bin fuskarta.
Uwani ce gaba, sai el'mustapha, sai ibrahim da sauran yan sanda kowane da bindiga a hannunsa.
Suna shigowa suka ci karo da jiddah xube a gurin rungume da arham, kafin el'mustapha yayi yunqurin xuwa inda take suka ji harbi from no where har suka sami wani dan sanda ya fadi gurin a mace.
El'mustapha da sauran suka koma baya har uwani Ma cikin tsoro.
Tsakanin su da yan sanda an rasa mai fitowa filin falon, qaton gaske kowa ya koma ya labe yayin da na waje ke ta artabu da masu son tserewa sai sautin bindiga kake ji na tashi.
Ga kurma ga el'mustapha kowane ya kasa fitowa.
Jiddah tun da taga el'mustapha taji kamar anyi mata albishir da gidan aljanna taji ina Ma tana da qafafu da taje gare sa da gudu, ina Ma xata iya tafiya ta bar arham da ta rarrafa ga el'mustapha, sai a lokacin ta lura da boyon boyo ne ake tsakanin el'mustapha da kurma kuma duk cikin su ba wanda ya san juna da matsayin wani illah dai sun tsinci kansu da fargabar haduwar juna.
El'mustapha ya dubi ibrahim, ya karbi bindigarsa ya hada biyu,
Yace be careful ibrahim xan shiga filin ina harbi, wait at my back har ka isa gurin jiddah, ka dauki arham daga jikinta ka fito dashi inaji saboda shine ta kasa tashi ka fahimce ni.
Ibrahim ya gyada kansa cikin gamsuwa,
El'mustapha yace ok get ready, one.... Two.... Three..... El'mustapha ya shiga falon kai tsaye batare da tunanin komai ba ta ko ina sakin bullet yake baya waiwaye wanda ya saka su kasa fitowa su harbesa sun lafe sun yi shiru suna jiran ya bari.
Ibrahim na fita da arham, el'mustapha yaba sauran yan sanda damar su shigo, nan fa sauran abokan kurma suma suka bayyana aka soma dauki ba dadi tsakanin su.
Ba laifi sun kashe yaran kurma da yawa harda mata haka suma an kashe yan sanda uku aciki,
Suna haka bullet din daya bindigar el'mustapha ya qare, ya jefar da ita, haka shima kurma bullet din tasa ya qare amma bai jefar ba,
Uwani na gefe cikin tsoro jikinta sai rawa yake kuma a lokacin ba abinda kurma ke buqata na ganin ya kawar da jiddah da uwani ko an kashe shi buqatar sa ta biya.
Jiddah kuwa matsawa tayi ta takure guri daya banda addua ba abinda take, xuciyarta sai bugawa take, ga mararta dake mata ciwo saboda tashin hankali da ta sami kanta a ciki, ta riqe kasan cikin tana addua sosai.
Idanun kurma na kan el'mustapha bai san meyasa yaji ya tsani mutumin ba sosai ya kashe masa mutane, cikin dabara ya iso bayan el'mustapha batare da tunanin komai ba yasa kan bindiga ya buga masa a kai iya qarfinsa,
Luuuu el'mustapha yayi kamar xai fadi cikin jiri, ya dafe gurin yana juyowa ya saki bullet sai a tsakiyar goshin kurma, nan take ya fadi gurin a mace, sosai hankalin uwani ya tashi.
Jiddah ma hankalinta ya tashi ganin jini na fita kan el'mustapha, da kyar ya kai qasa dafe da kansa yana kallon jiddah itama shi take kallo idanun ta taf da hawaye.
Come to me jiddah, show me how happy you are today, I miss you so much, you are olways in my heart.
Ta girgixa kanta tana hawaye, ta soma rarrafe har ta isa gare sa, meke damun ki jiddah, meya sami qafar ya tambaya bayan ya kai idanunsa akan qafar da ta kumbura,
Sun kashe qafar el'mustapha, I can't walk,
Hankalinsa yayi matuqar tashi yaji xafin ciwon kan nasa ya bar jikinsa ya soma taba qafar yana surutai kamar wanda ya xautu harda hawayen sa.
Uwani na ganin jiddah a jikin el'mustapha ta soma neman abinda xata halakasu dashi, tayi saa ta sami bindiga ta dauka dai dai lokacin da el'mustapha ya juyo yana fadin,
Jiddana baxata rasa qafarta ba uwani na tafiya akan nata, batare da tunanin komai ba ya sakar mata bullet a qafa, ta saki qara mai raxanarwa nan take ta xube gurin a sume.
El'mustapha ya qanqame jiddah a jikinsa yana sumbatar ta, ta ko ina, a rude yake yana neman rasa hayyacinsa, yana kallo aka fito da wasu da yan sanda suka kama a ciki suna fita dasu.
Ya maida hankalin sa gurin jiddah ya soma jijjigata yana kiran sunan ta, dif ba numfashi a tare da ita.
Sai kunji ni bayan sallah.
Happy sallah in advance to ol masoyan El'mustapha.
Kar ku manta da uwani ku cinye nama, a ajiye mata ko a turomin na bata🤤
Pherty luvs You ol.
EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers
Fertymerh Xarah💞
39
El'mustapha daukar ta yayi ya fito da ita, ibrahim na ganin sa ya fito da jiddah ya bude masa motar da sauri,
Goga daga inda yake labe yana hango mutanen da aka kama aka saka masu ankwa, ya baxa ido yaga an fito da kurma shiru, har lokacin da aka fara fitowa da gawarwakin su.
Jikinsa yayi sanyi hankalinsa yayi matuqar tashi ya juya da sauri ya bar gurin.
'Wannan jinin dake fita kanka el'mustapha ya kamata ayi wani abu akai cewar ibrahim yana kallonsa cikin tausayawa.
El'mustapha ya dafe gurin yana tafiya da kyar, jiri nake gani kuxo muje asibiti ni arham ne damuwata a yanxu sai qafar jiddah.
Me ya sami qafar ibrahim ya tambaya yana kallonsa,
Nima ban sani ba amma bata iya tafiya da ita kuma naga ta kumbura shiyasa na harbi uwani a qafa.
Ka harbi uwani? Are you serious, meyasa el'mustapha?
Bai yi magana ba ya soma tafiya dafe da kansa motar da aka kwantar da jiddah ya shiga, ya soma duba qafar cikin mamaki ko me ya sami qafar na ta?
Ya dubi wani sergeant da kyar, ina aka ajiye arham,
Sir yana cikin waccan motar,
Maidoshi wannan motar xamuje asibiti, sai kuje da wadancan mutane ku rufe su kafin naxo.
Da sauri yaje ya dauko arham din lokacin el'mustapha ya kishingida ya kwanta, ibrahim yaxo yaja motar bayan ya saka uwani a wata motar cewa aje da ita asibiti.
Suna isa asibiti, kai tsaye akayi admitting nasu, el'mustapha yaje akayi masa dressing gurin aka rubuta masa drugs.
Ya fito yana xaune sai gasu anty ikram harda su hajiya.
Oh oh ashe kaji ciwo shine baka fada ba da muna waya cewar anti ikram bayan ta xauna kusa da shi tana taba gurin.
Ya yatsina fuska yana kallonta,
Tace ina arham din?
Duk suna emergency har yanxu basu fito ba,
Ta sauke numfashi a hankali tana tsinewa uwani a xuciyarta.
Hajiya ta matso cikin jin kunya da nauyi,
Tace el'mustapha sannu da arxiki Allah ya basu lfy.
Yace amin kansa a sunkuye,
'Abba shiru kawai yayi baice komai ba saboda baqin ciki.
'Anty ikram tace ya kamata kaima kaje gida ka huta el'mustapha, ta dubi drugs din dake hannunsa, kasha maganin ne?
Ya girgixa kansa yana kallonta,
Baxan iya xuwa na barsu batare da naji halin da suke ciki ba, ko naje sister hankalina baxai taba kwanciya ba just leave me.
Aa el'mustapha you have to go, gani xan xauna sannan ga iyayen ta fa, just look at you, uniform din sun lalace da jini kaima kana buqatar kulawa, ta ciro Swan cikin jakarta ta bashi tana kallonsa, kasha drugs din naka tukunna nasan you are careless xaka iya xuwa gida ka ajiye su ne, take it in front of me ingani.
Ba musu ya fara shan maganin kamar yanda Doctor ya gaya masa, suna xaune likitan da ya shiga da arham ya fito, ya gayamasu ya farfado sai dai yana barci yanxu sun samu sun cire bullet din.
Jiddah ce shiru har yanxu, da kyar abba ya samu el'mustapha yaje gida saboda yayi wanka.
Suna gurin ibrahim yaxo ya sanardasu halin da uwani take ciki duk cikin su ba wanda ya kula har ibrahim ya gama magiyar sa ya fice.
El'mustapha kuwa drugs din daya sha harda na barci a ciki, yana xuwa gida wanka kawai yayi ya soma barci,
Banan kuwa tana son jin yanda jikin jiddah yake amma bata sami fuskar tambaya ba.
El'mustapha bai je asibitin ba sai bayan isha'i yana fitowa masallaci can ya nufa direct.
Ya gaida su hajiya yana fadin ya jiddah?
Sai ga hawaye na bin kuncin hajiya,
Tace har yanxu bamu san halin da take ciki ba, likitoci kawai ke shiga suna fitowa tun daxu.
Jikinsa yayi sanyi, hankalinsa ya qara tashi ya dubi anti ikram da kyar yayi magana.
Sister kixo kije gida,
Itama jikinta a sanyaye yake ta tashi tayiwa su hajiya sallama ta fice, el'mustapha na bayanta har gurin motarta, ta riqo hannunsa tana kallonsa.
Insha Allah jiddah xata sami sauqi, she will be on her legs, bana so ka saka damuwa a xuciyarka.
Ya bude mata motar batare da yayi magana ba, ta shiga tana fadin ihsan ta kira daxu baka nan, gobe xata shigo taje kaduna daxu ne, idan jiddah ta farfado let me know please.
Ya rufe motar yana fadin insha Allah, ki shafa min kan affan,
Ta tada motar tana murmushi kawai, yana tsaye gurin har ta fice kafin ya juya cikin asibitin,
Driver yana jiran ku hajiya, kuje gida dare yana yi.
Baxaa yi haka ba cewar abba, idan muka je gida sai a barka kai kadai a asibiti da majinyata har biyu.
Ba komai bane abba, nurses Ma suna kula da patient da kyau anan, damuwar yanxu jiddah bata farfado ba amma ba wani abu bane.
Kai da baka da lfy kaine xaka koma gida el'mustapha, mu kuma xamu tsaya mu kula dasu,
El'mustapha yace aa, idan haka ne abba kai xaka koma gida sai mu tsaya tare da hajiya amma ni baxan iya barin asibitin nan naje na kwanta batare da nasan halin da jiddah take ciki ba, ko naje banda nutsuwa ba barcin xanyi ba.
Da kansa ya raka abba har mota, ya dawo yana amsa call, mutane sai kiran sa ake ana masa barka da ganin matarsa.
Likitoci biyar ne kan jiddah, tunda aka kawo ta suka duba yaron cikin ta baya xaune dai dai wannan dalilin ne ya saka tuntuni suke aikin ganin sun maida yaron dai dai shiyasa basu sanar da yan uwanta ba kada hankalinsu ya tashi.
Cikin nasara kuwa suka yi aikin, sai dai rashin farfadowar jiddah ne abin tambaya?
Suna kan duba qafar jiddah sun kasa gano matsalar illah kumburin da kawai suke gani, duk da ba sun gama binciken ba suna cikin yin sane, Dr. Bakori shine babba a cikinsu, yayi matuqar tausayawa halin da jiddah da abinda ke cikin ta, duk kansu suna buqatar kulawa.
El'mustapha haka ya dawo kamar wanda bashi da lafiya a jiki, ya jingina da bango wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa, rungume da hannayensa a qirji.
Likitoci kam sun tsananta bincike akan qafar jiddah da dalilin rashin farfadowar ta har xuwa wannan lokacin.
Ya koma bakin barandar asibitin cikin tsananin sanyi ya xauna, jikinsa sai rawar d'ari yake amma bai damu ba, babu abinda yake sai addua,
Ya ciro wayarsa daga aljihunsa yayi switching dinta saboda mutanen dake damunsa da kira, baya son damuwa.
El'mustapha wata likita tana neman ka, yaji muryar hajiya a bayansa.
Xumbur ya tashi yana maida glass din sa a aljihunsa, bai saurari hajiyar ba yayi cikin asibiti da sauri tana bayansa.
Itace ta nuna masa likitar Dr Fulani Gafai,
Tace kaine Mahaifin Arham El'mustapha, ya gyada kansa da sauri xuciyarsa na bugawa.
Tace tun daxu yaron ya farfado yana neman maman sa, kaje ka duba sa.
El'mustapha yaja wani numfashi yana jin wani sanyi a xuciyarsa ya juya xuwa dakin da aka kwantar dashi, tare da hajiya suka shiga dakin.
Arham ya juyo yana kallonsa,
Daddy anty uwani tace driver ya rufe ni a mota, taje dani inda mummy shine naji wani abu a hannu so painful,
El'mustapha ya xauna a gadon, ya dora hannunsa a goshin arham kafin ya sumbace sa a goshi,
Kada ka sake maganar uwani, try to forget her..... Arham ya katse sa,
I saw mummy, tears rolling from her eyes, daddy take me to her.
Hannun ka baya ciwo ne el'mustapha ya tambayesa yana kallon hannun.
Akwai ciwo aryan ne yaji min ciwo,
Aa kada kayiwa aryan sharri, yana can yana neman ka a gida.
Daddy yayi kuka?
Yayi kuka sosai yana neman arham, anti banan ta Goya shi.
Daddy nima xata goyani? El'mustapha ya gyada kansa ya juya yana kallon hajiya.
Kayan da anty ikram ta kawo daxu naga harda kayan tea aciki, ko xaa hada masa ne.
Hajiya taje tana duba kayan, el'mustapha ya dora kansa jikin arham, kansa ke masa ciwo sosai.
Daddy kana da nauyi.... Yaji muryar arham, ya dube sa yana murmushi,
Kai kuma gaka raggo, ya tashi daga jikinsa, hajiya da kanta ta bashi tea din, ta juya tana kallon el'mustapha,
Ko a xuba maka abinci ne kaima baka ci komai ba fa,
Aa hajiya bani tea din nasha saboda maganina da nake so nasha yanxu bana iya cin wani abu mai nauyi.
Ta hada masa ta bashi,
Yana gamawa ya tashi xai fice, arham ya kirasa,
Daddy ka kaini inda mummy, I know where she is, inda wasu masu bindiga irin naka.
Kayi barci mummy tana gida, very soon xata xo ta ganka, make sure you takes your drugs from hajiya idan ta baka kuma banda rigima, xata kula da kai kafin nadawo.
Arham yayi shiru yana kallonsa, shikam jiddah yake son gani.
El'mustapha ya dawo yana kallonsa, me kake so na kawo ma yanxu,
Daddy bring Aryan,
Tau shikenan xan kawo maka aryan gobe in kayi alqawari baxakayi wa hajiya fitina ba irin na anti banan.
I promise daddy, kaxo dashi da mummy.
'Yauwa good boy xan xo maka dasu, apart from them me kake so na siyo ma.
Bana son komai hannuna yana ciwo ne,
Xai daina ciwo ne, bari na kira likita ta qara duba ka, ya dubi hajiya.
Kema kina buqatar kici abinci hajiya, arham ne sai kinyi haquri da rigimarsa as usual.
Murmushi kawai tayi, el'mustapha ya juya ya fice.
Ya isa dai dai lokacin da aa fito da jiddah har lokacin bata farfado ba, ICU aka nufa da ita yana daga bayansu.
Yayi shiru yana kallon agogon hannunsa, sha biyu ta gota na dare.
Allah ka farfado da jiddah lafia cewar el'mustapha bayan yaja numfashi yana furxar da iska a bakinsa.
Pherty.... ✍🏻
EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers
Fertymerh Xarah💞
_dis page 4 u bestyna Ummi Aysher_❤
40
'Washe garin ranar da sassafe ibrahim ya shiga asibitin,
Yana xuwa kai tsaye dakin da aka kwantar da uwani ya nufa, ta farfado tana xaune tana shan tea abinta hankalinta a kwance ba wata damuwa a tare da ita.
Shine ya taimaketa amma bata jin xata iya gaidashi illa idanu da ta